Karba tayi cikeda godia jikinta duk a mace da yanayin malam din sbd ko magana bayason yi Kai kawai yake gyadawa Majeed din alamar godiya.
Fita sukayi Yana riqeda hannun Inayar suka nufi makaranta Saida suka qarasa bakin kofar makarantar ta juyo tana kallonsa fuska a Dan shagwabe ta bude madaidaicin bakinta tace”
Abbi Idan kaje asibiti taredasu Umma yaganah waye zaizo ya tafi Dani Idan an tashi?
Na tafi na da kaina abbi Zan iya.
Fararen idanuwansa ya saukar Mata a ‘dan bude yace”
Koba yau ba duk ranar Dana samu kin fita kinbi hanya da kanki zakisan Hukuncin dazan dauka akanki,
Kina kina?
Gyada Kai tayi tareda sake cewa”
To Abbi na zaunane nayita jira har kazo?
Umma yagana Bata makaranta Idan antashi zanji tsoro aka barni,
Kazo da wuri kaji Abbi???
Gyara Mata zaman hijabinta yayi Yana gyada Kai cikeda kulawa yace”
Kidai jirani kinji abinda na fada,
Wuce karkiyi latti,
Allah ya bada saa.
Amin Abbi.
Juyawa tayi ta shige ciki shikuma ya juya ya tara mashin ya hau ya nufi gurin aiki Kai tsaye.
Bai wani jimaba gurin aikin ya bayyanarwa da manager uzurinsa ya fito ya kama hanyar asibiti sbd Yagana ta sanar masa suna Isa anbasu gado.
Koda ya Isa asibitin jikin malam din yaqara tsanani sosai Kamar Kar a iso dan haka ya karba takardun magani da abubuwan da aka rubutan.
Ba wasu kudaden ne dashiba shima Amma haka ya tafi gurin siyan maganin Dan yaji ko nawane kudin.
Ana Gama duba takardar a pharmacy aka miqo masa kudin a rubuce.
Dubu talatin harda shida da wata dari takwas akai yagani rubuce.
Ajiyar zuciya tareda numfashi ya sauke a hankali tareda kallon Mai shagon a hankali ya furta”
Nagode” ya juya ya wuce yabar gurin.
Bayada ko dubu goma a halin yanzu Dan kuwa duka duka dubu shida ce a account dinsa Kuma koshi kansa baya tabata Dan na siyayyar Inayah ne na abincin zuwa makaranta daya kusa qarewa.
Kallo takardar ya Kuma yi tareda sake lumshe fararen idanuwansa cikin tsananin tausayin malam din da yaganah.
A iya fahimta da Dan sanin da yayi musu yasan basuda kowa sai junansu,
Yasan dai Yan asalin jahar borno ne suna cikin Wainda sukayo gudun hijira tunda dadewa dangi da sauran Yan uwa duk sun mutu wasu Kuma Suma sun fada wata duniyar suna ganin garari.
Fuskarsa ya shafa ahankali kafin ya juya ya nufa titi Dan hawa mashin yakoma gurin aikinsa ya gwada rokon manager albashinsa na Wannan watan idan zai samu yanzu koba komai saura sati daya watan ya qare.
Kokarin tare mashin yake Yar qaramar wayarsa ta Itel ta ringa vibrating sbd ya kashe qararta bayaso.
Ciro wayar yayi daga aljihu yaga sunan yaganah ya dauka Yana cewa”
Assalamualaikum” cikin nutsuwar muryarsa Kamar kodayaushe.
Wata sanyayyar ajiyar zuciya Mai zafi tareda mutuwar jiki yaganan ta sauke kafin tace”
Abdulmajeed kadawo kawai malam yariga ya tafi lokaci yayi…
Wani irin kuka Mai sanyi ta fashe dashi tareda kashe wayar sbd sai alokacin kukan ya zo Mata.
Innalillahi wainna ilayhirrajiun” ya furta Yana maida wayar aljihu ya tsallaka titin yakoma cikin asibitin Yana jinjina Kai cikin jimamin mutuwar.
Kuka sosai Yaganah keyi daqyar ya iya furta Mata kalmomin ban hakuri da tawakkali dazai iya furtawa shima.
Basuda wani jamaa dagashi har ita yaganar har malam din Dan haka babu maganar tsayawa Jan lokacin jana’iza
Asibiti na Gama nasu aikin suka Basu gawar suka dawo gida da ita.
Sosai jamaar gidan Dana anguwa suka nuna alhininsu akai masa sitira aka kaisa.
Bai samu zuwa maqabarta ba sbd gabaki daya hankalinsa daya rabu biyu Yana kan Inayah da aka tadasu makaranta lokacin Dan haka makarantar ya wuce Kai tsaye ya daukota suka dawo gidan yabarta gurin yagana yabi sauran Wainda zasu maqabartar suka wuce.
