NOVELS

SAWUN BAYA 1 & 2 COMPLETE HAUSA NOVEL

????????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????
????
SAWUN BAYA
????
Book 2 ????????
????????????
????????????????????
SAWUN BAYA BOOK 2

     ????????????????????????????

                    *Na*
          *_Fadeela Lamido_*

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

® PEN: WRITER’S ASSOCIATION

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️


~only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers~


——–PAGE——-

https://www.facebook.com/110384724043172/

——–GROUP——–

https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/
       *Page 1- 4*
  Typing........????️

Wani irin gudu yake akan titin zuciyarsa cike da wani irin fargaba, rasa a inda yake yayi gaba daya mafarki ko gaske, tsintan kansa yayi da fara zufar da hawaye”

Cikin ikon Allah ya iso gidan nasu yayin dayaga jama'a curko curko wasu ma kuka suke yi"
    Sakkowa yayi kafarsa babu takalmi ko wayarsa be iya daukowa ba kamar zai tashi Sama haka yake tafiya har ya isa falon Mahaifinsa daya samu kofar bude"

    Tsaye yayi abakin kofar, yana me kallon abun dake faruwa cikin dakin"

   Yayin da duk iyayen su mazan ke zaune suna buga wayan sanar da abun dake faruwa daga can gefe kuwa Mutum ne shinfide anrufeshi da Zanin Annanin, yayin da yaga Munirah kwace Kan zanin, Annanin na gefe ta hada kanta da guiwa" kowa kuka yake tare da share hawaye"

   Sadiq kuwa kamewa yayi agurin tare da zuba hannunsa cikin aljihun sa"

     Jin kuke kukem dake tashi na dada yawa cikin tsawa sosai yace Wai meye kuke yi haka kamar wasan yara?

   Enisilim ne ya daga kansa ya kalleshi tare da mikewa ya karaso gurin sa dan ya tabbatar rudewa ce ta sameshi"

    Dafashi yayi yana fadin shigo kaga dan uwanka Allah yafimu so, ganin ya cuge agurin ya fara jansa izuwa har gaban gawan Sagir"

Tsugunawa yayi saitin kansa yana fadin Annanin Ina Sagir??

  Cikin sauri ta runtse hannunsa tare da hadeye wani abu me daci tace gashinan agaban ka Sadiq"

    Hannunsa yai saurin sawa ya yaye zanin tare da zuba idonsa akan sa, jikin sa babu ko kwarzane illa gefen kunnen sa daya kunbura sosai, fuskansa ta gara haske yayin dayai wani irin kyau kamar balarabe, wani irin sihirtaccen murmushi ne kwance akan fuskan sa wadda Sadiq yake ganin kamar shi yake mawa, wani gitaccen Kara Sadiq yasa batare daya shirya ba yayin da mutanen gurin suka Kara karfin kukan su ganin yadda ke kuka"

       Mahaifin sa ne yace meye haka Sadiq??

Abbanin yanzun nan muka rabu dasu fah, yanzu yanzu fah Abbanin????????  

  Yanzun yanzun din aina Allah ne Sadiq, muyi hakuri kawai dukkan me rai mamaci ne"

  Ganin inda Sadiq ya bude fuskan Sagir yasa Munirah ta dago tana kallon shi fuskanta wanke da hawaye cikin matsancin kuka take fadin"

  Ya rabbi kadau raina nima, bazan iya dauka ba, shiyasa kaketa cemin in hakuri Ashe tafiya zakayi kabarni, Amukarnin Sagir dan Allah katashi, tunjiya nakeson ganin ka, kace min yanzun zaka dawo, dan Allah katashi Sagir cikin rudu take mgnr yayin da take shafa fuskarsa cikin matsanancin kuka"

  Riketa Annanin tayi tana fadin Munirah sai hakuri muyi hakuri haka Allah ya tsara Allah yasa bazakuyi rayuwa tareba"

 Wani irin kuka Munirah take cikin Kara yayin da take fadin Ya rabbi ka dau raina ratuwata Bata da amfani"

   Haka shima Sadiq yana tsugune gaban Sagir din sai shashekar kuka yake sosai kamar karamin yaro"

 Shirye shiyen yin wankan gawan da ake yasa matan suka fita yayin da Annanin take rike da Munirah"

    Daker Munirah ta fita, yayin da mazan suka shiga suturta Sagir kamar yadda addinin musulunci ya koyar bayan an gama kammalawa sannan aka sake Kiran matan dan suyi addu'a, zuwa wannan lokacin fuskar Sadiq ta kunbura sutum yayin da fatar fuskarsa tai jawur"

  Munirah kuwa tazama abun tausayi kuka kawai take, yayin da take zaune dirshen  agaban gawan Sagir hakama Sadiq wannan lokacin durkushe yake gaban shi yana futar da sheshshekar kuka, Annanin ma nazaune gefe cikin dakiya take masa addu'a, da karfinta takeyi tare da yabon kyawawan dabi'unsa da yadda takejin Dadi kasancewarsa da agareta 

Tare da masa fatan aljanna madauwamiya”

  Yadda Sadiq ya kasa mgn hakama Munirah kuka kawai take, cikin fada Enisilim yace toh kutashi ku fida, shi Sagir adaidai wannan lokacin yafi bukatar adda'a ba kuka ba, wannan kukan ba soyayya bace wadda yasan bazai iya ba yaje daga waje"

 Ahankali Sadiq ya sausauta kukansa yayin daya doka zuwa saitin kunnin Sadiq bayan kusan minti 5 ya mike ya nufi kofar batare da yana kallon gabansa ba"

  Munirah kuwa takasa yin komai duk yadda ake Mata fada tai shiru takasa har Saida aka shigo daukan Sagir din domin kaisa gidan sa na gaskiya????????????????????

      Sadiq Mubark da Moh'd sai Kuma yayen su da wasu daga cikin a bokan su, ganin su hankalin Munirah ya Kuma tashi yayin da suna saka hannun su Kan makaran ta daura nata cikin matsanan cin kuka take fadin"

   Wayyo Allah na nashiga uku, zasu rabani dashi, Amukarnin karka tafi kabarni, Sadiq na zubar da hawaye ya kalleta da yadda tarike makaran dakau ahankali yace mata Sake Munirah"

   Allahu akbar, tasake fadi tare dakara saka karfinta, zasu rabani dashi, wayyo Allah na ya rabbi kadauki raina inhuta, bazan iya dauka ba wlh, zasu rabani dashi, wlh bazan iya rayuwa babu kaiba Sagir????????????????

     Hankali Sadiq ya daura hannun sa yana kokarin banbare hannnuta yana fadin, yi hakuri ki saki Munirah????????"

    Yadda yadda yasa mata karfe dole ya banbareta yayin data Kara kwallah Kara tana kokarin sake jawowa, ganin sun daga sama yasata fadin"

Wayyo Allah mijina!!!, Wayyo Sagir mijina!!! Ya rabbi kadau raina zuciyata zata fashe, riketa akayi dan haka dole ta tsaya daga nufin binsu da tayi"

         **********

Har aka yi Sallan Sadiq bebarjin ihun Munirah ba acikin kunnen sa, da yadda take Kiran wayyo mijina, har suka isa makabartan kukanta ne ke masa yawa sosai tabashi tausayi”

 Cikin dauriya da dakiya irin wacce Allah kisawa duk wani wadda yaiyi rashin danuwan shi suka saka Sagir adakin sa na gaskiya tare dayi masa addu'a sosai sannan suka juyo yayin da hawaye yaki Tsayawa a idon Sadiq, Mubarak da Kuma iyayen su maza domin wannan ne matuwa mafi zafi da aka taba masu cikin wannan family, har yanzun uwa da ubansu nanan Kuma acikin jikokin Sagir ne na farko da aka taba dauka dan haka sosai mutuwar tasa ta tabasu su"

    Sadiq ya kasa tsaida hawayen sa yayin da yake ta tuna wasu kalamai na Sagir yana share hawaye, kallon Mubarak yayi yace Ina Aliya take Mubarak??

    Asibitin zamuje yanzun"

Lumshe Ido yayi yayin da wasu hawayen suka zobo masa shiru motar tayi har suka shiga asbitin"

Cikin sauri yakebin bayan Mubarak yayin daya tura wata kofa yashiga”

Mahaifiyarsu Munirah ce zaune taci kuka itama ta koshi yayin da Aliya ke yashe akan gado jikinta duk jini, kanta Sadiq ya nufa da wuri ya zira hannunsa cikin nata yana fadin"

 Aliya??

