NOVELS

SAWUN BAYA 1 & 2 COMPLETE HAUSA NOVEL

Cikin kasa da murya ta gaidashi ya amsa adaidai lokacin da Alhaji Abubakar yake cewa Munirah zauna sosai Munirah"

    Zaman tayi yayin da Mubarak ya sata kallonta sannan ya dauke kansa"

      Haka nan taji zuciyarta tana tsinkewa wani Dan karamin akwati Alhaji Abubakar ya jawo ya bude kudi ya ciro masu yawa ya ajeye a tsakiyar falon, sannan yayi gyaran murya yace"

  Munirah kallah nan"

 Ahankali ta daga idonta ta kalli kudin sannan ta sauke idonta"

Kallan nan nace"

Ahankali tace nagani Baba"

 Menene??

Kudi ne"

  Ido ya zuba mata yayin da kanta ke kasa gabanta na faduwa"

 Munirah wannan Sadakin ki ne, yau da misalin 10:00am Baba tsoho ya daura miki aure da Sadiq acan Ingall"

  Runtse idonta tayi kanta akasa, duk yadda sukaso ganin fuskanta bata bari ba kanta na kasa ta kasa dagowa, cigaba yayi da cewa, Muna fatan zaku karbi wannan kaddarar gaba dayan ku hannun biyu, ayanzun Sadiq mijinki ne kina karkashin ikon sa ne, nauyinki ya tashi daga kanmu ya koma kan shi"

Hawayen Munirah suka hanga yana zuba akasa saboda ta dukar da kanta sosai kasa, dagowa tayi da nufin zatayi mgn suka hada Ido da Enisilim cikin sauri ta maida kanta kasa yayin da hawayenta sukaci gaba da zuba akasa"

    Alhaji Abubakar kuwa cigaba yayi da cewa, ke kiyi hakuri kiyiwa mijinki biyayya,  kiyi koyi da halin yar uwanki, yinayi, Bari nabari, ki nutsu kiba marada kunya, dan Allah Munirah, wannan auren ba mutum bane ya hadashi, hadin Allah ne, dan haka muyi hakuri gaba daya, kinji ko Munirah"

    Hannun tasa ta share majina"

 Munirah?, Kinajina ko??

 Ahankali ta daga kanta alamar eh"

  Yauwa Allah yai miki albarka, juyawa yayi ya kalli Munarak dake tsaye yace"

Mubarak ga leda zuba mata kudin ta shiga gida"

  Karban ledan yayi sannan ya tsuna ya zuba kudin ya aje agaban Munirah ya fice waje"

  Alhaji Mustapha ne yace Munirah toh dauka kije gida kinji ko?

   Kasa motsawa tayi agurin, digan hawayenta kawai suke gani"

    Cikin tsawa Enisilim yace, badake ake mgn ba!!!

 Cikin shashekar kukan daya kamata yanzun nan tace Abbanin jikina rawa yake yi dan Allah azo adaga ni"

 Wani irin kallo suka mata cikin tausayawa Alhaji Mustapha yace Allah sarki"

 Shikuwa Enisilim cewa yayi Akira masa Mammah Aysha, yayin da Alhaji Abubakar yake cewa ki kwantar da hankalin ki mana, ya kike haka kuma, wannan shine rufin asirin mu baki daya, kiyi hakuri"

Shigowan Mamah Ayasha Enisilim yace kama yariyar can takoma cikin gida"

Dagata Mamah Ayasha tayi suka fice batare data dau ledan ba, fitowa tayi rungume da Munirah yayin da Sadiq da abokansa kiyin alwalan mangariba"

  Afalon suka samu Annanin, hannun ta miko da nufin takama Munirah ta rungume, Amman sai Munirah tai saurin kwacewa ta wuce dakinta"

 Kan gadonta ta fada can tsayir ta kudundune ta cure guri daya, tunda ta dukule agurin Bata sake motsawa ba"

  Itako Lubbunah bayan tayi sallah part dinsu Munirah ta taho so kawai take taga wanni halin Munirah take ciki, wani Shashi na zuciyarta tausayin Munirah take yayin da wani shashin ke Mata dariya, saidai harta gama zamanta Munirah bata bude kofarta ba"

   Sosai hankalin Annanin yake atashe masamman idan ta tuna munirah batace komai ba, tunda ta shige dakin Bata fito ba, gashi yanzun har 9 nadare"

 Abunka dame baki, wadda ka gama kiyassta ga abun da zaiyi sai Kuma taga batayin ba, yadda take ji azuciyarta har gara Munirah tayi haukan da wannan shirun da tayi, domin batasan me take nufi dashi ba"

 Waya ta dauka ta Kira Enisilim bayan ya dauka tace"

  Munirah fah tunda ta dawo gurin ku batacewa kowa komai ba.....

Har ke??

  Wlh Ina kokarin tabata ma ta kwace"

 Jimmmm yayi sannan yace ki barta"

    Toh Amman dai bayau za 'a kaita part din nashi banko??

   Me za'a jira?

    Yanzun fah Tara ta wuce, ko wanka batai ba"

     Ai ba bakon guri zataba, idan rigima takeji idan taje gidanta tayi wankan, gani nan zuwa"

Sauke wayar Annanin tayi jikinta sanyaye sannan ta nufi dakin Munirah"

Munirah??

   Shiru taji harta Kira sau uku babu amsa Dan haka tace Bazaki bude ba??

        Ahankali taji an bude kofar yayin dataga idon Munirah har basa buduwa Sabo da tsabar kuka"

   Ido ta bita dashi, sannan tace, Munirah fushi kike dani kuma?, ai bani nakar zomon ba, yar uwarki tabar miki amanan mijinta abun da zaki duba kenan........

     Cikin sauri Munirah ta koma ta fada Kan gadon yayin da Annanin tabita abaya tana cewa, shikenan yanzun dai Malam yace kiyi wanka ki fito"

   Bazan iya wanka ba sanyi nake ji"

Jimmm, Annanin tayi, sannan ta juya tabar dakin”

Misalin 10 nadare Mamman Aysha da hauwa suka shiga dakin, Yayin da aunty Khadija ta biyosu abaya, daker suka sata tai wanka ta fito, nan ma da taimakon su ta shirya"

 Turaroka suka fesa Mata sannan Mammah Ayaha tace toh taso"

  Ina zaku Dani?????

   Cikin rareashi Mamah Aysha tace, Ina kuwa zamu dake inda ya wuce dakin mijin ki?, Tashi muje dare na yi"

 Tana fitar da wani irin nishi take fadin"

  Banda Miji Mamman, mijina ya mutu Sagir, kubarni dan Allah????????

Munirah kidaina yaudaran kanki, kinji ko? ki tashi muje”

  Wayyo Allah na, Amukarnin Sagir katashi ka gansu zasu hadani da makiyina,???? wlh bazan iya zama dashi ba, banson shi da in dauna dashi gara mutuwa ta daukeni yau????????

Tsawa Hauwa ta Mata sannan tace ki kama bakin ki Munirah, tashi muje, kafin ranki yabaci"

   Aunty Khadija ce tace tashi mana Munirah meye haka?

Aunty Khadija ko duniya ce zata taro bazani ba wlh, haka kawai dan kasa ta rufe idon Amukarnin Sagir sai ahadani da Sadiq bayan ansan ya tsaneni????????????

  Wai baki tashi saina kwada miki mari?? Mammha Aysha tafada afusace"

    Kuka take sosai duk mutanen dake falom suna jinta tana fadin banson shi wlh, nafi karfin shi, idan Kuma kuka matsa min naje gidan shi wlh saiya gane kuren shi, Kuma indai shi ba maye bane mezaiyi dani, ai wannan ma ba aure bane"

Tashi muje yagane kuren nasa, kimishi duka har sai ya tsuguna yabaki hakuri, nan ne zansa kin cika mara kunya….

  Daga bayan su sukaji Mubarak na fadin, tunda ita ta haifeshi ba, idan kika Bari nazo gurin nan saina karairaya ki.....

   Mikewa tayi da sauri, yayin datai kasa da murya ta yadda su Mammah ne kawai sukejin abun da take cewa tace"

 Kuma ruwan zafi zan watsa mishi ya mutu"

 Dariya sukayi, inda Maman hauwa tace ki watsa mishi yau, gobe da safe idan anyi zana'idar sa sai mukoma Agadez"

 Wucewa tayi cikin shashekar kuka suna isa falon Enisilim na shigowa Jin kukanta yace meye haka Kuma?, inace ai Kun kaita?

 Ai ki tayi Malam, tunda nabaroka taki tashi, tana nan tana aikin mgnrta data Saba"

  Munirah wuce kuje"

Kara rushewa tayi da kuka Abbanin ban son shi Allah kuwan……

 A'a a'a ban tambayeki ba, wuce kawai nace kiyi, indai har kinason farin cikina toh ki zauna dakin mijin ki"

   Abbanin dan Allah ku tausaya min dan ya Rasulillahi????????"

   Cikin tsinkewan zuciya yace kije dakin ki Munirah dan Allah, kiyi mana biyayya"

  Fashewa tayi da kuka sosai ta zame ta tsuguna akasa, Mubarak ne yace ni kubarni in kaita"

 A'a Mubarak wuce abun ka, Kuma ku zauna, Munirah rabu dasu tashi ni zan rakaki da kaina"

Ganin har yanzun tana tsugune yasake cewa tashi muje mana”

Hannunta ya kama yayin data fada jikin shi rungumeta yayi yana me samata albarka acikin ranshi sannan ya fara tafiya da ita ahankali"

   Hawayen dake gefen idon shi ya share sannan yace, kiyi hakuri Munirah, yarinta ne ke damun ki, inaji ajikina wata rana zakiyi farin ciki da wannan auren, Ina son ki sosai Munirah,  ke nake kallon inji sanyi, wannan auren gata ne aka miki, keda Sadiq tarbiyan ku iri daya ne, gida daya kuka tashi, ke jinina ce, Sadiq ma nawa ne, kiyi hakuri mun miki laifi bamu tambayi ra'ayin ki ba, amman abun da nake son kisa aranki shine, duk jinin tsoho bazai cutar dake ba, ni ubanki baza'a hada baki dani a cutar dake ba"

Sanyin dataji zuciyarta tayi da kalama Enisilim yasa ta fadin"

   Abbanin ya tsaneni fah, wlh besona????????"

Bagaskiya bane Munirah, duk dangi subada shedan akan cewa kece kike gwada masa kiyayya, shi besan ma kinayi ba, ki nutsu dan Allah"

  Adaidai wannan lakacin suka isa kofar da zata Sada su da Falon, turawa yayi ya shiga har falon tana Kan kirjin sa, gaban kujerar ya zaunar da ita tare da Kara rarrashinta"

   Yana fita ta fashe da kuka me karfi, yayin da wasu maganganun da take gayawa Aliya suka shiga dayu Mata, lokacin da take cemata yau zata kwana kurku, ko tace gidan Sadiq da lahira kusan daya suke, cikin matsanancin kuka ta bude murya tace Ashe nice zan kwana akurku, gani aduniya Amman wadda yake lahira yafini Jin dadi, Aliya ta tafi ta huta nine zan zauna da munafuki yana kallon ka idon shi arufe, ya dinga wani lassan lebe kamar mejin sanyi, jikina yafi karfin ka bazan taba yadda ka tabani ba, banso ka adaba yanzun ma bazan soka ba, soyayya irinta yan uwa ma taka ban tabaji ba, bare soyayya irinta aure, bantaba kawowa wani abu makamancin aure zaishiga tsakanina dakai ba, inyi Yaya dakai?, ai wannan ma rashin adalci ne????????, bazan taba yadda ya tabani ba, jikina bana kowanne banza bane, iri irin wannan mgnr zuviyar Dana fili taitayi tana share hawaye, yayin data kalli falon tana me tausayawa kanta"

              *********

Ango albushirin ka, ankaita da ker, ai yau naga hauka wajen Munirah, tana cen tanata kuka, kamar za'bar garin da ita"

    Dariya abokan Sadiq guda biyu dake gefen sa sukayi, shikuwa kawar dakai yayi yai murmushi

  Mubarak ne ya kalli Sadiq dakau, cikin Mamaki yace, toh fah, wannan wankan fah?, yanzun fa nabarka da manyan kaya, yanzun Kuma ka matse kaida zaka dakin amarya sai Kuma kayi wata shiga haka kamar haka Ingall?

