
Zama Inayah tayi gefen umman tareda yamutsa fuska tana kokarin yin magana umman ta katseta tana cewa”
Abbinki kinfi kowa sanin fadan bacin ran dazai nuna Idan yasan kina skipping ranakun zuwa school,
Banason bacin ransa akan Rashin dalilinki.
Kai Umma yaganah Abbi fa idan yaji abinda ya hanani zuwa bazaiyi fada ba.
Inayah please Mana,
Ki daure ki cire Rashin son makaranta a ranki bayan kinsan Abbinki yanada riqaqqen raayi akan son karatunki.
Bari sai Akira likita tazo ta sake duba fuskar taki,ok?
Gyada Kai tayi tareda miqewa tana kokarin barin dakin tace”
Good morning,ban gaishekiba Dana shigo.
Wani qayataccen murmushi Umma yaganah ta sake tana kallon fatar wuyan Inayar dake bayyane tana sheqi sbd yanayin rigarta cikin Yar dariya tace”
Barkanki da safiya kema Inayah Majeed.
waiwayowa tayi ta kalli Umman tana Yar murmushi sbd friends dinta ne masu Kiranta Kai tsaye hakan Amma ko umman sau tari hakan take kiranta itama.
Dining ta nufa ta zauna hankali kwance Tasha black tea da toasted bread biyu da kwai ta tashi tabar gurin ta nufi dakinta tana sake Danna Kiran Mahaifinta dataketa Kira tun dazu takasa samunsa sai yanzu Kiran yashiga.
***Zaune yake a palon madaidaicin duplex dinsa dake Singapore tareda CM Nuradden Aminin huldodinsa suna meeting akan aikin da zaaiwa sabon kamfaninsa da aka bude reshensa a portharcourt Nigeria.
Kan couch Mai zaman mutum biyu yake zaune sanyeda sky blue English kaftans masu tsananin taushi da tsadar dake bayyane.
Wayarsa dake gefensa ajiye ya waiwaya a natse ya kalla ganin hasken data kawo alamar shigowar Kira ko saqo.,
Fararen idanuwansa yafara Dan juyowa ya kalla CM Nuradden dasu Ahankali cikin nutsuwa yace”
One minute.
Hannunsa yakai ya dauki wayar kai tsaye tareda kaiwa kunnensa cikin nutsuwar murya da Allah yayi masa Mai tattareda kamewa saidai kasancewar ‘yarsa ce tilo datafi masa kowa da komai daya mallaka a duniya ahakan muryar tasa a bayyane take da kauna da kulawa
Kai tsaye ya furta”
Yes,INAYAH.
wata ajiyar zuciya ta sake tana zama bakin gadon dakinta cikin tsananin kauna da kewan mahaifin nata tace”
Good morning Abbi.
Ahankali ya dago fararen idanuwansa ya kalli agogon Patek Philippe dake daure a hannunsu ya maida idanuwanta ya dan kalli CM Nuradden
yasan Inayah zataci lokacin magana dashi sosai Dan Kuma CM flight zaibi yakoma Nigeria zuwa 11 dan haka Kai tsaye cikin nutsuwa da kulawa yace”
Morning Inayah,
Kintashi lfy?
Lfy kalau,
Abbi haryanzu kana Singapore?
Yaya aiki?
When are you coming back?
Cikin nutsuwa ya amsa ta da cewa”
Inayah Ina magana da CM yanzu,
Anjima I will you back,ok?
Ki kula,Ki gaida Umma yaganah.
Ok Abbi sai anjima.
I miss you.
Kashe wayar yayi tareda ajewa gefensa kafin ya dago ya kalli CM dake jiransa dan harya fara shiga yanayi na damuwa sbd sanin wayar Inayah ga mahaifin nata sai tasa a rasa meetings masu mahimmanci dazasu kawo manyan dukiya da dama Dan ansaba
Indai akan Inayah ne AA MAJEED nada raunin duba al’amura da dama masu mahimmanci Kuma hakn wani al’amarine da kusan duk wnada yake hulda ko mu’amala dashi yasani,
‘yarsa Inayah itace Rauninsa da kowa yakasa sani duniya akansa sai Aminin nasa Cm Nuradden sai Kuma Umma yaganah sbd sune sukeda cikakkiyar shaidar yanda ‘yarsa take a Ransa fiyeda duk abinda yakeda,
Hakama ‘yarsa Inayar itace qarfin Rayuwarsa,
Duk Wannan arzikin da dukiya Mai yawan daya Tara basukai masa mahimmancin farin cikin yarsa na wuni daya ba,
Inayah da kanta tasan itace hasken rayuwar Mahaifinta kaman yanda itama kowa yasanta yasan Mahaifinta shine abinda Bata iya hada girma da tsananin kaunarsa da komai,
Shine Abbinta,shine mahaifi Uba Kuma mahaifi UWA.
