BABBAN YARO BOOK 2 COMPLETE NOVEL

18/11/2019
[11/19, 10:01 AM] BintuUmarAbbale: BABBAN YARO
MALLAKAR_ BINTA UMAR
LITTAFIN MALLAKINA NE KUN BIYA KUDIN KARATU NE KAWAI DUK WACCA TASAN ZATA CI MIN AMANA TA FUTAR MIN DA LITTAFINA TO TUN WURI TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA, GASKIYA DAYA CE, HAKA MA AMANA DAYA CE DUK WANDA YACI TA SAI TA CI SHI
56
Cike da mamaki yake kallon Asma’u wacce tayi tsili-tsili da ita tasan tabbas yaji maganar da take fadawa Mimi ga yanayin kallon da yake mata.
K’araso wa yayi dakin sosai hannun shi rike da wata Leda har ya zauna gefan Mimi idanunsa na kàn Asma’u yana tuhumar ta da idonsa, sunkuyar da kaina nayi kamar wacce tayi wa sarki k’arya.
Gyada kansa yayi hade da rungumo k’afafun Mimi yana kallona yace.” Manene hujjar ki, na bata wannan gurguwar shawarar.?
Kunya ta hanani in d’ago kaina na kalleshi.
Dariya naji yanayi kasa kasa yace.” Saboda mugunta kike zugata ta bujere min a shimfid’a kina mata bakin ciki tafi ki ta ko wane fanni, ga lada ga dad’i zata kwanta a kirjin mijinta shi kike wa bakin ciki ai na gane yanzu.”
Kaina na dago in kallonsa yanda ya wani matse Mimi a jikinsa yayi mugun bani haushi a zuciya ta nace “Wannan guy wai wane irin tantiri ne?
Ba tare da nace komai ba na mike tsaye hade da gyara hijab dina INA kallon Mimi dake lumshe ido a ka fad’ar sa, nace” Ni Zan tafi idan kin dauki shawara ta kan ki kika yiwa Allah ya bamu alkairi.”
Kofa na nufa da sauri.!
Mimi ta yunk’ura da sauri ta mike ta biyo bayana cikin dingisa k’afafu shima bayan ta ya biyo lokacin har na Isa parlor Tarar gabana tayi hade da marairaice fuska tace “Don girman Allah kar ki tafi yanzu ki bari sai gobe.”
Kallon baki da hankali nayi mata wai in Bari sai gobe lallai Mimi, ni idan nabar gidanan nayi rantsuwar babu Wanda zai sanya ni na kara dawowa cikin shi, kokarin bude kofa nake in futa yazo ya bake kofar Yana min wani kallo kasa-kasa yace.” Malama Madam tace ki bari sai anjima kya tafi kin ji, yanzu ki shiga kicin kiyi mana girki ni da ita.”
Hararsa nayi a lokacin sai ya bani dariya saboda nasan duk abunda yake yi domin ya bani haushi pretending yake ina kallon wani Abu boyayye a k’wayar idonsa.
Nace”Wallahi da Kai da Mimi babu Wanda zan yiwa girki Kaji na fada maka ma.”
Babu yabo babu fallasa yace.” Wato kinanan da Wannan gantsarar taki ko? Na hanani sanya Wannan bakin hijab din kinki ji ke gaki da baki kamar shuni.”!!
Naji haushin ba’ar da yayi min sosai na kalleshi fuskata a daure nace”,Bani hanya na wuce.” Ki yayi ya tsira min ido, Mimi ta k’araso gurin jikinta a sanyaye tace.”My heart ka k’yaleta ta tafi tunda baza ta zauna ba.”
Kallonta yayi yace.” Ok tunda kince a k’yaleta ta tafi kar ki k’ara kiramin sunan ta, idan anjima, dama don kin damu a dauko ta ne.”
Hannunsa ta rike tana murmushi,
Matsawa yayi daga jikin kofar na bude na futa ko kallonsu ban yi ba.
Harabar gidan na tsaya INA waige-waige karaf ! Muka hada ido da Mujahid ya futo daga part din shi, jikinshi sanye da kayan kwallo shi da wani boy da bool a hannunsa suna bugawa a filin gurin.
Saurin dauke kaina nayi na fara tafiya
Da sauri Mujahid ya mik’ewa yaron shi, boll din ya Isa gurin ta fuskar sa dauke da kayattacan murmushi.
“Asma’u” sanyayyar murya shi naji yana ambatar sunana, tsayuwa nayi hade da sakin fuskata nace”Na’am kana lafiya.”? Ya saki murmushi tare da fad’in”Lafiya Lou nake sai dai tunanin ki ya hanani Sakat! Jiya da kyar nayi bacci wallahi.” Dariya na danyi nace”Ka fiye ban dariya har da rantsuwar ka.”
