Gyada Kai tayi ahankali tana cewa”
Abbi…
Kallon yagana yayi yana ciro 500 ya miqa Mata tareda jakar inayar Yana cewa”
Ku shige zan koma daga Nan.
Juyawa sukai yaganar tayi ciki da ita tana Mata wasa.
200 yaciro ya miqawa Jamilu Mai gadin Shima kafin ya juya ya wuce yanajin yanda yake jero godiya Yana adduar Allah ya Raya musu Inaya.
MAMUH
ZAFAFABIYAR
AYSHATOUH INAYA
A MAJEED
LOVE/ROMANCE
[10/13, 11:57 AM] +234 703 121 9749: Mamuhgee 6
Arewabooks@Mamuhgee
Yagana aiki takeyi a qaramar private school din dake kusa da anguwar tasu amatsayin nanny Mai kula da yara Amma gidansu na haya ‘daya da ABDULMAJEED din da yarsa Inayah,
Tun ‘yarsa na jaririya shi kadai ke dawainiya da lalurar kulawa da ita sai yaganar wadda Rana daya suka tare gidan hayar itama tazo tareda mijinta da kusan yake kwance ba lafiyayyeba,
Da farko sbd babu yanda zaiyi ne yasa ya amince yaganar datai masa tayin taimaka masa da rainon ‘yar tasa da Kai tsaye ya sanar Mata da ya rabu da mahaifiyarta.
Yagana itace tayi rainon Inaya hartai wayo ta girma tasan Mahaifinta har takewa yaganar qyuya akansa shiyasa daga baya Takoma gurin Mahaifinta gabaki daya saidai idan zai fita takaita gurin yaganar Amma daya dawo yake zuwa ya taho da ita
Da haka harsuka koma rayuwarsu su kadai,
a dakinsa yake Mata wanka cikin qatuwar robar wankanta daya siyo
Zata tsaya aciki kokuma ta zauna aciki yayi Mata wankanta tas ya shiryata.
Rayuwarsa da ‘yarsa wata irin rayuwace dasuke abarsu su kadai dagashi sai ita sai yagana data Dan shigo ciki,
Duk duniyarsa babu wani buri ko abinda yake gabansa bayan ‘yarsa INAYA dayake iyayin komai dabai sabawa shariah ba Dan inganta rayuwarta da Bata wadatacciyar tarbiya da nutsuwar rayuwa,
Bayan INAYA babu wani Abu dayake so da kauna a duniyarsa,
Ita kadaice abinda yakeda,
Ita kadaice Nutsuwarsa da abinda yake kalla yaji qwarin gwiwar cigaba da yaqi da gwagwarmaya Dan inganta rayuwarsu musamman ganin yanda takeda tsananin qawa zucinsa kasancewarsa Mahaifinta Kuma mahaifiyarta.
Kafin tayi wayon datake dashi yanzu yasha wata irin gwagwarmayar wahalalliyar rayuwa Dan samarda abinda zai rainar masa ita.,
Karatun jamia yake alokacin hakama bayada aikin komai face kalolin aikin wahalar daya ringa yi Yana samarda abubuwan da kowane baby zai buqata.
Cikin wani irin tsananin hali yasamu ya kammala karatunsa yayi service yafara zuwa yan ayyukan da zasu ringa taimaka masa Dan lalurarsa data ‘yarsa.
Sana’ar gadin wani gida yafarayi tsawon watanni kafin Mai gidan yabar qasar Dole ya nema wata aikin.
Daqyar yakuma samun aikin security a wata private hospital.
Da Wannan aikin yake rayuwa kafin raga baya yasamu aikin wankin mota yana hadawa dashi.
Shekarar inaya uku yafara tunanin aure badan Jin dadinsaba ko Dan yanajin buqatar hakan
Kawai dai zaiyi auren ne Dan ya samarwa ‘yarsa kwanciyar hankalin samun mutum ataredasu ko zata sake tayi rayuwa Kamar kowanne yaro,
Amma badan wai ya Samar Mata uwaba,
Har abada shine uba Kuma uwar INAYArsa,
Har abada babu mace data Isa ta zamto uwa ga INAYA,
Shine uwa Kuma uba
Ita kanta Inayah duk da qarancin shekarunta tariga ta Dan San halayen Mahaifinta Dan haka ta daina ambatar sunan mahaifiya tuni sbd Hani da yayi mata da hakan aduk lokacinda bakinta ya furta Mama.
Alokacinda yayi neman auren farko ga ‘yar Mai Basu sallah a masallacin anguwar da farko lafiya kalau yafara zuwa fira bawai danma yasan Mai zaiyita fadaba sbd shi miskilin mutum ne shiyasa Bai cika shiga mutaneba,
Iyakacinsa da ‘yan anguwar da mutanen gidan hayarsu gaisuwa
Itama gaisuwar sbd sanin mahimmancinta a addini ne.