Numfashi CM ya sauke ya sauke yana kallon A MAJEED din sbd ya dauka zaman jiran yagama wayar ya samesa ne saigashi Allah yasa yau A MAJEED din ya taqaita.
A MAJEED ya fahimci zullumin da CM ya shiga dan haka ya taqaita wayar
Cikin nutsuwa ya dauki takardun da zai saka hannu akai yafara signing Yana cewa”
Sauran takardun na AIA sa hannun Inayah zaa saka a takardun Amma ba yanzuba saita kammala karatunta tukuna so agama aikin kawai kafin lokacin.
Alright Inshallah.
Sai 10 suka rabu da CM bayan daya daga cikin ma’aikatansu yakaisa airport ya wuce.
11:30 shima yabi jirgi tareda secretary dinsa suka bar Singapore zuwa Australia.
****Badan tasoba haka tayi Shirin makaranta ta fice daga gidan zuwa school bayan tayi waya da qawarta da itama duk sunne ba wani son karatun sukeba sunfi ganewa Gayu da rayuwa kawai irin ta ‘yayan gata masu abin duniya.
Duk da Bata wani son karatun sosai bashi yasaka Bata maida hankali ga karatunba idan taje,
Wuyarta dama dai taje din sbd idan taje sosai take maida hankali ga karatun Kuma Allah ya taimaketa tanada qwaqwalwar daukan karatun sosai Dan ahakan Bata taba failing ba
Koyaushe tana samun grades masu kyau,
Kawai dai Allah Bai saka Mata wani son karatun bane
Abinda Allah yasaka Mata so shine Tanada shaawar yin aure kawai sbd ta daina zuwa makaranta tayi rayuwarta yanda taga dama daga shopping sai zuwa beauty parlor dasu spa sai yawan qasashen dataga dama.,
Ko yanzu kusan rayuwarta hakanne,
Batada wani aikin bayan yawon shoppings da zuwa su spa day guraren gyaran jiki sbd Bata hada gyaran jikinta da komaiba Wanda kusan hakanne yasa koyaushe fatarta da jikinta koina yake sheqin hutu da lafiya cikakkiya da zallar gyara na musamman,
Yawon qasashene Bata wani Yi sbd duk qasashen datake zuwa tareda Abbin take zuwa kokuma zuwa umrah ko Hajj tareda Umma yaganah Dan haka Bata wani samu tana yawon yanda takeso sbd haryanzu dasuka samu sauyin rayuwa mai tsananin nisa Abbinta baya barinta tana yawo yanda takeso duk da kuwa ba wani zama yakeyiba Amma dokarsa na aiki a gidan duk inda yake kuwa.
Hakan yasa takeson aure fiyeda karatu musamman ma auren irin na wayayye irinta dazai barta tayi rayuwar datakeso ta Rashin takura da damuwa kawai suyita soyayya suna shaqatawa sbd love na cikin abubuwan datake yiwa kanta shaawar samun kanta aciki hakanne ma yasa bayan abbinta da yaganah to Babu Wanda takeso sama da saurayinta Zaid.
Soyayyar Zaid tayi wani irin nisa a ranta Kaman yanda shima yake tsananin son Inayan,
Kusan yanayin rayuwarsu daya sbd shima iyayensa masu arzikine sosai Amma suna Nigeria Dan asalin portharcourt ne karatu yake a qasar,
Kaman yanda take wayayyar Yar gata girman turai hakan yake shima sbd tun Yana yaro shima kusan a qasahen turawan ya tashi tareda iyayensa sai daga baya Suka koma gida sukabarsa Yana karatu.
Dan haka da rayuwar Zaid tayi daidai da tata sai soyayyarsu takeda wani irin qarfi da shaquwa.
Abbinta yasan raayinta na Rashin maida hankali kan karatu yakuma san aurene takeso fiyeda karatun Amma yaqi nuna Mata ya sanin sbd karta sake samun damar nuna batason karatun,
Shikuma raayinsane riqaqqe dakuma buri akan bazatai mata aureba saita Gama karatun.
MAMUH
ZAFAFABIYAR
AA MAJEED
AYSHATOUH INAYAH
LOVE
ROMANCE
MARRIAGE
ZAFAFA BIYAR
INAYAH
MamuhGee
GURBIN IDO
Safiya Huguma
SANADIN LABARINA
Hafsat Rano
FARHATAL QALB
(Miss Xoxo)
BABU SO
Billyn Abdul
Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k
BREAKDOWN OF ZAFAFA BIYAR VVIP SINGLE PAID BOOK
4 BOOKS 4500
3 BOOKS : 3500
2 BOOKS : 2500
1 BOOK: 1500
YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS????????????????????????