Dakyar ta qarasa da maman kofar dakinta tana kokarin kwantarwa kan shimfidar datai Mata a wajen
Maman ta Dan janye tana waiwayowa ta kalli hadiza da har lokacin take tsaye a inda take cikin mutuwar jiki da qamewar zuciya.
Hadiza?
Hadiza kece agurin tsaye?
Sai alokacin ta daqo qafafunta ta janyo jiki ta qaraso gaban mamar ta zube tareda fashewa da wani irin kuka dukkanin zuciyarta na Mata wani irin radadin qunci da damuwa da baqin ciki.
Kukanta ya tabbatarwa da maman tabbas hadiza ce kuma cikine ajikinta ta samo ta dawo dashi.
Cikin rawar murya ta firgici Inna tace”
Hadiza cikine ajikinki?
Ba musu ba Jan dogon yanayi ta dago jajayen idanuwanta ta kasa kallon innar ta bude Baki murya a shaqe tace”
Eh.
Hadiza Ina nufin ciki fa na haihuwa?
Kuma amsawa tayi da “eh..
Hadiza daga Lagos fa kikaxo da Wannan cikin.,
Aure kikai acan bamu saniba?
Girgiza kai tayi ahankali tareda cewa”
Aa inna,Amma wallahi tallahi……
Zubewar innace da sautin salatin Yaya Umar Mai qarfine yasa maganarta yankewa hankali tashe ta dago tana kallonsa idanuwanta jajir.
Inna gurin mama ta nufa tana Kiran sunanta,
Aishatu?
Aishatu? Aishatu Dan Allah karki kashe kanki sbd wannan mugun abun kunyar da hadiza tadauko,
Innalillahi Aishatu Dan Allah karki tafi ki barni banida kowa,
Malam ya tafi ya barmu ke kadai Kika rage karki tafi ki barni.
Kuka Inna ta fashe dashi tana Kiran sunan inna data jima da somewa.
Sabon tashin hankali hadiza tasamu kanta aciki
Da sauri tayi kan maman itama tana kiran sunanta cikin mummunan mawuyacin hali sbd ita kanta tanaji batada lafiya.
Wani Mummanan Marin Rashin Imani da baqin ciki Umar ya sauke Mata lokaci daya Yana kallonta a qazance ransa a matuqar bace yace”
Karki kuskura ki tabata,
Shekara kusan biyu kena bakya gida
Bakizo musu da kudin dakikaje nemaba sai tsohon cikin banza¿
Gashinan Zaki kasheta lokaci daya da baqin ciki,
Tashi na daina ganinki wlh kafin na illataki daga ke har abin banzan da kike dauke dashi.
Yanda yayi maganar a tsananin fushi da bacin Rai har Yana sake yowa Kanta yasata Jan jiki tayi can gefe tana wani irin kukan zuci Mara sauti.
Kwasar mamar sukayi sukai cikin daki da ita sai firfita Inna ke Mata tana kuka Wanda yake na firgici da tsoron halinda Aishatun zata shiga dakuma zallar baqin cikin al’amarin da hadizar take tafe dashi.
Duk dubarunsu da ruwa dasuka ringa shafa Mata Bai saka ta farfafo saima qarasa rikicewa sosai da jikin yayi gabaki daya.
Hankalinsu duka yatashi Dan haka dole Yaya Umar din ya fidda waya yakira Yaya kabiru,
Shima rabon zaai gabansa ne yasashi zuwa gidan tunda asuba sbd ruwan da aka kwana ana zubawa yasashi tunanin gininsa da akeyi acikin gidan da baa kammalaba Wanda yasa ai masa daki daya da bandaki
amarya yakeson yi to anan zai kawota ya gwamutsa cikinsu innar.
Koda Yaya kabirun ya iso tuni innar tayi nisa Amma basuyi yunqurin kaita asibiti ba saima wani sabon tashin hankalin daya barke tsakaninsu sbd ganin hadiza ce silar koma meya samu mamar.
Kabiru buga rantsuwa yayi akan wallahi saita bar gidan da cikin,
Bazasu taba barinta ta zaunaba a gidan baqin cikin rainon ciki da goyon shege ya kashesu mama
hakama bazasu yarda ta Bata musu sunan dasukai gwagwarmayar samarwa kansuba lokacinda take Lagos tana zubarda mutuncinta da qimartaba.
Yaya Umar dinma bayan kabirun yabi akan Takoma inda tafito da cikin.
Rokonsu takeyi tana wani irin kukan tausayi da tsananin quncin datake ciki akan su yarda da ita Bata taba aikata Zina ba Amma Sam babu Wanda ya saurareta saima qara harzuqa dasukeyi da tsananin fushi da bacin rai,Yaya Umar Dukan mutuwa yakeson yi Mata Amma Inna dake kuka sosai ta Hana ta riqesa tana bayyanarda nata fishin itama.