Ahankali ta bude idonta ta kalleshi sannan tamaida idonta ta runtse, juyawa yayi ya kalli mutanen dake dakin, ganin Haka duk sukayi waje yayin dayai saurin maida hankalin sa gurinta"

    Aliya?, Kibude idon ki mana"

  Jiran budewan yake harna tsayon wani lokaci ganin babu alamar zata bude yasa shi shafa kansa tare da fadin"

    Wayyo Allah na, Aliya kimin mgn mana, idan bazakiyi mgnba,  dan Allah ki bude idon ki ki kallan, Ido ya zuba Mata natsayon lokaci sannan ya sake cewa, kema Zaki tafi ki barmu ne??, Dan Allah karki tafi kinga Sagir ya tafi kiyi hakuri ki zauna tare damu dan Allah Aliya ki zauna damu"

 Hannun sa yaji ta runtse cikin nata besan sanda ya saki ajiyan zuciyaba sannan ya tsuguna ya sunbaceta yayin da yaji itama tayi ajiyan zuciya, ahankali ya sake cewa"

   Aliya"

 Bude Ido ta sakeyi Karo na biyu, Ido suka hada yayin da Sadiq yace meye ya same ku haka Aliya, lafiya dau muka rabo, meya sameku bayan rabuwar mu"

Ahankali ta mayar da idon ta ta kule ganin Haka Sadiq ya hada kansa da jikin gadon yana me share hawaye”

Kujera Mubarak ya Mika masa yana fadin zauna Sadiq"

 Dawa yayi da baya ya zauna sannan ya share hawaye tare da bude buturin gaban rigarsa sabida zafin da yakeji"

    Mubarak Wai garin Yaya haka ya faru??

  Hmmm waddan da dai suke wajen abun ya faru sunce wata motace ta shigo masu Kuma me waccen motar ma be ko motsaba kamar Sagir Aliya ce kadai adauketa darai wajen"

Innalillahi wa'innalaihir raju'un Sadiq ya fada tare da sake share hawaye sannan yace ko minti 20 bamuyi da rabuwa ba, ninasa masa Aliya amota, duk nine najawo wannan abun da ban fita agidan ba da Sagir bazai fitaba shima, ni bamma San meyasani fitan ba???? haka kawai natashi nafita ninajawo, nine wlh, kafin afara daura aure Banda niyar fita haka kawai nashiga wani yanayi wadda narasa gane kansa????????????????????

Kadaina irin wannan mgnr mana, ko Sagir yafita ko be fitaba bazai wacce wannan lokacin ba, yakamata ko wanni musulmi yasa wannan aranshi, idan lokaci yayi koda ciwo ko babu, ko awanni irin yanayi kake na arziki ko na tsiya da lokacin ka yayi za'a zare ranka ne kawai dan haka ka daina daurawa kanka laifi"

     Idan shi lokacin sa ne yayi Aliya fah?, Kanafa gani ko mgn Bata iyawa, bude idonta ma ya gagara"

   Zata samu sauki insha Allahu, addu'a take bukata yanzun Allah ya tashi kafandanta"

Ameen, idan Bata tashi ba bazan taba yafewa kaina ba, nasan batason fita awannan lokacin biyayya kawai tamin tabini, Allah yabaki lafiya Aliya”

    Kuka yayi me isarsa sannan ya tsagaita, kallon sa Muburak yayi yace muje gida nasan za aita neman ka masu zuwa gaisuwa"

 Ni kaje kawai Mubarak, ni Ina nan, Sagir ya riga ya tafi, wadda yazo gaisuwa nagode Amman ni Ina nan zan zauna na kula da matata"

   Kazo muje mana anjima sai mudawo tunda ga Umma tana nan anan "

 Bazan iyaba Mubarak kuje kawai"

Cikin sanyin jiki suka fita shida Muh'd sukabar Sadiq agurin"

 Ganin Sadiq na gurin Umma ta zauna awaje yayin da Sadiq yaita zama har dare"

                 ************

 Kallon kowa daidai take, yayin da dacin zuciyarta yake sake karuwa, wannan lokacin saidai kawai hawaye yazobo tasa hannu ta share tare da kurban ruwan da Annanin ta aje Mata agefe batacewa kowa komai saidai idan lakacin Sallah yayi tayi takuma saka tagumi"

  Annanin ce ta duba agogo taga karfe 11 nadare ta wuce, mayar da kallonta tayi Kan Munirah tace"

   Munirah kallah agogo kiga dare yayi, tashi kihau gado"

 Hawaye ta share tare da girgiza kanta"

       Munirah dan Allah kiyi hakuri hakanan tashi ki kwanta, dagata tashigayi ta daurata agadonta tana fadin"

Kiyi hakuri karki jawowa kanki wani ciwon Kuma sai hakuri"

  Gefenta Annanin ta kwanta saidai itama ta kasa bacci Amman batason Munirah tagane Dan haka tai shiru kamar tana bacci"

  Wani irin shashekar kukane yasata saurin tashi zaune Munirah tagani ta zame kasa cikin wani yanayi dake nuna rashin hankali tace"

 Annanin shikenan yanzun mu muna kwance akan gado Sagir yana cikin kasa????????????

Hawaye Annanin tashare cikin kauda Kai sannan tace”

 Munirah kiyin hakuri dan Allah kidaina irin wannan tunanin"

 Bazan iyaba Annanin, toh waini meye amfanina?, Meyesa aka halicceni?, Ki tayani addu'a Allah ya dauki raina nima"

A'a saikace ba musulma ba Munirah, Sagir nina haifeshi amman kinga nayi hakuri kema kiyi hakuri ki kwanta kiyi baccin ki dan Allah"

Ni bazan iya bacci ba Annanin, duk ga mutanan arasa wada za'a dauke sai Amurkanin Sagir"

Bakinta Annanin tai saurin dannewa Munirah zakiyi sabo"

 Ba Sabo bane ba wlh annanin, kiyi tunani ki gani ga Wanda yadace a dauke nan dayawa Amman aka dauk.......

       Nace kiyi shiru ko, kwanta, jikinta ta kwantar da ita haka suka zauna sai kusan 12 Sadiq ya turo kofar"

Dagowa Annanin tayi ta kalleshi sannan tayi ajiyan zuciya tare da sauke Kan Munirah dake cinyanta, tahowa tayi tare da bude masa hannunta"

    Cikin sauri ya fada jikinta tare da rungumesa, wani irin fashewa yayi da kuka wadda yasa Munirah ta tshi zaune tana kallon su"

Bayan sa Annanin take duka cikin rarrashi take fadin”

Yi hakuri, bakomai Sadiq Allah yafimu sonshi, Kuma shi tashi tayi kyau, kowa yabon halinsa yake, mayya da yara, Kuma yarabu damu lafiya insha Allahu Sagir yadace dan haka mudaina damuwa, mutuwa tanakan kowa dole kowa zai mutu"

     Sausauta kukansa yayi yayin da Annanin tashiga share masa hawaye tare da fadin"

   Ya jikin Aliya??

Jikinta yana bani tsoro Annanin, batasan inda kanta yakeba, batacewa komai Bata motsi Annanin saidai tabude idonta ta rufe"

Insha Allahu zata tashi Sadiq ka kwantar da hankalin ka"

  Sheshshekar kukan dayaji yasashi dagowa daga jikin Annanin yace waye can??

Munirah ce, ta kasa bacci, tunda Sakon nan ya samemu take kuka”

Dafe kansa yayi yayin daya tuna mgnr su ta karshe da Sagir lokacin dayace masa ya kula da Aliya, yana bude bakin sa sai yace, ni Kuma tawa danabarta a gida wazai kular min da ita, kawar da idonsa yayi ya share hawaye, yasan dole mutuwar Sagir zata jigatata"

Ahankali yace akwai ruwa ne akusa"

      Ruwan da tajewa Munirah ta nuna masa yayin da ya tsayaya Rabin kofin yakai saitin bakinsa, addu'a yayi ya tofa cikin ruwan sannan ya girgiza ya mikawa Annanin yana fadin bata wannan Tasha zatayi bacci insha Allahu"

   Kinsha tayi duk yadda Annanin taso Tasha taki Saida tayi kamar zata daketa sannan ta amsa tasha kadan"

    Sallama yayiwa Annanin sannan yabar dakin, daren ranar nan be iya runtsawa ba kwata kwata, washegari yanayin Sallah ya koma Asibiti"

             Misalin 2 narana, Sadiq ne rike da hannun Aliya, Munirah na zuwan su kenan tana jikin mahaifiyar ta tana sheshshekar kuka"

 Rarrashin ta takeyi sannan tace matsa kije kiga Aliya kibar kukan haka?

 Matsawa tayi suka jeru da Sadiq, cikin sauri ya mike ya matsa gefe tare da zuba hannunsa cikin aljihun sa yana binsu da kallo"

Cikin kuka Munirah tasa hannunta cikin na Aliya, cikin dashesgiyar muryarta tace"

 Aliya?

 Ahankali ta bude Ido ta kaleta fuskan ta dauke da wani irin Murmushi"

Kinga andauke mana Amukarnin Sagir ko?, Duk ga mutane amman sai Sagir aka dauka?

 Runtse Ido Aliya tayi tare da Kara runtse hannun Munirah"

 Allah yabaki lafiya Aliya,???????? munrasa Amukarnin Sagir, idan muka rasa ki gidan ya mutu gaba daya, duniyar tabar dadi bazata sake Dadi ba, babu sauran wani Jin dadi ko farinciki, nidaman tun jiya nasan narasa komai nawa, narasa farin cikina bazan sake barin ciki ba????????

