NOOR AL HAYAT COMPLETEUncategorized

NOOR AL HAYAT 91-100 END

da ido, Har suka shigo kaduna, Daga khadijah har Aliyu duk jikinsu a sanyaye yake, tuni Shureim yayi bacci bayan motar, Aliyu na gama parking ya juya yana 

kallon khadijah da ta bude motar ta fita, fitowa yayi shi ma ya bude back seat ya fiddo Shureim, ya rufe motar ya bi bayanta, bedroom dinsa ya shigar da 

Shureim ya kwantar da shi, ya fita ya shiga dakin khadijah, kwance ya sameta tayi lamo jikin pillow, ya xauna gefenta yana kallonta, ita dai bata yarda ta 

kallesa ba, kamo fingers dinta yayi yace “You need not to worry this much Iman, kin san condition din ki fa” Bata san lkcn da ta fashe da kuka ba ya dagota 

ya rungume ta, ta kwantar da kanta kirjinsa tana shesshekar kuka, murya can kasa yace “Kiyi addu’ar Allah ya basu lafiya Iman” Sun fi minti biyar a haka, Ya 

dago kanta a hankali yana kallonta, rufe idonta tayi, yyi murmushi yana kallon cute lips dinta, kamar tasan me yake yi ta kwace kanta ta mike ta koma can 

karshen gado ta kwanta, shafa kansa yyi yace “Ki tashi kiyi sllh” daga haka ya mike ya nufi kofa ta bi sa da ido har ya fita, throughout ranan haka khadijah 

ta kasa samun natsuwa, Aliyu yayi lallashin har ya gaji, duk ta 6ata mood din little Shureim ma, Bayan magrib ya dawo masallaci ya shiga bedroom dinsa dai 

dai lkcn da wayarsa ya katse, karasawa yayi ya dauka yaga Mumy ce ta kirasa, ya xauna gefen gado ya shiga kiranta, tana dagawa yayi mata sallama, jin 

yanayin muryarta a hankali yace “Mumy baki da lafiya ne?” Mikewa yayi yace “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” lkci daya ya ajiye wayar ya koma ya xauna ya 

rike kansa, bai san lkcn da hawaye ya dinga xuba idonsa ba, ya fi minti biyar a haka kafin ya mike da kyar ya share idonsa ya dau makullin motarsa ya fita 

daki, yana ta tsaye corridor kafin ya bude dakin khadijah xaune ya ganta kan darduma ta jinginar da kanta da gado, Shureim na xaune kusa da ita, kasa 

karasawa cikin dakin yayi yana daga bakin kofar yace “Iman xa mu je can gida yanxu” ta kallesa kafin tace komai har ya juya ya wuce, a tunaninta gaida Mumyn 

xa su je su yi, ta mike ta linke pray mat din ta ajiye, ta kama hannun Shureim suka fita bayan ta kashe wutan dakin, ganin yanayin Aliyu ta kallesa da 

damuwa tace “Ko dai wani abu ya faru ne?” Yana driving idonsa kan titi yace “Nothing” har suka isa gida bata sake cewa komai ba, yayi parking ya fito ita ma 

ta fito tana rike da shureim suka bi bayansa, sosai gabanta ya fadi ganin mutane a parlorn, Aliyu ya isa gun Mumy ya durkusa gabanta, khadijah ta kasa 

karasawa xuciyarta na bugawa, upstairs ta wuce xuwa dakin baby da sauri, baby na ganinta ta fashe da kuka sosai, cike da karfin hali khadijah ta durkusa 

gabanta tace “Me ya faru baby” Baby tace “Iklima…” Hawaye ya shiga sakko ma khadijah ta hade kanta da gado tana salati a ranta. Daren ranan a gidan suka 

kwana gaba daya, mutuwar Iklima ya girgixa kowa barin khadijah da Baby, da ta tuna yanayin da suka sameta daxu da rana sai taji hawaye ya ki tsaya mata ashe 

mutuwa xata yi, gashi ko magana bata samu ta mata ba saboda tashin hankali, babu wanda ya wani rintsa a gidan har asuba. Washegari da safe Umma suka xo 

gidan da Nanny don yi ma Mumy gaisuwa, da Umma ta tashi tafiya Shureim yace xai bi ta, haka Umma ta wuce da shi don har da kukan sa, sai bayan da aka yi 

sadakan uku Khadijah da Aliyu suka koma gida da daddare, har sannan shock din bai bar ta ba, har ranta taji ta yafe ma Iklima don ita a iya tunanin ta ma 

bata mata komai, ajiye abincin da Mumy ta basu su tafi da shi tayi a nan tsakiyar parlor ta wuce sama Aliyu da ya bi ta da kallo yace “Iman” juyowa tayi 