Riqonsu tadawo yi akan su fito da mama akaita asibiti
Nan ne Umar yabi takan qafafuwanta ynaa neman tattakawa a fusace yace”
Uban waye Zaki fadawa akai mama asibiti? Lokacinda kike zubarda mutuncinki kinyi tunanin halinda zata shiga Idan taganki da wanna abun.
Kukanta qafewa yayi alokacin sbd a yanzu mahaifiyarta kawai takeson yiwa bayanin gaskiyarta,
Mahaifiyarta dake cikin mawuyacin hali takeson tabbatarwa Bata lalaceba Kaman ynada suke tunani.
Gurin Inna ta rarrafa tana roqonta akan subarta taga mama Dan Allah.,
Wallahi tallahi Inna ban taba aikata abinda kuke tunaniba,
Inna ku yarda Dani Dan Allah,
Wlh Inna cikina kwanci yayi sai yanzu yatashi,
Inna wlh cikin Salisu ne,Dan Allah inna ke ki yarda Dani…….kuka ta fashe dashi Mai tsananin ciwo tana sauke kanta sbd babu sassauci ko alamar yarda da ita atareda kowa.
Tashin hankalin data samu kanta dawowarta bata dauka zata tadda hakanba.
Duk wani sauki da rahama Bata samu daga yayyunta har innar ba qarshema haka ciwo ya tasar Mata Wanda tabbatar naqudace Amma tashin hankali yakasa barinta tanema guri ta nutsu ko haihuwarce zatazo.
Irin wulaqanci da tozarcin da yayunta sukai Mata bazai taba barin tasamu sassaucin nauyin zuciyarta ba har abada,
Sunkuma tabbatar Mata da wallahi bazata taba rainon cikinba a gidan bare haihuwarsa,
Idanma ta haifesa koko zasusa abasa yasha ya mutu su sun huta itama ta huta da renon ‘dan da babu uba hakama shi kansa Dan ya huta da girma a duniya yatashi cikin gori da wulaqanci.
Masiface da tozarci Wanda ya haddasawa maqota sanin abinda tadawo dashi daga Lagos din suka ringa zuba Mata cikin fushi da bacin Rai,
Da yawa wasu sunshigo da sunan duba Inna Dan su tabbatarwa da idonsu cikin shege tayo daga zuwa Lagos….
Bata taba kukan Rashin mahaifintaba da Rashin Salisu kamar ayau datai wunin tsananin baqin ciki da danasanin tafiyarta Lagos sbd da agaban iyayenta cikin ya farfado da babu Wanda zaiyi Mata Wannan yankan qaunar.
Idanuwanta sunyi wani irin kumburi da Bata iya gani sosai.
Daddafawa tayi bayan tasamu dare yayi su Yaya Umar sunbar gidan ta shigo dakin da mahaifiyarta take ta zube gabanta Daqyar sbd tsananin azabar naquda.
Hawaye ne suka gangaro Mata takai hanunta dake rawa ahankali ta dafa na mahaifiyarta tareda rintse ido wasu hawayen na tsananta Mata gudu.
Kuka takeson yi ganin yanda mahaifiyarta ke numfashi ahankali alamar samun sauki saidai bazata kukanba Dan naqudarta tagama zuwa kusa,ta gyara zamanta da qyar tana hada wani irin zufan gaske tako Ina jikinta azababbiyar azaba takeji Dan haka ta damqe hannun mahaifiyarta da qarfi tana sake wani irin gurnanin Nishi tana Kiran sunayen Allah a azabance.
Inna na dakinta kwance zazzabi Mai tsananin gske ya kwantar da ita da wannan babbar masifar data kunno musu Kai Dan haka batasan meyake faruwa da hadizan ba.
Naquda Mai tsananin wuya da azaba takeyi gadan gadan
Tagama jiqewa sharkaf da zufa
hakama mama tuni tafara bude idanuwanta cikin tsananin ciwo,
Tanajin ‘yarta na nakuda Kuma Mai wuya da azaba Amma babu abinda zata iya yimata hakama babu Wanda zai taimaka Mata…
Hawaye da ‘dacin tausayin ‘yartane ya gangaro gefen idonta
ta Dan motsa hanunta dana hadizan yake Kai ta kama hannun hadizar ahankali idanuwanta na zubowa da wasu hawayen masu zafin gaske.
Hadiza taji mamar Amma bazata iya magana ba ko juyowa takalleta saima wani wahalllen Nishin datake fitarwa tana fidda Rai ga rayuwa,.
Jin take da zata mutu agurin wannan naqudar data godewa Allah ta huta da Wannan rayuwar da babu komai acikinta sai qunci da damuwa.