Runtse hannunta kawai Aliya keyi yayin da takewa Sadiq Alamar ya matso da idonta, matsowa yayi, ahankali Munirah ta zame hannunta yayin da Sadiq ya rike hannun nata yana matsawa da Ido ta sakeyiwa Munira mgn cikin sauri ta kawar da idonta gabanta na sake faduwa”

 Mubarak ne yace Munirah matso Aliya na miki mgn"

  Cikin tsoro tsoro ta matsa, hannunta take dagowa yayin da Sadiq yake kokarin cire hannunsa Amman saiyaji ta rikesa tana kokarin dago da hannun nasu gaba daya, cikin kokarin saukaka Mata yacewa Munirah kawo hannun ki"

Cikin zabura tamaida hannun nata can baya ta hadesu abayan tare da girgiza kanta tana me fashewa da kuka”

 Mahaifiyar su Munirah tana daga gefe tana kallon duk abun da yake faruwa, hawaye take sharewa, yayin da hankalin ta ya tashi sosai munira ma fashewa tayi da kuka bayan ta isa jikin bango ta hade hannunta da bangon"

 Ahankali Aliya ta saki hannun Sadiq tare da cigaba da dagowa Munirah da hannun, Mahifiyar su ce takama hannun Munirah saidai cijewa Munirah take dan haka tasa Mata karfi tana fadin"

 Kina kallo tana kiranki koma dai meye saiki duba halin da take ciki aiko?, Cikin sheshshekar kuka ta tsaya agabanta yayin da Annanin su ta kama hannun Munirah tasa ana Aliya, tsayawa tayi ta kalli fuskan Aliya ahankali ta bude idonta ta kalli Sadiq sannan tadan dago hannunta, cikin sauri Annanin takalli Sagir dayai kasa da kansa yana tsiyayar da hawaye hannunsa ta kama dayai kasa dashi sannan ta dafe hannun Aliya Dana Munirah ta daura na Sadiq akai, kin sake tayi tana danne da hannun Sadiq dayake Kan na Aliya da Munirah dan tasan tana cire hannunta Munirah zata fizzge nata, kallon Aliya ta sakeyi taga ta lumshe Ido tare da ajiyan zuciya, itama lumshe Ido tayi hawaye suka zubo Mata sannan ta kalli Sadiq tace rike su Sadiq"

  Kamar jirah yake ya kama hannun nasu duk biyun dakyau, duk da irin fizzge hannun da Munirah take son yi bazata iyaba hawaye yaketa tashewa yayin da Munirah ta kunshe baki tana wani irin kuka baki rufe kamar rago"

    Sun dade haka sannan sukaga Aliya tayi wani irin Murmushi tare da barin idonta abude "

Ido Sadiq ya kura Mata ganin yadda tabar idonta abude yanzun”

Annanin kuwa cikin matsancin kuka ta bude kofar dakin ta fita, hakama Mubarak fita yayi yana share hawaye"

 Wani likitane ya shigo ya isa Kan Aliya bayan yayi aune aunen sa ya kalli Sadiq yace ku sake ta"

Sakin hannun nasu yayi yayin da Munirah tacire nata tana kallon Aliya da idonta suka kafe, zani likitan ya karfa ahannun Annanin ya rufe Aliya dashi ganin Haka Sadiq ya tsuguna agurin tare da daura hannunsa duk biyun akansa"

 Munirah kuwa fita tayi aguje yayin da Mahaifiyarta tabi bayanta"

       ???????????????????? Wayyo 
 Allah kasa mucika da Imani"

       Sadiq da Mubarak ne suka dauko gawan Aliya daga Asibiti, kuka ahankali sukeyi zuwa wannan lakacin tamkar hawayen su ya kusa karewa, itako mahaifiyar Aliya cikin ranta take fadin wannan wacce irin kaddara ce me zafi"

  Munirah ma guri daya ta zubawa ido sai take ganin kamar an canza duniya"

  Ko kafin suje gida samun gidan sukayi curco curco, labarin ya riga ya isa"

   Bayan an kawo gawan Aliya enisilim fada yaita masu Annanin cewa suyi da jiki ai maza akaita"

  Haka ko akaya nan danan aka suturtata bayan yan uwa da dangi sun Mata addu'a aka nufi kaita gidanta"

   Karfe 6 na yamman har anyi an gama yayin da suka dawo gida suka tsuguna"

    Zuwa wannan lakacin Sadiq yayi kuka irin wadda betabayi ba, yadda yake kuka betaba tunanin akwai abun dazai sashi kuka haka ba, daya motsa Sagir da Aliya yake gani kowanni cikin su kokarin kyautatawa kowa sukeyi su haka halin su yake, badai su sucuceka ba ko a kalami saidai Kai ka Cuceshi su, afili yace"

Tunda nake bazan taba cewa ga abun da Sagir yamin ba, saidai ni in mishi, hakama Aliya bazan ce ga abun da take min ba, saidai insa Mata doka tabishi ko Bata so, ya Allah Ina rokon ka kasa Aljanna tazama makoma agare su????????????????????????

  Cikin irin wannan rashin dadin nazuciya da rashin walwala har sukayi kwana 10 da rasuwar su"

 Xuwa wannan lokacin Munirah tarame sosai idan tana tafiya tamkar iska zata hure"

 Haka shima Sadiq yayi rama Sannan kullum cikin kuka yake gefen idonsa har wani baki yayi"

   Gidan babu wani Dadi kowa ka gani bashi da wani walwala, hakama mahaifiyar Sagir tarame sosai har zazzabi Saida tayi"

Munirah kuwa Mutuwan Sagir yataba mata rauwarta kamar yadda mutuwan Aliya ya taba rayuwar Lubbuna"

 Yau tun Safe Munirah ke kuka domin yau Da suka cika Sati biyu da rasuwa Kuma ayaune mutanen ingalla zasu koma dan haka hankalin Munjrah ya tashi sosai Zahrah da suke kwana tare yau zasu wace"

   Ganin sai hada kaya suke ta tashi taje gurin Annaninta cikin kuka tace"

      Annnanin Nima zan bisu Ingall"

A'a Munirah babu inda Zaki, ai gidan sai abun yai masa yawa"

 Nidai dan Allah kubarni inje can karki hanani Annanin"

Shikenan, kije ki tambayo malam idan ya amin ce shikenan"

 Mikewa tayi tana sanye da Dan karamin hijjabi suka fito daga can gurin shakatawan suka hangesu afarfajiyar gidan da alama wani zama suke na musamman, iyayen nasu maza Uku sai Kuma Baba tsoho da Matarsa sannan Sadiq dake zaune acan gefensu ya lankwashe hannun sa duk biyun akirji, yayin da yazubawa guri daya Ido fuskar nan tasa babu alamar walwala"

  Hankali suka zaga kofar da ake shiga guri tare da Sallama"

 Shiru sukayi gaba daya tare da bin Munirah da kallo, da alama surri suke yi agurin"

  Cikin fara'a sosai Alhaji Mustapha yace Munirah Yaya dai??

 Baba ninaxo ne ince maku zanbi su Ingall"

  Cikin sauri Enisilim yace a'a keda kike kuka za'a baroki acan Kuma kece Zaki iya zama acan???

Batare data shirya ba tace wlh zan zauna ni da nake fatan zuwa lahira ma a ina ne bazan zauna ba?

 Murmushi sukayi gaba daya sannan Alhaji Mustapha yace"

   Ba'aja da ikon Allah Munirah, kiyi hakuri sannan ki amshi kaddara Banda rigima"

 Aina amsa Baba, shiyasa ma nake son naban garin"

  Baba tsohone yace babu inda zaki kin amsa din ne kike cewa zakibar garin, da wani bakin ki me kaudi anan gurin, wannan bakin naki yasa iyayen ki kamar ma tsoronki suke ji"

 Kwalkwal tayi, cikin turo baki tace, tsohu babu ruwanka, nidaman nasan basona kake yi ba, Kuma duk gaku nan Amman aka dauke Amukarnin na, ga babba memakon adau Kai aka dauki karami"

Kawar dakai Alhaji Mustapha yayi hakama enisilim daya fahimci da Sadiq take, shi kansa Sadiq din cikin sauri ya kawar da kansa can gefe yayin dayaji gaban sa yayi wani irin faduwan"

 Tsohone yace dan gidan ku bazan tafi ba saiga 'ya'yan ki, Kuma ki gaya min waye Babban da akabari?......

Mammah ce tace ko shakka banai da Sadiq take, aina gaya maka halinta”

  Ni babu ruwana da halinta,  wannan matsalar kuce, juyawa yayi cikin canza harce, da yaren buzanci yace, Sadiq kana tsoron kaudi??

   Cikin daure fuska sosai kamar beson maganar shima cikin yare yace"

A’a”

 Lumshe Ido Munirah tayi acikin ranta take dawo da zancen nasu, bakin ki yana da kaudi shiyasa iyayen ki ke tsoron ki, da Kuma yanzun dayace ni babu ruwana da halinta, tuna me yacewa Sadiq bayan ya canza harce yasata mikewa batare data shirya ba.......

????????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????
????
SAWUN BAYA
????
Book 2 ????????
????????????
????????????????????
????????????????????????????

                    *Na*
          *_Fadeela Lamido_*

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

® PEN: WRITER’S ASSOCIATION

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️


~only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers~


——–PAGE——-

https://www.facebook.com/110384724043172/

——–GROUP——–

https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/
  *Page 5- 7*
Typing......????️

Bayan ta tsaya binsu da kallo tayi daya baya daya yayin dasuma suke binta da kallo”

Cikin sauri tabar gurin cikin gudu gudu ta isa part dinsu, Kan gadonta ta kwanta tai rufda cikin cikin zurfin tunani yayin da take share hawaye"

 Sai bayan kusan awa daya da shigowan ta Zarah ta shigo ganin shigowan nata Munirah tai saurin tashi zaune tana kallon zahra tace"

     Tun dazon kina gurin ne???

