Kukan fitar hankali tayi tsawon lokacinda Bata saniba agurin har Saida taji idanuwanta da fuskarta sun kumbura kafin ta iya miqewa ta kama hanyar komawa gida.
Isarta gida Bata Bari kowa ya gantaba ta shige daki ta aje Jakarta ta fito tayi alwala Takoma dakin sallah kawai tayi ta fara rokon Allah mafita tana hawaye
Ahaka ta Gama ta miqe Takoma ta kwanta Bata Kuma fitowaba sai washer gari.
Gurin aikima datazo nokewa kawai taketa faman yi tana kame kame sbd ganin Kamar kowa zai fahimci cikin jikinta Dan haka duk tabi tayita Jin kanta a muzance.
Tana tashi aiki Bata koma gidaba Kai tsaye gurin wani gurin scanning din daban ta nufa takuma yi,
Shima result daya tasamu na akwai ciki.
Wani gurin takuma zuwa Shima duk daya,
Haka tayita yawon guraren scanning ana Bata result daya
Ta tattara tadawo gida hankalinta zuwa lokacin yagama barin jikinta,
Tashin hankali da tsananin tsoro takeji yanzu sbd ta tabbata takuma shaidar kanta Idan har Wannan cikin na haihuwane bana aljanuba to wlh cikin Salisu ne ajikinta Wanda yabarta dashi tunda tasan Bata taba ko tunanin ‘da namiji ba bayan rasuwar salisunta.
A daren kwana tayi wani irin kuka da quncin zuciya mai nauyin gaske.
Tayaya zata fuskanci duniya da ciki a jikinta?
Cikin da bai tashi fitowa ya bayyana kansaba sai data baro gaban iyayenta tazo Lagos,
To tace me akan cikin?
Zaa yarda da itane?
Cikin qanqanin lokaci damuwa da kunci sukaiwa rayuwarta mugun baibayi,
Sam tarasa walwala da kwanciyar hankali da nutsuwarta,
Kullum cikin zullumi da tashin hankali take tashi takuma wuni acikinsa sbd ciki dai yanzu gadan gadan fitowa yakeyi Yana girma ahankali Kaman yanda kowanne lafiyayyan cikin keyi.
Lokaci na Ja tadain shiga mutune Sam yanzu Takoma tamkar mujiya sbd yanda cikin yagama fitowa kowa ya ganta Kai tsaye zai shaida cikine a jikinta,
Hankalin mama Indo yayi Mummanan tashi da girman mamakin ganin Wannan alamari,
Tashin farko Bata yardaba da anata gulmar cikin Hadizar sai data tinkareta ta ganarwa idonta ta tabbatar musamman yanda hadizar takasa hada ido da ita sai hawayen baiqin ciki takeyi.
Babu kalar diban albarka da Rashin mutuncin da mama Indo batai mata tareda gori da zagi kala kala karshe ma haka ta tara mata jamaa agabansu tai mata Mummanan wulaqanci har Wanda baima Gama sanin halinda take cikiba yasani,
Take gurin aikin dama gidansu aka fara zundenta,
Masu zaginta da masu tausayinta dama wainda suke ganin ba komai bane Dan tayi cikin,
Haka aka ringa yi da ita tun tana daurewa zuciyarta harta fara gazawa sbd babu inda take Jin Dadi ko sassaunci alamarin duniya yataru yayi duhu,
Babbar fargabarta da tashin hankalinta Kar mama inda ta sanarwa su mama da Inna halinda take ciki
Dan haka duk tabi ta daga hankalinta wata sabuwar damuwar da tashin hankali yakuma shigarta.
Ahankali Ahankali lokaci yakuma tafiya Amma a rayuwar hadiza kullum da’da zurfafa take cikin tashin hankali da damuwa da qunci take sbd rayuwa tayi mata tsanani sosai sbd ciki kam ya tsufa sosai kowanne lokaci zata iya haihuwa,
Kullum adduarta Allah yasa ta Haifa abunda yake cikin yazo ba rai ta huta ta tattara Takoma gida sbd bazata iya zuwa gaban iyayenta da Wannan cikin ko abinda zata haifa barema yayyunta data San basuda imanin karbanta da abinda zataje dashi,
barinma yanzu dasuke siyasa bazasu yarda da abinda zai taba qimarsu dasuke tunanin sunada ita a manyansu.
Wani sabon tashin hankalin ta shiga Rana tsaka da gurin aikin suka sallameta bataredama sun jira watan yaqare anbata albashintaba.
Lokacinda taringa roqar Manager tana basa hakurin yabarta zata iya aikinta koda cikin Amma ya rufe ido ya sallameta tareda Bata awanni akan ta tattara tabar gidan kamfani tunda gurin aikinne suke Basu gurin zaman Dan haka Kai tsaye gida Takoma bayan tagama ganin tonan asiri da tozarci iri iri daga gurin abokan aikinta da jamaar hotel din.
