NOVELS

SAWUN BAYA 1 & 2 COMPLETE HAUSA NOVEL

Cikin sauri da dakiya tafara takawa, tana Kara gabato su harta zo daf dasu tana kalon su ta gefen idonta yadda Sadiq ya kama bakin Hafsat yana tsotsewa"

  Tana zuwa saitin su Sadiq din yai saurin Sakin Hafsat yayin da ya juyo sukayi Ido biyu da Munirah, dauke idonta tayi akansa ta shige ciki, itako Hafsat bata kula da itaba har Saida ta juya baya shiganta falon Mamah kawai tagani"

  Munira kuwa kamar me tafiya a kan iska Babu sallama ta fada dakin Mamah tare da wucewa can kurya tahau gado tayi rufda ciki hakanan ta tsinci kanta da zubar da hawaye tare da wani irin zafi cikin makogoron ta"

 Mamah ce ta biyo bayan ta harta iso bakin gadon, Kiran sunanta take Amman Babu amsa, zama tayi gefenta sannan ta saka hannu ta roko Munirah tana fadin"

  Lafiya kuwa mene ya faru"

 Cikin wani irin Murya tace Mamah ruwa zansha"

Babban Goran ruwa Mamah ta dauko me sanyi sannan ta cika kofi ta mika mata"

 Tashi zaune tayi ta karba ruwan yayin da ta takai bakinta sai kofin ta sauke tana mikawa mama tare da fadin, Kara min"

 Cikin Ido Mamah ta kalleta batare da tace komai ba ta Kara cikawa ta mika mata nan ma Saida Tasha rabi sannan ta juyi ranin kan kirjin ta"

 Zaro ido Mamah tayi ganin ta juye ruwan sanyin akirjinta sannan fuskarta hawaye face face yayin da idonta yariga dayai jawur"

Cikin tsananin firgici Mama tace ke!! Munirah meke damun ki??

   Babu, tafada tare da juyawa ta kwan ta"

Babu?, amman kika shiga wani hali, nidin ne bazaki gayawa damuwarki ba?, to wa kike dashi agarin nan da zaki gayawa damuwar ki?

 Tashi Munirah ta sake yi, akoro na biyu sannan ta nufi toilet din Mamah ta wanko fuskanta ta fito tana share fuskanta tare da fadin'

Mamah ni gida nake so?, tafiya zan yi”

Cikin Ido ta kalleta yayin da ta hange rigima kwance cikin idonta, cikin mamakin kalamin ta tace”

   Amukarnin ku ya bata miki rai ne???

 A'a ni gida kawai nake so"

 Toh shikenan ki kwanatar da hankalin ki bara yazo sai na gaya masa"

  Ni bazam jera hanya dashi ba"

Au???? kekadai zaki tafi?

     Eh

  Toh naji, yanzun ki kwanta ki huta Bari yazo inji yadda za'ayi"

 Wani hawayen ne ya sake zubo mata adaidai lokacin da Zahrah  ta shigo Munirah ke cewa, ni yau zan tafi"

Kallo suka bitashi Mamah da Zahrah yayin da Zahrah tace me Kuma ya faru?

  Hmmm ???????????? Munirah ce ta tashi da yamman nan kamar me shafan aljanu gatanan waj gida zata tafi Kuma bazata jera hanya da Mijinta ba"

      Dariya Zahra tayi sannan ta zauna tana Fadin meya faru toh Munira"

 Juyar dakai tayi tare da Kara share bawaye"

 Zahrah ce ta kalli Mamah tace daman dazon fa tace gabanta na faduwa irin faduwa dayai tayi Sanda Amukarnin Sagir da Aliya zasu rasu kila shiyasa hankalinta ya tashi"

  Cikin gamsuwa Mamah tace to banda abun ki Munirah ai addu'a zakiyi ba koke koke ba"

  Nidai gida zani????????????

Ganin yadda take kamar a rikece ta daga wayarta ta Kira Sadiq cikin kankanin lokaci sai gashi har cikin dakin ya shigo tsaye yayi abakin kofar yace, lafiya??