  Eh Ina gurin"

Mgnr me suke yi??

 Bawata mgn suke ba kawai hira ce suke"

Ido takurawa Zarah, jikinta macce yake sosai dan haka ta tabe baki sannan tace, bawani nan ni naji ajikina wata mgn suke, jikina nabani akwai abun dazai faru, Kuma ni dan narasa Amukarnin Sagir  baza'a takurani ba, bama zai yiyu bane wlh"

Munirah ki kwantar da hankalin ki babu ma abun da zai faru insha Allahu, tsoro dai kawai kikeji, Amman ba komai, su yanzun ma cewa sukayi mubari sai anyi arba'in sannan mu wuce bawata mgn bace suke yi"

  Ajiyan zuciya Munirah tayi sannan tace, Allah yasa haka Zahra, kin San tsoron da nake???

   A'a 

 Tsoro nake karsu ce zasu min aure?

Babu wannan mgnr Munirah, idan ma akwai ai bawani abu bane badan Allah ya karfi Sagir ba dayanzun kina dakin ki"

 Wannan daban Zahrah, ni yanzun babu aure araina har abada, bazanyi aure ba, zamana zanyi ahaka har tawa tasameni, dan Sagir kadai akayo ni"

Cikin sanyin jikin sosai tace haka ne, ki kwantar da hankalin ki"

Tsaki taja tare da kawar dakai sannan tace kinsa abun dake kona min rai?

 A'a Munirah sai kin fada"

Nakara tsanar Sadiq, shine nan ya kashe Amukarnin na, Kuma shiya kashe Aliya"

 Subuhanallahi, dan Allah Munirah kibar irin wannan mgnr"

 Himmmm nayi shiru, shiyasa daman ban fadawa kowa ba, dan nasan baka zakuce, Amman bazai taba gogewa ba, shine nan ya fita da Aliya bayan daura aure, sabo da tsabar jaraba, wlh natsane shi, shine nan ya rabani da masoyina, Ashe shiyasa tun farko natsane shi"

  Wani irin hadiye yawo Zahrah tayi sannan tace, kidaiyi hakuri Munirah, mutuwa lakacin ne, da bakin ki kikace min Sagir nata cewa kiyi hakuri, tunda bikin ku ya taho hakuri yake yawan baki, bakyayin tunanin Sabo da irin wannan lokacin yaita baki hakurin?, yanzun duk abun da akace miki dan Allah karkiyi mgn ko bazakice toh ba, toh kiyi shiru kawai da bakin ki"

     Wani irin kallo Munirah taiwa Zahrah, Sannan tace nifah babu memun wayau, tunda nake aduniya Amukarnin Sagir ne kadai ya taba min yawo tunda ya mamayeni ya mutu yabarni, da ace nagane wayo zaifi wlh duk inda yaje saina bishi, dan haka babu wadda zan sake Bari yamin wayo aduniya, basan sake yadda da kowa ba,  Kuma bansan girman tsananin son da nake mai ba Saida na wayi gari naga babu shi adoron kasa,????????????, dan haka nifa abarni kawai son Sagir bazai taba gogewa azuciyata ba bare har na iya zama da wanin sa, Kuma da suke cewa Ina da kaudi suje suyi ta cewa ni ko ajikina, dan Sagir yamin wayo sai Kuma in daina mgn acuceni, Allah dayaini da bakina yamin ne dan in kwatanwa kaina yanci dashi"

    Wanni irin kallo Zahra tamata sannan tace haka ne, Amman dai duk da haka, kiyi hakuri, wadda ya mutu ya riga ya mutu, nidai mutuwar nan ta tabamin zuciya dakau, Kuma nagane babu kyau ka tsani abu da yawa, dan bakasan abun da Allah zaiyi nan gaba ba"

    Babu zato babu tsammani taji Munirah tace toh nidai ko sama da kasa zata hade bazan auri Sadiq ba????????????????"

  Baki Zahra tabude sannan tace toh ke waye yace miki Zaki aurei???

      Oho miki, ainasan zaman can da akayi wani kulle kullen munafunci tsohu ke kullawa Kuma kin sani bazaki fadamin bane, wlh ji nake kamar inje in samu rami inshige inyi zamana nidaya har mala'ika yazo daukan raina

       Himmm Ashe kuwa Zaki dade aramin"

Bangane zan dade arami ba???

 Toh ai ba yanzu Zaki mutu ba"

   Wani irin kallo taiwa Zarah sannan tace wlh Zahara kin zama muna fuka, mikewa tayi cikin fushi tabar dakin, yayin data samu mahaifiyar ta afalo"

  Yaya dai Munirah??

   Annanin nifa tsoro nakeji"

 Tsoron me??

Ni kar ace za amin aure da Amukarnin Sadiq

    Wanni irin kallo Annanin ta Mata sannan tace daga Ina Kuma wannan mgnr?, 

   Naji tsuho dazon yana wasu mgn ne ai"

Da kikaji yana mgn yace miki wani Abu ne???

   A'a

Toh ki kama bakin ki, banson rigima meyasa ke kin fiye rashin hakuri ne?

  Toh nidai Annanin ko sama da kasa zata hade bazan auri Sadiq ba"

 Cikin tabe baki Annanin ce toh ai saiki kwantar da hankalin ki, tunda ko sama da kasa zata hade bazaki yadda ba banga abun damuwa ba, kina ma da yadda zakiyi kenan"

  Itama Munirah bin Annanin tayi da wani irin kallo tana me share hawaye"

 Tashi Annanin tayi ta nufi dakin mahaifin su yayin da ta sameshi yana zaune da Qur'ani agaban sa ta zauna cikin sanyin jiki"

 Ahankali ya dago ga kalleta sannan yace"

  Har yanzun bazaki kwantar da hankalin ki ba ko?, Sai kin jawowa kanki ciwo ne ko?, Kowa fah tashi yake jira??

Munirah ce take daga min hankali enisilim, yanzun tazo ta sameni tanata kuka Wai tsoro take kar ahadata aure da Sadiq, duk tasa kanta adamuwa, yariyar nan ita kadai ta ragemin, banson ganinta cikin irin wannan yanayin"

  Daga Ina Kuma ta samu wannan mgnr???

 Bansanin Mata ba, Amman dai tabbas cikin fargaba take......

Kiramin ita tazo yanzun yanzun nan”

      Fita Annanin tayi, ba jimawa Saigasu sun shigo tare, fuskan Munirah akunbure ta zauna tsakiyar falon, akasa kusa da kafar mahaifinta"

   Munirah??

Na'am"

Munirah?

Na'am Abbanin, 

    Mgn nakeson nayi dake me mahimmanci, inason ki bude kunnen ki ki saurari abun da zance miki, kinaji na?

Ahankali tace eh"

 Inason ki aje tunanin komai aranki, saboda Sagir ya tafi yabarki da auren sa akanki, kenan Ina nufin Zaki masa iddah, na tsayon wata hudu da kwana goma, surutu banaki bane, sannan ki cire aranki akwai wani tunani aranmu, babu tunanin komai aranmu, ki nutsu ki kwantar da hankalin ki, zancen tsohu Kuma zolayan ki yake matsayin sa na kaka agunki ba wani abu ba"

    Ajiyan zuciya Munirah tayi da karfi sannan tace Abbanin cewa yayi nacika kaudi, Kuma naji ya tambayi Amukarnin Sadiq wai yana tsoron kaudi ne, shi......

Tsaki Malam yaja, sannan yace nagaya miki ba ruwanki da zancen su, wannan zancen su ne sukeyi, ba abun daya shafeki bane, aini ca nake Munirah mutuwan Sagir da Aliya lokaci daya zatasaki hankali?

Wlh Abbanin nayi hankali fah"

Toh ni banson surutu, ki kama bakin ki kinji ko?, Kuma banson inji kin Kara zancen zuwa Ingall ayanzun ne zamu gane irin son da kikewa Sagir din, ki zauna ki nutsu kiyi idda mekyau sannan kicegaba da masa addu’a”

   Sosai jikinta yai sanyi, ahankali hankalinta ya fara dawowa ajikinta Jin akwai iddah Sagir akanta yasa hankalinta ya kwanta sosai, Kuma sannan abikin Abbanin ta tabbatar babu wani zance da suke kullawa"

        Adaren ranar Kuma ta sakejin lbrn tafiyan mutanen Ingall din gobe cikin tuhuma tacewa Zahrah kikace Kuma kunfasa tafiya"

  Toh ai lokacin dana shigo basu gama zaman ba daga baya ne suka yanke wannan shawaran"

    Ajiyan zuciya kawai tayi domin ita ayanzun ji take tamkar tayi bankwana da farin cikin ta gaba daya"

                 *********

Sadiq kuka haka kamar karamin yaro, har sai yaushe zakabar kukan nan Sadiq”

