BABBAN YARO BOOK 2 COMPLETE NOVEL

Zazzafar ajiyar zuciya ya sauke yace.” Ya jikin Momyna. ” ? Dr jahid yace.” Alhmdullahi jikinta da sauki hakama babynta insha Allahu zata samu kulawa ka kwantar fa hankalin ka.”
Hamdala yayi a fili yana godewa Allah yace.” Muje in ganta OK.” Ganin yanda ya daga hankalin sa yasa Jahid din kasa yi masa musu, domin babu halin yace. Masa ba’a futo da ita ba tukkuna, dole ya jagoran CE shi har dakin da Mimi take kwance.
22/11/2019
[11/23, 10:28 AM] BintuUmarAbbale: BABBAN YARO
MALLAKAR_ BINTA UMAR
LITTAFIN MALLAKINA NE KUN BIYA KUDIN KARATU NE KAWAI DUK WACCA TASAN ZATA CI MIN AMANA TA FUTAR MIN DA LITTAFINA TO TUN WURI TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA, GASKIYA DAYA CE, HAKA MA AMANA DAYA CE DUK WANDA YACI TA SAI TA CI SHI
60
Lokacin da zasu shiga dakin da Mimi take ji nayi kamar in biso domin na k’agara na ganta, Ashe bani kad’ai ba har su Umma, nauyi ya hanata magana granny tace”Muma zamu iya shiga gurin ta ne.”? Mujahid yace.” A’a granny Ku bari a futo da ita shima Dan dai mijinta ne, kuma in na hanashi zai iya shak’eni ga yadda yake muzurai.”!
Dariya suka yi ni kam yak’e kurrum nake yi nasan da babu shi tsaf! Mujahid zai shiga dani gurin Mimi.
Kusan Mintuna ashir yayi a ciki sannan ya futo domin shi Mujahid din tunda ya raka shi ya futo ya koma bakin aiki. Kallonsa muka yi dukaninmu,
Tsayuwar sa ya gyara kusa da kakarshi ya futo da wani farin hankici daga aljihun sa, yana goge fuskar sa.
Granny tace”Ya jikin nata ta farko amma.”?
Girgiza kansa yayi kamar ba yaso yace.” Bata farko ba amma dai Jahid yace.” Zuwa magariba zata farko insha Allah.”
Hamdala tayi tana kallon mu cike da farin ciki tace”Kunji abunda Mujahid yace ko. ? Muna sauraren ikon Allah.”
Umma tace”Shine abun dubawa kuma shine abun godiya.” Shiru ne ya ratsa gurin na minti biyu kana yace.” Zan wuce ina sa meeting da ma’aikatana bayan sallahr isha’i.” Umma tace”Ubangji Allah yayi maja jagora mun gode kwarai.”
Da “Ameen yake amsawa ya futa daga reception din cikin tafiyar shi ta zaratan maza. Yanzu ya samu kwamciyar hankali kuma jakinsa na bashi cewar akwai nasara kan aikin da a kaiwa Mimi fatan shi ta farfado lafiya domin yanzu a zuciyarsa yaji yana yi mata wani sahihin so na gaskiya ga wani mugun tausayin ta da yake ji mussaman idan ya tuno rayuwar ta, ubanta ya gudu ta taso bata San mahaifiyar ta ba, shiyasa kullum yake jinjinawa Ummansu Asma’u uwace ita me baiwa D’a mama a yanda ya fuskanta yanda ta rike Mimi tamkar ita ta haifeta tana kula da ita sosai kular da bata yiwa ‘yar cikin ta Asma’u.
Aikuwa kamar yanda Dr ya fada bayan sallahr magariba Mimi ta farko kuma sa sunana a bakin ta, take Jahidi ya zo ya kira ni.
Ina shiga dakin muka hada ido da ita. Idanunta duk sun kode sunyi ja sosai.
Kallona take yi har na karasa kusa da ita gefan bed din na zauna hade da kamo hannunta na rike tamau.
Nace”Mimi ya jikin naki.”?
A hankali tace”Da sauki Habibty kice wa Jahid ya bani ruwa nasha yak’i ya bani. “
Mujahid na kalla cikin tuhuma yace.” Ba yanzu za’a bata ruwa ba.”
Hannuna ta rike lebanta duk ya bushe, Mimi tayi mutukar bani tausayi. Nan na zauna ina rarrashin ta, su Umma suka shigo dakin. Tunda ta ganta hankalin ta ya kwanta.
Granny kuwa fad’i take”Sannu kinji ko kishiya ta ko wace haihuwa da irin ta sai dai fatan Allah yasa Ku gama lafiya.”
Dr Jahid futa yayi daga dakin ya barmu da Mimi. Hannuna na nata bacci ya kara dauke ta.
Kin tashi nayi daga gurin bare in cire hannuna daga nata har wajan k’arfe goma na dare, Amjadu ya shigo lokacin granny har ta soma gyangyadi.