 Banyi kau bane????

 Kallon sa Mubarak yayi dakau sannan yace"

   Kayi kau sosai wlh, sai ka koma dan Yaro, kawai ban saba ganin za'a shiga daikin amarya bane da kananan kaya"

     Cikin kawar dakai yace, ni ahaka zani"

     Yar dariya Mubarak yayi sannan yace Amaryar ma akunbure take fah,  har duka naji tace zata maka"

Dariya abokan Sadiq suka  sake yi karo na biyu, Sadiq kuwa dauke kansa yayi can gefe kamar badashi ake mgnr ba"

   Wai bakaji na ne Sadiq?

 Juyowa yayi kadan, ya kali Mubarak alokacin yadanyi wani murmushi kadan yace"

 Najika mana, akace  dai yau danbe za'ayi?

     Cikin dariya Mubarak yace inace zaka tsaya adan dake ka ko Yaya ne??

  A'a Sam, idan ashirye take Nima ashirye nake ai, nama fita shiryawa, dan ninasan wacece ita"

    Dariya suka sakeyi yayin da Mubarak yace Niko Ina ji maka tsoron yariyar nan da alamar zata wahalar dakai"

   Zadai mu wahalar da juna, dagowa yayi daga jiginan da yayi jikin motar, hannunsa duk biyun yasa cikin aljihu, bakin gilashi sanye a idon sa ya fara takawa tare da fadin Saida safen ku  .......

????????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????
????
SAWUN BAYA
????
Book 2 ????????
????????????
????????????????????
????????????????????????????

                    *Na*
          *_Fadeela Lamido_*

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

® PEN: WRITER’S ASSOCIATION

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️


~only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers~


——–PAGE——-

https://www.facebook.com/110384724043172/

——–GROUP——–

https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/
         *Page 12- 15*
 Typing.......????️

Cikin murmushi sukace Allah ya taahemu lafiya”

  Ko waigowa Sadig beyi ba har yanzun hannunsa na cikin aljihun sa"

 Cikin dan gudu gudu ya haura matakalar dake bakin part dinsa sannan ya juyo ya dagawa abokansa hannun ya juya ya tura kofar

   Cikin sauri ta kalli fofar adaidai lokacin daya maida kofar ya rufe ya maida hannunn sa cikin aljihu sannan ya fara takowa cikin falon"

Mikewa Munirah tayi da sauri, yayin da wayarta dake kan cinyanta ta fadi kasa, ko kallonta batai ba cikin firgici da rawar jiki ta zaga can bayan kujeron ta tsaya tana raba ido cikin shirin fashewa da kuka"

 Tsayawa yayi cak yana kallon ta, suna nesa da junah sosai, fuskar sa daure tamau, yayin da yake matsa hannunsa dake cikin aljihun sa tare da lasan lebensa nakasa"

   Jikinta rawa yahau yi gaba daya, tunda ga inda yake tsaye yana hano inda jikinta ke rawa yayin da ya kafesa da idonsa"

Itama shi take kallo sai dai bata iya kallon cikin idonsa sabo da bakin Gilashi daya sanya"

  Zagayowa yayi ya iso tsakiyar falon, ganin yana nufota ta kwallara kara"

 Cak ya tsaya yana kallon ta, har yanzun hannun sa cikin aljihu, kallon da ya mata yasa ta tushe bakinta yayin da hawaye ke zubowa a idon ta"

    Hannun sa daya ya ciro cikin aljihun tare da fadin meye haka??

    Dauke idonta tayi akasan sa tare da cigaba da kukanta, kujera ya zauna yana me daura kafa daya akan daya yace zagayo ki zauna"

       Kokarin zagayawa take tacen lungu yace tanan zaki biyo"

  Yadda ya hade ransa babu alamar wasa yasata zagowa ta gefensa ta zago ta zauna hannun kujera"

   Batare daya kalli gefenta ba yace ki zauna dakyau"

    Gyara zaman ta tayi, yayin da wa waigo ya kalleta kadan ya maida kansa gefe tare da fadin ki share hawayen ki sannan ki cire mayafin ki kisha iska"

      Share hawayen tayi sannan ta kara gyara mayafin ta"

      Idonsa ace yace, ki cire nace"

   Mikewa tayi da sauri tare da karayin kwalkwal da idonta"

 Daga kansa yayi sama ya kalleta, har yanzun jikinta rawa yake yi, tausayi ta bashi sai dai besan ta yadda zai nuna mata tabashi tausayi ba ahankali yace"

  Ki zauna"

 Nidai a'a

  Tsawoyu wa zakiyi tayi??

   Kaita daga alamar eh"

   Mikewa yayi tare da fadin shikenan, butirin hannun rigarsa ya shiga budewa tare da fadin gani ance kince duka zaki min, kin shirya?..........

Cikin zaro ido ta kallai"

 Eh nasami lbrn, ina jiran ki, daga nan har zuwa ranar da kika shirya ina jiran ki, amman ki sani nima fah ashirye nake"

    Cikin zunburo baki tace ni bance ba sharri aka min"

      Kallonta yayi cikin ido sannan ya nuna mata gaban shi da hannun sa yace muje"

     Gaban shi ta shiga batare da tayi musu ba waigowa tayi taga ya fara tahowa dan haka ta fara tafiya yadda yake tafiya da sauri har yazo ya wuceta"

Wani kamshi ne ya daki hancinta lokacin da suka shiga cikin dakin, koda bata tsaya kallon dakin ba tasan ya tsaro, gaban gadon ya tsaya ya ciro wayoyin ya aje agefe sannan ya juya ya shiga toilet, Munirah kuwa durkushewa tayi kasa yayin data kafa goshinta akan gadon ta fashe da kuka"

  Acikin ranta take fadin nashiga ukuna, ni ban masan yadda sanyi ba yau, narasa abun yi, Allah kadawo dani cikin hankalina ya rabbi, kasa mun nutsuwa, idan ban nutsuba cutata zai yi"

 Sheshshekar kuka taitayi har ya fito ya kalleta yaja tsaki, sannan ya wuce gaban madubi ya gyara jikin sa, tamanin yadda yake fasa turare kamshin nashiga cikin cikinta"

 Karan kukanta ya cika kunnensa amman ko ajikinsa bayan ya gama gado yahau ya kwanta sannan ya mika hannun shi ya kashe wutan dakin duhu ya bayyana"

 Kusan minti shabiyar ta dauKa acikin duhun sannan ta share hawayen ta cikin muryan kuka tace"

      Ni ai ni daya nake kwana adaki, ban iya kwana da wani ba"

 Murmushi yayi  cikin duhun, sannan ya mike ya sauka agodon ya kunnan haske, tare da fadin muje in nuna miki dakin ki"

    Mikewa tayi fuskanta akunbure tana fadin ni nidaya zani banjin tsoro"

   Nasan bakijin tsoro ai, wai naga bakisan kan gidan bane"

  Bazan kasa ganewa ba tun da duk cikin gidan mu ne"

Lumshe ido yayi haka ne nikuma daman cirani nazo ba"

      Bude kofar yayi, yana kallota ta fice tana cigaba da share hawaye, be rufe kofar bah har Saida yaji shiganta dakin sannan ya maida kofar ya rufe"

    Munirah kuwa sosai ta kulle, fakewa tayi ta kirkiro jarumta kawai, so take taga ransa yayi baki, amman babu alamar zaiji haushin, dan haka ta kwanta ta fara kuka daren ranar haka ta kwana Bata runtsa ba"

  Shima gyara kwanciyarsa yayi agajiye yake sosai dan haka yana kwanciya bacci me karfi ya dauke shi"

       Washegari bayan ya dawo sallah subahi lekawa yayi ya ganta ta cure akan gado juyawa yayi ya koma nasa dakin bacci ya sake komawa"

             **********

Lubbunah dan Allah tashi ki mikawa su Sadiq breakfast”

   Yamutsa fuska tayi, Umma katowa dani sai kuma inje gidan kanwata da Sassafe"

 Yar dariya Annanin tayi sannan tace kisa aranki Sadiq kika kaimawa ba Munirah ba"

       Tam, amman ki kira shi kice mishi ganinan zuwa saiya tsaya daga kofa ya amsa"

     A'a, ni so nake ki shiga ki gano min Munirah, shiyasa nace kikai badan hakaba Anass zan bawa"

 Umma kinfasan halinta, zan iya zuwa yanzun tamin rashin kunya"

 Toh ke biye mata zakiyi?, ai sai kiyi hakuri kodan darajan yayan ku"

 Mikewa Lubbunah tayi badan ranta yaso ba, ta dauki abincin tai waje"

      Falon ta Sanu Sadiq yana zaune rike da waya, cikin girmamawa ta gaidashi tana kokarin aje abinci yace kai mata ciki"

  Sallama tayi tare da tura kofar zaune ta sameta ta fito wanka tana kuka idonta jawur"

     Juyowa tayi ta kalli Lubbunah idonta jawur sun cika da ruwa tace"

     Kin ganshi afalon??

 Bakin Lubbunah cike da dariya tace waye??

      Sadiq"

Eh yana nan zaune, wani abu ne???

    A'a, tun dazon nake son na fita amman dana leka saina ganshi"

    Toh ke ina zaki"

Fashewa tayi da kuka Lubbunah nagaji da zama, jiya kwata kwata bayin bacci ba, wlh da nan part din gwanda akai ni makabarta nasan mutuwa nayi, duk an tsaneni, kowa be kaunata, da Amukarnin Sagir nanan baza Amin haka ba"

  Tausayi taba Lubbunah sosai, dan taga alamar taushi atare da Munirah, dan haka tace Munirah, indai zakibi shawarata ki kwantar da hankalin ki ki zauna da mijin ki lafiya, aure ba abun wasa bane"

 Lubbunah kenan fah zama zanyi dashi har abada?, ahaka zan zauna dashi yana cucure fuska, yadda yake yanga ko mace bata haka, yaje ya gama taba kare da doki nima ya tabani?, Idan nabari ya tabani ai nazama banza, ni yanzun abun dake damuna nidashi kadai ne agidan wlh, dayaga abun da zan mishi, wlh, ruwan zafi zan watsa mishi ko be mutuba sai halittar sa ta canza, inga dame zai dinga takamar"

   Shikenan tunda bazakiji shawara ba, yanzun da safe kinje kin gaidashi?.......

   Uba na ne????