 Mammah duniyar tamin fadin, babu Sagir babu Aliya, Mammah idan kin tafi waye zai matsamin inci abinci????? Mammah Aliya ce ke biyoni har daki tun Ina ganin kamar takura min take harnazo nafara karba, ko banson inci zata bani abaki, bayan nagama takwashe kayan Bata damuwa da duk wani yanayi dazan nuna mata, Kuma ko nakici bazai hana gobe ta sake dauko wani takawo ba, Mamamma cikina ne Amman zakiji tana rokona Amukarnin dan Allah kaci mana, yanzun waye zai min haka Mammah??, Ina kewanta sosai Mammah inajinta sosai acikin zuciyata, idan na Bata Umarni ko Bata so bi take"

 Kansa ta shafa sannan tace sai hakuri Sadiq, banyi Mamakin furta kana sonta ba, duk da cewa banso ba, Amman nafahimci tana kyautata maka, Kuma daman ita zuciya tana son me kautata Mata ne, Kuma in Allah ya yadda zaka samu wadda zata kautata maka fiye da Aliya insha Allahu"

Bazan taba samu ba Mammah, Allah yajikan Aliya yasa aljanan ce makomarsu gaba daya, Bata taba bata min raiba, hakama Sagir, suna da kirki sosai"

Kai shiru Sadiq, Allah yasa sun huta, kayi hakuri ka dinga cin abinci, Kai namiji kanayin haka Munirah Kuma tayi Yaya?, Hakuri duka namu ne gaba daya, nasan zaku fimujin mutuwar, saboda kun shrya zaman aure da junan ku, saidai Kuma dama muna tamu ne Allah na tashi, Kuma nashin shine gaskiya, dan haka kuyi hakuri dan Allah, sannan ku amsa wannan kaddarar hannun bibbiyu"

     Karfe Tara jirjin Mutanen ingalla ya tashi cikin rakiyar Sadiq da Mubarak sai Lubbunah sosai suka zubar da hawaye wanjen rabuwa"

              ********

Gidan yazama babu dadi gaba daya lubbunah da Munirah daman bawani shiri suke ba, Sadiq da Mubarak kuwa ayanzun suna yawan zama tare Dan ayanzun ma Mabarak kusan ya koma part din Sadiq saidai ba wani mgn Sadiq keyi ba, ko anji suna hira toh akan dai  Sagir ne, Sosai Mubarak yake Mamakin yadda Sadiq beson mgn, ayanzun idonsa na hango masa wasu abubuwa game da yadda yake hango yadda rayuwarsa zata tafi nan gaba, watan biyu kenan da rasuwar tasu Amman har yanzun gidan bedawo daidai ba, kallon sa Mubarak yayi yai dariya ahankali Sadiq ya dago ya kallesa tare da daga kafarsa daya ya daura Kan daya yana fadin meye kake min dariya Kuma??

 Dariya Mubarak ya sake yi sannan yace, Ina tuna yadda rayuwa zata can maka ne nan gaba kadan, naga dai Kai saikai zaman awa daya anan gurin baka cewa kowa komai ba"

 Lumshi Ido Sadiq yayi tare da dan murmushi kadan, sannan ya daga wayar Sa yana Dannawa"

Muryan Mubarak ya sake ji yana cewa, Mata basa son suka mijin su yayi banza dasu yana Danna waya, yanzun zakaga wayar tazama kamar kishiyar su, Kai Kuma kasaba da haka yakamata ka rage…..

   Sabo dame???

Kar azo ana samun matsala"

Tsaki Sadiq yaja da karfi, ni ba irin waddan nan mazan bane"

   Dariya Mubarak ya sake yi sannan yace, adaibi ahankali a lallabata"

   Nagaya maka ni ba haka nake ba, banson irin wannan zancen kabari haka"

Bazan Bari ba, zaman kuramen ya isheni, na dawo kusa dakaine dan mudan dinga ragewa juna damuwa ta hanyar tattanauwa, Amman sai kayi wani banza Dani, idan hakane ai gara nakoma part din mu"

  Ka koma dan Allah ni ka daman"

Bazan koma daki ni daya in zauna kamar maye ba????, cikin sauri Mubarak ya cire kwalla agefen idonsa sannan yacigaba da cewa, ni bansaba kwana nidaya ba, Sagir ba haka yake min ba”

Lumshe Ido Sadiq yayi sannan ya aje wayar sa agefe tare da fadin so kake nayi wasan danbe dakai ?

Ko bakayi wasan dambe Dani ba ai mayi hira dai ko?

   Lumshe Ido Sadiq yayi yayin da hawaye suka zubo masa???? hakama Mubarak hawaye ya share sannan ya taso ya dawo kusa da Sadiq kansa ya kwantar Kan kirjin sa yana fadin ni Ina son ka fara sabawa da mgn kafin wani lokaci, idan aka tafi ahaka kanwarmu baxataji dadin zama dakai ba"

Lumshe Ido yayi sannan ya bude yana fadin banso wannan mgnr Mubarak

  Dole in maka Sadiq, Sannan Kuma inson in tunatar dakai idan ka fahimci Sagir yata barin maka wasiyya daya daga cikin wasiyyar da yabar maka wadda ita tafi tsayawa araina wata rana anagobe daurin aure da daddare najishi yana cewa kana barinta tana jamaka gemo, abun ya tsaya mun arai sosai"

Natuna Mubarak ban mantaba, Amman ni banson wannan mgnr ayanzun, atakaice madai kabar kallonsa amatsayin wasiyya"

 Shiru Mubarak yayi sannan ya dago kansa daga jikin Sadiq yana me share hawaye tare da fadin"

Shikenan nasan kowa da irin shi Amman akwai abun da nake ji cikin raina”

Lumshe Ido Sadiq yayi sannan yace Nima haka”

 Wanni irin kallo Mubarak yai masa sannan yace enisilim yace gobe zamucigaba da karatu"

 Ya Gaya min"

Mikewa Mubarak yayi ya canza riga sannan yace nina fita….

Adawo lafiya Sadq ya fada vatare daya dago ba"

        Washegari misalin 8 na dare wata katuwar darduman ce shinfide kamar yadda suka Saba, wannan ne karon farko da zasu zauna karatun tun bayan rasuwan su Sagir Kamar ko yaushe Munirah ce tafara zuwa gurin tun daman can tana riga kowa fara zama agurin, saidai wannan karon Bata zauna gurin data Saba zamaba, kujeru guda Ukun dake gefe ta nufa wadda su Sadiq Sagir da Mubarak suke zama, ta tsakiyar ta zauna wadda ta kasance itace ta Sagir"

   Mubarak da Sadiq ta hango suna tahowa cikin farar jallabiya cikin sauri ta dauke kanta Dan rabon data ga Sadiq tun ranar da ta samesu dasu baba tsohu, tsayon wata daya kenan"

   Wani irin kallo yai Mata sannan ya wuce kujerar tata yana fadin koma waye akujerar nan ta tashi kawai"

Kallon kujerar Mubarak yayi tare da Dan taba Sadiq yana nuna masa Munirah saidai fusge hannun sa yayi yaki juyowa ya kalleta”

    Cikin zunburo baki ta mike ta koma wadda ke kusa da ita, wadda ta kasance itace ta Sadiq, hannu Sadiq yasa ya dauke kujearar da Sagir din ya Saba zama ya mikawa Lubbunah data shigo yanzu nan ki shiga da wannan cikin gida

     Amsa tayi ta juya shikuwa Mubarak zama yayi kusa da Munirah yayi datai saurin cewa Amukarnin Mubarak Ina wuni"

Cikin kama girman sa kamar yadda ya Saba yace, Lfy Lau Munirah ya mukaji da hakuri?

  Alhamdulillah"

  Adaidai wannan lokacin Sadiq na tsaye akanta ya zuba hannunsa cikin aljihun jallabiyar sa, idon sa sanye da gilashi"

Kasa da murya Mubarak yayi Munirah ki tashi mana baki ganin Sadiq tsaye, kujerar sace fah”

 Aina zauna awata yace in tashi????

Eh yana nufin ki zauna inda kika Saba zama.....

Mikewa tayi cikin zun buro baki Takoma inda ta Saba zama, adaidai wannan lukacin Lubbuna ta dawo ta zauna kusa da Munirah"

Mubarak kuwa kallon Sadiq yayi yace zauna toh”

Wani irin kallo yaiwa Mubarak sannan yasa kafa cikin fada ya daki kujirar ta kifa har Saida Lubbunah ta zabura"

Mikewa Mubarak yayi ya daga kujerar sannan ya kama hannun Sadiq yana fadin zauna”

Zama yayi fuskansa daure sosai ba’a iya ganin idon sa saboda gilashin daya sanya”

       Malam ne ya shigo gurin yayin da suka shiga gaidashi sannan ya samu guri ya zauna, har zaiyi tambaya kamar yadda ya Saba cewa dawa zamu fara, kome ya tuna Kuma sai yace Sadiq Bismillah"

  Enisilim nariga shi, Munirah tafada tana zunbura baki"

  Kallonta Malam yayi sannan ya girgiza Kai ya kalli Sadiq yada dauke kansa yana fadin Ina sauraron ka Sadiq"

Cikin nutsuwa ya shiga karatun sa bayan yagama ya mike ya bar gurin yayin da Malam yace nagaba"

 Ganin Munirah sai kuka take taki matsawa hakama Mubarak sai kallon Munirah yake yasa Lubbuna ta matsa kusa bayan ta gama Mubarak yayi nasa sannan Enisilim ya mike kusan atare da Mubarak suka wuce abin su"

  Bayan Mubarak yaga shigan Enisilim gida yai saurin juyawa da baya ko tantama bayayi Enisilim fushi yayi me tsanani da Munirah komawa Gurin yayi har yanzun Munirah na zaune sai share hawaye take yi, ahankali ya Kira sunanta yayin data dago ta kalleshi"

      Meyasa bakijin mgn?