Da yawa mutanen anguwar da mutanen gidansu na haya kallon me girman Kai da Rashin mutunta mutane suke masa saidai Kuma basa iya fada gaban idanuwansa sbd kwarjinsa da kamewar mutuncin kansa duk da kasancewarsa qaramin matashi.
ABDULMAJEED ABBI kamar yanda yarsa ke kiransa kusan hakan kowa ya sansa,
Wani irin baudadden mutum ne da babu Wanda yake iya gane inda ya dosa,
Meye ne acikin ransa?,
Meye abinda yake tunani?,
Waye shi?
Sam babu Wanda yace yataba ganin koda murmushinsa bare dariyarsa sbd
Bayan ‘yarsa babu Wanda ya taba yiwa koda murmushin bare dariyar
Dan haka kusan kowa baya masa dogon shishigi
ciki kuwa harda yan saka idon anguwa da munafukan anguwa kowa ya kama kansa dashi
Zagi dai ne Idan anzauna dattijawan anguwa da Basu San su kama girmansuba sai sunyi saka idon kullum cikin zaginsa sukeyi sunayi dashi a fakaice
Idan yawuce ta gabansu yayi musu sallama ya gaishesu haka zasu ringa washe Baki suna amsawa suna yabonsa da yabon ‘yarsa
Daya wuce zasu fara zundensa.
Aurensa da Hafsat yar liman ya lalace ne bayanda aka zuga mahaifin nata da cewar ana zargin zafin zuciyarsa da baqar zuciya kamar kuturu ya ringa azabtarda matarsa da duka da yunwa da wahala da baqin talauci ta gudu ta barsa da jinjirar ‘ya bayan ta haihu,
Wasu Kuma suka ringa fadar bada aure ya Haifa yarsaba Dan haka hafsatu renon ‘yar gaba da fatiha kawai zata tayi.
Wannan zugar ta lalata maganar aurensa da Hafsat wadda take tsananin sonsa Kuma shi kansa har cikin ransa ya yaba da nutsuwarta yayi shaawar auranta ta zauna da Inayah.
Bayan an hana masa auren hafsa bai cire raiba sbd yanzu sosai yakeda shaawar samarwa Inayah Mai zama da ita Dan haka tunanin yin auren yashigesa sosai bawai Dan har lokacin tunaninsa ya sauya akan Mata bane dakuma Wai Jin Yana son aure ko mace ba,
Sam Mata bayada shaawarsu ko kadan,
Baya Kuma Jin tunaninsa da tsananin yanayinsu zai sauya a zuciyarsa har abada.
Fatima yakuma nema aure a bayan layinsu
bayan ya Dan kwana biyu Yana zuwa fira gunta daganan ya aika Mijin Yagana da Daman shine kawai yake tsananin ganin girmansa da mutuncinsa ya nema masa aurenta.
Kamar yanda tafaru farko hakance takuma faruwa
Har anbasa auren daga baya aka fasa sbd wasu maganganun da aka Kuma kaiwa mahaifanta itama.
Cikin qanqanin lokaci Saida ya nema aure so hudu ana hanasa daga Nan Mata suka Kuma ficewa a Ransa kwata kwata
Musamman sbd yanda aka dauki hanyar aibata masa ‘ya sai hakan yakuma tsananta qamewar zuciyarsa akan Mata da mutane,
Bai Kuma shaawar neman kowace macen ba,
Yacire maganar aure daga ransa kwata kwata har abada bayajin zai Kuma kallon kowace mace da sunan wani abu face sunansu na mace.
Daga Wannan lokacin burinsa ya sauyu ya karkata ga ilmantar da ‘yarsa yakuma dage ba dare ba Rana da Neman aiki da mafita dama Kuma karatu dayakeson qarawa sbd babban burinsane Dana mahaifinsa tun Yana raye.
Aikin wahalarsa dayakeyi ya matuqar tsananta Dan kuwa bayan security na asibiti da aikin wankin mota yanzu harda sana’ar ‘dan acaba yanayi Idan yasamu abokin aikinsa na gurin aikin security ya basa Aron mashin dinsa yayi.
Rayuwa Mai tsanani da wahalar gaske yake gudanarwa,
Baya samun cin abincin dazai kosar da cikinsa,
Duk Rana da dukan ruwan dayake Sha na fafatawar ayyukan wahalar dayake duk na inganta rayuwar Inayah ne,
Ita yake siyawa Yar sitirar sakawa sbd ko sitirar arziki basudashi,
Abincinta da Shanta sune yake iya kokarin samarwa,
So da dama haka yake wuni da yunwa saidai yasha ruwa da Dan biredi haka ya kwanta amma Inayah baya taba Bari ta nema abinci ko abin buqata ta rasa.
Ahaka yake gudanar da rayuwarsa acikin wani irin tsananin hali.