Toh Munirah ce tasa rigima wai ita tafiya zatayi"

  Ina zata??

Gida wai"

Gida Nigeria?

Eh"

Toh shikenan taje sai nazo, juyawa yake kokarin yi, yayin da mama tace zonan”

  Dawowa yayi ya tsaya ciki kallon idon sa Mamah tace"

Ba'ayin haka Sadiq, wacce irin magana ce taje sai kazo, sabo da baka damu da ita ba, wani abun fah ku kuke jawa kanku amaku sannan kudawo kuna cewa an maku rashin kunya, ka kalli yariyar nan halin da take ciki"

   Kallonta yayi sannan yai saurin kawar da kai yace"

Mamah tana fadane kawai amman nasan ba inda zata iya zuwa konan kofar gidan akabarta na tabbatar batasan Ina zatafi ya fitar da ita daga cikin garin nan ba”

   Koma dai menene be dace ba"

Shiru yayi tare da saka kansa kasa zuwa can ya dago ya kalli Zahrah yace ke tashi kibar nan gurin"

Cikin sauri ta fita sannan Sadiq ya matso bakin gadon Ahankali Yana binta da kallo inda tayi can gefe da idonta”

 Kallo yaita binta dashi zuwa can yace"

  Kiyi hakuri daman kwana uku ya rage mu wuce, lokacin sati biyu kenan"

    Yadda ta dauke kanta ko motsi batai ba"

Juyawa yayi zai fita Mamah tace zo dawo"

 Ai bakaji ba kota hakura"

Kashhh Mamah kema da taya bera bari kike ki rabu da ita mana"

  Wani irin kwallo Munirah ta bishi dashi harya fice sannan ta kalli mama ta kawar dakai"

  Kinga Ki kwanatar da hankalin ki kinji barsa damuwa irin wannan kwana ukun ma ai kamar yaune"

      Tunda Munirah ta kwanata agurin sallah kadai ke tadata har kusan Tara na dare sannan Mamah tace tashi taje ta kwanta"

     Cikin kawar da fuska tace anan zan kwana"

     A'a Munirah idan tsoho yaji zaiyi fada, idan tsoron hanya kike ji tashi muje in raka ki"

     Noke kai tayi daga kwance yayin da Mamah ta sake cewa"

  Toh koshi zan kira ya tafi dake"

   Kanta ta daga ahankali dan haka mama ta dauki waya ta Kira Sadiq"

   Dare nayi kazo ka dauki matar ka, bataji me yace ba tadaiga kawai Mamah ta sauke waya"

     Kallon Mama tayi sannan ta dauke idonta tare da lumshe su tace"

     Yace basai nazo ba ko??

    A'a yace ki kwana anan, wata kila dan yaga bakijin dadi ne"

   Tashi Munirah tayi ta zauna tace"

    Dole yace in kwana anan tunda Hafsat gunshi zata kwana"

 Wani kallo Mamah ta mata yayin da taga hawaye layi biyu afuskanta cikin tsananin mamaki tace"

Meya kawo wannan mgnr Munirah?

  Kamar jira take ta fashe da kuka cikin sheshshekar kuka sosai"

Binta da kallo Mamah tayi sannan tace
   Yi shiru ki gaya min me ya ke faru"

Cikin sauri ta share hawayen sannan tace Babu komai”

  Jimmmm Mamah tayi zuwa can tace toh kidaina zargi domin babu kau, idan ma akwai wani alaka tsakanin su ada ne banda yanzun ita Hafsat ma ta Samu miji aure zata yi"

 Mamah da idona na gansu fah na gansu nan waje nan yana taba ta"

  Runtse Ido Mamah tayi sannan tace"

Shikenan naji Munirah, yanzun kinsan me nake so dake?

