NOOR AL HAYAT COMPLETEUncategorized

NOOR AL HAYAT 91-100 END

Umma” da haka suka bar gidan suka dau hanyar gidansu jawahir, can ma basu dade ba bayan sun yi ma Umman jawahir sallama suka koma gida. Da daddare ganin 

Aliyu xai takurata ta dinga turo baki tana kwace kanta jikinsa, ya kai bakinsa kunnenta murya can kasa yace “Baki son mu tafi da babynmu daga nan Iman” ta 

marairaice masa tace “Ni dai ka kyaleni bacci nake ji” yace “Plss” kukan shagwaba ta fara masa wanda hakan ya rikita sa, bai kyaleta ba sai da yaga ta fara 

bacci da gaske, ya fi awa daya kankame da ita, ko da yaushe jin abarsa yake intact, murmushi yayi ya manna mata kiss a lips daga karshe ya kwantar da ita ya 

shiga bathroom. Washegari suna breakfast tana kallonsa tace “Abban Shureim, Ina son mu je katsina mu gaida Uncle dina” ya kalleta yace “When, Kin san gobe 

da safe xa mu wuce” Tace “Toh idan mun dawo bikin su baby sai mu je?” Yace “A’a idan kin ce mu je yanxu ma sai mu je ai” ta langwabar da kai a hankali tace 

“Mu je plss” yace “Alryt then” karfe sha daya suka bar gidan, suka dau flight xuwa kano, daga can yayi masu charter na taxi da xai kai su har kt, tun da 

suka shigo kt misalin karfe daya da rabi na rana gaban khadijah ke ta faduwa, taxin ya ajiye su dai dai gidan kawunta, ita kanta tayi mamakin yanda ta gane 

gidan, Aliyu ya fito ita ma ta fito tana kallonsa tace “Mu shiga” Bin bayanta yayi suka shiga gidan, Babu kowa compound din da ya xama wani iri kamar gidan 

da yayi shekara hamsin, Har parlor ta isa da sallama Aliyu ya tsaya daga bayanta, kallon kawun nata dake xaune k’asa a one side of the parlor yana fama da 

ciwon kafa sosai tayi, ta kalli Hajiya maimuna da ta fito kitchen jin sallama ta gaisheta a sanyaye, daga ita har yaran dake parlorn kallonta suka dinga yi 

kamar basu santa ba, ita dai tasan basu gane ta bane, Ta isa har kusa da ita a hankali tace “Mama Khadijah ce” bude baki Hajiya Maimuna tayi tana kallonta 

da wani irin mamaki, Khadijah ta sauke idonta kasa, ba ita ba har kawu Jibril shi ma bude baki yyi lkci daya hanjin cikinsa ya kada don kullum da threat din 

Barrister Sudais yake kwana yake tashi, Aliyu ya xauna kusa da shi yace “Ina yini kawu?” Kawu ya kallesa yana maxurai yace “Lafiya lau daga ina, wa ku ke 

nema” Aliyu yayi kasa da murya yace “Ni ne mijin khadijah, mun xo gaishe ku ne kawai kawu” da sauri yace “Toh madalla… Gaisuwa ce kawai koh” Aliyu ya 

gyada masa kai yace “Eh kawu” khadijah ta karaso har gabansa ta durkusa kanta a kasa tace “Ina yini kawu?” Yace “Lafiya lau” Kai kana ganin yanda yake 

maxurai kasan duk a tsorace yake, Aliyu yayi murmushi yace “Ka kwantar da hankalin ka kawu, xumunci kawai ta sa ni in kawo ta tayi” Yana gyada Kai kamar 

kadangare yace “Madallah” Khadijah dai ta kasa cewa komai, bata taba xaton ganin Kawunta da iyalensa a halin da ta samesu ba, ganin gaba daya mutumin is 

uncomfortable Aliyu yace “Kawu xa mu koma yanxu, don gobe da safe xa mu wuce uk shine tace in kawo ta…” Kawu ya kasa kallon khadijah sai gyada kai yake 

yana cewa Madallah Kamar xararre, Dubu hamsin Aliyu ya ajiye gabansa, Kawu ya dauka yana kallonsa, lkci daya idanuwansa suka kada yace “Maa sha Allah, 

nagode nagode nagode Allah yayi albarka” Aliyu yace “Ameen” a sanyaye Khadijah tace “Allah ya baka lafiya kawu” hawaye ta gani idonsa amma yana ta boyewa 

bai son su gani yace “Toh Amin, sai a yayyafe….” murmushin karfin hali tayi tace “Nima ku yafe min kawu, Allah ya yafe mana baki daya” hatta Maimuna sai 

da tace da khadijah a yayyafe da xasu wuce, ganin bata ga kishiyarta ba tace “Mama Ina mamansu Usman?” Maimuna tace “Ta amshi takardar ta ta wuce kusan 

shekara kenan” khadijah bata ce komai ba duk jikinta yayi sanyi har suka bar gidan xuwa inda xa su samu mota xuwa kano. Sai bayan la’asar suka shigo kano, 

