INAYAH COMPLETE HAUSA NOVELINAYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

INAYAH 1-10

Lokacinda ya fara Bata kudin sosai ta nuna masa Rashin Jin dadinta sbd sune suka taimaketa bawai itace take taimakonsu ba,

Kai tsaye ta nuna masa Karya Kuma nuna mata kudi da sunan biyanta akan zaman datake da Inayah harma dashi..

Ganin ta nuna Rashin Jin dadin hakan sosai yasa Bai Kuma tinanin Bata dinba Amma Kuma bayajin ya nutsu da Rashin Bata Wannan haqqin nata Dan haka cikin dabara ya jata banki ya bude Mata account batareda ya sanar da ita asalin dalilin hakan ba,duk wata Yana Sanya Mata 3k a account sbd shi mutum ne da bayason haqqin kowa akansa,
Bayason Alfarmar mutane sbd Rashin yarda da kowa musamman akan sha’anin da duk ya shafi Inayah duk da yaganah ta musamman ce a rayuwarsu yanzu,
Tsananin qauna da shaquwar dake tsakaninta da Inayah yasa tasamu matsayi Mai girma a idonsa harma da wani bangare mai girma na zuciyarsa.

Haryanzu dasuke rayuwa da Umma yaganah shine maiyiwa Inayah wasu abubuwan Kaman koyaushe Idan zata Sanya Kaya tafi zuwa gurinsa ya zabar Mata Wanda zata saka,
Shine suke Cin abinci tare kaman yanda tasaba hakama bacci a dakinsa Saida Umma Yaganah tayi da gaske kafin suka samu ta daina kwana gurinsa sbd wani irin Sabone datayi da hakan tun tana jinjira tareda Mahaifinta take bacci harta Wannan girman shiyasa takasa sabawa da rayuwa ba gurinsaba.

Shi kansa duk dare ya ringa haske haske fitilar wayarsa Yana leqowa dayaji motsi sbd duk inda yake bayajin cikakkiyar nutsuwa Koda rana Koda dare Idan baya ganinsa guri daya da ita,

Allah ya sanyosa cikin irin iyayenda sukeda wata irin taka tsantsan akan tarbiya da safety na rayuwar ‘yayansu,
Sam Sam bayada yarda ko nutsuwa akan komai indai gameda ‘yarsa ne Cikinma ahakan yasamu nutsuwa sosai dakuma yarda matuqar sosai da Umma yaganah.

Umma yaganah tun Bata iya rayuwar Majeed dinba harta iya ta karance komai nasa musamman tsaftarsa dake wahalar da ita farko Amma daga baya ta saba shiyasa yanzu take tsananin Jin dadin rayuwarta dasu hankali kwance su ci Mai kyau da lafiya su Sha Mai kyau da lafiya.

Kullum safiyar fari yana dawowa masallaci yake ficewa morning jogging (gudun safe),
Koda yake dawowa Inayah tagama Shirin makaranta zai rakata makarantar yadawo yayi wanka wata ran ya tsaya yaci abinci kafin yafita wataran baya tsayawa sbd kaucewa lattin Isa gurin aiki,

Baida wani Abu dake gabansa bayan jajirwa tuquru akan aikinsa sai kulawa da gidansa,

Bayada aboki ko daya a yanzu,
Baya doguwar mu’amala da kowa data wuce ta aiki saita gaisawa da Yan gajerun abubuwan da baa rasaba na mu’amalantar mutanen.

**
Ansamu cigaba ta bangarora da dama na rayuwarsu Wanda ciki ya hada da sauyawar gidan dasuke ciki zuwa mai kyau da yalwa da tsari sbd yanzu Inayah nada nata dakin,
Shima Abbin yasake zama magidancinsa sbd yazama baban matashiyar budurwa ga Kuma tarin aiki da masters dinsa dayake kammalawa takardun kawai suka rage masa Kuma da yardar Allah Yana karba zasu bar Nan sbd komai nasu yagama kammala.

Daga Boko Inayah Umma yaganah ce ke zuwa su dawo tare yanzu sbd shi aikinsa baya barinsa dawowa ya rakota gida shiyasa umman ke zuwa yanzu,
Inayar tayita fushi tana nuna batason ana zuwa dawowa da ita Amma Abbin yaqi daina rakata hakama yaqi Bari Umma yaganah ta daina zuwa dawowa da ita duk da ta girma sosai suna kiris da shiga SS 2
Qawayenta har dariya suke Mata suna kiranta da ‘yar Abbi da Umma yaganah,
Wasunsu Kuma burgesu abin yake sbd ganin yanda da girmanta ma Mahaifinta Bai daina ji da itaba ko Dan batada qanne ne wata kila,
Gashi baya Bata kudi ko kadan duk abinda takeso ko buqata shine yake siya Mata Amma baya Bata Kuma baya Bari ana Bata.

