INAYAH COMPLETE HAUSA NOVELINAYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

INAYAH 1-10

Yaya Umar kuwa sanaa kowacce yi yakeyi baida tsayayya guda daya Amma dai yafi yin ta dillancin harkar Saida filaye da gidaje Dan Yana samu sosai acikinta shiyasa yafi yya Kabiru rufin asiri,
Qarshema dai fadawa yayi siyasa sbd uban gidansa dayasashi fitowa Dan samun kudin jam’iyyar da zasu fito ta karkashinta tunda sunsan dai ba ci zasuyiba Amma sunsan jam’iyyar zata Basu kudi sosai Dan haka gadan gadan yafada siyasa baji ba gani,

Yaya kabiru daya fahimci akwai samu sosai a harkar take ya marawa Umar din Baya Dan Shima ya samma masa Idan ta ‘bulle.

Itakam hadiza ganin zaman baida wata mafita
Ga Abdul ya isa sakawa makaranta tuni
Sbd abbansa koda ya rasu yanada burin sakasa makaranta alokacin,

Yanzu komai ya juye musu Kuma tanada burin bawa Abdul din ilimi Dan ya anfana rayuwarsa,

Gasu Inna da mama kullum cikin dubaru ake
Yau aci kwadon kwaki,
Gobe aci kwadon qanzo,

sai ankwana hudu ko Biyar Daqyar ake hada cinikin da zaai musu tuwon gari da miya.

Dole hadiza ta tashi ta Saida katifarta da ita kadai ta dawo da ita sai tarkacen kayan kitchen ta kwashesu takai kasuwar Yan kayan hannu ta saida ta tattaro kan kudin taraba biyu ta siyo musu abinci da kayan abincin tadawo gida.

Sana’ar kosan safe dakuma awarar Rana tafara da sauran kudin yafara juyuwa.

Kasancewar ita Inna da sauran karfinta sai tana taya hadizar aikin sana’ar musamman awarar datafi wuyar sha’ani.

Cikin ikon Allah lokaci qanqani saigashi sana’ar ta samu karbuwa sosai duk da farko taci tsananin wuyar wuta da Rashin jamaa masu siya tunda baa saniba,

Babu ranarda Bata konewa shiyasa kusan koina tagama kokkonewa hannuwa da qafafu
Har fuska ma wani lokacin idan Mai yayi watsi.

Ba laifi yanzu basa neman komai a gurin kowa Wanda dai zasuci saidai Dan abinda baa rasaba.

Inna ma tuni dole suke komai tare sbd aikin yanawa hadizan yawa ga koko dasuke hadawa dashi yanzu da safe,
Da Rana ma yanzu ba awarar kawai sukeba harda dankalin hausa da wainar rogo.

Dole dai yanzu innace take aikin kosai da kokon safe ita Kuma tana awarar da sauransu da Rana sbd dukkaninsu aikin yayi mutsu tsananin wuya musamman tunda aikin wuta ne,

Mama ba cikakkiyar lafiyayyaceba shiyasa Basu taba barin ta shiga sana’ar ba,

Tunda mahaifinsu ya rasu haka take yau lafiya gobe ciwo,
Hawan jini da ciwon sugar ke tsananin damunta Dan haka lallabawa kawai takeyi tana rayuwar.

Ahaka hadiza ta samu ta sanya Abdul a makarantar gwamnati yafara zuwa
Kullum ita ke rakasa da qafa tadawo
Idan antashi haka take komawa ta dawo dashi sbd akwai Dan nisa sosai.

Hutun farko na makarantar tabi taqarasa hargitsewa sbd yanda kullum saita kaisa ta daukosa ga lattin fara sanaarta datakeyi Idan taje daukosa,

Dole Inna ce take fara yimata kafin ta dawo daukosa ganin mutane sun fara janyewa ansamu wata Yar baqin cikin ta fara sana’ar a makwaftansu.

Ganin Inna ma wahalar duniya tafara sakota gaba sbd ayyukan sun mata yawa ko baccin arziki bata samu sosai dole mama ta ringa karba tanayi sbd Suma su ringa samun sassaauci tunda Allah yasa yanzu da aikin suka dogara kacokam.

Tsawon lokaci rayuwar tana yanda take garesu ba wani dogon sauyi saima ciwo daya kwantar da mama Dan haka suka sake zagewa da Sanaa ga Inna itama karfinta yayi qasa,
Ga Abdul yanzu karatun nasa yafara nisa tunda Yana aji biyu yanzu.