Kuka zuwa Wannan lokacin ya ‘dauke mata zuciyarta bayan radadi da tsananin qunci babu abinda take Mata
Dan haka ta tattara kayanta da duka abubuwanta ta fito Kai tsaye ta nufi inda zata shiga motar dazata kaita tashar da zata siya ticket din motar komawa Adamawa.
Tunda tashiga mota zuciyarta tai Mata nauyinda Bata ko iya kuka sbd dole dai Takoma gida ta fuskanci Wannan sabuwar qaddarar data zo Mata.
Har motarsu tayi wuni guda a Tasha tana zaune guri daya sallah kawai ke tada ita har dare yayi suna tashar Basu tashiba sai tsakiyar dare motocinsu suka tashi aka dauki hanya.
A hanya asuba tai musu,Rana tayi musu,yamma tayi sunata Dukan hanya har wani daren yakuma yi suka kwana ahanya sai ana gabanin asuba suka iso cikin garin Adamawa kowa ya sauka.
Lokacin har anfara Kiran sallar asuba a masallatai da dama Dan haka dole da yawansu suka tsaya anan tashar sukai sallar asuba ciki harda ita sbd batasan abinda zata tadda a gidan ba gwara tayi sallar ta nema sassauci daga ubangiji dayake jarabtarta da Wannan rayuwar.
Qarfe 5:24 mashin ya sauketa bakin kofar gidansu datai mamakin ganinsa bude lokacin ta sauka daga kan mashin din tana miqa masa kudin data fidda daga jaka tun a hanya sbd daga ta saka ya miqa masa ta shige gida batareda ta tsaya jamaar anguwa sun gantaba.
babu kowa tsit anguwar sbd garin da Bai Gama haske ba
ta kinkimi qatuwar Jakarta da akwatinta harma da wasu ledojin ta nufi cikin gidan zuciyarta na tsananta bugu duk da tayi imanin da iyayenta bazasuyi Mata zargin Zina ba tunda sune suke tarbiyanceta Kuma sunsan halinta da abinda zata iya dama wanda bazata iyaba koda kuwa inda yafi Lagos taje.
Ganin Sabon mashin fil a soron gidan yasata kallon kofar cikin gidan zuciyarta na neman karaya sbd fahimtar tabbas kodai Yaya kabiru kokuma Yaya Umar ne acikin gidan.
Siririyar shaqurarriyar sallama ta saki lokacinda ta shigo tsakiyar gidan daukeda kayanta kamar sabuwar bokanyar datayo gudun hijira.
MAMUH
LOVE
ROMANCE
INAYA A MAJEED ABBI
[10/13, 11:57 AM] +234 703 121 9749: INAYAH
Mamuhgee
Arewabooks@Mamuhgee
4
Inna ce dake kokarin fitowa bandaki riqeda mama ta amsa sallamar Kai tsaye batareda ta Gama tantance waye me sallamar sbd hankalinta gaba daya dake kan Mama data riqo wadda ko tsayuwa Bata iya yi Dan jikinta matuqar sosai yayi tsanani a kwanakin.
Sai data fito tsakar gidan da kyau ta dago tana sake amsa sallamar da hadizar takuma tana kallon mahaifiyarta data sauya kamanni gabaki daya sbd tsanani da azabar ciwo.
Hawayene suka ciko idanuwanta da sukai zurfin Rama da irin kukan rayuwar datake ciki ta dago qafafuwanta dasukai Mata sanyi da nauyi ta tunkarosu tana Dan kasa kallon cikin idanuwansu da suka zuba Mata dukkaninsu.
Inna da qafafunta suka kusa sakewa sbd tsananin mamaki da faduwar gaba
A ‘dan rude muryarta na gwamutsuwa tace”
Hadiza kece Wannan a tsaye???
Jin hakan yasa mama da Bata gane kowa sosai ta Dan sake riqe hannun innar tana bude idanuwanta ko zata sake ganinta da kyau
Sai idanuwanta suka sauka kan tsohon cikin gaban hadizar
Ta Dan motsa kadan tana bude Baki cikin sanyin ciwo tace”
Lami?
Kasa amsawa Inna tayi sbd idanuwanta data kasa daukewa kan tsohon cikin Hadizar.
Lami?
Wace hadizar Kika ambata?
Hadizata ce tadawo?
Itace Wannan a tsaye?
wani busasshen yawu Inna ta hadiye tareda sake riqo mamar da kyau sbd hannuwanta dataji suna sanyi da daukar rawar tashin hankali mugun ganin datai safiyar fari.