  Kuka take kawai batace komai ba"

 Munirah barin tambayeki Zaki gaya min gaskiya??

Saboda tsoron Mubarak da take yasata fadin eh da saurin ta dan yanzun nan ya zane mutum

  Narasa gane yawan fada da kikeyi da Sadiq, meye matsalar???.......

  Aina rigashi zuwa amman ake barin shi yana farawa????"

 Wani irin dariya Mubarak yayi sannan yace yanzun ke dan Allah saboda wanan kike kuka??, Yanzun gashi Enisilim yayi fushi dake Kuma kinsan fushin shi bashi da dadi"

Hawaye ta fara sharewa yayin da Sadiq yace shikenan, indai Dan wannan ne daga yau Sadiq bazai sake fara karatu ba sai bayan kin gama, hakan yayi miki??

 Badan ta yadda da zancen Saba tace eh Amman aranta tasan bazai taba yadda ba"

   Yauwa Sannan Kuma Ina son intabaye ki meyasa kika gaidani amman kika kasa gaida Sadiq??......

????????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????
????
SAWUN BAYA
????
Book 2 ????????
????????????
????????????????????
????????????????????????????

                    *Na*
          *_Fadeela Lamido_*

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

® PEN: WRITER’S ASSOCIATION

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️


~only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers~


——–PAGE——-

https://www.facebook.com/110384724043172/

——–GROUP——–

https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/
  *Page 8- 7*
Typing......????️

Shine bemin gaisuwa ba tunda Amukarnin na ya rasu”

 Shiru Mubarak yayi yana kallon Munirah sosai yaga karfin halinta yayin da yaketa kare Mata kallo harta fara tsarguwa da hakan ta dukar da kanta kasa"

  Ahakali Mubarak yace ke yanzun atunanin ki dole ne yai miki gaisuwa ko kin manta Sagir kaninsa ne uwa daya uba daya?

Cikin turo baki tace toh Nima ai uwa daya uba daya nake da Aliya meyasa bemin gaisuwanta ba?

  Aliya Matarsa ce Malama, ki maida hankalin ki.....

Kasa tayi da murya Nima ai Amukarnin Sagir mijina ne in haka ne"

  Cikin tsananin Mamaki Mubarak yace me kikace??

  Shiru tayi ta kasa maimaitawa idon akasa"

    Allah ya shiryeki Mubarak ya fada yana kallonta kasa kasa tare da fadin"

Shikenan lokaci yayi dazakibar wannan rigimar taki Munira, dan bazance rigiman kuba dan ke kadai kike yi, Sadiq zai miki gaisuwa insha Allahu, Amman banson in sake ganin baki gaidashi ba, Dan ba Sa'anki bane, mgn nagaba Kuma barin gaya miki, hankalina yadawo kanki acikin gidan nan, kibar ganin Sagir ya rasu kowa na tausayin ki, kiyi amfani da wannan daman kice zakiyi abun da ranki keso, wlh idan kike Bata min rai zan aje tausayin ki danakeji araina inci ubanki, idan kin shiga hankali ki kuwa kowa zai tausaya miki tare da Kara riritaki har hankalin ki ya kwanta"

   Hawaye ta share tare da jinjina kanta"

 Tashi ki wuce gida"

Mikewa tayi ta wuce yayin da yake binta abaya har ta shiga part din su sannan shima ya wuce gurin Sadiq”

      Sai yazun kuka gama??, Sadiq da yake zaune shiru yayi tambayar"

 A'a natsaya gurin Munirah ne"

Kawar dakai Sadiq yayi zuwa can Mubarak yace”

   Wai meyasa kacika fushi ne akan Munirah??

   Da sauri ya kalli Mubarak Dan be tsammaci tambayan ba, har rawan baki yake wajen fadin"

Ni bana fushi da ita Sam, ita kanwata ce har yanzun, kawai nakula batun yauba, tanajin haushina, duk sanda zamuyi karatu ta dinga fadin narigashi narigashi, kullum saita fada bata gajiya haryau, ban taba kallon taba akan wannan, to meye Kuma??

  Kai Kuma baka tabayin tunanin koda rana daya bane kabar mata tafara?

 Inbar Mata?, dole ne sai anyi abun da ranta yake so?

 Ba dole bane, amman abun da nake son ka gane, yariyar nan yanzun zuciyanta yana cikin wani hali, mu yakamata mujata ajiki ta yadda zamu dinga rage mata kewan Sagir, Kuma kasan wani yaron fada da daure fuska besashi ya fasa abu, kamar yadda Sagir ke Mata da kowa zaiyi Mata hakan zata daina abun da take yi......

Lumshe Ido Sadiq yayi Mubarak nifah bana fahimtan inda kasa gaba”

Baka fahimta??

 Eh"

  Shiru Mubarak yayi sannan yace Ina nufin daga yau dan Allah idan anje karatu ka dinga barin ta tana farawa"


     Da sauri ya kalli Mubarak, bazanyi hakaba Mubarak, saidai tadaina zuwa gurin harsai nagama na wuce"

      Jimmmm yayi sannan yace shikenan hakama yayi idan mun tashi su sai ayi masu nasu ita da Lubbunah

        Kawar dakai Sadiq yayi yana nazari acikin zuciyarsa"

 Shima Mubarak kallon sa yayi ya dauke kansa domin ya rasa da wacce kalma zaiyi amfani dashi wajen yi masa dayan mgnr"

     Zuwa can yayi gyaran murya ahankali yace"

Sadiq wai kayiwa Munirah gaisuwa kuwa??

Kallon sa yayi ban gane ba"

  Ajiyan zuciya yayi sannan yace dazon natambayeta meyasa Bata gaidaka ba sai...............

Cikin Taran numfashin sa Sadiq yace saitace me???

 Shine take cemin Kaine baka Mata gaisuwa ba"

 Wata irin dariya ya fitar batare daya shirya ba, in Mata gaisuwa sabo da ita kadai akama mutuwa bandani ko?

Nasan bahaka take nufi ba, Kuma balaifi bane dan kunma junan ku gaisuwa ai"

   Hmmm, lallai yariyar nan yar rainin wayau ce, shikenan zan mata gaisuwa, itafa gani take ni ayaki aka ciwoni, badan gidan nan bane ni"

 Murmushi Mubarak yayi sannan yace, wanni irin a yaki Kuma?

 Shikenan, naji zan mata gaisuwa duk ranar da muka hadu Amman ninasan daman can bata gaida ni"

           ********

Washegari misalin 8 nadare Enisilim na zaune yaga wucewan Munirah sai sauri take, cikin tsawa yace zonan”

   Dawowa tayi ta Dan duka yayin da Malam yace"

Har kin fito rige rigen??

  Ba rige rige nake ba Abbanin nagama abun da nake ne"

 Toh ki koma gida, idan maza sun gama sai kizo keda Lubbunah, haka Sadiq ya tsara"

   Dagowa tayi ta kalli mahaifin ta suka hada Ido cikin sauri ta maida kanta kasa tare da juyawa cikin gida"

Sosai Abbanin yaji Mamaki Jin batace komai ba ta koma gidan"

           *********

Tasyon sati biyu aka dauka suna haka, kullum Sadiq da Mubarak ne ke farawa sanann Lubbunah da Munirah, dan haka bama ya ganinta bare yai Mata gaisuwan shi kanshi Enisilim haka yafi masa, domin yadda Munirah kewa Sadiq bakaramin kunya abun ke bashi ba”

   Munirah ta rame sosai ta rage mgn acikin gida, idan ba wani mgn ake me mahimmanci ba bakajin bakinta ko Kuma ana zancen Sagir Kona Aliya sannan zakaji tayi mgn"

   Idan kuwa takama hiran Sagir batason abari, haka zataitayi kwalla na taruwa a idonta tana sharewa"

     Bata da abokin fada daman Aliya ce da Sadiq yanzun Aliya ta mata nisa, Sadiq Kuma ta jima Bata ganshiba, saidai aduk sanda aka ambaci sunansa tanajin wani irin baccin rai wadda yake kasa boyowa akan fuskanta harsai ta nuna kowa ya gani"

   Ayanzun duk dangin babu wadda besan Munirah ta tsana Sadiq ba, inma basu tabaji daga gareta ba toh lbrn ya isa kunnen kowa"

      Yanzun Wata uku kenan da rasuwar Su Sagir dan haka kowa ya kama har kokin sa yayin da iyayen su maza duk suka koma kasuwancin su"

 Munirah ce kawai zakaga kamar kullum Kara shiga damuwa take dan yariyace ita me yawan mgn da dariya da tsokane tsokane, fadi ba a tambayeki ba, amman yanzun duk batai kodan babu abokin yi ne oho"

           *******

Sadiq, ji wata yariya dan Allah, kalla yadda take danme dana namiji”

  Juyawa Sadiq yayi ya kalli budurwar yariyar da Wanda ya kokarin Kai Mata cafka, cikin sauri ya tsaida motar tare da dauko gilashin shi ya daura a idonsa sannan ya bisu da kallo"

Kokarin kamata yake tana zurawa da gudu da dan siririn gyalenta ahannun ta, daganin su irin sangartattun yaran nan ne wadan da aka shagwaba su"

  Mubarak ne yace Ina zuwa barin rabasu shima in banda hauka meye na fada da mace"

Har Mubarak ya bude kofar, Sadiq yace ka barsu, Ina tunanin Tamudiriccin sa ce, baka ganin suna kama”

Kuma fah hakane suna kama, Amman yariyar Bata da kunya”

  Sosai ma, ko zaka dan mamayeta ta baya ka kama mishi ita, idan taga bakinta najini zata Bari"

Dariya Mubarak yayi a'a nikam babu ruwana haka kawai, cikin daga murya Mubarak yace Abokina Yaya akayi ne kake fada da mace???

