Abdulmajeed yabarsu akan suyi shawara kafin lokacin tashin nasu yayi ahaka akabar zancen Idan yayi shawara da yagana.
Bayan komawarsu daki tace zatai fitsari dayake yanzu tafara girma dole badan yasoba yake barinta zuwa bandakin gidan Amma qaidane Bata Idan so nawa zata shiga bandakin saiya wanke Mata shi dasu Izal germicide harma dasu Dettol kafin tashiga Kuma harta Gama tafito Yana tsaye bakin bandaki Yana gadinta.
Idan Kuma baya gidane to yagana ma ta saba itace zatai Wannan aikin haka zata wanke takuma tsaya harsai inayan ta fito.
Su hand sanitizers kuwa baya Bari suna qarewa yake siyowa sbd ita din,
Data fito toilet din kokuma tafito filin gidan tayi wani abin yake tsaftace Mata hannaye dasu sbd shi wani irin mutum ne Mai tsananin tsaftar gaske shiyasa a wani fannin mutanen gidan da anguwar dama Yan gurin aikinsa ke ganin kamar yana qyamar mutane.
Yanzu dinma datace zata bandakin kayan wanke bandakin ya dauka tareda fitila mai tsananin haske ya fice yaje ya wankesa tas tashiga Yana tsaye ta fito ya wanke Mata qafafunta da hannayenta suka koma dakin.
Da kanta ta Kuma gyara shimfidar lafiyayyar katifarta tayi Addua ta kwanta ya gyara mata rufarta kafin ya miqe ya dauko jakar takardunsa na karatun masters dayakeson farawa da yardar ubangiji Idan su yagana su amince zasu zauna dashi da Inayah sbd zaifi nutsuwar karatun idan yasan yarsa yanzu tana tareda mutane nagari zai ringa zuwa makaranta hankali kwance yadawo yaje aiki.
MAMUH
ZAFAFABIYAR
AYSHATOUH INAYAH
LOVE/ROMANCE#[10/13, 4:51 PM] +234 703 121 9749: Mamuhgee 7
Arewabooks@Mamuhgee
Washe gari asubar fari yatada ita suka nufi bandaki tun kafin sauran jamaar gidan su firfito,
Fara wanke bandakin yayi tas bayan ya tsayar da ita gefen wajen bayin inda ruwan bazai taba taba.
Yana cikin wankewar jamaar gidan Yan son banza suka fara fitowa da duhun asubar sbd su samu sauran tsaftar Albarkacin Inayah.
Baban habiba ne agaba da qatuwar butarsa ya nufi bayin yaja ya tsaya daga gefe sbd sanin daga Inayah har Abbin nata basa rabar mutane.,
Yana tsayuwa oga Abdul Ganiyu ya iso da nasa qatoton cikin riqeda bokiti ya tsaya shima.
Fitowa Majeed yayi daga bayin da fitilarsa Mai tsananin haske ya kallesu Dan yasaba ganinsu kowacce asuba sune manyan Yan jiran banza a gidan sauran Basu qarasoba tukana.
Inayah ya kalla tareda kamo hannunta ya dan janyo daga jikin bangon datake tsaye ya miqa Mata fitilar tareda qatuwar butarsa ta roba shikuma ya daukar Mata bucket din ruwa suka shiga ya ajiye Mata ya fito.
Tsayawa yayi bakin kofar daga nesa kadan
Sai alokacin ya Dan kalli su bbn habiban a natse ba sauti sosai ya musu barka da asuba.
Baki washe suka karba suna masa sannu da kokari na wanke bayin.
Suna tsaye a gurin Daya bayan daya jamaar gidan masu son amfani da bayi lokacinda yakeda tsaftarsa suka firfito sukazo suka bi layi sbd gari na Gama wayewa kowa yafara kaida kawo cikin mintuna ashirin bayin gidan zai masifar rikicewa a lalatasa gabaki daya sai Mai hakurin qazantane kawai zai iya Shiga
Shiyasa da yawansu Allah Allah sikeyi siga Majeed yadawo gidan zaiyi amfani da bayin kokuma ‘yarsa zatayi shiga
Take zasu fara shirin Yana fitowa su Shiga sbd tsafta.
Hankali kwance a natse tayo wankanta da sabulunta na Dettol da soso Mai taushi tayo alwala ta fito saida ya rakata har daki ta shige kafin yadawo ya shiga yafito yayi alwala ya fice zuwa masallaci da har an tada sallah.
Sam babu mutum daya a gidan daya yarda dashi akan ‘yarsa datake ‘ya mace,
Bama gidan ba kawai ko makaranta koyaushe cikin nanatawa yaganah kular masa da ita yake,
shiyasa qafarsa qafarta duk inda zasu sai idan yaje gun aikine tana gurin yaganah wadda itama take taka tsan tsan da Inayan ganin Mahaifinta yanda Sam baya sake ko Wasa da al’amarinta tako Ina.