 Mijin ki ne"

Mijina yana kasa, kasa ta rufe masa ido”

 Lumshe ido Lubbunah tayi sannan tace Allah ya jikanshi, ni barin in tafi"

 Hawaye ta goge shikenan, ku kuna cikin gida kunajin dadin ku ni kuma an kawo Ni nan an girke, sobodani ba'a kaunata, zalinci yayi yawa aduniya

 Nidai nace kiyi hakuri dan Allah Munirah, mikewa Lubbunah tayi yayin da Munirah ma ta mike tana bin bayan Lubbunah tana fadin"

      Yanzun tafiya zakiyi kibarni?, shikenan saina zauna dagani sai halina?, Bakina yaita min ciwo, ganin Lubbunah na kokarin wucewa tai saurin rike mata lafaya"

   Cikin mamaki Lubbunah ta kalleta tare da fadin, yanzun me kike nufi??

 Kizo mu zauna tare"

  Caf, lallai Munirah da karfin hali kike, tare aka mana auren??

     Batace komai ba tana dai rike da lafayanta har yanzun"

Ki sakeni Umma tana jiran na fah"

  Ganin Bata da niyar Sarkinta yasata kiran Sunan Sadiq"

  Har tacire rai da amsawan sa taji yace Lubbunah lafiya dai"

 Amukarnin rikeni tayi wai bazan tafi ba"

 Shiru taji yayi zuwa can tafara jin takon sa da karfi"

  Tsaye yayi yana kallon Munirah da idonta suka cika da hawaye suna daf da zubowa"

 Ido ya zubawa Munirah wannan karon babu gilashi a idonsa yayin da yake sanye da yar karamar riga ta shan iska, yadda yake kallonta itama haka take kallonsa saidai ita akwai fargaba da firgici a idonta shi kuma dake yake bubu wargi"

   Idan ta tsaya me zata miki??

    Lunshi ido tayi tare da turo baki"

  Ganin taki mgn yace sake ta"

 Ahankali ta zame hannunta yayin da Lubbunah ta raba ta gefensa ta wuce yayin da Sadiq din yabi bayan Lubbunah"

   Hannunsa ya zuba duk biyun cikin aljihu kamar yadda ya saba sannan yace Lubbunah barin ganki"

  Tsayawa tayi cak adaidai kofar da zata kaita wajen gidan"

  Gilashi shi ya ciro yasa a idonsa sannan ya maida hannunsa aljihu yana me cewa"

   Me Tamudiriccin tace miki akaina??

  Cikin rashin fahimta tace batace min komai ba"

 Ba gaskiya bane Lubbunah, kinjima aciki nasan tayi zancena ki gaya min ba komai"

  Cikin daburcewa Lubbunah tace mgn tayi dai kawai tana nuna tana kewan gida ne"

     Lumshe ido yayi sannan ya bude tace bata sona ko???

  Wasa da hannu ta tafara a'a batace haka ba"

  Jiba, Lubbunah banine na tambaye ki ba?, inason ki gaya min yaya kuka yi da ita?

    Kawai dai tana korafi akan auren, sannan kuma tana neman abokin hira tace bakinta ciwo yake mata.......

Wani dan gutun dariya yayi sabo da ita dole sai tayi mgn ko?, Ina jin ki??

Shine kawai Amukarnin"

Batace bata sona ba ko zata min duka, ko wani lbrn makamancin hakan??

  Batace ba Amukarnin, Amman dai naji tace zata iya watsa maka ruwan zafi"

 Toh fah, abun har yakai haka?

 Amukarnin nalura fada kawai take yi fah"

Lumshi idonsa yayi shikenan jiki Nagode"

  Komawa yayi ya zauna yana fesar da iskan bakinshi zaman kusan awa daya yayi sannan ya mike ya fita"

    Part din mahaifiyar sa ya nufa, ita da Lubbunah ne zaune bayan ya gaida Annanin Lubbunah ta mike ta fita"

   Cikin sa ya shafa tare da fadin Annanin kallah"

 Juyawa tayi ta kalli cikin sa dayake shafawa tace"

 Bana aika maku da abinci ba"

     Bata bani ba"

Ai da saikace mata ta zuba maka"

 Annanin ban iyaba, ban saba yin haka ba"

Juyawa Annanin tayi ta dauki yawarta ta danna tasa akunne, zuwa can tace lafiya lau Munirah ya gidan, bajin amsan da tabata ba yaji Annanin ta sake cewa"

    Meyasa baki bawa mijin ki abinci ba?, Zuwa can yaji tace a'a zakiyiwa kanki horon yinwa ne?, kici abinci zan nema mafita kinji?, Shikuma dan kin bashi abinci bashi zai nuna kina sonshi ba, kiyi hakuri kibashi ai durkusawa wada ba gajiyaw bane......

Cikin fushi Sadiq dake sauraronta yace Annanin banson fah"

 Mikewa tayi ganin yanason ya hanatajin zancen Munirah bayan tagama sauraronta tace"

Eh nima ina bayan ki, karki sake yai miki wayau"

 Sauke wayar Annanin tayi tare da fadin kaje zata baka"

Banso, bazanciba, kinata wani lallabata, yanzun zaki sa ta dinga jin ita wata ce”

 Ai daman ita wata ce katashi kaje kaci, in kanajin yinwa, idan kuma bakaji kaika sani, zanga yadda zayi wannan zama dakai da Munirah"

Mikewa yayi kawai ya fice batare dayace komai ba gidan ya bari baki daya”

        ********

Misalin 7:00 Sadiq ya dawo gida dakinsa ya nufa bayan yayi wanka ya fito yana daura agogo”

 Zama yayi afalon ya daura kafa daya kan daya cikin daga murya yace Tamudiriccin!!

Kin amsawan tayi tun yana kiran Tamudiriccin har yagaji yace Munirah!!!

Yadda ya kira sunan cikin tsawa yasata amsa batare data sani ba"

Fitowa tayi dauke da kayan abincin da aka kawo nadare daga gidan Umma"

  Tana zunbura baki ta aje yayin da tana zubar da kwalla ta zuba mishi"

  Mikewa tayi zata wuce yace zauna"

  Zama tayi saidai har yanzun zubar da hawayen take, kallonta yayi sosai duk ta rame Akwai alamun  tun jiya data samu lbrn auren batasa komai a cikinta ba cikin ransa yayi wannan tunanin"

 Abincin ya faraci sannan ya kalleta da gefen idonsa yace kinci abinci??

Ni bana ci"

Da rana fah?

Banci ba”

Meyasa?

Banci”

Da safe kinci??

 A'a

Lumshe ido yayi sannan yafara cin abincin yanaci yana lunshe ido”

Haushi yabata sosai, bata dauka zaiciba shiyasama ta yadda ta kawo mishi, meyasa bazan mishi rashin mutunci bane wai, tana zaune yaci rabin abincin sannan yasha ruwa ya koma ya kwanta abayan kujerar kusan minti sha biyar sannan ya bude idonsa”

Mikewa yayi sannan ya dauko abincin daya rage ya dawo gaban kujerar da take”

 Abincin ya aje adaidai kwankwasonta sannan ya daura ƙafarsa daya akujerar, daya kuma akasa, yana fadin"

  Dan Allah kullum ki dinga kincin abinci har indawo in same ki"

 Acikin ranta tace ko bakace ba haka zanta zama har mutuwata tazo"

 Gani tayi ya cika lokali da shinkafa yasa abakin sa, kawar da idonta take kokarin yi taji ya kama kanta da kyau, bata hankaraba ya tura bakin sa cikin bakinta ta yadda ko motsi bazata iya ba haka ya riketa"

 Duk da cewa ta datse hakora ta da harcen sa yaita dannan abincin har ya juye mata shi tas, duk da haka be cire bakinsa ba yana harde da harcenta saida ya tabbatar ta hadiye sannan ya rike kanta ya sake zuba wani lomar abakin ta, duk da irin danben da take kokarin yi dashi behanashi yimata duran abincin ba, yayin da yana zubawa take saurin hadiyewa sabo da yadda na farkon ya wahalar da ita shikuwa data hadiye yake sake zuba wani, duka kuwa kaiwa take batare da taga kama ba, sosai yaji tana da karfi dan saida yayi da gaske duk gurin yayi kaca kaca da miyar shinkafar, zuwa wannan lokacin kwance yake jikinta"

Tas ya dura mata rabin abincin daya rage sannan ya sake ta, jin tana kokari yin amai yasake turmusheta, tare da cafkar bakin ta yana tsotsewa kamar ya samu sweet, tsun kuli tafara Kai masa a duk inda hannunta ya sauka duk da haka be sake tabata ba har saida yaji tayi gyatsa sannan ya mike yana fitar da numfashi”

     Ganin ya dagata ta dunkule waje daya tare da fashewa da kuka sosai"

Shikuwa Sadiq rigarsa ya cire har yanzun yana maida numfashi kallonta yayi yace tashi kije kiyi wanka idan ba haka ba zan kira Anass ya sameki agurin"

    Cigaba tayi da kukan batare data kulashiba ganin haka ya wuce ya bude kofar tare da kwalawa Anass kira"

  Tabbatarwa da tayi Anass ya amsa yasa ta mike ta nufi dakin tana rufe da idonta cikin zubar da hawaye"

    Tanajin sa yanabawa anass umarnin ya gyara gurin, kuka taci sosai sannan ta shiga tai wanka yayin da takejin duk jikinta ciwo yake mata"

     Duk yadda zatayi ta kakaro amai tayi amman yaki fitowa dan haka taita jerah Allah ya Isah sannan ta sha ruwa tai sallah isha'i ta kwanta"

  Wani irin bacci ne me nauyi ya dauketa sosai takejin dadin baccin"

   Sadiq kuwa bayan yayi wanka ya gyara jikinsa zama yayi afalon yana kallon labarai"

Misalin 11:34pm ya mike yana hamma ya nufi dakin Munirah”

  Tsakiyar gadon ya hangeta bacci kawai take, Murmushi yayi sannan ya juya ya fita"

   Dakinsa ya koma ya rufe kofar ya fada gado tare da karanta addu'ar bacci"

     Bacci me dadi yake yayin da yayi nisa a baccin yafara jin kira da karfi"

    Sagirrr!!! Sagirrr!!! Sagirrr!!!

Cikin kwakwalwar sa yakejin kiran dan haka ya tashi afirgice yana me kasa kunnen sa”

    Sagirrr!!!

 Zabura yayi tare da sauke ƙafarsa akan gadon..........

????????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????
????
SAWUN BAYA
????
Book 2 ????????
????????????
????????????????????
????????????????????????????

                    *Na*
          *_Fadeela Lamido_*

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

® PEN: WRITER’S ASSOCIATION

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️


~only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers~


——–PAGE——-

https://www.facebook.com/110384724043172/

——–GROUP——–

https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/
         *Page 16- 18*

Typing….????️

 Yadda yakejin kiran sunan  tamkar acikin dakinsa saidai yasan shi kadai ya kwanta"

  Cikin sauri ya nufi dakin ya tura kofar, hangota yayi zaune Saman gaddon   fuskanta face face da hawaye tana danne da kirjinta"

   Har bakin gadon ya isa ya tsaya tare da kama kwankwasonsa da duk hannun nasa guda biyu yana fadin, menene??

      Sagir????????????

         Sagir??, Ina jinki meye faru??

   Zubar da hawaye take tana cigaba da fadin wayyo Sagir dina,,????????????

