NOOR AL HAYAT COMPLETEUncategorized

NOOR AL HAYAT 91-100 END

ta katse wayar ta, Sha biyu saura suka dau hanyar gida tare da Safeenah, Deejah da Maimoon, a waje drivern yayi park duk suka sauka motar suka masa godiya, 

khadijah ta bude gate din tana gaida mai gadi dake gaisheta shi ma, sauran duk suka gaisa da shi sannan suka bi bayanta, a hankali ta murda kofar parlorn, 

Babu kowa ciki sai sanyin ac da tv dake a kunne, ta shiga su Safeenah na biye da ita har cikin parlon duk suka xaxxauna, tana murmushi tace “Bari in kawo 

maku ruwa” Bata jira cewarsu ba ta wuce Kitchen ta dauko tray da cups ta bude fridge ta daura lemo da ruwa a kan tray din ta dawo ta ajiye masu, Safeenah na 

murmushi tace “Thanks sis” murmushin tayi ita ma ta wuce sama, a hankali ta bude kofar bedroom din Aliyu, xaune ta samesa yana operating laptop, ta hade rai 

tace “Baxa ka taho ku gaisa da su ba” ajiye laptop din yayi yana murmushi yace “I was waiting for ur instruction ne dama kar in yi laifi” hararansa tayi ta 

juya ta wuce, yana murmushi ya mike ya bi bayanta, har ya shigo parlorn yana kallon su Safeenah yace “Sannun ku da xuwa” duk suka gaishesa da fara’a, ya 

xauna saman kujera yana murmushi yace “Lafiya lau, fatan kun baro mutan gida lafiya” duk suka ce “Alhmdllh” yace “Maa sha Allah” sannan ya mike yana kallon 

khadijah ya koma sama, mikewa tayi tace “Mu je sama ku yi alwala it’s almost time for zuhr” tashi suka yi gaba daya suka wuce sama xuwa dakinta, sai bayan 

da suka idar ta cire hijab dinta tace “Let me cook something for us” mikewa suka yi gaba daya Safeenah tace “We will do that together” dariya kawai khadijah 

tayi, tuwon shinkafa da lafiyayyen veg soup suka hada gaba daya, aikin yayi sauri saboda yawansu, Safeenah na gama kwashe tuwon a leda tace “Toh ina xa a sa 

ma mijin ki” khadijah tace “It’s not necessary, namu ne kadai, nasan eatry xai je shi” Deejah ta saki baki tana kallonta tace “Eatry kuma Namecy?” Murmushi 

kawai khadijah tayi, Maimoon tace “Uhmm lallai ma, tun yanxu xa ki fara sakaci haka Khadijah?? Har kina son mijin ki ya tafi wani waje ya ci abinci” 

Kallonta khadijah tayi bata ce komai ba, Safeenah ta dauko wani kwali mai dauke da cooler mai kyau ta fiddo babba da karami ta tafi sink ta wanke shi tas ta 

tsane sannan ta sa tuwo ta rufe, Deejah ta dau na miyan ta xuba miya da isasshen nama a ciki ta rufe duk suka daura a tray, ita dai khadijah na tsaye tana 

kallonsu kamar an dasa ta, Maimoon ta dauko plate mai kyau da spoon da cup ta dauraye ta daura kan tray din, Safeenah ce ta hada xobon dake ajiye tun daxu 

suna jiran ya huce, xobon ya ji kayan kamshi da abarba da cucumber, ta xuba kananun kankara kan thick xobon, sabon jug ta dauko ta kusa cika jug din ta 

rufe, tana kallon khadijah tace “Sai ki kai masa daki, ko shi ma waitress din eatry xa su maki??” Khadijah bata san lkcn da tayi dariya ba sai dai bata ce 

komai ba ta dau tray din abincin da drink ta fita kitchen din ta wuce sama, a hankali ta tura kofar dakinsa, yana xaune yana danna laptop har sannan, ya 

dago yana kallonta har ta iso inda yake ta durkusa ta ajiye tray din ba tare da ta kallesa ba ta mike ta nufi kofa ya bi ta da kallo har ta fita, yayi 

murmushi sanin this might not be her thinking, infact it’s not even her thinking… Khadijah ce xata kawo masa abinci haka kawai, shafa kai yyi yana 

murmushi. Kafin ta koma kitchen din duk sun wanke duk abubuwan da suka bata, Maimoon ta fito masu da abincin nan tsakiyar parlor, Xaunawa suka yi gaba daya 

suka ci a tare, Deejah ta gyara wajen ta tafi da komai kitchen, suna ta xaune parlor suna hira khadijah ta dinga jin kamar kar su ce xasu tafi, ta dinga 