 Waigowa yayi cikin fara yace ita ta matsa saita bini, yanzun Kuma mun fito duk ta isheni.....

 Cikin sauri tace toh mutum da bakinsa sai ahanashi mgn, Ina ruwanka da mgnta, ai badakai nake yi"

    Cikin murmushi yayan nata yace nikuma wlh bazaki shigar min mota ba saikin kama bakin ki"

 Toh mukwana anan, wlh bazanyi shiru ba haka kawai ai badakai  nake ba Ina ruwan ka toh"

 Zama yaron yayi asaman motar, sannan ya sauko yana kokarin shiga motar yake da sauri yayin da yariyar itama ke kokarin shiga dayan gefen juyowa yayi da baya ya bita aguje yayin data ruga aguje shikowa cewa yake ki tsaya mana saina karya ki"

Murguda baki yariyar take tare da fadin wlh duk inda kayi saina bika, ai Mommy cewa tayi muje tare"

 Dariya Mubarak yaitayi yayin da Sadiq yake zaune shiru yana kallon su fuskan sa babu yabo babu fallasa"

     Mubarak ne yace Abokina ba girmanka bane fah, Wai ba kanwar ka bace???

    Me aikin muce"

Karya yake, haushi yakeji ana cemin auta

        Dariya Mubarak yayi sannan ya sauka amatar ya karasa gurin su sannan yace"

 Gaskiya aboki wannan be dace ba, kaga duk wadda zai wuce nan saiya kalle ku, kayi hakuri kuje gida haka nan"

 Ai daman gidan zamu Amman saita bani wayarta  saboda ta dameni da surutu"

  Aida kawayena nake surutun na badakai ba motar banza motar wufi tafiya tafara tana murguda baki tare da cewa Kuma wlh saija maka an kwace motar, nisa tayi tana cigaba da magana yayin da yaron yaketa murmushi yana kokarin shiga motar sa"

 Daker Mubarak ya lallabasa yaje ya dauketa yayin da suka shiga motar su Mubarak nacigaba da dariya yace wannan yariyar duk yadda akayi irin su Munirah ce"

 Tuki kawai Sadiq keyi bece komai ba, Mubarak yacigaba da cewa daza'a hadasu kawance ni Ina tunanin yariyar nan ma tafi Munirah rawar kai"

  Woooo, bata fita ba, dama ne kawai Tamudiriccin Bata samu ba, amman bata da kunya, abokin yine bata samu ba, duk gidan mu babu wadda zai biyewa Munirah su rika irin wannan haukan, wannan yariyar da alamar ba'a kwaba mata, Tamudiriccin kuwa har yanzun Bata samun yadda take so, shiyasa takejin haushina, ko Sagir dayake sake Mata baya Bari tamai abun da taga dama"

Kuma fah haka ne yariyar nan saidai Allah ya shirya mana ita”

Maida Hankali Sadiq yayi akan tukin sa har suka iso gida be sake cewa komai ba, part din Annanin Sadiq ya nufa rabon shi da zuwa yama manta, zaune ya sameta ta rafka tagumi har ya isa gabanta bata cire ba, hannunsa ya Mika ya zame hannun datai tagumin dashi yayin datai saurin dagowa ta kalleshi, cikin yaren su yace Annanin meyasame ki"

  Gefen idon ta tashare sannan tace Sadiq sai yau, ko tausayina bakaji??

 Annanin kiyi hakuri har yanzun baki daina kuka ba ko???

Ina zan daina kuka Sadiq baccin narasa Sagir, shine me shigowa kullum safe ya gaidani sannan ya zauna muyi hira yana kallona kamar wata abokiyar sa, baya boye min damuwar sa haka Nima kafin nagayawa kowa damuwa ta saina fara gaya masa, wani zubin ya tausaya min wani lokacin Kuma yaita dariya yana fadin Annanin kika tsofa rigima zakiyi, Ashe Allah besa zaiga tsofan nawa ba bare inyi rigiman, yanzun ko nayi rigimar waye zai kulani........

 Kara hade fuska Sadiq yayi sannan yace Annanin me kike nufi to??

    Ina nufin Banda wadda zanwa rigimar Kai ko gaidani bayi bake ba Ina zansa ran kulawa daga gareka"

 Kallonta yayi cikin Ido sannan ya mike tare da fadin shikenan"

 Zonan, bangane shikenan ba??

 Toh ni me zance miki, bakince Banda amfani ba????"

   Bahaka nace ba, zo ka zauna"

  Hannunsa ya zuba cikin aljihu sosai idonsa yai jah"

Mikewa tayi ta iso gaban sa bance baka da amfani ba, Ina Gaya maka damuwata ne dan inason ka dinga kamanta irin na kanin ka, bakuma Ina koshi halin ka bane, kaikadai ka rage min, ahalin yanzun duk wani buri nawa yana kanka, Kaine wadda zaka kawo min jikoki da jikin ka, Kai kadai Sadiq dagani har Mahaifin ku ayanzun kaine burin mu, nasan narasa Sagir har abada na amsa wannan kaddarar hannu biyu Amman Ina bakin cikin rasa Aliya da kayi amatsayin matar ka, ita daya ce zata iya janyo hankalin ka, abunan da yake cikin karkashin zuciyarka bana farin ciki dashi, har yanzun hankalina yaki kwanciya akan wannan "

Kamar daga Sama taji yace meyasa hankalin ki yaki kwanciya??

   Saboda nasan baza'a zauna lafiya ba"

      Shiru yayi yana nazari, zuwa can ya daga kafada tare da fadin shikenan, kicewa Abbanin nace banso, dama ban amsa ba" cikin sauri yabar dakin yayin da tani bayanshi da kallo"

      Yana fita Takoma bakin gadon ta zauna tare da dafe kanta"

         Washegari misalin 7 na safe Sadiq ne ya shiga har cikin dakin baccin Annanin, gaita yayi cikin Sakin fuska kamar bashine jiya taita daure fuska ba, cikin ladabi yace"

  Annanin tafiyace ta kamani zuwa Kano"

  Lumshe Ido tayi halan daga office Kuma shine baka gaya tun jiya ba??

Mancewa nayi, Kuma tafiyan zata dauki wata daya amman Inna samu lokaci zan leko”

Toh Allah ya taimaka Baban ku yasani ko??

Eh nagaya mishi”

Toh Allah ya tsaremin Kai aduk inda kake”

Ahankali yace Ameen sannan ya mike ya fito, boyoshi tayi suka fito tare, yana kokarin shiga motar ya hango Lubbuna rike da Munirah sun fito daga mota”

Annanin ce tai saurin karasawa gurin tana fadin"

Lafiya?

Munje Asibiti ne"

Munjrah ta kalla tace Munirah meke damun ki??

  Kirjina nane yake ciwo"

 Allah ya sauwake Annanin ta fada yayin da Sadiq ya shiga motar ya zauna batare daya ko kalli gurin ba, bayan Annanin taga shigansu gida itama gun Sadiq ta koma ta shafa kansa tare da fadin"

Munirah babu lafiya fah"

Kawar dakai yayi sannan yace Allah ya Bata lafiya ni zan tafi”

 Toh Allah ya tsare ya Kuma bada sa'a, murmushi yayi tare da fadin Ameen nagode"

                     *********

Bayan wata daya, Munirah ce zaune ta dada ramewa zaune taki tayi tagumi sabo da wani irin faduwan gaba da takeji kwana biyun nan, yanzun ma wani faduwan gaban takumaji yasata saurin mikewa tare da dafe kirjinta, Lubbuna dake tsaye kusa da ita tace meye haka”

 Inajin faduwan gaba irin wadda nakeji gafda rasuwan su Amakarnin, yanzun Kuma waye zai Kuma tafiya?

 Lumshe Ido Lubbunah tayi tare da fadin"

Har kinsa gabana ya fadi, Amukarnin Sadiq yana hanya yau zai dawo, Allah ya tsareshi ya kawoshi gida lafiya”

  Cafdi, ba Ameen ba, aikema kinda indai mutuwa za'ayi agidan nan saidai shi"

 Ba ameen ba??, Wai ke kina da hankali kuwa??

 Lafiyata kalau, nifa tunda Amukarnin ya mutu kowama ya mutu bandamu ba"

  Cikin Mamaki Lubbunah tace Amman baki da hankali Munirah, har iyayen ki kenan??