Sallamar sa naji dakin gabana ya fad’i , ciki-ciki na amsa masa, domin Lokacin Umma na toilet aunt Hauwa kuma ta tafi, muryar baban su Munnu na ji sun shigo tare.
Amsawa nayi da sauri na juya INA masa barka da zuwa.
Kan Mimi ya tsaya cike da tausayi da al’ajabi yake fadin”Ashe Abunda ya faru dake kenan Mimi.”
Umma dake futowa daga band’aki tace”Sannu da Zuwa.”
Baban su Munnu ya juya suna gaisawa da Umma.
Nan yake jajan ta mata abunda ya faru yana kara addu’a ga Mimi tare da fadin”Sam shi bashi da labarin abunda yake faruwa in banda shi Amjad din ya fada masa a waya.
Umma tace”Alkairi shi ake fada bata tashin hankali ba, duk da dai nasan hakkin Ku ne a fada muku munyi laifi.”
Baban su Munnu yace.” Ya wuce yanzu babu Lokacin yin k’orafi ta lafiyar ta Muke ubamgji Allah ya bata lafiya .”
Duk wannan abun da ake gogon yana tsaye kusa da kan Mimi ya rutsawa fuskar ta kallo kamar wani maye gani a zaune bayan haka kuma ko kunyar su Umma baya ji.
Sallama Baban su Munnu yayi mana ya kama hanya ya futa Amjad din ya bishi a baya Umma kuwa zama tayi kan wata kujera tana fadin”Ni na manta shaf ban sanya kin kira Munnu a waya kin fada mata halin da ake ciki ba, in yaso ita sai ta fadawa Baban nasu.”
Nace”Wallahi nima na manta shafa.”!
Granny ce ta bude ido da sauri tana kallanmu ni da Umma tace”Kaddai bacci nayi a gurin nan.”? Umma tayi murmushi tare da fadin”Bacci kika yi amma bai yi tsayi ba.” Mayafin ta ta gyara tana fadin”Haba shiyasa kamar a mafar ki naji muryar k’ato ya shigo ko.”
Nida Umma ka kalli juna wanene k’ato kuma.”? Kafin muga tunani mu ya shigo dakin hannunsa rike da wasu manya manyan ledoji.
Kusa da Umma ya aje ledojin cikin nutsuwa yace.” Umma zamu tafi gida. Ga abun bukata nan insha Allahu babu matsala.”
Umma tace”Godiya muke Ubangiji Allah yayi albarka a rayuwa. “
Granny mik’ewa tayi tana wa Umma sallama, shikam tuni ya futa ko kallon inda nake zaune bai yi ba, Kai sai ince tun d’azu da safe da muka hada ido dashi ban kara ganin ya kalleni ba ko da wasa
Shige da fucen sa kawai yake.
Naji dadin Wannan sauyin da aka samu ta b’angaran shi.
Ya daina samun ido zan sake sosai dama idanunsa mugun dafi ne a tattare dani.
Alhmdullahi Mimi kullum samun sauki take yi yau kwannmu goma a sibiti kuma Alhmdullahi jikinta yayi sauki sosai tunda tana cin abunci Mara nauyi kuma tana zuwa ko INA, kwakwaran motsine dai Dr ya hanata
Amjadu kuwa kullum sai yazo shi da granny tare da kayan ciye-ciye hummm mu dake muke jinya maimakon muyi rama muka yi kiba ta sati biyu sosai na ware ganin baya shiga harkata ko yazo gaisuwace take hadani dashi, to shima tunda yaga jikin Mimi yayi sauki baya wani dadewa yake tafiya sabgoginsa, Kullum ina cikin Ac fatata tayi luwai gashi kullum muna tare da Mujahid muna shan soyayarmu ko Amjadu yazo ya tadda mu baya nuna damuwar komai karkari su gaisa ya wuce ciki.ko a fuska baya nuna Alamun wani Abu wai don ya fanni tare da jahid ni ni kaina yanzu tunani sauayrwa shi nace tafarar daya duk wannan rawar kan da yake akaina ya daina yi, ta lafiyar matar shi yake.
To nima hakan yayi mun dad’i yanzu zuciyata ta Riga ta tsayar min da Mujahid a matsayin miji maganar mu har gaban su Kawu Yunusa domun da suka zo duba Mimi sun gaisa da Mujahid din a matsayin sa na me Neman aure na.
Kwanan Mimi goma sha takwas ta warware sosai ni kuma dama tuni na koma gida saboda makaranta, take Mujahid ya sanya ranar sallamar Mimi tare da tsauraran matakai babu yawan motsa jiki da cin abun mai nauyi babu kar zurga zurga tayi yawa, shima Amjad din banda tsawwala gurin yin sex wannan sune sharadan da Dr ya shimfid’a wa Mimi.