Ita kanta lafiyarta wani lokacin qaranci take mata sbd ciwon mararta har lokacin Yana taso mata akai akai gashi wani babban ikon Allah dayake kamata shine tunda tayi Bari lokacin rasuwar Salisu har yau Bata taba yin wani al’adar ba,

Tayiwa Inna maganar innar tace mata wasu matan na hakan musamman Idan suntaba samun matsala ta Bari Dan haka ko jinin Al’adar zai koma ya ringa zuwa daidai sai tayi wani auren kilan.

Da Wannan zancen ta tattara maganar Rashin zuwan Al’adar ta watsar tafara neman wata sana’ar sbd wannan din ta daina tafiya sosai sbd kusan anguwar ganin ana samu duk sun fara sana’ar shiyasa yanzu ba mutane sosai.

Ganin wata sana’ar taki samuwane
Duk Wanda tafara Bata karbuwa gashi jarin nata tafiya gurin hidimar gidan yasa dole tafara zuwa aiki wani gida acan GRA da mama Indo qanwar Inna ta Samar mata.

Fara aikinta sai rayuwa kuwa ta sauya musu Dan yanzu da albashin suke komai.

Bata wani jimaba da fara aikin saigashi hajiyar suka tattara suka bar qasar itada ‘yayanta dole tadawo zaman gida ba wani aikin.

Jin bazata iya zaman ba aikin komaiba yasa takuma zuwa tasamu mama inda dake shirye shiryen tafiya Lagos itama aikin Sanaa tace takuma samar mata wani aikin.

“Babu wani gidan aiki Idan ba Lagos Zaki shirya ki bini ba kya ringa musu aike daga can kokuma abaki Aron kudi ki bar musu Idan munje can kya ringa biyana da kudin aikinki??”

Haka mama indo ta sanar mata Dan haka batada wani sauran zabi bayan amincewarta sbd suna cikin tsananin halin nema gskia.

Ko data sanar dasu Inna farko sunso hanawa Amma ganin yanda mama Indo tai musu bayanin aikine kawai a wani babban restaurant na masu kudi da aka bude Kuma sunada masauki Mai kyau da restaurant din suka tanadarwa ma’aikatansu a tsaftace cikin kwanciyar hankali.

Hakan yasa suka amince tareda bawa mama Indon Amanar kula da hadizar duk da ba yarinya bace.

Kudi sosai hadiza ta karba gurin mama Indo ta siyawa su mama abinci Mai Dan yawa tareda dinkawa Abdul uniforms har kala biyu da sabbin takarman zuwa makaranta da slippers harma da sababbin litattafai.

Sauran kudin taje takuma siyo musu sabulan wanka da omon wanki dasu lalle da kanwar dazasu ringa saidawa daga zaune cikin gida ta damqawa Inna sauran kudaden a hannunta.

Daga Yaya Umar har Yaya kabiru babu Wanda yayi yunqurin hanata tafiya sbd su yanzu siyasar gabansu ta ishesu shi Yaya kabiru harda tattara  aikinsa yayi ya ajiye sbd ganin sun fara samu ba laifi.

LAGOS
Da farko tafara Shan wuyar rayuwar garin data aikin dasukeyi sbd wani sabon hotel ne da aka bude aka daukesu aikin Dan haka wainda basajin turanci bangaren restaurant aka ajesu gurin harkar abinci.,

Farko ganin baa bacci kwana akeyi aiki yasa tafarajin zuciyarta tayi sanyi da rayuwar,
Amma ana Bata albashin farko taga irin yawan kudin sai kawai ta tattara kyuya da damuwar komai ta watsar ta zage da aiki gadan gadan.

Kasancewarta mai tsananin kokarin aiki da Amana da ladabi yasa cikin wainda aka daukesu tare watansu biyu aka qara mata matsayi tareda dauketa daga kitchen aka maida bangaren tsafta,
Ma’ana bangaren masu Kai abinci dakunan manyan Idan sunyi odar abinci Dan haka kusan yanzu hutawa takeyi sosai sai anyi odar abinci taje takai.

Gidan dasuke cikin kudinsu na albashi ake Dan tsakura duk wata ana biyan haya Dan haka hankalinta ya kwanta sosai gashi ahakan duk wata take turawa su Inna Yan canji ta hanyar Mai pos din kusada gidan nasu data baro.

Kwanciyar hankali da hutu da Kuma nutsuwar datake samu yasa tafara sauyawa sosai sbd abinci Mai kyau na hotel din sukeci,
Nama da kayan Dadi kala kala haka suke ci dan haka tafara sauyawa sosai,

Mama indo dai ita a bangaren abinci take har lokacin Kuma babu ranar sauyata daga gurin sbd yanda ta iya wata irin lallausan sakwara da Amala,Eba,semo
duka dai kalolin swallow babu Wanda mama Indo Bata qwareba shiyasa saka barta agurin Kuma itama ahakan ba qananun kudi take samuba sbd yanda suke tsananin son aikinta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button