Babu wani zaman karban gaisuwa dasukai saidai Wanda yazo yaje har kofar dakin yagana yayi Mata gaisuwa ya wuce sun daiyi Mata tasu karar sun zauna ranar daya rasun daga ranar saidai masu zuwa jefi jefi har akai sati biyu.
Tunda akai rasuwar babu ranarda Inayah Bata fashin makaranta zai kaita da kansa ya wuce aiki
Idan lokacin tashi yayi zai Baro gurin aikinsa ya rakota gida kafin ya koma.
Wani sabon Nauyin ne yakuma hawa kansa na Yaganah sbd kallok uwa dayake Mata gakuma tausayin halinda take ciki din na Rashin miji,Dan uwa,abokin fira,abokin rayuwa Wanda suke tare tun kuruciya gashi ko tashin hankalin daya sakosu gudun hijira Bai rabasuba sai yanzu da Mai gaba daya tazo wato mutuwa.
Sbd matsayin Yaganah agun Inayah yasa Dole ya dauki nauyinta ya ratayawa kansa Dan haka yanzu komai nasu tareda ita yake siya sbd ko aikin ta daina zuwa Dole sbd takaba,
Ta wani bangaren Kuma mutuwar ta tabata sosai Dan komai ya fice Mata arai
Daqyar Inayah ke samu tana dan sakata magana wasu lokutan.
Rasuwar tasa Dole yakoma ya saki gidan daya kama ya karba kudinsa kafin Yaganah ta Gama zaman takaba zai nema musu wani Mai Yar damar Inshallah.
Dan haka kudin saiya tattara ya hada ya siya musu abinci isasshe da siyayyar makarantar Inayah suka shiga jss 1.
Watan malam din shida cif da rasuwa sukabar gidan suka koma sabon qaramin gidan daya kama din Wanda yamafi na farkon kusa da gurin aikin nasa,
Dakuna biyu ne a gidan da qaramin toilet harda broken tiles dinsa.
Daki daya ya dauka
Dayan Kuma haka Dole dai yaganah da Inayah suka zauna daki daya Amma wasu kayan nata na dakin baban nata sbd sabo.
Katifar Inayah ta farko ya dauka sai ya siya musu wata Yar katifar Mai Dan girma tareda zanin gado da pillow sbd sanin Inayah da bacci da pillow.
Labulai ma ba laifi ya Samar musu iya daidai nasu sai kayan aikin abinci da kusan duk nasun ne na da.
Ahaka cikin Dan rufin asirinsu suka fara gudanar da rayuwarsu a sabon guri cikin nutsuwa.
Bayan tarewarsu anguwar Basu wani dauki dogon lokaci sosaiba Yan anguwar Suma suka gane halayensa na Rashin shiga mutane da kamewar Kai dan haka suke mutuntasa duk da zamansa matashi ba wani babba ba.
Kwarjinsa hadi da Kamun kansa da Rashin shigewa al’amuran jamaa musamman wainda Basu shafesaba yasa duk inda ya zauna ake mutuntasa sbd shi kamilin mutum girmamasa akeyi Koda baida wasu manyan shekaru.
Islamiyar dake cikin anguwar ya sakata tareda sauya Mata makarantar bokonma sbd waccan din tayi nisa Dan haka gabaki daya yanzu komai nasu ya Dan sauya,
Yagana ke girkin abinci da tsaftace koina na gidan ta sakewarta Takoma tamkar yanda take a da dinta,
Sosai take kulawa da Inayah tamkar jikarta data Haifa uwarta,
Shi kansa Baban Inayar yana cikin kulawar yaganan Dan kuwa abincinsa baa Wasa dashi,
Musamman data fahimci shi Mai tsananin tsaftar gaske ne sai baa Wasa da qazanta a gidan ko kadan.
Yan anguwama ganin irin kauna da kulawa Mai girma dake tsananinsu yasa suke daukar yaganar a matsayin mahaifiyarsa.
MAMUH
For More pages ku garzaya arewabooks
LOVE/ROMANCE
INAYAH#AYSHATOUH
ZAFAFA BIYAR
ZAFAFA BIYAR
INAYAH
MamuhGee
GURBIN IDO
Safiya Huguma
SANADIN LABARINA
Hafsat Rano
FARHATAL QALB
(Miss Xoxo)
BABU SO
Billyn Abdul
Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k
BREAKDOWN OF ZAFAFA BIYAR VVIP SINGLE PAID BOOK
4 BOOKS 4500
3 BOOKS : 3500
2 BOOKS : 2500
1 BOOK: 1500
YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS????????????????????????
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902
IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA????
09134848107
[10/13, 4:51 PM] +234 703 121 9749: Mamuhgee 8
Arewabooks@Mamuhgee
Farkon zaman yaganah dasu duk wata Yana fidda kudin Albashinta na zama da kulawa da Inayah,