“Am serious wallahi babu karya a magana ta jiya da kyar nayi bacci Allah ya Dora min so da kaunar ki kamar raina.” Shiru nayi ina kallonshi fuskata a sake, yace.” Kin lek’a amare har zaki tafi.” Nace” Wallahi kuwa.” Agogon hannunsa ya kalla tare da fadin”Gaskiya ana rana bari in futo da mota in kai har gida.”
Nace”Aikuwa da ka kyauta.” Juya wa yayi da sauri ya nufi part dinshi, kallo na bishi dashi ina murmushi guy yana da kyau da sanyin hali ga nutsuwa.
Mintuna uku naga motar shi na futowa daga nashi gurin, saurin dauke kaina nayi ganin shine yake driving din.
Kusa dani ya tsaya yana yi min Hon!
Banza nayi dashi ina kallon part din Mujahid aikuwa sai gashi ya futo cikin motar shi, ya k’araso gurimu tare da futowa.
Fuskar sa a sake ya mik’awa Amjadu Hannu tare da fad’in “Ango! Ango.”!! Dariya suka yi a tare Amjadu ya Sosa kanshi As’usuel yace.” Wato dama wayo kuka yi min Ashe haka ake Jin dad’i shine kuka b’oye min.”
Mujahid ya bashi hannu suka tafa, tare suna kyalkyala dariyar shakiyan ci, Mujahid yace.”Baka da wasa fa wato har an wuce gurin kenan. “
Amjadu yace.” Tuntuni Alhaji yanzo sai jiran sakamako.”
Dariya suka kece da ita a karo na uku suna tafawa.
Ji nayi tsayuwar gurin ta ishe ni, domin gani nake yi duk abunda yake yi kamar da hujja yake yi, motar Mujahid na fufa jikina duk babu k’wari ,wai ni guy nan yakewa wannan tozarci, wallahi babu abunda zai kara kawo ni gidansa
Bude motar nayi na shiga na zauna abuna.
Amjadu yana kallonta a take ya gimtse fuskar sa daga dariyar da yake yi, kafin ya Ankara Mujahid ya saki hannunsa tare da fadin”Bari i n kai wife dina gida insha Allah.”
Fuska ya had’e sosai yana kallon bayan Mujahid da yayi gaba, har ya bude motar sa ya shiga idonsa na kansa yana mamaki yaushe suka shaku shi da Asme yasan halin yarinyar da girman kan tsiya.
Duk yanayin da ya shiga ina kallon shi, tunda motar Mujahid tana gefan tashi, naji dadin ganin yanda ya shiga halin damuwa
Kawai sai na shiga dariya babu gaira babu dalili, shima Muhajid din dariya yake yana kallona cike da so ya kunna motar shi muka wuce motar Amjad din da sauri.
Gumi ne yake tsiyaya a jikinshi wato wulakanci. Da yarinyar nan zata yi mishi kenan, da kanshi ya futo domin ya kaita gida, Dalili ya aiki su Rambo shine zatayi masa wannan cin mutumcin ya lura fa Mujahid da gaske yake ganin yanda yake zak’ewa akan yarinyar bude motar yayi a fusace! Ya nufi part dinshi yana wani taka k’asa da k’arfi sai huci yake yana jin wani irin kishin ta a zuciyar sa.
Hira sosai muke da Mujahid sai yanzu na kare mishi kallo kyakyawa ne sosai yana da d’an kiba amma ba sosai ba fari ne amma ba kai Amjadu ba, fuskar sa kullum a sake, take naji ya kwanta min domin duk cikin samari na babu Wanda na tab’a sakarwa fuska kamar shi, a yanda yake fada min shi da gaske yake aurena zai yi kuma, baya so aja wani dogon lokaci, to nima gaskiya ya kwanta min a rai naji zuciya ta ya kwanta min shiyasa na bashi numbar wayata da zamu rabu, tare da yi min alk’awarin zai kirani da daddare mu sha shira nace masa ina sauraren sa.
Ko da na koma gida a lokacin aunt Hauwa ta tafi gidan sai Umma kadai tana gyare-gyaren abunda ba’a rasa ba, tana kallona cike da mamaki take fadin “,Har kin dawo kenan.”? Nace” Eh Umma zaman me zanyi”
“Lafiya dai ko.”? Umma ta fada tana kokarin futa daga dakin, ta San dai ta tsuniyar gizo bata wuce ta koki.
Shiru nayi mata domin ina jin nauyin fada mata dalilin kiran Mimi di.
Rayuwa kenan yau kwanan Mimi biyar a dakin mijinta, inda Umma kullum ya zauna zancan Mimi take yi, duk da cewar kullum sai sunyi waya da ita, wani lokacin ta bani wayar mu gaisa ta k’araci korafin ta ta gama , sai dai in ce mata kawai tayi hakuri zan zo. Wani lokacin kuma idan ta kira wayar kin karba nake yi ko in tashi in bar gurin.