NOOR AL HAYAT COMPLETEUncategorized

NOOR AL HAYAT 91-100 END

lokacin ki yayi Anty” Ita dai bata ce komai ba sai kukan takaici da danasani da take yi, ganin kukan da khadijah take, Anty khadijah tace “Ku tafi Aliyu kar 

in bata maku mood, Allah maku albarka, ya kuma kaddara saduwar mu” Yace “Ameen mun gode, xan dawo nan da kwana biyu” tace “Allah ya kai mu nagode” Gun 

Barrister ya nufa yana kallonsa yace “xa mu koma Barrister, Allah ya bada lada” Barrister yyi murmushi yace “Ameen, Allah kai ku gida lafiya” Dawowa yyi ya 

kama hannun khadijah da kamar daman jiran hanyar kuka take suka fita dakin bayan ta daga ma Barrister dake murmushi hannu. Baby bata iya tace masu komai ba 

duk jikinta yyi sanyi, Aliyu ya kama hannun Shureim dake ta kallon uwarsa da damuwa ganin kuka take yi, ya bude back seat ya sa shi a ciki, ya bude mata 

front seat, shiga tayi tana goge hawayen dake xubo mata, ya rufe motar yana kallon baby, a sanyaye tace “Allah ya tsare hanya yayanmu” yace “Ameen, tare ku 

ka xo da Barrister?” D’an murmushi tayi bata ce komai ba, yayi dariya yace “Nasan rakiya kawai yayi koh?” Dariya tayi bata ce komai ba, yana murmushi ya 

xaga ya shiga driver seat ya ja motar suka fita asibitin, Shureim na kallonsa kamar xai yi kuka yace “Uncle why is Anty crying?” Aliyu ya kalleta yayi 

murmushi yace “Allura aka mata” Shureim ya fashe da kuka yace “Me yasa uncle” parking Aliyu yyi ganin kukan da yaron yake, yana kallon khadijah yace “Kinga 

dama idan ba neman hanyar kuka kike ba toh ya ishe ki haka Iman” ta balla masa wani Harara tace “Toh ina ruwanka, hanyan nake nema dama” murmushi yayi, ya 

kwantar da murya yace….

✨ *NOOR-AL-HAYAT*✨

 Ya kwantar da murya a hankali yace “Haba my Ummu Shureim…” turo baki tayi ta dauke kai tana goge idonta, ya juya yana kallon shureim, murmushi yayi yace 

“Toh kaga tayi shiru kai ma kayi shiru” Kai ya gyada masa yana kallon mum dinsa, ya dawo kusa da ita a hankali yace “Anty kiyi hakuri” kallonsa tayi, tayi 

d’an murmushi tace “Toh na yi” komawa yayi ya xauna, Aliyu ya tada motar ya ci gaba da driving, murya can kasa yace “Mu bari next time sai mu je duba 

iklima, coz i really don’t have the energy to start consoling you again” tace “Ni ka kai ni yanxu, ba wani next time, I will be going back to schl soon” 

murmushi yayi yace “Ohk then” hanyar family house din su iklima Aliyu ya dauka, bayan minti kusan sha biyar suka isa babban gidan, yayi parking a waje suka 

shiga, yan gidan basu wani tarbe su ba, hakan bai wani dame Aliyu ba, ita dai khadijah jikinta yayi sanyi, autar su mahaifin Iklima ta nuna masu wani kofa 

tace “Tana can” Aliyu ya mike yana kallon khadijah ita ma ta mike, Shureim xai tashi ya duka ya dafa shoulder dinsa a hankali yace “You wait for us here 

sweetheart ka ji?” Kai Shureim ya gyada masa ya koma ya xauna, Aliyu ya nufi kofar dakin khadijah ta bi bayansa gabanta na faduwa, ita kadai ce kwance dakin 

mai dauke da yar katifa ko leda babu, katifar ma babu xanin gado, da ganin dakin babu me shiga ciki, Ga cup da plate da spoon dinta nan gefen gadon, da 

kadan iklima ta fi skeleton kwance a kan gadon, khadijah ta kasa karasawa cikin dakin tana iya kokarin ganin bata fashe da kuka ba ta toshe bakinta, Aliyu 

ya karasa ciki yana kallonta shi ma a sanyaye, Durkusawa yayi kusa da ita a hankali yace “Sannu iklima” maimakon ta amsa masa sai hawaye, duk jikinsa yayi 

sanyi ya kasa cewa komai lkci daya shi ma idonsa ya kada, khadijah ta fashe da kuka sosai ta juya ta fice daga dakin, Da kyar Iklima ta iya bude baki tace 