tana kallonsa, yace “Baxa ki ci abincin ba” ta girgixa masa kai, yace “Ba fa ki ci komai tun daxu ba” Bata ce komai ba ta haura sama, kitchen ya shiga ya 

dau plate ya wanke sannan ya dawo parlorn ya bude abincin ya dibar mata ya rufe sauran ya wuce sama, kayanta ya sameta tana cirewa, tana ganinsa ta durkushe 

kasa da sauri kamar xata yi kuka tace “Baka iya sallama ba ne” d’an murmushi yayi ya sauke idonsa daga kallonta yace “Yi hakuri” ta turo baki tace “Ka ajiye 

ka tafi” Ajiye mata abincin yayi ba tare da ya kalleta ba ya juya ya fita, zani ta dauka ta daura ta xauna kusa da shinkafa da miyar da ya ajiye mata ta dau 

spoon din ta fara ci a hankali, Bata wani ci da yawa ba don har sannan bata da appetite ta mike ta shiga bathroom, sai da ta wanke bakinta sannan tayi wanka 

ta fito, Hijab ta sa ta dau sauran abincin da ta rage ta fita da shi ta dawo dakin, ta dau lkci xaune gaban madubi tana shafe shafenta ya bude kofar, xaro 

ido tayi ta duka, ya koma da sauri yace “Ohh sorry, Assalamu alaikum…” Tayi saurin daukan hijab dinta ta sa ganin har ya sake shigowa ta hade rai tace 

“Bana son haka Aliyu, ba sai an amsa ake shigowa ba” dariya ta basa sai dai bai yi ba, ya mika mata wayar hannunsa yana kallonta yace “Gashi Dr Ayman xai 

maki gaisuwa” ta hararesa ta karba wayar tace “Toh ni ka fita” juyawa yayi ya fita dakin, ta kai wayar kunne, muryar Khaleel taji yace “Uhm lallai, ya fita 

koh?” Murmushi tayi murya can kasa tace “Ina yini Doctor” yace “Lafiya lau khadijah, ya gida?” Tace “Alhmdllh, ya jawahir” yace “She’s fyn, ya karin 

hakuri?” A sanyaye tace “Mun gode Allah” yace “Allah ya mata rahama” tace “Ameen mun gode” yace “Maa sha Allah, good nyt” tace “Alryt, my regards to 

jawahir” yace “In sha Allah” daga haka ya katse wayar, ta ajiye gaban madubin ta mike ta cire hijab dinta ta dau kayan baccin da ta fiddo ta saka, ta linke 

Hijab dinta ta ajiye sannan ta kashe wutan dakin ta kwanta, har bacci ya fara daukanta taji an bude kofar dakin ta bude ido da sauri, tana ji ya rufe kofar, 

Bai kunna wutan ba yana tsaye daga inda yake a hankali yace “Iman, wayana fa?” Shiru tayi bata ce komai ba, ya fi minti daya tsaye kafin ya juya ya fita a 

hankali ya rufo mata kofar, sai a sannan ta mike xaune, tana ta xaune kan gadon kafin ta sauko ta tafi gun mirror ta dau wayarsa ta saka hijab ta fita, a 

hankali ta bude kofar dakinsa ta shiga.

Ta fi 10 seconds a tsaye ganin babu haske a dakin, bata kunna wutan ba saboda akwai d’an hasken na corridor kuma a bude ta bar door din, ta nufi gaban 

mirror a hankali don ajiye wayar hannunta, lkci daya ta juya jin an rufe kofar dakin duhu ya gauraye ko ina, saurin ajiye wayar tayi ta nufi kofar tana cewa 

“Why is that….” Xaro ido tayi ganin kamar nufota yake yi ta dinga komawa baya kamar xata yi kuka tace “Meye haka Aliyu, ka bude min kofa in fita, I only 

brought you ur mobile phone” murya can kasa yace “Why did you pretend you were sleeping” jingina tayi da banga xuciyarta na bugawa ta marairaice tace “Laifi 

ne don na kawo maka wayarka? to ka bani in mayar I thought you need it ne dama” Yana d’an murmushi yace “Better… dauka ki mayar” tace “Toh ka matsa” a 

hankali ya koma gefe idonsa a kanta, ta taho xata wuce gabanta na faduwa kawai ta ji ya fixgota xuwa jikinsa ya rungumeta gam, jikinta ya dau bari tace 

“Wayyo na shiga uku, meye…” Bai bata damar karashe abinda xata ce ba ta xaro ido tana kallon kwayar idonsa, passionately yake kissing dinta, tun tana 

kokarin kwace kanta har tayi give up, lkci daya jikinta ya mutu gaba daya ta ji ta kasa tsayuwa, bata ankara ba bayan lokaci me tsawo sai ganin su ta tayi 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button