Yagana tana samun aiki a private school ta primary ya dage yayo wahalarsa yasamu ya saka Inaya duk da kusan shekarunta sunyi qanqanci Amma haka ya sakata sbd a gida yagana ta dena zama aikin take zuwa
Shima gashi yanzu ya sake dagewa da ayyukan wahala iri iri da yawon Neman aiki
Dan haka kullum yake kaita makarantar idan yadawo da wuri ya biya ya daukota Idan baidawoba anan take zama tareda yagana har sai antada Yan primary kowa ya tafi sai sudawo gida ta zauna gurin yagana harya dawo,
Yana dawowa yake tsayawa gurin yagana ya dauketa su shige Bata qara fitowa dakinsu sai washe gari Idan zaije sallah wani lokacin yakan kaita gurin yagana yaje yadawo
Wani lokacin Kuma rufeta yake a dakin yaje yadawo sbd itama Kaman tayi gadon mahaifin nata miskilace ta gaske batason zuwa koina tafison ta zauna gurin Abbin nata.
Musamman sun saba rayuwarsu daga ita sai shi.
Wani tsautsayi daya samesu shine dakinsu daya fara zubar ruwa ta sama Idan ana ruwa yasa tunda damunar ta tsayu sosai yadaina baccin dare,
Zaune yake kwana yayi gadin Inayah tayi bacci sbd gudin yanayi na tsautsayi ko zai riskesu,
Da safe kafin su fita zai kwashe ruwan daya taru a dakin ya goge musu ya gyare dakin dako ledar qasa babu sai Rabin dakin ne kawai keda Leda Shima gurin katifar Inayah sbd kada sanyi ya kamata.
Sauyin aiki akai masa daga security na asibiti zuwa na wani super market.
Ranar farko daya fara aiki a super market din yahadu da wani class mate dinsa a gurin.
Da farko Nuradden ya bayyanarda mamakinsa sosai ganin A MAJEED a matsayin security sbd sanin tsananin ilimi da kyakkawar takardun da MAJEED din yake dasu Dan haka Bai wani boyeba ya bayyanarda mamakinsa tareda yimasa tayin wani aikin wanda yafi Wannan.
Da farko MAJEED yaso kaucewa tayin Amma Nuradden din ya dage tareda tabbar masa ba daga garesa bane taimakon dagaske maikatan ake nema.
Amincewa yayi washe gari ya Isa makekiyar maaikatar kasuwancin mahaifin Nuradden din cikin saa yasamu aikin cashier na daya daga cikin manyan malls dinsu sbd sunason fara jarabta aikinsa kafin su basa wani aikin daya kamata shima sbd Nuradden yayita zuzuta musu ilimi da MAJEED din yakedashi
Dan hkaa ahankali cikin yardar Allah yafara aikinsa na cashier a gurin.
Tunda yasamu aikin cashier a taqon mall din rayuwar tafara yi masa sauki shida yarsa harma da yagana da mijin yaganar sbd shi din mutum ne Mai alkhairi musamman ga mutanenda suke tsananin kaunar Inayah,
Duk Mai kaunar Inayah to tabbas matsayinsa a cikin ransa Mai girma ne,
Yanda yake tsananin kaunar ‘yarsa Jin yake komai zai iyayiwa duk namijin daya aurawa ita duk ranarda ya cutatar masa da ita,
Wasu lokutan har fargabar yanda zai fara fuskantar bayar da ita aure zuwa wani gurin yake Dan haka alqawarine Mai girma acikin ransa na zai wadatar da ita da ilimin Mai zurfi sbd rayuwa a gidan wani tayi Mata sauki.
Majeed sam Bai damu da abun hannunsaba duk lokacinda yasamu ‘yan kudade baya qyashi haka zai kashewa Inaya sauran Kuma ya bawa su yaganah Suma tunda ba laifi suna cikin yanayin rayuwa suma,
Basu taba haihuwaba itada mijinta wanda yake zaune baya iya fita nema sbd yanayin Rashin lafiya dayake ciki na sugar gashi anyanke duka qafafun nasa biyu duk sbd lalurar a keke yake rayuwa,
Dan haka shigowar Inaya da Abbin nata rayuwarsu ba qaramin taimakawa rayuwarsu yakeyiba
Hakannema yasa duk yanda ake gulmar da zindensa babu ruwansu basa shiga sbd sukam majeed kusan shine rufin asirinsu yanzu
Suma qarshe aka ringa binsu da zagin makwadaita Dan sungansa kalar ‘yayan masu arziki dama Kuma a wani bangaren da yawansu suna masa kallon Wanda yafito daga zuriar masu hannu da shuni Kuma duk iya gulma da bin diddiqi ankasa sanin asalinsa dakuma inda yafito.