Khadijah sai bata fuska take irin ita ta gaji din nan, ya langwabar da kai yace “Toh ai we still have 3 more hours journey kike bata fuska madam” ta xaro 

ido tana kallonsa tace “Ni dai na gaji wllh” murmushi yayi yace “Just reserve this comment, xa su maki amfani anjima idan mun isa gida da daddare” Kallonsa 

kawai take kamar mai son gane ma’anar abinda yace, can tace “Kamar ya?” instructing din mai adai daitan da ya tsayar masu yyi yace “Airport xa ka kai mu” 

Khadijah ta turo baki ta shiga shima ya shiga yana matsa cinyarta a hankali, tayi kara tana kallonsa, dauke kai yayi da sauri yana murmushi, har suka isa 

airport idonsa na kan wayarsa da yake dannawa, ya siyar masu tickets na kaduna, hudu da rabi jirgin ya tashi, cikin few minutes suka sauka kaduna. A gajiye 

ta shiga parlor ta wuce dakinta direct ta fada kan gado, bayan kusan minti biyar ya bude kofar dakin yana kallonta yace “Sallahn fa?” Kallonsa tayi a 

hankali tace “Xan yi” yace “Toh tashi kiyi” Sai da ya idar da sllhn shi ma sannan ya fita eatry siyo masu abinci, yana dawowa ya shigo dakinta, xaune ya 

sameta kan darduma yace “Come down mu ci abinci” Tace “Sai na fara wanka” yace “Toh jira ni in xo muyi” mikewa tayi da sauri ta shige bathroom din ta sa 

makulli, yana dariya ya juya ya fita dakin. Karfe goma na dare tana kwance parlor kan 3 seater har bacci ya dauketa taji an dauketa kamar baby, ta bude ido 

a hankali tana kallonsa, ya manna mata kiss a lips dinta ya shiga bedroom dinsa ya kwantar da ita saman gado, ya kwanta shi ma ya shige jikinta… Kamar 

xata yi kuka tace “Bacci fa nake ji” yayi kasa da murya yace “Wai baki son mu tafi da tsaraban baby mai kama da ke UK ne?” Hararansa tayi ta juya masa baya 

tana turo baki, ya marairaice mata yace “Plsss Ummu Shureim” kukan shagwaba ta fara masa as usual, nan ta kara rikitar da shi, ita ma dai kamar jira take ta 

bada kai bori ya hau, they couldn’t just get enough of each other, ta kankamesa kamar xata koma jikinsa su xama daya, ya kai bakinsa kunnenta cikin sanyin 

murya yace “I love you Iman…” Shiru tayi idonta a lumshe, bayan wani lokaci ta kwanta kan kirjinsa a hankali tace “I love you more Abu Shureim” kissing 

dinta ya shiga yi, and that really turn her on. Da asuba tare suka yi wanka ya ja su sallah a dakin, a hankali ta dawo kusa da shi ta durkusa murya can kasa 

tace “Good morning Abu Shureim” ya jawota jikinsa yace “Morning Ummu Shureim….” Murmushi tayi tace “I am missing him” yace “You better don’t, shi din me 

iyaye ne da yawa, so kar ma ki wani sa shi a rai” shiru tayi bata ce komai ba, yace “Ki hada abubuwan da kika san xa ki bukata, anjima xa mu wuce airport” 

tace “But I have everything back there, a can gidana…” Kallonta ya dinga yi kafin yyi murmushi yace “Kina tunanin xan je gidan ki in xauna wife?” Shiru 

tayi tana kallonsa, yyi yar dariya yace “Lallai, I rather rent a new flat, balle ma muna da apartment can din, kawai I prefer staying a gun aunt dina ne 

saboda kadaici” murmushi tayi bata dai ce komai ba, sai dai ita ma hakan ya mata, coz she don’t think xata iya xama gida daya da su Khaleel, it’s just not 

possible, lakutan hancinta yyi yace “Kin fi son can ne saboda yar uwar ki” da sauri tace “Not at all, ur wish is my command sir….” Rungume ta yayi yace 

“That’s sweet of you baby”

A year and a half later….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button