addu’ar Allah sa su manta kawai su kwana, suna nan a haka har aka kira la’asar suka wuce sama xuwa dakinta duk suka yi sallah, sai a sannan suka fara shirin 

komawa gida, duk jikin khadijah yayi sanyi ta xauna can karshen gado tana kallonsu a sanyaye, Dariya Deejah ta dinga mata, Safeenah na gama gyara fuskarta 

ta dawo kusa da ita tace “Kar ki damu sis xa mu dinga haduwa frequently in sha Allah kin ji, Kuma ga waya xa mu dinga communicating” hawaye ne ya cika idon 

khadijah, Safeenah tayi dariya tace “Tabb, to mu fa gobe da safe xa mu koma Abuja, Deejah kadai ce a nan, kema nasan soon xa ki koma uk saboda karatun ki” 

Ita dai khadijah bata ce komai ba, bayan duk sun gama Safeenah tace “I notice something khadijah, it seems har yanxu baki kwantar da hankalin ki da mijin ki 

ba, are you still thinking of the past koh? I will advice you to just erase that of ur mind idan ba haka ba baxa ki taba samun kwanciyar hankali gidan ki 

ba, nobody is above mistake khadijah, barin ma irin wannan mistake din da aka yi ba da gangan ba, wllh idan baki maida hankali kin rungumi mijin ki ba kina 

ji kina gani wata a waje xata yi hakan ga mijin ki very handsome gentleman, Wallahi Kar ki kuskura wata ta hango maki shi a waje, don rashin samun kulawa 

gun ki xai sa ya ba ta waje dama, Haba sai kace ba wayayya ba Khadijah…” turo baki khadijah tayi, Safeenah ta dawo kusa da ita ta kamo hannunta tace 

“that’s just it, kiyi hakuri ki xauna xuciya daya da mijin ki, forget the past, ni na tabbatar mijin ki yana son ki kema kuma kina son sa sosai” Khadijah ta 

sauke idonta a hankali, Maganganu sosai Safeenah ta yi mata da yasa duk jikinta yayi sanyi, daga karshe ta mike tace “Toh mu xa mu tafi khadijah sai mun yi 

waya” khadijah ta mike a hankali tace “Bari in gaya masa” daga haka ta fita ta shiga dakin Aliyu suka kusa cin karo don fitowa xai yi shi ma daga dakin, 

jawota yayi jikinsa ya rufe kofar yana kallon eye balls dinta, ta sauke idonta tace “Sake ni” ba musu ya saketa yana murmushi, tace “Xa su wuce” yace “I was 

thinking kwana xa su yi” ta girgixa kai tace “Gobe da safe xa su wuce Abuja” yace “Ohk ba nan suke ba dama?” Tace “Deejah ce kadai a nan” yace “Alryt am 

coming now” juyawa tayi ta fita, turarruka da kayan kwalliya na lefenta ta debar masu mai yawa suka sauka downstairs tana jin kewansu, ba a dau lkci ba 

Aliyu ya sauko, dubu talatin ya ba su gaba daya, suka ki amsa, khadijah ta hade rai ta karbi kudin hannunsa ta bude jakar Deejah tace “Ae ba ku kuka ce ya 

baku ba toh” Murmushi kawai Aliyu yake yana kallonta, suka masa godiya yace “No thanks sisters, or shud I drop you?” Safeenah tace “A’a mun gode xa mu tadda 

driver bakin titi” yace “Alryt then, Allah ya kiyaye hanya” duk suka amsa masa da Amin, har bakin gate khadijah ta rakasu, Maimoon tace “Kin ga ki koma haka 

mun gode sosai Khadijah, Allah bar xumunci” sai a sannan hawaye ya cika idonta cikin sanyin murya tace “I am going to miss you all” rungume juna suka yi 

gaba daya, tana ji tana gani suka wuce ta juyo ta koma ciki tana goge hawayen dake xuba mata, Aliyu dake parlor ya dinga kallonta har ta wuce sama. Ko minti 

talatin su Safeenah basu yi da barin gidan ba Barrister ya xo, Aliyu ya bude masa kofa suka gaisa, Barrister ya xauna kan kujera yace “Ya gidan” Aliyu na 

shafa kai ya xauna shi ma yace “Alhmdllh, ya aiki” Barrister yace “Mun gode Allah, ya mum shureim” Mikewa Aliyu yayi yace “She’s upstairs” daga haka ya wuce 

sama, bude kofar dakinta yayi ya ganta kwance ta rufe fuskarta da pillow, ya isa kan gadon ya xauna kusa da ita ya dagota a hankali yace “Ummu Shureim” Bude 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button