***Ahankali Lokaci yaja sosai har INAYA ta kammala nursery tashiga primary hartayi nisa tana primary 4.
Har lokacin a mall yake aiki saidai ba laifi yasamu qarin girma sosai harya zama assistant manager,
Alhmdlh komai Yana tafiyar musu a daidai dan kuwa babu kalar Jin dadin da Inayah Bata samu gurin mahaifinta sai Wanda baa rasaba daidai gwargwadonsa.
Yanason tashi yabar gidan ya kama haya wani gurin sbd ‘yarsa datake girma gashi gidan gidan tarone mutane iri daban daban
amma Kuma sbd rayuwar kadaici da zata iya wargaza Mata walwalarta data fara samu sakamon girma data fara shiyasa Bai tashiba gidan har lokacin Amma zuwa lokacin yanada halin sauyawa din tunda sunfara samun rufin asiri.
Inaya na gaf da kammala primary 4 yasamu hayar wani gidan acan hanyar gurin aikin nasa Dan haka yafara musu shirye shiryen tashi duk da ba wani kayan suke dashiba bayan katifar baccin Inayah sabuwa Mai dakan mutum daya,
Sai qaton bargon dayake shimfidawa qasa ya kwanta sai jakar kayansu da ‘yan abubuwan amfanin cin abinci.
yasamu su yagana da maganar tashin nasa dakuma tayin dayakeda niyar yimusu ko Allah zaisa su amince.
A zaune ya samu malam Aminu Mijin yaganar a kofar dakinsu kan tabarma Yana Dan sauraron radio dayake dare yayi Dan har qarfe tara takusa bugawa.
Inayah batai bacciba sbd assignment datake dashi dazai koya Mata Kaman yanda yasaba yimata tishin karatunta na bokon Dana addini kowanne dare kafin tayi bacci Dan haka tareda ita yaqaraso shimfidar malam Aminun Yana riqeda hannunta jikinta sanyeda doguwar rigar bacci Mai kauri da har qasa sai qaramar hular sanyi akanta,
Hatta qafafunta suna sanye cikin safa Mara nauyi sbd Sam baya Wasa da duk abinda zai taba masa lafiyarta shiyasa ko Yaya yaji Alamar sanyi to baya Wasa ko bacci zatai saida socks.
A natse Kaman yanda yake koda yaushe ya zauna gefen tabarmar Yana bude Baki cikin kamilalliyar muryarsa Mai nutsuwa yace”
Barka da dare Malam,
Yaya lafiyar jikin?
Allah yaqaro afuwa da nisan kwana.
Sosai cikin kulawa malam din ya amsa Yana kallon Inayah data zauna gefen mahaifin nata yace”
Inayah yau bakiyi bacci da wuriba Kika biyo Abbin naki cikin sanyin Nan.
Ahankali ta kallesa tana sake Dan guntun murmushinta da qaramar muryarta tace”
Ina wuni malam?
Sake Yar dariyar kulawa da shaawar nutsuwarta data abbinta yayi Yana amsawa kafin yace”
Ki shiga ciki gurin ummen taki yagana tana sallah ne.
Sake riqe hannun abbinta tayi tana sauke Kai Dan
Saida Abbin ya Dan kalleta da fararen idanuwansa yayi Mata alamar taje din tukuna ta miqe ta nufi kofar dakin da sallamarta a Baki ta shige.
Cikin nutsuwa yayiwa malam din tayin zama dasu a sabon gidan hayar daya kama Mai daukeda dakuna uku zuwa.,
Baya boye boye shi mutum ne Mai magana kai tsaye Dan haka Kai tsaye ya sanarwa da malam din sbd yanda Inayah tayi sabo fa yagana dakuma yanda INAYArsa zata cigaba da walwalarta cikin mutane Idan taga Basu kadaineba a gidan.
Da farko malam shiru yayi Yana nazarin al’amarin
sbd Kai tsaye suje su qarawa Abdulmajeed din nauyi Kaman Bai kamata ba tunda Shima yanzunema ya ‘dan damu walwala ta abin yi.
Amma Kuma ata wani fannin kaman yanda Abdulmajeed din yafada rayuwar Inayah kam Idan babu mutane zata iya rasa walwalarta Duk da idan tana ganin Mahaifinta Bata buqatan kowa Amma ai shi mutum rahama ne,
Kuma itama yaganarsa Yana so tasamu mutanenda koba ransa zasu dauka amanartaba tunda Suma ba kowane dasuba Kaman su Abdulmajeed din.