     Nidai Vance ba, wadda kike mgn dai dashi nake"

     Himmm, Allah yabaki lafiya Munirah"

 Allah dai yabamau lafiya, Kuma ninasan sabo dashi gabana bazai fadi ba, Allah yasa mota ta kundumeshi ya mutu har gawan shi kar agani, duk bashi ya jawo su Amukarnin suka motu ba, shima meye amfanin shi"

 Wannan karon Lubbunah mikewa tayi tana fadin halin ki bashi da kau Munirah, wannan wacce irin kiyayya ce?

     Hararan bayan Lubbunah tayi sannan Takoma ta zauna tana me dafe kirjinta"

         Adaren ranar Annanin take tambayan Munirah, Munirah Wai yau kwanan su Sagir nawa da rasuwa.......

  Suna cikin wata na biyar kenan"

Allah sarki Allah yai masu rahama"

Ameen tace tare da share hawaye"

 Kina musu addu'a kuwa?

 Sosai Annanin"

 Kin kyauta"

Mikewa Munirah tayi ta leka window tare da fadin"

 Wai me akeyi tun dazon nakejin hayaniya"

 Annanin tanacigaba da aikace aikacen ta take fadin"

 Sadiq ne ya dawo dazon, wata daya kenan baya gari"

   Toh masu hayaniyar fah??

 Ina tunanin abokansa ne suka taho tare"

  Sakin labulen tayi, fasa lekawa tayi ta dawo ta zauna adaidai lokacin da Annanin ta sake cewa"

 Gobe Enisilim zashi AGADEZ"

   GOBE GOBE nan lafiya kuwa?

Lafiya lau, gaba daya zasu tafi harda Mubarak da Sadiq"

 Cafdijan harda su Baba da Abbba??

Gaba daya maza gidan zasu wuce"

Ashe tsohu yana da manyan baki, Allah sarki Amukarnin Sagir dayanzun dashi za’aje”

  Iyee, rayuwa kenan idan kin tunasu ki dinga masu Addu'a"

      Kwallah tacire  
  Sannan ta koma ta zauna, washegari tun da Sassafe taji Karan motoci anata hayaniya acikin gidan, batai Mamaki ba domin tasan da tafiyan, sakkowa tayi domin tayi Sallama da mahaifinta afalo ta samesa yana gyara Babban rigarsa daka ganshi kaga buzun Agadez, yau tsoho zaiga yaran sa uku a Ingall"

Murmushi Enisilim yayi sannan yace nasan zaifi farin ciki dazuwan Sadiq da Mubarak fiye da zuwan mu ai"

    Sunkuyar dakai tayi sannan tace Allah ya tsare hanya Abbanin yaushe zaku dawo toh?

   Wata kila gobe da Yamma mutaso ko Kuma ko kuma jibi da Sassafe"

  Toh Allah ya tsare hanya"

Ameen Enisilim ya fada har ta juya yana kallonta yana murmushi shiganta daki ba dadewa taji tashin motar su, zuwa can taji gidan yayi shiru kwanciya tayi kawai tai shiru"

Misalin 10 na Safe Annanin ta shigo tana yafe da lafaya hannunta rike da yar karamar jaka tace Munirah tashi muje ki rakani, mikewa tayi da sauri rabon data fita ta manta labaya ta yafa sannan ta dauki wayarta ta biyo bayan Annanin”

      Driver ne ke Jan su yayin da taga sun nufi gidan matar dake masu lalle"

Annanin lalle zakiyi kenan"

Hannun mu yayi fari wannan karon babu kyan gani muje amana har ke"

   Batayi musuba domin sun riga sun sama da kunshi baya rabo da hannun su dan haka basu daukeshi wani abu ba"

    Cikin kankanin lokaci hannunsu yadau haske gaba daya ita da Annanin kowa dai yasan yadda Jan lalle kiyin kyau akafar farar mace sosai tai kyau yatsunta kafa da hannun yayi gwanin ban sha'awa"

 Karfe 4 na yamma suka koma gida sai alokacin taga wani irin gyara da akayiwa part din Sadiq gaba daya gefensa ya haske gidan gani take kamar ma Kara fadada sa akayi, juyawa tayi ta kalli Annanin tace"

    Shikuma wannan ya mike kafa aduniya harda wani fenti"

      Kallonta kawai Annanin tayi ta dauke kanta"

        Washegari tun da Sassafe taga su Anninn da Umma wato mahaifiyar Sadiq sai shirye shirye sukeyi abinci, kusa sai shigo dashi ake kula kula, ganin shigowan Umma part dinsu yasa yasa tace Umma Wai shirye shiryen me kuke yi?

Bana komai bane Munirah, masu gidan ne zasu taso daga ingall, anjima kadan, kinga dole mu nemar masu abin da zasuci"

     Yau zasu dawo kenan, in nine tsoho bazan Bari su dawo yau ba"

  Murmushi Umma tayi sannan tace wa Annnin kisata tayi wanka mana jirgi zasu biyo fah, Kuma suna tare da Mamma Aysha da Mammah Hauwa"

           Misalin Karfe shidda na yamma motocin suka fara shigowa cikin gidan, yayin da duk su Annanin da Lubbunah sukayi waje"

 Hayani takeji sosai adaidai lokacin da take kokarin fitowa wanka dan haka ta matsa bakin window dakinta ta yaye labulen"

  Mutanen data hanga cike da gidan yasata faduwan gaba kowa shaddarsa kwalli take yayin data hangi Sadiq yayi wani irin shiga wadda Bata taba ganin yayi irinsa ba, gani tayi ya canza Mata gaba daya, yakara tsayo da fari ga wani irin kwarjin wadda ya hana ta tagen wanni irin shigace ajikinsa wadda tasata ganin kwarjinin sa, gani tayi sai bashi hannu ake yayin da yake amsa cikin fara'a, idonsa sanye cikin bakin gilashi, tana Shirin sakin labulen arikice ta hange Mamma Aysha ta tsaya gabansa tanai masa guda acikin kunnen sa....

  Da karfi tace, me ake yi?......

????????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????
????
SAWUN BAYA
????
Book 2 ????????
????????????
????????????????????
????????????????????????????

                    *Na*
          *_Fadeela Lamido_*

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

® PEN: WRITER’S ASSOCIATION

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️


~only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers~


——–PAGE——-

https://www.facebook.com/110384724043172/

——–GROUP——–

https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/
           *Page 9- 11*
     Typing......????️

Fitowa tayi abirkice daga ita sai towel, kofar fita falon sukaci karo da Annanin itama tana shigowa ganinta haka yasa tai saurin yamutsa fuska Ina Zaki haka???

 Yauwa Annanin me akeyi agidan nan ne?, Wai me akeyi dan Allah??

 Hannunta tasa ta rike hannun Munirah tace muje ciki"

Cijewa Munirah tafara, au bazaki shiga ba, sakin hannunta tayi sannan ta wuce tana fadin, jeki toh, haka dai Zaki fita ko?, toh jeki"

  Cikin matso hawaye tace toh me akeyi agidan Annanin dan Allah?

Shine nace kishigo ciki in gaya miki ai”

    Dawowa tayi jikinta sanyi sosai ta zauna kusa da Annanin, itako Annanin mayafinta ta cire sannan ta kalli Munirah tace bawani abu ake ba fah, Munirah inace kinsan su Enisilim sunyi tafiya Kuma sun dawo yau"

Shine aka cika agidan??

Eh mana 'yan sannu da zuwa ne sukazo"

  Cikin ya mutsa fuska tace toh aina hango Mamma Aysha tana guda awaje kamar aure ake fah Annanin?

   Auren wa??

 Nima ban sani ba"

Tsaki Annanin taja, dan Allah kidaina damun kanki, tashi muje ki shirya kema kije kiyi masu sannu da zuwa"

  Mikewa tayi saidai duk da haka arude take takasa tsayarda zuciyarta guri daya"

 Shiryawa tayi cikin wani sabon kayan da Annanin ta fito Mata dashi sannan ta yane jikin ta da wani hadeden lafaya me kyau, jikinta sanyi sosai ta fito, yayin da suka hadu da Lubbunah tana shigowa, kallonta tayi tai murmushi duk da Munirah tana cikin wasiwasi Saida tace Allah ya isa"

Murmushi Lubbunah tayi tare da fadin kinci bashi yariya”

   Wacewa tayi inda ta iske Annanin kitchen Annnanin nashirya toh"

 Kije suna can part din Abban ku"

Tam tace, tare da fitowa, takalmi me tsini ne akafarta sosai dan haka idan ka ganta saika dauka yanga ne takeyi, har yanzun gidan cike yake da Mutane kin kallon inda su Sadiq suke tayi, saidai ta kula tunda ta fito ita suke kallo"

    Harta isa gurin bata kalli kowa ba Bata Kuma gaida kowa ba"

  Takalma ne birjik akofar falon da alama harda baki aciki, matsawa tayi daga gefe ta cire nata sannan tayi sallama bayan an amsa Mata tashiga"

  Ganin fuskokin sun Mata yawa tai saurin tsugunawa tana gaidasu tare da masu ya hanya"

Cikin sakin fuska sosai da fara’a suke amsawa yayin da taga Mutanen dake gurin suna mikewa suna fita har ya rage su Enisilim su Uku kadai Sai Mubarak daya shigo yanzun nan”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button