       Hankalin sa ne ya tashi sosai, saidai bayason tagane tashin hankalin nashi, kula yayi sosai kamar pic ne dafe da akirjinta ahankali ya karasa ya zare pic din ya juyo dashi ya kallah"

   Sagir ne tsaye yana murmushi, hankalin Sadiq sosai ya tashi, Munirah ya sake kallo cikin wani irin yanayi cikin sanyin jiki sosai yace Tamudiriccin??

     Kuka kawai take har yanzun batabsr Kiran sunan Sagir ba"

    Cikin wani irin yana yi ya zauna abakin gadon sannan ya juya ya kalleta, Tamudiriccin meyene ke damun ki haka??, Kinyi mafarki da Sagir din ne???

     A'a????????????

    Toh menene??

    Shine ya tafi yabarni anan????????

 Lumshe idonsa yayi, sannan ya bude, beson yace yi hakuri amman anan gurin yazamar masa dole, hannunta yake kokarin rikewa tare da cewa kiyi hakuri kinji, kiyi addu'a ki kwanta kiyi bacci"

    Kara tankwashe kafa yaga tayi babu alamar zata bari, shikuma sosai kiran sunan Sagir din da take yake tayar masa da hankali, mikewa yayi shikenan tunda bazakiyi shiru ba sai kiyi tayi, amman kiyi iyaka daidai kunnen ki  ni karki daman"

Ganin yana kokarin ficewa tace ni kabani pic dina toh, bangaji da ganin sa ba, ina tsananin sonsa kuma ya tafi yabarni"

 Lumshe idonsa yayi yana jinjina mgnr har cikin ransa batare daya bude ido ba yace"

   Wannan yayi kadan, kibari zan bayar mayar miki dashi babban gilashi ta yadda zaki dinga ganin kamar shine atsaye agaban ki"

       Ni wannan nake so akirjina kadai zan rika daurawa"

   Runtse idonsa ya sakeyi sannan yace sai amiki guda biyu daya kamar tsayon ki daya kuma wadda zai mamaye kirjin ki, ko bakison kamar tsayon ki??, amiki daidai tsayi na??

    Nika bani abuna"

.

Bazan fah bayar ba, sai an kara mishi girma"

   Yaushe??

Ke zaki fada"

Yau"

Yau ta riga ta wuce gobema ban miki alkawarin ba saidai jibi”

     Kara karfin kukan tayi yayin da ya fita yaja kofar yana jinta tana cigaba da kiran Sagirrr!!


 Kasa komawa dakinsa yayi sosai yaji hankalin sa ya tashi, ransa ya kuma bacci sosai, duk da yanayiwa zuciyarsa fada amman ya kasa jurewa, 

    Zama yayi afalon tare da dafe kansa tsintan kansa yayi da fadin tacika rigima da yawa, ni yanzun yaya zanyi da ita ne"

 Yadda take kwala kiran Sagir yana matukar daga hankalin sa, pic din dake hannun sa Na Sagir ya kallah, murmushi yake cikin hoton kamar dai yana raye, fuskansa ya fara shafawa yayin da yaji hawaye na zubo masa, kuka yayi sosai  har yaji idon sa suna zafi, kasa dauke idon sa yayi akan pic din, jin gina yayi abayan kujerar tare da sheshekar kuka, saida yayi me isan sa, sannan ya mike ya nufi dakin sa har ya isa bebarjin kiran Sagir da Munirah keyi ba"

 Wayarsa ya dauka ya bude, pic din Aliya ya bude, yana kallonta, tsaye take cikin nutsuwa babu shirne attare da ita, gawani alamun kunya dako da yaushe baya rabo da fuskanta, ko sunanta ka kira saita nuna taji kunya tukun take amsawa, hawayen dake ziraro masa ya share sannan ya ya kalli na Sagir dake hannunsa yace Allah sarki, Allah ya jadda rahamarsa agareku"

    Rasa inda zai saka ransa yayi dan haka ya mike bayan ya aje wayarsa da pic din Sagir ya koma dakin Munirah"

   Wannan karon cikin mazurai ya shiga yana fadin"

Ke!! Bazakima mutane shiru ba??

    Rage karfin kukan nata tayi yayin data bishi da ido cikin zunburo baki"

Kusan minti 15 suka dauka haka sannan ya fita bajimawa ya dawo da ruwa kadan akofin ya zauna gefenta yayin da kunnensa ke jiyo masa jiniyan kukanta"

    Addu'a yayi cikin ruwan sannan ya gigiza ya nika mata amsa kisha"

Ni banasha????????????

   Sai kinsha"

 Bansha wlh, ganin ya mike ta daga hannunta tana me kare jikinta da fuskanta"

Hannun nata ya murde tare da  jawota jikinsa ya bankareta tare da dannan kofin"

Cikin sauri ta bude bakin ta ya zuba mata saidai taki hadiyewa dan haka ya kama kofar hancinta ya matse har saidata ya tabatar ta shanye sannan ya sausauta rokon da yaimats sannan ya dannata ya kwanta kan gadon tare da danneta da kirjin shi"

   Duk jikin su ya jike da sauran ruwan addu'a daya zube ajikin su, haura kafarta ta shigayi  dan kirjin shi kawai ya daura mata amman sai ihu take tana zaka kashe Ni, wayyo Enisilim!!"

  Yana sauke numfashi yake fadin, bazan daga kiba Allah sai kinyi shiru da bakin ki, surutun ne banso kimin shiru!!!

   Zanyi, wlh zanyi amman saika dagani????????

       Bazan dagaki ba"

Wayyo!! Nauyiiii!!! 

 Allah zan miki mugunta, idan kika bari na kirga uku bakiyi shiru ba wahala zan baki 

Dagani to nai shiru"

  Girgawa ya fara yi yana shirin fadin na ukun ta kunshe bakin illah numfashi da take saukewa"

   Tureshi tafara yayin da ya bita da ido yana fadin rufe idon ki kiyi bacci"

Rufe ido tayi da saurinta yayin da ya dan kara sausauta rungunar dayai mata"

   Daman yagaji sosai nan danan tafara sauke ajiyan zuciya daga can kuma yaji jikinta ya sake alama tayi bacci"

    Komawa yayi gefenta ya kwanta tare da mata matashi da hannun sa, kansa ya dago ya kalli fuskanta hannunsa ya mika yana gyara mata gashin kanta daya baje akan gadon har fuskanta"

Bayan yagama gyarawa murmushi yayi sannan ya sun bace ta, baki wuya goshi sannan ya sake gyara mata gashi"

Shiru yayi yana kallonta yana murmushi daga can ya fara tufa mata addu’a sannan ya sake sunbatanta aguraren da yayi da farko”

    Har yanzun kansa na dage a fuskanta ahan kali yakai dan yatsansa a saitin dukiyarta ya dan goge inda yake tunanin nanne samansa, ganin bata mutsaba yasake kai hannunsa ya dan murza ahankali"

 Hannunta yaga ta miki ta goge saman dukiyar tata yayi da ya zaro ido tare da dage hannunsa yana yarbawa kamar wadda ya taba wuta yayin da lebensa fuka hadu suka furta Wayyo,,????????

        Tsayawa yayi cak saida ya tabbatar bata tashi ba sannan ya mayar da idonsa kan dayan ahankali yakai gemun sa yana dan gogawa"

  Yadda tayi tazon ta sakeyi dan haka yai saurin janye wa yana sauke numfashi ya koma gefenta ya kwanta tare da daura hannunsa kan kirjinta"

         ********

Kiran Salla ne ya tada Munirah jin nauyi a kirjinta tai saurin ture hannun, shikuwa Sadiq yadda yaji an fizzgi hannunsa yasashi bude ido cikin tsare gida yace meye haka???

   Kawar da idonta tayi tare da fadin"

       Danne min kirjina kayi"

 Lunshe ido yayi sannan yai saurin tashi zaune yana fadin"

Kirjin banza, ina ruwana da wani kirjin ki"

 Wani gutun harara ta zafga masa saidai be kalletaba ya juya yabar dakin"

          *******

Misalin 6:44am Sadiq ya sake shigowa dakin Munirah yana sanye da farar jallabiya yayi nadi irin na buzo, bakin gilashi sanye a idon sa yayin da yake rike da Qur'ani hannun sa"

 Cikin sauri Munirah dake nike sallayarta ta kawar da kanta"

Kusan minti biyar yayi a tsaye sannan yace nina fita"

    Koda  bece mata komai ba tasan gurin Enisilim zaije suyi  karatu, tsintan kanta tayi da son zuwa kodan taga mutanen gidan, ahankali tace nima zani"

 Lumshe ido yayi zuwa can yace sai kinzo"

    Wucewa yayi abun shi, cikin ransa yana mamakin halin Munirah"

  Munirah kuwa bayan bayan shi tabi da harara bayan ta tabbar daya fita ta mike ta dauki lafayanta ta nada tana me fadin azzalumai, kazami kawai, insha Allahu sai kaga karshen ka, karshen ka bazai kyau ba, yana wani yanga da wani tsinin hancin sa kamar biro, yana wani rurrufe ido kamar tson mashaya, takalminta ta zura da saurinta ta fice adakin cikin gudu gudu"

             ***********

Lubbunah ce ta saurin mikewa azabure yayin data hango mutum cikin fararen kaya aguje"

 Cikin tsananin rudu ta shige bayan Mubarak tana me nuna masa abun da take hangowa"

  Hannunsa yasa ya riketa yayin dayabi inda take nuna masa da kallo"

    Tsaye yayi kawai cikin Mamaki yace Lubbunah kamar Munirah ce fah"

 Fitowa Lubbunah tayi abayan Mubarak hakan yayi daidai da shigowan Munirah gurin cikin zubar da takalma ta"

 Ke!! Lafiyar ki?, Anya kuwa kina da hankali????"

    Ni lafiya ta lau sauri nake"

  Sauri??, Ina Mijin ki?

Amukarnin Sadiq gashi nan zuwa yana hanya"

 Cike da fushi Mubarak yace yasan kin fito??

     Eh"

Ajiyan zuciya Mubarak yayi sannan ya nemi guri ya zauna"

Suma zama sukayi yayin da Lubbunah ta kalli Munirah cikin kuskus tace"

      Wai Amukarnin Sadiq din biyo ki yayi ne??

  A'a tafiyata daban tashi daban yana can yana ranga ahanya"

Murmushi Lubbunah tayi tare da fadi baki da hankali Munirah”

     Cikin Sallama Sadiq ya shigo gurin kamar tare suke da Enisilim, kallon Munirah yayi cikin mamaki domin shidai yasan ya barta agida, ajiye mamakin sa yayi agefe ya zauna"

        Gyaran murya Enisilim yayi sannan yace dawa zamu fara??

     Lubbunah da Mubarak Sadiq suka kallah yayin da Enisilim ke kallon Qur'ani dake gaban sa, shi kuwa Sadiq kansa ya dauke can gefe"

   Enisilim ne ya sake cewa Bismillah fah"

   Mikewa Munirah tayi ta matsa kusa, shiru gurin yayi harta gama"

   Cikin tsananin murmushi Enisilim yace yau Munirah hankalin ki ya kwanta"

 Dariya Mubarak yayi tare da fadin Ashe zamuga wannan ranar??