Lokacinda period yafara zuwar Mata yazo Mata a yanayi Mai zuwa da ciwon Mara Dan haka hankalinsa yayi matuqar tashi musamman wata na biyu da abin zai sake zuwa saiyafi na farkon sbd na farkon Bata wani wahalaba gashi umma yagana ma Bata tsaya fada masa ko meneneba kawai dai ya dauka zazzabine tayi ta Kuma warke,
Amma Wannan watan dayaga yanda take zuba amai tana kukan ciwon Mara hankalinsa tashi yayi damuwa sosai kan fuskarsa.

Asibiti ya dauketa suka kaita sai acan likita ke masa bayanin menene ciwon,

Da farko Bai Gama ganewaba sai daga baya Umma yaganah tasake masa budadden bayani akan jinin haila ne Inayar tafara.

Tsit yayi Yana kallon kofa da fararen idanuwansa zuciyarsa na Dan yin nauyi sbd wani matakin girman ne Inayah takuma hawa yanzu tarbiyarta da kula da ita zaifi hatsari.,

Shi gabaki dayama Banda Umma yaganah tai masa bayani baiwani San yayane Mata ke wannan al’amarin,
Sam bayada sani ko kadan akan Mata da yanda suke su irin wannna din duk kuwa da yanada ilimin addininsa daidai gwargwadonsa Amma Sam baida sani anan, a ilimance a al’adance a rayuwance ma Dan haka Koda suka dawo gida gurin aiki yakoma
dazai dawo yazo Mata dasu pads daga gurin aikinsa,
Dazai siya dinma Dole cikin ma’aikatansu Mata wata ta zabar masu masu kyan ya siya yazo dasu yabawa Umma yaganah,
Su panties Bai siyaba sbd yasan koyaushe cikin siya Mata undies sababbi yake sbd kiyayewa da tsaftarta.

Tun daga Wannan lokacin duk wata haka ake fama da ita har aka samu ta saba ta iya danne ciwonta idan lokacin period din yayi tadawo ma bamai sanin lokaci yyai tayi ta gamawarta sabanin farkon da duk wata Abbin yasan lokacinda takeyi sbd yanayinta da wuyar datake Sha.


Shekara daya da Gama masters dinsa komai nasu yagama sauyawa tako Ina,

shekaru sun qaru sun fara zama manyanci,
Arziki ya fara zaunuwa ta hannu ta banki,
Hakama rayuwa ta sake budewa tako wane fannin sbd tuni yabar mall a asalin kamfanin yake aiki kuma a babban matsayi yafara zama sbd qualification dinsa da zurfin Aiki da iliminsa dayakeda.

Da farko sosai Yaso samun matsala sbd Yan hassadar zuwansa da finsu matsayi da yayi
Hakan ya haifar masa da matsala sosai har yaji yafara gajiya da gurin aikin musamman sbd bayason Al’amarin damuwa da tashin hankali.

Ta wani bangaren yanata samun invitation na offern aiki daga guraren dayayita neman aiki dasu tun wancan lokacin
Yanzu sai babban matsayi Mai kyau suke masa tayi Amma dai sbd halacci ya zabi ya zauna Nan din Amma al’amarin Yana neman gagara.

A gida sbd lokaci girma sosai dayazo masa yasa yanzu akwai qarin ganin girman juna sosai fiyeda da tsakaninsa da Umma yaganah sbd yanzu yafara wuce matsayin matashi Dan haka ganin girman tsakaninsu yafara qaruwa Amma dai ita sakewa har lokacin akwaita sosai tsakaninsu Bata sauyaba.

Inayah kuwa haryanzu shaquwarta da abbinta saima abinda ya qaru sbd yanzu ma kusan itace ke gyara bagarensa duk da sunada Mai aiki dake zuwa tayi aiki Takoma gida sbd Abbin dayace Umma yaganah tasa asamo sbd Inayah karatu take bayason tana tsayawa aiki,
Hakama itama Umma yaganar yakamata ta huta a rayuwa yanzu tunda an bautu iya bautuwa yanzu hutu yazo ahuta tunda Allah yakawo damar.

Daga Umma yaganah sai Inayah ne kawai suka San abinda yakeso dakuma abinda yafi buqata Dan haka acikin akwai Mai aikin gidan har lokacin Umma ce kawai ke girkin dayake ci hakama Inayah ce yanzu ta karbar Mata gyaran palonsa zuwa dakinsa duk da dama can bedroom dinsa ne kawai Umma yaganah bata shiga Inayah ce kawai Mai shiga shima Idan bayanan datai girma yanzu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button