INAYAH COMPLETE HAUSA NOVELINAYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

INAYAH 1-10

Yanzu yanada arzikin siyan mota Amma har lokacin Bai siyaba sbd yanke shawarar komawa Lagos a reshensu na aiki dake can sbd Nan din fitinar tafara yawa yadda abubuwan aikin nan din sun fara rushewa Dan kuwa maha’intar kamfanin sun fidda zalamarsu a fili take komai yafara rushewa.

Yana ganin hakan ya rubuta takardar aje aiki yafara aikawa Nuradden dake Lagos ta email.

Da farko hankalin Nuradden yatashi da barin aikin na A Majeed sbd sun riga dama suna kokarin rasa reshensu na can Idan A Majeed yabar aiki zasuyi Rashin babban gifted Dan haka da wuri ya sanar fa mahaifinsa dake Singapore halinda ake ciki.

***Kwana biyu Yana hutawa sosai a gida cikin iyalinsa hankali kwance musamman daya kasance dama baya wani yawo sosai daga aiki sai gida sai wasu guraren qalilan sai Kuma makarantar Inayah da har lokacin Yana zuwa kaita.

Ganin Abbinta gida kwana biyu kuwa Inayah sai takejin Dadi sosai sbd Dana aikinsa Yana riqesa sosai Lokacin Kuma yake gida itama Kuma makarantar yamma Dan gaka yawanci sai dare suke samun lokacin zama dashi.

Satinsa biyu a gida Yana hutu ana ukun ya shirya zuwa wani aikin da akeson daukarsa saiga sakon Amb Ibrahim Dikko mahaifin Nuradden daga Singapore.

Sabuwar offer ce na aiki dasu a Singapore.

Kai tsaye farko dakatar da offer din yayi sbd bayajin zai iya barin qasar yaje wata qasar aiki yabarsu Inayah anan su kadai Dan haka Kai tsaye bayan kwana biyu yayi rejecting offer din.

Wancan aikin ya karba harya fara Amma Nuradden suka kasa barinsa sunata bibiyarsa.

Sake sabon nazari yayi akan aikin sai kawai ya amince bayan an amince masa da zuwa dawu Inayah Amma Lagos zasu zauna tsawon lokaci kafin.

Lokaci qanqani suka dauka kafin suka tattara suka koma Lagos gabaki daya acan suka dasa sabuwar rayuwa.

Da farko sunsha wahalar rayuwar garin kafin suka saba saidai kam makaranta da Dole da qarfin hali Umma yagana ce aka koyawa mota Kuma Allah yasa ta iya tunda ba wani manyata tayiba dan haka ya siya musu mota itace take kaita tana daukota,
Koda minti daya Bata taba Bari tayi lattin Isa makarantar daukan Inayah ba sbd maimaicin dokar hakan daga gurin mahaifinta.

Aiki yamasa yawa sosai yanzu dan haka sosai baya wani zama,
Haha tafiye tafiyen garuruwa harma da ‘yan wasu qasashen daya fara sbd aikin nasa shiyasa yanzu Dole tarbiyar Inayah tadawo hannun Umma yaganah gaba daya saidai koyaushe cikin Kira da maimaita akula yake nanata musu.

Inayah na kammala secondary school bada jimawaba ya tattarasu suka koma Singapore sbd hankalinsa daya rabu biyu.

Rayuwarsu a Hougang Singapore wata sabuwar wayayyar rayuwace ta hutu da Jin Dadi sbd arziki daya zaunawa Abbin.

Watansu tara a Hougang suka dawo cikin asalin Singapore Singapore,

Bayan aikin kamfani wani karatu yasake jonawa cikin shekara biyu ya kammala tareda samun wani babban aiki a Australia suka bar Singapore.

Bayan barowarsa Nigeria ko shekara hudu Bai gama rufawaba kamfanin gabaki ya rushe akai gwanjonsa Wanda shine tashin farko ya siye kamfanin da malls malls din na can Nigeria harma Dana Singapore ya damqawa Nuradden da mahaifinsa Wanda manyanci yasa shima yace abawa Nuradden din yaci gaba da kularwa da A Majeed din dasu tunda yanzu komai ya zama mallakinsa ne
Amma hallacinsa yasa yabar kamfanin a hannunsu suci gaba da kulawa.
Sun sallami dukkanin ma’aikatan dasuke zargi da ha’incin Daya kaisu ga rushewa suka rasa komai aka Kuma zuba sabbin ma’aikata bayan ansake gyara companies din da malls malls dinsu.
BAYAN WASU SHEKARU…..