  Mikewa Munirah tayi ta shiga toilet batare datace komai ba"

  Cikin tashin hankali Mamah tabita da kallo Munirah tajima sannan ta fito idonta jawur ta wuce gadon ta gwanta"

   Cikin nutsuwa Mamah ta karasa gabanta ta rike hannunta kiyi hakuri kinji, Hafsat kuma babu inda zata kwana indai tana gidan nan bata da gurin kwana sai dakin nan kinji ko"

Toh kawai tace tare rufe Ido"

Ahankali Mamah ta sake cewa dan Allah karki Kuma tada zancen har wani yaji, shi kansa Sadiq yagane tashin hankalin ki cewa zai son sa kike…….

 Bude Ido tayi, ni ina ruwana dashi, koma menene bakune kuka jamin ba tunda kune kuka hadani dashi, alhalin kunsan ya tsanan

  Kidaiyi hakuri kawai nace miki"

Kawar dakai tayi bata sake mgn ba, ko fuskarta baka iya gani”

    Da daddare ita da Zahrah suka kwanta gado daya yayin da Mamah da Hafsat ma gado daya suka kwana"

      Kiran Sallah farko Hafsata ta sako daga kan gado, bayi ta shiga tana fitowa ta hangi Munirah zaune akan gado tana me kurawa maHafsat ido"

     Kawar dakai tayi adaidai lokacin da Munirah tace"

      Karuwa"

Wani irin lumshe Ido Hafsat tayi tare da tarin takaici da bakin ciki, sunan da Munirah ta kirata dashi, zafi tare da daci takeji cikin zuciyarta saidai bata da hanyar nuna bacin ranta domin hakan na nufin fallasa abun da sukeyi ita da Sadiq kowa ya sani dan haka ta zauna tana jinjina sunan datai kiranta dashi”

    Ta gefen idonta take kallon yadda Munirah ke zafga mata harara ji tayi bazata iya dauka ba dan haka ta mike ta fita"

     No Sadiq ta Kira Yana dauka tace"

       Ka gayawa Munirah karta Kara cemin karuwa niba sa'arta vace"


  Zaman gilashin sa ya gyara sannan yace"

  Kinaji na?

  Eh"

Ba karuwa ba, koda wani irin suna ta kiraki karki kula ta,

   Amukarnin ban iya jurewa gaskiya, duk guda nawa take"

  Hannunsa yasa a aljihu sannan ya fara takawa Yana rike da wayar da daya hannun sa yace"

   Zaki biye mata ne kuna mayarwa juna mgn, koko danbe zakiyi da ita?????

  Aina kirakane kaja mata kunne niba tsararta bace"

    Cikin fada yace Umarni kika bane kenan?, 

          A'a ba nufina kenan ba"

    Tsaki yaja sannan yace nadai gaya miki karkice zaki taba yariyar nan"

    Kashe wayarta tayi cike da haushi tare da tarin bakin ciki akwai alamar Amukarnin ya fara son Munirah , tsayawa tayi tai shiru cikin yanayin tunani idan bata manta ba ita da Munirah abokan wasa ne Kuma ita tana gabane da Munirah, tabbas abun kunya ne ta aikata da mijin kanwarta wadda yake mtsayin yayan va daya saidai tutuni take son ciresa cikin ranta amman baya cirowa afili tace koma dai menene bekamata a kirani da karuwa ba, cikin dakin ta shiga ta dauki hijabinta ta data sallah"

    Munirah da Zahrah ma duk sunyo alwala inda suka jeru nan suna Sallah"

 Bayan sun idar da Sallah Munirah ta riga kowa mikewa tana ninke Hijabinta take fadin"

    Zahrah ki dinga saka karuwai cikin addu'a Allah ya shirye su, susan darajan kansu subar likewa mazan bariki"

   Runtse Ido Hafsat tayi yayin da Zahrah ta shafa addu'ar tana fadin"

         A'a nikam ba neman waddan da zanwa addu'a nake ba, ke Ina ruwanki da karuwan?, Meya dame ki dasu"

   A'a wlh babu, kinsanni da shiga sharo, indai nagani sainai mgn, amman dai ba'aji dadi ba tirrrrr da karuwanci"

 Kasa jurewa Hafsat tayi dan haka ta juya ta kalli Munirah cikin harara tace ke dawa kike?