Vaseline na Dettol dake ajiye akan qaramin tebir da kayan shafarsu da wasu daga cikin litattafan abbinta dake Kai ta dauka tareda komawa ta zauna bakin katifarta ta fara shafawa a natse ga sauran baccin dakecin idonta Amma dayake tafara sabawa da tashin asuba tunda tayi wayo abbin ke tada da asuba kullum shine saukinta,
Sama sama tagama shafa Vaseline din Bai wani shafu ba sbd tasaba abbinta ke Mata makomai yanzu ne dai take su wanka da shafa Mai da kanta tareda saka Kaya duk da hakan haryanzu wasu lokutan shine yake saka Mata wasu kayan Idan takasa sanyawa daidai.
Qaramin body mist dinsu ta shafa kafin ta Sanya vest da qaramin zaninta na atampa ta saka hijab tayi sallah tana gamawa tun kafin Abbin yadawo Takoma ta kwanta sbd bacci takeji sosai Kuma Yana shigowa karatun zai sakata suyi dan haka da wuri ta koma baccin.
Acan masallaci ana Gama sallar yayi adhkar da adduoinsa ya fito sbd da wuri yake dawowa Idan yafita sallah idan har yasan a daki yabarta ita kadai.
Kallonta yayi Kai tsaye Yana shigowa yaga harta koma bacci
Dan haka ya kyaleta ya dauki nasa kayan wankan ya wuce gurin wanka.
Saida yakuma wanke bayin kafin ya shiga yayo wankan ya fito yadawo daki ya shirya fes cikin blue polo shirt da baqin wando.
Qaramin gas dinsu daya siya kwanakin ya janyo ya fito dashi kofar dakin ya kunna ya Dora ruwan zafi.
Dakin ya dawo ya dauki Yan canjinsa dake aje kan table din dakin ya fita.
Raba mutane ya ringa Yi Yana wucewa sbd kusan kowa yatashi gidan anata hada Hada,
Masu sana’a nata hidima da kokarin hada sana’arsu akan lokaci,
Masu fita aiki da hidimar yau da kullum Suma sai kaida kawon Shirin fitar sukeyi,
Masu zaman banzan gidan qalilan ne
Daga ‘yan Mata biyu masu zaman kansu suna kawo mazan dasuka ga dama sai dattijuwa iya kande dake sana’ar zaune wato saka ido da kayan Mata saikuma baban habiba da shima baya fita nema ko sana’ar komai sai ta saka idon shima Amma bayan su duka jamaar gidan suna fita nema da sanaa.
Shagon kofar gidan ya Isa ya tsaya daga gefe sbd mutanen dake ciki su rage.
Mintuna uku ya dauka a gurin kafin suka Dan rage ya qarasa yayiwa Mai shagon sallama a natse.
Cikin washe Baki hafizu Mai shago ya amsa sallamar Yana cewa”
Barka da safiya Baban Inayah
Ina kwana?antashi lfy?
Ya Inayah?
A taqaice ya amsa da kalmar
“Lafiya kalau alhmdlh”
Dari Biyar ya miqa masa yace”
Bread daya zakaban da Kwai biyu.
Cikin sauri kuwa ya hada masa abinda yace din a Leda ya miqo masa tareda sauran canjin Yana cewa”
Mu wuni lfy baban Inayah.
Amin nagode Mal hafizu.
Ciki yadawo ya fara juye ruwan zafin a cup babba ya maida sauran ruwan ya dafa Mata indomie da dafaffen qwai ya juye a qaramar kularta ta makaranta ya saka Mata a basket tareda cika Mata robar ruwanta mahadin kular ya jefa Mata biscuit din digestive daya ya ajiye gefe sai alokacin ya tada ita ta fita bakin kofar dakin nasu tayi brush ta wanke fuska sukaje tayo fitsari tadawo tayi Shirin makaranta suka Sha tea kafin suka fito tana biye dashi Kamar cingum yanda wasu ke kiranta akan baban nata.
Gurinsu yagana suka nufa Dan gaisawa dasu kafin ya wuce Dan haryanzu baya Bari yagana ta wuce masa da ita kullum safiya saiya kaita yake wucewa aikinsa saidai suk hade can.
Cikin yanayi suka samu su yaganar sbd jikin malam din daya tashi jikin dare da zazzabi ya kwana Mai qarfi.
Cikin kulawa yai masa ya jiki kafin ya ciro dubu daya ya miqa Mata yace”
Yaganah ki kokarta asamo adaidaita saiki kaisa asibitin Zan Kai INAYAH makaranta daga can Zan biya gurin aikin saina bada uzurinda Zan sameku asibitin muga abinda Allah zaiyi.