   Dariya akayi gaba daya banda Sadiq da Munirah"

   Sai nagaba Enisilim ya fada"

Wannan karon Sadiq beyi mgn ba dan haka Lubbunah tayi nata  bayan ta gama Mubarak yayi nasan sannan Sadiq"

      Bayan sunyi addu'a suka suka mike yayin da Munirah tabi bayan Enisilim kamar yadda ta saba"

Cikin sauri yace a’a maza kibi mijin ki”

Cikin kwalkwal da ido tana zan gaida Annanin ne"

A'a zan gaya mata sakon gaisuwan ki"

Badan ranta yaso ba tabi bayan Sadiq wannan karon tafiya take kamar kwai ya fashe mata”

     Afalon ta sama shi har zata wuce shi yace"

    Yaya akayi kika rigani zuwa?......


    Bana yanga ahanya"

 Lumshe ido yayi sannan ya daura kafa daya kan daya yace"

  Zauna kiyi min hirah......

   Ni daya?

  Eh"

Ani ba radio bace"

   Cikin lunshe ido yace nadauka radio ce ai, tunda bakin Ki yana ciwo idan bakiyi mgn ba, bari kiji da kyau, bazan yadda ki takura min ba, idan zaki saki ranki gara ki saki, babu ruwana da wasu kalam ki, nasan ni abokin gabanki ne, amman ni inason inji dadi, kuma kalamanki bazasu hani yin abun dana so ba  inyaso daga baya sai mu daura daga inda muka tsaya"

 Sauraron sa kawai take amman ko kalma daya ma bata fahimta acikin zancen ba,  abu daya ta fahimta yana nuna bubu abun zai fasa"

        Komawa yayi ya lumshe idoData bude lebenta ahankali tace can ta matse maka"

     Gani tayi ya mike dan haka itama ta zabura wani irin kallo yai mata sannan yace zamu hadu anjima zaki gaya min yadda akayi kika rigani kaiwa dazon.......

 Cikin sauri tace ni basai mun hadu anjima ba, gudu na yi"

 Murmushi tayi kadan batare daya kalleta ba yace"

Toh karkici  abinci kijirani har inzo"

 Ni abincina zanci bazan jirah kowa ba"

 Ficewa yayi cikin ransa yake dariya yayin da yana fita tace

Mugu kawai, duk abun da nake baya damun shi, saboda yasa zalunci agaba, daman ba kyaunata yake ba shiyasa ya yadda da wannan hadin dan ya gana min azaba, insha Allahu bazai dawo gida lafiya ba"

    Dakinta ta wuce waya ta dauka ta kira mahaifiyarta bayan sun gaisa tasa Kuka"

Meye haka Munirah?, Keda zakiji dadi ma kina cikin gida nan"

Ta yaya zanji dadi ankaini kurkuku an kulle, ashe har dake ma baki sona, ni dagayau babu ruwana da kowa agidan, kadama wadda ya kara nuna yasanni"

Hmmmm kai Munirah har yanzun dai yarinta na damun ki”

Cikin kuka tace Annanin??

Na'am"

Wai meyasa kuke cewa yarinya na damuna?

  Saboda har yanzun kin kasa nutsuwa"

Annanin, dan nace banson shi shikenan sai ace ban nutsu ba, toh ai Annanin shi hankali yana nufin kaso wadda baka so ne??

 A'a yana nufin kayiwa iyayen ka biyayya, kuma ko baki so ki danne ki daure sai kiga Allah yai miki sakayya da alheri"

Nidai Annanin kusani wani abun ba zama dashi ba, wlh banson shi natsane shi kuma indai kuka bari na cigaba da zama dashi wlh saina konamu ni dashi"

 Cikin tsayawa Annanin tace toh karki fasa, idan kin fasa kin raina Allah, na lura duka kike so?, Wanni irin mgn ne wannan kamar cin kashi, ko dan kinga anabari ki, toh har yanzun baki wuce duka ba, ki shiga hankalin ki, idan ba haka ba ko Mubarak ya ishe ki"

    Katse kiran tayi bayan taji Annanin ta rufeta da fada, Zarah ta shiga kira taba dauka ta fashe da kuka"

  Munirah menene??

 Ni ke kadai garan duk duniyar nan, kowa daya bude baki saiyace bani da hankali, ko ace bani da kunya, waisu saina zauna da Sadiq sannan zan cika me hankali, Zarah dole ne mutum yaso abun da baya so?, shikenan ni har abadan bazanyi hankali ba dan bazan taba son shi ba, dake mayen mata ne duk abun danai mishi bayyajin haushi, dake munafiki ne saidai kiga yana murmushi"

Tsaya kiji Munirah"

Ni bazan wani jiba, duk ba tsoho bane yaja min, insha Allahu sai Allah ya saka min, banson nakara Sati daya aduniya bazan sake cin abinci ba har in mutu, babu ruwana da kowa kuje kuyi tajin dadin ku

       Katse kiran tayi, cikin share hawaye haka ta wuni sosai Sadiq din ke kara kular da ita"

       Misalin 8:00pm Sadiq  ya dawo tunda taji tsayuwar motarsa jikinta yahau rawa"

       Cikin sauri ta sauko ta nufi kitchen tafara zuba abinci, jin shigowan sa ya kara sakata karkarwa,  nasa tafara haɗawa taje ta aje sannan ta debi nata tafara ci"

    Harta kusa cinyewa be fito ba, saida tagama tana gyara wajen taga shigowan shi, hannunsa dauke da mayan gilass din pic har guda biyu"

Cikin ranta tace ashe da gaske yake????

    Zama yayi yana kallonta bayan ya gana kare mata kallo yace"

  Kinci abun ci?...

En naci"

Kahh banso ba, dan Allah gobe karkici kinji?

  Dauke kanta tayi can gefe, 

 Babba gilashi hoton dake hannunsa ya mika mata duk biyu, hannu ta mika ta amsa"

      Cikin lumshe ido yace guda biyu ne dau naki kibani nawa"

Kallon pic din tayi har cikin zuciyarta ya burgeta sosai yai kyau gaban ta mika masa bayan ya kalla ya gigiza kansa tare da fadi na bayan ne nawa"

Tunaninta duk iri daya ne dan haka ta kai idonta gurin”

Wani mummunan faduwan gaba taji, runtse idonta tayi zuwa can ta bude tare da yi masa wani irin kallo.........

????????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????
????
SAWUN BAYA
????
Book 2 ????????
????????????
????????????????????
????????????????????????????

                    *Na*
          *_Fadeela Lamido_*

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

® PEN: WRITER’S ASSOCIATION

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️


~only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers~


——–PAGE——-

https://www.facebook.com/110384724043172/

——–GROUP——–

https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/
        *Page 19- 21*
     Typing........????️

Cikin sauri ta sake maida kallon ta kan pic din dake hannunta”

Jimmm tayi sannan ta maida dayan ta hade su guri daya"

Bani nawa taji ya sake fada”

Batare data kalleahi ba tace"

    Ina so duka"

Kansa acan gefe yace bangane kinaso dukka ba??

Itama cikin zunburo baki tace kabar min"

  In bar miki??, 

Kaita daga yayin da ya waigo ya kalleta tai saurin dukar dakai”

    Wannan ba adallaci bane Tamudiriccin, inace jiya kika rungume pic din kina fadin wayyo Sagir din ki?

  Ai Aliyar ma yaya tace"

Lumshe ido yayi, naji Sagir dinki Aliyan ki, ni kuma ki mayar dani inda aka roro ni, amman wannan pic din bazan bar miki shifa soboda shi nake kallo nakejin dadi, Ina kewanta sosai, bata barina da yunwa tunkan na aureta take kula dacina acikin gidan nan, dan haka nake alfahari da ita,  haka bayan na aureta tamin biyayya wadda bana tunanin akwai wata wadda zata iyayin irin sa, nayi rashin da har abada bana tunanin zan iya samun makwafin sa ba, bani abu na"

 Kwalkwal ta yi da ido tana kare rike hoton"

    Shikenan idan har kina son pic din Aliya saai in saya zaki yi"

   Zan saya to, nawa??

    Kallonta yayi ya lumshe sannan yace"

         50k

    Wani irin kallo take mishi cikin kasa kasa da murya tace wannan abun ne 50k?

         Cikin Yaren buzanci yace toh kibani abuna mana"


  Mikewa tayi tana turo baki naji zan biya, kace bayan ka aureta ma tama biyya ai ranar da aka daura auren ta rasu"

   Lumshe ido yayi batare daya bude idon ba yace naji ni makaryaci ne kenan?

   Hanyar dakin ta ta nufa cikin daga murya yace, yau zaki bani kudin idan ya wuce yau bazan sayar ba"

    Wucewa tayi batace komai ba tana shiga dakin ta watsa su akan gado tare da sauke ajiyan zuciya, rasa meke damunta tayi"

  Enisilim ta shiga kira bugu biyu ya dauka cikin girmamawa ta gaidashi"

 Amsawa yayi yana shirin jin korafi daga gare ta yaji tace"

      Abbanin, dan Allah kudi zaka bani"

          Jimmmm yayi, cikin tunani domin tunda yake da ita bata taɓa roƙon sa kuɗi ba cikin sanyin murya yace, nawa kike so??

          50k

Toh da safe zan aika miki dashi”

   Jimmmm tayi sannan tace dan Allah Abbanin kaban yau"

 Jimmm yayi, take zuciyarsa ta shiga saka masa abubuwa da dama, inda zuciyarsa tafi karfi wajen ganin Munirah guduwa zatayi dan haka yace"

 Munirah, tsakanin ki da Allah me zakiyi da kudi??

  Jimmmm tayi itama, zuwa can ta shiga in Ina Amukarnin ne na saya wani abu agun shi kuma yace waishi  idan ya wuce yau ya fasa"

   Jimmm yayi sannan yace, Munirah niba yaro bane, wannan ba zancen da hankali zaidauka bane, nidai nasan nabaki tarbiyya daidai gwargwadon iyawa ta dan haka ina rokon ki karki zubarmin da mutuncina, ina tabbatar miki idan kikasa kafa kibara dakin mijin ki toh fa na yafe ki"

     Abbanin nifa wlh gaskiya nafada"

  Toh naji, kibari da safe zanyi mgn dashi"

        Abbanin ka kirashi ma yanzun kaji"

 Toh naji, saida safe, katse kiran yayi batare dayajira wata mgn daga gare ta ba"

     Jira taitayi har kusan 11 Enisilim be aiko ba, ayanzun tsoron shigowa Sadiq kawai take ji  tunanin kiran Umma tayi dan haka cikin sauri ta kirata"

      Bayan ta dauka gaida tayi sannan tace"

  Munirah lafiya kuwa??

  Umma kudi zaki ara min"

 Cikin fargaba tace kiyi me dasu da tsohon daren nan?

       Abu na saya kuma daren nan ake son kudin"

Ikon Allah, Munirah aina kikayi sayyar ke kuwa?