   Ajiye hijjabin Munira tayi jikin gadon sannan tahau gadon ta zauna tare da fadin wadda ya tsargu"

 Mikewa Hafsat tayi ahankali ta matsa jikin gadon tare da nuna Munirah da yatsa tace wlh ki kiyayeni, ban wasa da yariya, niba sa'arki bace"

 Hankalin Munirah akwance tace karki Kara nunani da  yatsa danni girman mutum bebani tsoro, yanzunan in miki rashin mutunci ba wani abu bane guri na"

    Saukan mari taji me zafi akumatun ta yayin da tai saurin dirowa ta cakumu Hafsat"

  Zahrah kuwa Kira ta fara kwalawa Mamah kusan atare suka shigo da Sadiq da dawowarsa masallaci kenan"

      Gaba dayan su kansu sukayi yayin da Hafsat naganin Sadiq ta tsaya cak itako Munirah sai hankoro take tana fadin wlh saina rama"

    Mamah ce tace meya faru ne wai"

     Zahra ce tashiga maidaita yadda akayi bayan tagama Sadiq ya kalli Hafsat yace Mena gaya miki awaya?, bance miki karki taba ta ba??

       Kasa tai da kanta Nina kasa hakuri ne......

 Kanta rufe baki ya dauketa da mari harsaida tace wayyo Allah, juyawa yayi ya finciki hannun Munirah hannun Mamah zai juya tace barta anan"

    Mamah idan ba tafiya nai da ita ba fadan bazai kare ba, sakin Munira tayi yai waje da ita"

  Hafsat ko kuka tafara yi tana fadin karamar yariya tamin rashin kuya ita ba'aga lafinta ba saini zai daka?????????

  Tabe baki Mamah tayi sannan tace ai daidai kenan, ya miki kau, ke kika watsar da kanki ai mace kamar tangaran take data fadi ta fashe shikenan, namiji fa?, gashi duk da tarin rashin kunyan nata ya mangare ki akanta, sabo da mutuncin ta a idon shi, tuntuni nake karanta miki ki kama mutunciki amman dayazo garin nan kin dinga rawar kai kenan"

     Sosai jikin Hafsat yai sanyi inda taita zubar da hawayen takaici"

              ********

Kan gado ya direta tare da fadin”

 Keba karfi ba sai neman rigima"

 Kuka tasa wadda ta rasa Kona menene"

  Karki daman, nine na dake ki da zaki dawo nan kina min kuka?, Meyasa bakiyi acan ba?

       Kukanta taci gaba dayi yayin ya matsa gaban madubi ya cire riga sannan ya bude akwatin sa ya dauko wasu takardu ya koma kujerar dake kallon gadon ya zauna har yanzun Munirah kuka taka kasa kasa"

Cikin nuna ko in kula yacigaba da rubutun sa, kusan minti 15 kenan be daina jin tashin kukan nataba dan haka yace"

    Nafara gajiya da halin ki fah, koda yake nasan abun da kike so dazaran kin fara irin wannan abubuwa wani abu kike nema, barin xo in baki"

 Wani irin kallo tai masa tare da tunanin inda mgnrsa ta dosa, ahankali ta rage karfin kukan nata tare da rufe idonta har bacci ya dauketa"

    Tabbatar wa dayai tai bacci yasa shi ya maida takardun sannan ya fice dakin"


                  *******

    Naso ace acikin kwana 14 da zamuyi agarin nan ace tsakanina da Muneera akwai kyakyawan fahimta"

  Mamah ban taba kawo tunanin zamuzo garin nan har mukwana 12 muna nan ahaka ba, ni yanzun harna fara tunanin Anya kuwa Munirah zata so ni??????