MAMUH

ZAFAFABIYAR

A.A MAJEED

INAYAH

AYSHATOUH

RIBABIYU

Dan samun cigaban labarin follow me @Mamuhgee at arewabooks

INAYAH
MamuhGee

GURBIN IDO
Safiya Huguma

SANADIN LABARINA
Hafsat Rano

FARHATAL QALB
(Miss Xoxo)

BABU SO
Billyn Abdul

Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k

BREAKDOWN OF ZAFAFA BIYAR VVIP SINGLE PAID BOOK

4 BOOKS  4500
3 BOOKS : 3500
2 BOOKS : 2500
1 BOOK: 1500

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS????????????????????????

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA????
09134848107Mamuhgee 9
Arewabooks@Mamuhgee

A.A MAJEED’s
659 Melrose victoria mosmon,
SYDNEY,AUSTRALIA.
A hankali ta qarasa zare navy blue turkian doguwar rigar dake jikinta ta jefar kan brown Chiara Andreatti sofa dake babban bedroom din nata.

Kyakkawar fuskarta datai ja ta Dan kalla ta cikin mirror tana Dan yamutsa fuska kafin takai hannunta akan fuskar ta shafa gefen damarta da wani Dan qaramin pimple ya fito mata qwaya daya tal daya hanata fita koina tun shekaran jiya.

Ajiyar zuciya ta sauke tareda zare fararen undies dake jikinta ta nufi toilet dasu a hannu tana shige ta jefa cikin laundry ball dake gurin ta nufi inda brushes dinta suke ta dauka daya tareda diban Toothpaste tafara brush tana kallon fuskarta jikin mirror tana sake Jin damuwar kurjin fuskar tata,

Tana gamawa  jacuzzi ta nufi ta shige tareda sakarwa kanta ruwan dumi tana Dan lumshe ido sbd damuwarta ta Dan saketa.

Mintuna qalilan ta dauka tana wankan kafin ta fito daure da brown towel kanta ma daure da brown towel din qarami
fatar jikin qyalli takeyi tana bayyanarda tsananin hutu,Jin Dadi da tsadaddiyar kular datake samu ta hanyar amfani da skin products masu tsananin kyau da tsada.

Kai tsaye gaban madubin dakinta ta nufa ta zauna tareda kunna hand dryer tafara busar da gashin kanta data kunce bobmarley braids (kitso/kalban Bob Marley) jiya da yamma.

Doguwar malaysian riga ta saka har qasa Mara nauyi ash kala ta zira Burberry slippers ta fito daga bedroom din nata hannunta riqeda wayarta tana kokarin saka Kira.

Qamshin turarenta na Versace(Bright crystal) ne yafara bayyanarda fitowarta daga bedroom dinta zuwa babban yalwataccen palon gidan dake.

Zubbi Mai aikinsu tun a Singapore Yar Amana wadda Alhaji Nuradden Aminin Abbi ya Aiko musu daga Nigeria itace ta dago daga kunna qatuwar Humidifier dake palon bayan tagama gyare koina na gidan ta tsaftace ta kalli hanyar da Inayah ta fito tana kallon kyakkawar fuskarta ta saki dan gajeran murmushi tana cewa”

Good morning Inayah.

Kallonta Inayah tayi da fararen idanuwanta tana amsawa Kai tsaye da cewa”

Morning zubbi.

Hanyar bedroom din Umma yaganah ta kalla tana cewa”

Umma yaganah ta tashi?

Yes ma” zubbi tafada tana qarasowa Dan shiryawa Inayah breakfast dinta kan dining ta nufi babban Australian kitchen dinsu ta shige.

Kai tsaye ta murda kofar dakin ta shige tana qaramar sallama da cewa”

Umma yaganah yauma bazan fita koinaba fuskana ta sake kumbura da ja…

Zaune umman take kan wata tattausar sofa kalar ash na komai dakin dayake ash Mai haske,

Farin glass ne a idonta tana karanta wani Arabic hisnul Muslim
Jikinta sanyeda doguwar rigar plain cotton Swiss Mai tsada light pink.

Dagowa tayi tana kallon Inayah cikin kulawa da tsananin bayyananniyar kaunar Inayah data Dade da shiga jininta ta ajiye littafin gefe kan table tareda maida hankalinta kan Inayan gaba daya tace”

Yau kam saikin fita Inayah,
Meyesa kike Wasa da karatunki ne yanzu?
So kike abbinki ya dawo yasan kwana biyu bakya zuwa makaranta?
Karatun likitanci fa kikeyi karki manta,
Ahakan zakiyi wani abin arziki kullum cikin shiriritar Gayu ya hanaki Wannan da wancan?

Akan pimples bazakice kindaina fitaba sai kin warke Dan haka
Ki Gama breakfast kije kiyi Shirin zuwa makaranta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button