  Umma agun Sadiq ne"

 Lumshe ido tayi ganin har yanzun Munirah bata girmama Sadiq cikin sanyi tace duk da cewa dai wannan mgnr kuce amman kice mishi nace ya baki gobe yazo ya amsa kudin"

  Cikin kukan shagwaba tace Umma bazai yadda ba fah saidai in yau zaki bashi"

 Toh ya turo min account number sa yanzun"

Kashe wayar tayi sannan ta nufi falon saidai bata sameshi agurin ba dan haka ta nufi dakin sa"

  Sallama tayi ahankali ta shiga yana zaune laptop agaban sa yana aiki dashi"

 Lebensa daya motsa yasa tagane ya amsa, saidai ya daure fuskan sosai"

Ahankali  tace, umma tace ka tura acct no ka"

Lumshe ido yayi sannan ya lashi lebe yacigaba da aikin sa

       Ganin ta dade tsaye bece komai ba ta juya ta fita, wanka tayi tai shirin kwanciya zuciyarta  cike da damuwa wadda ta rasa hanyar da zata billowa lamarin"

     Gadon tahau ta kwanta duk zuciyar ta bubu Dadi"

 Shigowansa ta hango saye cikin kayan bacci,  beko kalli kan gadon ba taga yana waige wage adakin sannan ya wuce inda ya hango abun da yazo neman"

Daukan nasa yayi tare da gyarawa nata zama ya daura na hannunsa akirjina sa ya fice"

   Fitan Sadiq yayi daidai da zubowa hawaye daga idonta"

 Tashi tayi ta zauna tana cigaba da zubar da hawayen take fadin"

 Nashiga uku an hadani da makiyina, bakayi karya ba kuwa dakace bazaka taba samun kamar Aliya ba, ai anayin aure sabo da soyayya ne, nikuma banson ka, banda ma zallici ya maka yawa, yama za'ayi ka yadda da aurena?, Haka kurin yariya dani ahadani da kwarto me tsose bakin yaran mutane, Allah ya isa miyon ka dakabani nasha, 'yarka ce ni da zaka matse ni ka dura min abinci, nasan ko bance Allah ya saka min ba saiya saka min wlh Allah ya isah ban yafe ba, harda wani wai yana kewanta, munafiki bansan kana kewanta ba saika aure hoton tukuna, mayen mata kawai"

    Wata zuciyar ce tace mata kinata masifa ke daya wadda kike danshi besan kinayi ba'a

Tsaki taja sannan ta sauka kasa ta dauki pic din tana shafa fuska sa tace"

     Dayanzun munajin dadin mu, da tare dakai nake yanzun dana tsukane ka munyi danbe, gemon sa ta shafa tace da kullum sainaja nan gurin, abun dake baka dariya kenan, kaita dariya inajin dadi, duk abun da zan masa fushin ka akaina kadan ne, kuma banso inga kayi fushin, Allah yajikan ka Sagir, kuma tanadin dana maka bazan taba barin Sadiq ya moreshi ba har abada, katafi baka taba taba wani ba wani bangare najikina ba, sannan nima nayi kokarin tsare kaina, nasan indai zan bari tabani zaiyi dan shi nakula bejin tsoron Allah"

 Kusan kwana tayi agurin, tayi kuka hawayen ya bushe anjima ta kumayi gafda za'a kirah Sallah asuba wani tunani ya fado mata cewa yanzun Sadiq yana can shima ya kwana da hoton Aliya ahannu"

     Tsintan kanta tayi da da mikewa ta leka dakinsa hangosa tayi kwance kan gado hotun agefen sa"

    Falon ta dawo ta zauna cikin rasa abun yi, kiran sallah ya tabbatar mata yanzun zai fito, bajiwa kuwa ya fito yana gyara wuyan rigarsa ganinta afalon tabashi mamaki"

  Ke!!! Me kike anan guri??

       Iska nake sha"

 Toh yayi, juyawa yayi zai fice ta sakeyi mgn"

Batare daya juyoba yace me kika ce??

        Ahankali tace, ban son ka"

   Mene??

  Ban son ka nace"

 Toh naji, shikenan in wuce??

 A'a

Toh inajin ki”

Sakina zaka yi"

 Bakina Ni bazai taba furta wannan kalmar ba"

Toh ka rubuta min"

 Na manta da alkalamina a Ingall"

  Dagowa tayi suka hada ido sannan tace, barin kawo maka nawa"

Ni hannuna baya iya amfani da alkamin wani"

Cikin turo baki tace toh nidai nace banson ka"

Ainaji, kuma daman nasani bakya sona"

Jin tayi shiru yasashi ya wuce abun shi, acikin ransa yace lallai yariyar nan tana da karfin hali"

 Ko bayan ya idar da sallah fitowa yayi yana mejin zafin mgnr sakin data mishi, shiyafi komai kona mishi rai"

   Inda ya barta agurin ya sameta, kallonta yayi yace"

 Kinyi salla kuwa?

   Turo baki tayi ni ban sallah ne "

  Toh yayi, jini kike? 

     Turo baki tayi tare da kifkifta ido sannan ta kawar da kanta

kokarin shiga dakin yake yaji tace”

Ni ka sakan......

 Cikin mazurai sosai ya dawo gabanta ya tsaya, nagaya miki uzurina ai bazaki samu abun da kike so ba agurina Ni"

    Cewa fa kayi kamanta alkalami ka a Ingall?

   Eh

Hawaye ta fara matsowa ni ai nace ban son ka, tunda nace ban son ka ba shikenan ba saika sakeni ai"

    Tsaki yaja cikin jan ido sosai yace ke idan kika kara cewa in sake wlh sainai miki dukan tsiya

     Mikewa tayi hawaye sosai afuskanta wlh ban son ka kuma har abada bazan soka ba"

    Nima bance kisoni ba, ko ki soni ko kada Allah yasa ki soni dole ki zauna agidan nan kuma ki haifi ya'yana, banson ki daina cewa baki sona kinji ko"

     Cafdijan, toh zamu gani kuwa, wlh bazaka taba samun yadda kake so ba har ka gaji ka sakeni"

 Wani irin tokari yakai mata yayin datai saurin kaucewa, cafkota yayi tare da kai mata mari"

  Kara ta kwallara cikin fashewa kuka"

Jikinsa na rawa yace kira cewa in sakeki kiga abun za zan yi”

     Tana dafe da kuma tun ta tace toni mena maka, daga mgn sai akama dukana sabo da iyayena basu damu dani ba suka baka ni batare da an gaya min ba, nikuma wlh bame taba min jiki na"

   Meye ajikin naki?, magana ba mgn ba kice wani jikina jikina, ke!! Wai tunanin ki akwai abun da zaki iya yi ne?, Wlh ko yau nagadama zan kwanta dake"

   Sauke hannunta tayi cikin kifkifta ido tare da huhura hanci da murguda baki irin yadda marasa kunya yara keyi ta nufi dakin tana ta fadin hiii'innn hiii'innn  lallai????

         Bugo kofar tayi lokacin da yake cewa idan na rikeki sai kin manta dangin ki"

                  ********

Umma ya min duka zai kashe Ni wlh zuciyata naimin ciwo, ya tattakani kuma ya mareni”

Bismillahir Rahamanir Rahim, me kika masa??

  Wai dan nace ya sake ni"

 Cikin sanyin jiki Annanin tace"

 Toh ke meye naki nacewa ya sake ki?

Umma ban sonshi"

Kafin Annanin tai magana taji muryan Mubarak yana cewa nagaya muko sai an zane yariyar nan, rashin duka ke damun ta"

  Cikin sauri ta kashe wayar tare dajin wani irin faduwan gaba"

     Hoton Sagir ta kama ta runguma har ga Allah gani take Sagir ne kaɗai gatan ta, domin ayau ta tabbatar wa kanta cewa bata da gata tunda tasan ko Enisilim ta gayawa ya dageta fada zai mata"

   Muryan Mubarak dataji yasata saurin mikewa ta jingina da bango hoton Sagir rungme akirjinta"

        Tare suka shigo da Umma cikin saure ta shige jikin Umma yayin da Mubarak ke kokarin kai mata duka "

    Annanin ce tace karka taba ta tsaya tukuna inji"

Cikin fada yace ke!! Dan uba ki bazaki nutsuba ko?

 Shigowan Sadiq cikin shirin fita duk suka kalleahi hankalin sa kwance suka ganshi"

Cikin ya mutsa fuska yace Lafiya me tayi ne???

Lallai, me tayi kake tambaya?, bayan ka gama cin ubanta"

   Kawar dakai yayi yayin da Annanin tamaida kallonta kan Munirah hoton hannunta ta karba ta kallah sannan ta kalli idon Munirah tace"

   Me kike yi haka, meye amfanin daukan hoton Sagir?

    Sunkuyar dakai tayi, yayin da jikin Annanin yai sanyi sosai ta kalli hoton ta kalli Munirah zuwa can tace"

          Munirah ko kina tunanin Sagir zai dawo ne??

  Kanta ta girgiza, yayin da Sadiq yazuba hannunsa cikin aljihu ya kureta da ido yadda tayi kamar jikinta yai sanyi"

     Annanin ce tace toh meye amfanin daukan sa da kike yi, kina son ki dinga tayarwa kanki da hankali koda yaushe ko, kwata kwata wannan hoton be dace ba adakin nan, ina laifin ma kusa afalo sai ki dauki pic ki rike kina kallo kina kuka, toh sai yaushe hankali zai kwanta, nina haifi Sagir Amman aduk sanda zan kalla hoton shi wunin ranar banayin sa cikin sukuni, dan haka wannan ma tafiya zanyi dashi, idan kin kwantar da hankali ki zan dawo muku dashi kusa afalo tunda dan uwanku ne.......

    Shima akwai na Aliya a dakin shi"

Cikin sauri Sadiq ya kawar dakai yayin da Annanin tamaida kallon ta gunsa tana fadin”

 Au abun da kuke yi kenan?

  Kansa ya sake kawarwa cikin daure fuska sosai Annanin tace Mubarak jeka dauko min , wucewa tayi ta fice adakin, tana fadin idan kaga dama ina neman ka"

Bata jirayi amsa da ba ta fice , hararan Munirah yayi sannan ya fito dakin adaidai lokacin da Mubarak ya fito da pic din Aliya “

 kallon sa yayi sannan yace"

Meye naga kanata faman huci??

   Munirah naso na zane"

Meta maka?

Wani irin kallo Mubarak yaimasa cikin ido"

    Shima Sadiq gilashin idonsa ya cire sannan yace matar auren zaka buga??

   Dariya Mubarak yayi batare daya shirya ba sannan yace batajin mgn ne"

      Kaifa kanina ne?

Dariya Mubarak ya sakeyi sannan yace nikuma ai Munirah kanwata ce"

 Toh kardai ka soma taba ta, wlh karka tabata, nasan tana nuna min kiyayya amman batayi gaba na, gabana tsiwa kawai take min dan haka abunta baya damuna, yau daya tamin rashin kunya kuma nasan abun daya bata haushi, dan haka kada wadda ya sake sa mana baki, kubarni da ita"

 Cikin murmushi Mubarak ya karyar dakai tare da fadin shikenan"

   Har suka isa part din Annanin Mubarak Satan kallon Sadiq yake cikin ransa yake tunanin da alama Sadiq yafara son Munirah"

Dan haka yaketa satan kallonsa yana murmushi”

Bayan Mubarak ya kaiwa Annanin sakon ficewa yayi, yayin da Sadiq ya zauna agurin"

Cikin bacci rai Annanin tace biye mata zakayi kaima, baka ga yadda dan’uwanka ke mata ba, yanzun kai bazaka lallabata ba?