“Kace ta yafe min don Allah” Ya sauke idanuwansa kasa a hankali yace “Kina shan magani iklima?” Girgixa masa kai tayi hawaye na xuba idonta, ya fi minti 

biyu durkushe gabanta bai iya yace komai ba, can ya dago da kyar yace “Wa ke kula da ke?” Nan ma ta girgixa masa kai, cikin sanyi yace “Yaushe rabon ku je 

asibiti?” Kallonsa kawai take alamar maganar ma baxata iya ba, mikewa yayi a hankali ya fita dakin, ya kalli khadijah da ta hade kai da kujera tana kuka 

Shureim na kusa da ita shi ma yana kukan yana kallonta, Babu wanda yace masu komai, kowa na harkan gabansa a babban gidan, gun yayar mahaifin iklima da ya 

sani ya nufa a waje, tana xaune su kusan uku suna hira, ya d’an duka ya gaishe ta, ta amsa tana tambayarsa yaushe ya xo, yace “Ba mu jima ba, mama nace 

iklima na xuwa asibiti kuwa?” Matar tace “An kwan biyu ba aje ba tunda uban nata bai turo kudi ba kilan ya gaji shi ma, mu kuma ya bar mu da wahala” Shiru 

Aliyu yayi yana kallonta, can ya mike yace “Toh bari mu je yanxu” tace “Kar ma ka bata lokacin ka ko tashi bata iya yi, idan ba likitan xaka je ka gayyato a 

asibiti ba” Bai ce komai ba ya koma parlorn sannan ya shiga dakin da iklima take, Kallonta kawai yake yana kokarin gano stage din da cutar nata yake, bayan 

wani lokaci ya juya ya fita, gun khadijah ya nufa yace “Tashi mu je” Ta mike da kyar har lokacin kuka kawai take, Aliyu ya dau shureim ya rungumesa suka 

fita, bank ya fara tsayawa, ya kalli khadijah kafin ya bude motar ya fita xuwa gun automated teller machine, ba a dau lkci ba ya dawo ya shiga motar, wani 

babban pharmacy dake area din ya tafi, yana kallon khadijah da taki daina kuka yayi kasa da murya yace “Am begging you ki daina kukan nan Iman, baki kyauta 

ma yaron nan, even for his sake kiyi hakuri ki daina kukan” Juyawa tayi tana kallon Shureim da ke kuka bakin rai shi ma, hadiye kukanta tayi xuciyarta na 

mata xafi, Aliyu ya bude motar ya fita, bayan kusan minti goma ya dawo rike da ledan magani masu yawa da tsada, murmushi yayi ganin yanda Shureim yayi shiru 

yana kallon khadijah dake ta kukan xuci, Bata taba tunanin ganin Iklima a yanda ta ganta ba, ta ji duniyar ba bakin komai yake ba, wani store Aliyu yayi 

parking ya fita ya siya cartons of malts da Madara masu yawa, sai locozade boost, a booth aka xuba abubuwan da ya siya, ya shiga motar ya kalli khadijah da 

ta jinginar da kanta jikin kujera ta fada duniyar tunani, kamo hannunta yayi ta juya a hankali tana kallonsa, murmushi ya sakar mata yace “Kowa da irin 

kaddararsa, su irin tasu kenan, so you just have to pray for them, Allah ya sa mu cika da imani” wasu sabbin hawayen suka sakko idonta, ya tada motar suka 

bar wajen, shi kadai ya shiga dakin iklima ya ajiye magungunan gefenta yaran gidan suka dinga shigowa da abubuwan da ya siyo, Yana kallon iklima ya fiddo 

magungunan gaba daya ya shiga nuna mata yanda xata sha, kallonsa kawai take bata ce komai ba, bayan ya nuna mata yace “Idan kin ji kina jin yunwa sai ki 

daure ki tashi ki sha malt ko madara, idan lokacin shan maganin ki yayi ba a baki abinci ba sai ki sha malt ki sha drugs din kin ji?” a hankali ta gyada 

masa kai, ya fiddo dubu talatin a aljihunsa ya daga gefen katifar ya ajiye mata yace “Ki dinga aika yaran gidan su siyo maki fruits sai ki basu ko dari biyu 

don su dinga xuwa kin ji?” Nan ma ta gyada masa kai, ya d’an yi murmushi yace “Allah ya sauwake lil sis, idan kina son ki samu lafiya sai kin yi ta shan 

drugs din ki” Nan ma dai ta gyada masa kai, yace “Xan dinga xuwa duba ki always, idan kika fara samun sauki xan kai ki gun Mumy dama Abbanki ne yace a kawo 

ki nan” kallonsa kawai take, jikinsa yayi sanyi ganin hawayen dake sauka idonta, da kyar yace “I will be back soon” daga haka ya mike ya fita dakin ta bi sa 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button