 Cikin hade giran sama data kasa yace Annanin nifa duk ta inda tabi dani haka zan bita"

Ashe kuwa zaman bazai taba dadi ba, karshen ta saidai araba auren, ai inace ko auren soyayya kukayi saika bita ahankali"

Ni bazan bita ba Annanin ita zata bini "

 Au haka kace?, toh shikenan, nikuma zan zuba muku ido inga yadda za'ayi, nasan dai kana son Munirah, daka daina takura kanka ka nuna mata so, idan kuma kace kai ba hakaba nan gaba ko ka sakoni ciki bazan shiga ba"


      Toh mema zai faru Annanin wacece ita"

 Murmushi Annanin tayi bayan taga yadda yake mgnr fuskanshi daure sannan tace"

      Matar Sadiq ce ita, aikuwa yariyar tawa kaima kasan ta wuce ace mata haka, son kowa kin wada ya rasa, ko ka manta wancen lokacin da keke ajiyan zuciya kullum cikin jan ido?

Murmushi yayi kadan sannan yace banso Annanin, duk kauta ai bata fini ba”

  Kaidin banza, ai macece ita"

    Mikewa yayi yana fadin bata iya komai ba sai tsiwa da rashin kunya"

    Tsiwan ya burgeka ai "

Kashh Annanin gaskiya ki bari banso”

     Bazan bari ba, miskilin banza da wufi kawai, zaka sani ai"

 Sauri ya kara tare da murmushi sosai afuskan sa"

  Motarsa ya shiga har ya isa Office murmushi ne fal ransa

       Hakama bayan ya taso aikin daka ganshi kasan yana cikin farinci, kai tsaye  part dinsa ya nufa bega Munirah afalo ba kuma be nemeta ba har yai wanka ya wuce masallaci, koda ya dawo gurin iyayen nasu ya zauna dan yaga su atare sunacin abinci, shima nan yacibtare dasu be barosu ba sai 10:00pm, 

 Wanka ya sakeyi yaishirin bacci har ya kwanta yaji wani irin yanayi ya sameshi, tunda yafara sanin sha'awa betaba yin wata biyar batare daya taba mace ba sai wannan karon dan haka yaudin yakejin sha'awa na dada fisgarsa"

  Munirah ce taita fadu masa arai duk da cewa bayason ya tabata ayanzun, amman abun da yakeji yana neman ya zarta nako yaushe, domin betabayin sex ba Saida Aliya Kuma yau irin yanayin da yake hangowa kenan dan haka sha'awan da yakeji tafi ta kullum betabajin irinta ba"

Kokarin cijewa yaitayi amman ya kasa, sakkowa yayi agodon sannan ya fara tafiya tare da kare abunsa data kumbura"

    Rigar bacci ne ajikinsa daidai guiwa yayin da gabanta abude yake  inda take da madaure daidai cibiyar sa"

     Gilashin sa ya dauka kan madubi ya sanya a idonsa sannan ya fice"

    Munirah kuwa daman jiya bata samu bacci ba dan haka yau tunda wuri tai bacci, kan gado ya sameta kayan baccine ajikinta baya iya tantance irinsu, saboda yadda ta bankare cinyoyinta duk waje kirjinta kuwa duk da cikin rigar bacci suke kamar tsirara haka yake kallon su lukui lukui 

 Harcen sa ya fito dashi ya lashi lebensa na kasa sannan yayi wata mgn ahankali.......

????????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????
????
SAWUN BAYA
????
Book 2 ????????
????????????
????????????????????
????????????????????????????

                    *Na*
          *_Fadeela Lamido_*

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

® PEN: WRITER’S ASSOCIATION

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️


~only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers~


——–PAGE——-

https://www.facebook.com/110384724043172/

——–GROUP——–

https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/
    Page 22- 25

Typing……????️
Ahankali ya karasa gabanta, tare da zama abakin gadon”

  Ido ya zuba mata ta cikin gilashin sa yake hangota sai Kara bankarwawa take"

Yanayin kwanciyar ya kallah, wacce karon ma daya shiga dakinta haka ta lankwashe, acikin ransa yace wannan yariyar bekanata abarta taje wani waje ta kwana ba, lebensa ya motsa yana me cewa idan ba haka ba ana iya samun matsala"

 Mikewa yayi tsaye sannan ya dauki ƙafarsa daya ya daura kan daya tare da dan dukawa kanta, kallonta yayi na tsayon lokaci yayin da yake sauke ajiyan zuciya"

    Har yanzun yana cikin bakin gilashin fuskarsa daure tamau yayin da wajen sa da gilas din idonsa kadai ne baki aji afuskanta, daga inda yake duki ya fara hura mata iska bakin a kirjinta"

  Cikin sauri takai hannunta ta goge gurin yayin daya koma daya gefen ya hura nan na hannunta takai ta goge tare da kara lankwashewa"

 Murmushi yayi, ahankali ya furta Tamudiriccin,????

     Gani yayi ta sake motsawa tare da jan wuyan rigarta sama"

          Hannun sa yasa ahankali yaja rigar kasa har abebaden ta suka bayyana"

  Ajiyan zuciya sake yi cikin shashiyar murya yace"

 Keee!!!

 Ahankali ta bude idonta ganin sa asaman kanta gabanta ya fadi sosai"

  Dugon hancinsa kawai take gani sai kuma bakin gilas dinsa wadda yasa bata iya ganin idonsa, waigawa tayi ta kalli ƙafarsa Faransa saul dake gefin cikin ta sannan ta daga kai ta sake kallon sa, rumfa yai mata sosai cikin dakiya tare da yamutsa fuska tace"

Meye??....

Nazo kibani nunannen mangoro ????”

   Nunannen mangoro??

 Eh"

Bandashi"

Baki dashi??

Eh, idan kuma ka gani ka diba mana ni ina ruwa na"

  Kawar da kansa taga yayi kamar yana neman wani abu dan haka itama ta maida hankalin ta inda yake kallo din, wani irin fizga taji anyi wa wuyan rigarta inda taji tsinkewan sa tana shirin mayar da kanta gunsa kawai taji sa ajikin ta yayin daya kafa bakin sa kan...???? yana masu wani irin tsotsa"

  Kokawa ta fara yayin da take bige fuskansa tana kurma ihu"

  Hannunsa yasa ya danneta amman duk da haka hanbareshi take tare da kwace hannunta yana sake kamawa wani lokacin tai nasaran ture kansa yayin da yake maida bakinsa dayan gurin, har yanzun gilas dinsa na idonsa yayin da yake fitar da numfarfashi yana sake yage rigar jikin sa sannan ya kara danne Munirah"

   Jin inda take kurma ihu ya saki can ya kama bakinta, dole tabar ihu saidai gurnanin kuka yana danne da hannunta"

 Hankalinsa yagama tashi gabaji bagani inda yafara kai hannunsa inda Munirah bata taba tunanin zai iya yimata hakan ba rigicewa tayi sosai tare da kara dagewa, sosai yaji Munirah nada karfi dan haka ya bude mata karfinsa gaba daya dan yasan idan yabarta zai shiga wani hali saidai kashh alokacin da yake shirin shiganta ya kula bata da tsarki yayin da mgnr su ta asuba ta dawo masa, kahhhh ya fadi da karfi sannan ya mirgina ya koma gefen ta ganin ya sauka tai kokarin guduwa yayin da yasa hannunsa daya ya jawota yayin dayai mata runfa ya sake kama kirjinta akaro na biyu"

   Allah ne ya bata saka'a ta kwace hannunta ta maka masa agefen kunnensa,  take gilashin sa ya karye ya fada fuskanta inda tai saurin yi jifa tashi kasa"

 Karan gilashin dayaji ya tabbatar masa ya tashi aiki, tunawa yayi yaji jigida a kugunta batare daya cire bakinsa akirjita ba yasa hannunsa ya kama jigidar ya murde sa shi akugunta ta saki kara sannan ya finceketa ta ta tarwate yayin da kakejin karan watsewan sa akasa"

  Kuka tasa sosai dan sosai inda ya murde jigidar ke mata zafi karfinta ya fara karewa shima tanajin sa sai wani gurnani yake yi rasa hanyi tayi dan haka ta lankwso wuyanta ta yayin data kafa masa haƙora ta awayan shi cikin gantsara masa cizo"

  Duk irin dakewan darayi amman gani tayi kamar kara kaime yake inda yake wani irin gurnanin kamar mayunwaci zuwa can taji ya kankameta tare da sauke ajiyan zuciya, Kuma ataitai wannan lokacin ya sake hannuwanta daya dane"

Itama cire bakinta tayi a wuyansa tare da fadin Allah ya is.....

   Radadin dataji agefen cikinta ya hanata karasawa, kara ta saki me karfi jin Sadiq na cizonta"

Shima Sadiq Jin inda ta kwallara kara yai saurin sakinta sannan ya koma gefen gadon ya kwanta"

  Kuka Munirah ta cigaba dayi zuwa wannan lokacin muyarta ta dishe shafa gurin daya cijeta tayi, yanzun zafin ya dan rago kirjintama zafi yake hakama bakinta, runtse idonta tayi tana fadin, wlh Allah ya isa, bazan taba yafewa ba, wutar kabarin ka ka tsotsa kuma"

    Cikin Wata irin murya yace naji bakomai"

          Ai wannan ma zallici ne, in ba hakaba nace ban son ka banson ka amman ka nace"

Nima banson ki ai, Tsohu ya hadani dake, badan hakaba me zanci dake mummuna dake, kazamiya......

    Wlh ni ba kazamiya bace tunda bana kama bakin wani in danne shi in tsotsi miyon shi, duk cikin kuka take mgnr dan haka Sadiq yayi murmushi yana me lumshe idonsa yace"

Nine karazamin kenan??

   Kuka taci gaba dayi yayin daya rufe idon shi har yanzun yana kwance agefenta inda yakejin kukan ta na damun shi"

 Idonsa ya bude sannan ya tashi zaune ya mika hannun ya dauki rigarsa dake can karshen gadon yana daga zaune ya yasa sannan ya daure daidai cibiyar sa ahankali ya bude abun rufan yaja rigar kasa sannan ya sauka agadon yanacigaba da gyara rigar ya nufi toilet dinta"

   Kara karfin kukanta tayi  ta yadda zai daneshi cikin sauri yai wankan ya fito daure da towel ko kallon inda yake batai ba kuka kawai take"

  Shikuwa Sadiq yana goge cikinsa yana kokarin fita dakin yace, idan kin gadama kiyi shiru ki kuma kwanta kiyi bacci ki dan banga abun da nai miki ba.....

     Allah ya isa!!!????

  Naji"

Kuma banson ka har abada bazan taba son kaba!!!

Nima bance kisoni ba ai, jan kofar yayi ya rufe mata sannan ya wuce dakinsa ya kwanta”

  Bacci befi na awa dayaba asuba tayi dan haka ya tashi yai alwala ya wuce masallaci koda ya dawo beje gun Munirah ba dan yasa irin zancen da zataitayi yau kenan"

            ****

Tamudiriccin??

Cikin Yaren su tace niba kanwarka bace”

Lumshe ido yayi sannan ya canza harce shima yace”

Meye nufin ki?, Bazaki tashi ki gyara gurin nan ba?

 Wlh bazan gyara ba ai bani nabata ba"

 Hannunsa ya zuba aljihu sannan yace"

  Nidake muka bata ai, kina nufin nine zan zauna nagyara mikin daki?

 To kowa ya gyara abun daya bata"

Murmushi yayi sannan ya kalli jigidar tada watse akasa yai murmushi sannan yace bazan gyara ba sai in kin yadda zaki ban mango ????”

  Tsaki tayi tare da kawar da kanta sannan tace wlh Allah ya bacci"

   Ko gyangyadi ma bayayi, juyawa yayi ya fice adakin"

  Sabon kuka Munirah tasa ita kadai tasan radadin da takeji jikinta tskuma zuciyarta, azzalumi kawai saidai yaita zallinci kuma shi saboda kafiran zuciya garai duk abun da za'amin bayajin zafi, jarabbe kawai me lashe yaran mutane, ko kunya bayaji fuska duk gemu yana ma kanwar bayansa mugunta,  ka tabani kuma kaji dadin Allah tsine, insha Allahu bazai amfane ka da komai ba, wannan dagani yasa yiwa ya'yan mutane fyade, duk iskanci ka nafi karfin ka, irin wadda mgnr zuciya Munirah taitayi tana kuka dan haka kafin wani lokaci zazzaɓi ya rufeta"

    Sadiq kuwa bayan ya kama hanyan Office murmushi yai tayi wani irin nishadi yake ji saboda dadin daya shiga daren jiya, dadi ne nadaban, nakuma musamman, domin kowa abune wanda suka dade suna daukan hankalin sa, kuma suna bashi ha'awa, wadda kamar mafarki daren jiya ya gaisa dasu"

    Dariya yayi har hakoransa suka bayyana tare da bada sauti sannan yace"

Yanzun nasan su, sun kuma Sanni, kuma naga sun amince dani, suna kuma kaunata dan haka Ni banda matsala”

Lasan lebensa nakasa yayi sannan ya shafa gashin kansa”

               ********

Lubbunah dan Allah kidanzo banda lafiya”

 Mijin ki fah?

Sadiq benan yaje aiki”

Toh ki kirashi mana"

Cikin sanyin murya tace dan Allah kizo mana Lubbunah”

   Keni bangi ina gurin aiki"

 Jimmmm tayi sannan dace dan Allah fah nace Lubbunah

    Munirah wlh da gaske nake naje gurin aiki amman kibari dana dawo nan zanyo"

     Katse kiran tayi sannan ta kira mahaifiyarta har sau biyu bata dauka ba, Enisilim ta kira shima be dauka ba, hawaye ne ya shiga gangaro mata akwai alamar fushi suke da ita jikinta sanyi yayi sosai wani irin yanayi ta shiga wadda yasata kiran Umma batare data shirya ba"

Bugu biyu ta dauka, tana fadin Munirah ya kike??

 Umma banda lafiya"

 Meke damun ki??

 Zazzaɓi da ciwon kai"

Ina Mijin ki”

Sadiq ya fita tunda safe?

 Kallon agogo Hajiya Fatima tayi 11:35am sannan tace besan baki da lafiya bane??

Kara fashewa tayi da kuka tace yasani”

   Cikin rashin jin dadi tace shikenan, zaki iya zuwa nan?

Umma bazan iya tashi ba"

 Toh sannu gani nan zuwa"

Sauke wayar Hajiya fatima tayi sannan ta dauki lafayanta jah ta nada tare da ɗaukan wayan ta tafice”

   Tun afalon tafarajin kukan Munirah, sanin Sadiq baya nan yasata shiga kai tsaye, tsayawa tayi cak tana rike da kofar yadda taga dakin yasata tai danasanin zuwa ta ji tayi kamar ta juya saidai ba yadda zatayi cikin kawar da idonta ta karasa shiga dakin tare dacewa Munirah ya isa kibar kuka"

Kanta ta taɓa taji zafi rau sannu tace sannan ta juya ta shiga toilet zuwa can ta dawo ta daga Munirah zaune tare da fadin Muje kiyi wanka sai akaiki asibiti"

    Mikewa tayi tare da dafe gefen cikinta da sauri"

 Munirah cikin na ciwo ne?

Kokarin bude cikinta take Annanin tai saurin cewa a'a???? bace ki nuna min komai ba muje"

Kara karfin kukanta tayi Umma cizon nafah yayi????????????????????

   Cizo?, Mugani"

Budewa tayi yayin da gurin yai jawur cikin baccin rai Annanin taja tsaki sannan tace muje”

  Gurin kokarin Shiga toilet din Munirah tace Umma barin yi, zan iya"

 Sanyi Annanin taji cikin ranta sannan tace Yauwa Munirah kiyi kwari da jikin ki"

     Shigewa tayi ta turo kofar yayin da Annanin ta waiga ta kalli dakin cikin rants tace ikon Allah ,????

 Rarasa ta ina zata fara tayi sabo da kunya irin ta buzaye, ta dade tsaye, yayin data rasa ta ina zata fara, kiran Sadiq tayi yana dauka tace kadawo yanzun nan kakai Munirah Asibiti, katse kiran tayi batare data jira amsan sa ba sannan ta sake kallon dakin"

  Daga can ta dauki tsintsiya, dakin dai babu datti illa wannan kwallayen jigidan sai kuma ballen gilas din Sadiq adaidai lokacin da take kwashewa Munirah Munirah ta fito"

       Tana rawar sanyi ta fito sannan ta isa gaban mudubin ta zauna tana kallon jigidanta idonta cike da kwalla tace Umma zubarwa za'ayi?

Toh meye fanin sa Munirah?

Umma inason Abina fa Annanin ta sayamin Agadez babu irinsa anan fah????????, wlh sayya biyani abuna bazan yadda ba????????

  Nidai nace kiyi hakuri, kibari ni zan sawo miki wani idan naje, dan Allah kiyi hakuri Munirah kibar irin wanannan mgnr"

  Kuka ta shiga yi tare da share  hawaye har Annanin tagama sharan bata bari ba bayan ta dawo tace bazaki bar kukan ba"

  Cikin wasa da yatsunta tace Umma bani da kowa yanzun Annanin da Enisilim subar daukan wayata kowa haushina yakeji zuciyata kullum ciwo take min bani da me sona duk duniyan nan daman Sabu da Sagir ne ake min fara'a yanxun kuma dan anga bashi kowa ya tsane ni"

    Cikin takaici Hajiya Fatima ta dafe kanta sannan ta kalli bakin Munirah kamar badaga cikinsa zancen ke fitowa ba tace"

   Suwaye ke basusan ki??, Munirah idan kina son kiji dadin rayuwar ki saikin gyara halin ki, banda hauka irin naki iyayen naki kikecewa basu son ki?, Ina tabbatar miki sun miki haka ne dan ki gane suna fushi dake kin ki kwatar da hankali ki, amman ba saboda kiyayya ba"

 Cikin share hawaye tace kenan dole saina bi abun da banso sannan zasu soma kulani?

Kusan hakan ne Munirah, amman yanzun ke Sadiq din kike cewa baki so?

  Ni ban son shi Umma"

 Wani abu ta hadiye sannan tace shikenan tashi ki shirya mujirashi afalo"

   Shiryawa tayi  suka fita falon  har yanzun jikinta zafi rau"

           *********

Yanzun karfe nawa?

Agogon dake daure ahannunsa ya kalla yace 01:14

   Sai yanzun kaga daman zuwa??

Kansa ya shafa sannan yace aiki nake lokacin yanzun ma na taso ne kawai”

    Meyasa ka fita bayan kasan Munirah babu lafiya"

Munirah ya kallah sannan ya kalli Annanin yace Ki daina biyewa zancenta Annanin karya takeyi lafiyarta kalau"

Lafiyanta lau?, ita ta ciza kanta kenan?

   Kawar dakai yayi da sauri sannan yace Annanin karya take makira ce kawai"

  Hmmmm wlh kaji kunya Sadiq, bantabaji ba tunta nake, wani irin haline wannan gareka??, Munirah fah Sadiq ka bude bakin ka ka kafa mata hakori????????

  Kawar da kansa yayi sannan ya daba wuyansa yana fadin"

   Diba Annanin, ita tafara fah?

  Wuyansa ta kallah gani tayi har nasa gurin ya fashe sannan ta kalli Munirah ta sake maida kallonta gun Sadiq tace macece ai ita dan ta cijeka ba wani abu bane wato ramawa kayi?????????????????

 Can gefe ya sake kawar da kansa hannun sa cikin aljihu yace"

    Eh Annanin namata hakane dan tasan ni bana bari, dan ni wlh ko kare ya cijeni saina rama.......

????????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????
????
SAWUN BAYA
????
Book 2 ????????
????????????
????????????????????
????????????????????????????

                    *Na*
          *_Fadeela Lamido_*

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

® PEN: WRITER’S ASSOCIATION

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️


~only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers~


——–PAGE——-

https://www.facebook.com/110384724043172/

——–GROUP——–

https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/
         *Page 26- 28*
       Typing.......????️

Dagowa Munirah tayi da sauri ta kalleshi adaidai lokacin da Umma kecewa”

   Au haka kace?, Shikenan, mikewa tayi ni barin je, tunda haka kace, amman ni bazan iya ganin wannan iskancin ba,  zanyi mgn da iyayen ku, subaka matarka kubar mana gidan, idan ka illatata sai kazo ka musu bayani"

Kansa ya shafa zuwa keya, Annanin toh ya zan mata, kuma da kuke iyayenta ku rasa yadda zakuyi da ita, tunda batajin mgn gara akoya mata hankali"

Ai kai kasan yadda zakayi da ita, wlh bazan iya ba, suma dai mance halin ka sukayi, har suka haɗaka da Munirah, yariyar nan ayanzun rarrashi take bukata"

Hannun Annanin ya kama suka fita waje, yayin da ya shiga ce mata ni fah Annanin ina sane nake mata haka, idan nabari haka duk zatai ta cijeni, yanzun kuwa nasan bazata sake ba"

Dagakanta tayi ta kalleshi, yayin da suke jerawa tace”

  Kana fa son yariyar nan, mezaisa bazaka lallasheta ba?, Idan kana mata haka tunawa zata dinga yi da Sagir, tana daukan ka mara kirki, ina baka sharawa karkayi amfani da cewa kafita karfi ka dinga kuntata ma zuciyar ta, ita tanajin bata son ka, can gefen iyayen ta nafushi da ita saboda tana cewa bata sonka, suna mata tilas ta zauna dakai, kai kuma kana mata mugunta, ina kake son taji sanyi?, Kaine mutum na farko daya kamata ka kwantar mata da hankali, wlh Sadiq matsawar baka rarrashinta  ba, hankalin ta bazai taba kwanciya ba, ko waye zai rarrasheta aduniya, baka ganin inda Sagir yake mata ne?, Indai ahaka zaka tafi bazatar tunanin sa ba"

  Sakin Annanin yayi ya zuba hannun sa aljihu yana tafiya yana fadin"

  Karta bari Annanin, kibari ki gani zanyi magani ta"

 Waigawa Annanin tayi ta kalleshi cikin tsabar takaici tace"

     Bazaka bari ba kenan?

 Wai ke Annanin sai in zauna taita cizona"

  Wata rana bazata cizaba ai, mace fah sarauniya ce Sadiq"

      Ni Kuma Sarkine ai Annanin"

 Cikin sauri Annanin ta kalleshi, yayin datai saurin kama gefen cikin shi ta tsungula sosai iya karfinta ta rike"

    Waigawa yayi bayan suna ganin babu kowa yace'

 Wayyo banso Annanin"

Zaka sake cizon Munirah??

  Dariya yayi, Annanin da zafi fah"

   Bazan sake ka ba wlh, saika amsa min, zaka sake bude hakuranka kacije Munirah?

Cikin nuna yanajin zafi yace a’a”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button