  Hmmmm, Sadiq kenan,ni nafi ganin laifin ka akan na Munirah, Saboda Munirah ta dade tana da korafi akan ka, tun Babu aure atsakanin ku, sannan bayan rasuwar Sagir dole aka mata, duk da cewa kowa yasan tsanar da ta maka, wadda itama take tunanin yadda takejin ka aranta kaima haka kake jinta, Sadiq ka taba tunawa Munirah kai ba haka bane azuciyar ka?, Ka taba nuna mata irin dubin kaunar da kake mata tun tana da kananun kuruciya?, ka taba bude mata sirrin zuciyar ka akanta?? ko ka taba bude bakin ka ka gaya mata kana son ta??

     Gilashin sa ya gyara sannan yace ni ban taba ba Mamah"

     Yakamata ka taba, domin Ina da tabbaci yadda kake da sirri azuciyar ka itama Munirah tana dashi akan ka, kota fahimta yanzun kota  fahimta nan gaba"

Mamah ban gane ba??, kina nufin Munirah tana sona ne??

  Hmm, Sadiq kenan ta yaya kake tunanin zata soka alhalin kai baka taba furta mata so ba"

  Mamah kenan, dole saina bude Baki nace Ina son ta?

 Idan atiti ka ganta zakaje gidan su neman aure ta ne batare daka furta mata so ba???, Koko dan andauka daga sama an baka kake ganin ba dole bane?, itama Munirah mamace kamar kowa, Kuma kowacce mace tana son aso ta sannan a nuna mata soyayyar azahiri"

 Cikin sanyin jiki ya sunkuyar da kansa zuwa can yace"

  Amman Mamah kinsan bakin Tamuddirincin bashi da saiti, Kuma bata da sirri" Amman shikenan zanyi yadda kika ce"

               ******

Hannun Munira cikin na Sadiq yayin da tai shiru kanta akasa"

Shikuwa Sadiq kokarin leka fuskanta yake tare da fadin"

   Tamuddirincin jibi zamu gida fa

   Batare data kalleshi ba tace Allah ya kaimu"

 Hannu tasa ta dafe kirjinta tare da fadin"

Innalillahi wa inna ilaihir raju’au ????

Yaya aka yi?, Menene??

Idonta aruntse tana budewa ahankali tace, nidai gabana faduwa yake yi sosai, irin yadda nake ji gabda rasuwar su Amukarnin Sagir"????????

Hannun sa yasa ya share mata hawaye yana fadin, tun yaushe kika farajin haka?

Tun jiya da rana kuma banayi awa biyu batare daya buga ba”

   Murmushi ya sake yi  sannan yasake share mata sauran hawaye yace"

  Toh ko nine zan mutu wannan karon?

Kilah, ai kowa mutuwa zai yi"

Hakane”

Shiru yayi tsayon wani lokaci yana kare mata kallo zuwa can yace”

 Ina son zanyi wata mgn dake me mahimanci amman kafin nan dan Allah ki nutsu kibani hankalin ki kiji abun da zan gaya miki......

????????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????
????
SAWUN BAYA
????
Book 2 ????????
????????????
????????????????????
????????????????????????????

                    Na
          _Fadeela Lamido_

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

PEN: WRITER’S ASSOCIATION ©

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️


~only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers~


https://mobile.facebook.com/Pen-Writers-Association-100990022185172
            Page 57- 58

Typing…..
Wani irin kallo tamai sannan ta maida kanta kasa”

Kasa yayi da muryan sa sosai yace"

 Kinajina

Kanta kawai ta daga yayin da take wasa da zoben dake hannun ta”

Kallon hannun yayi sannan ya kalli fuskar ta datai kasa dashi yace ki dago kanki mana”

Ai inajin ka"

Lumshe Ido yayi cikin rasa abun cewa gaba daya yama rasa ta Ina zai fara”

 Kallonta yake cikin lumshe Ido sannan ya mike ya koma saman kanta tare da rankwafowa yayi kissing din komatun ta sannan ya zauna daf da ita tare da kama hannunta yana wasa da zoben cikin yimata irin wannan kallon wadda bata so"

 Tunawa tayi da mgnr Umma da tace daya mata irin kallon itama ta rama dan haka itama ta rage idon ta sosai tana binsa da kallo daman cike take da haushin shi"

   Murmushi ne ya bayyana afuskarsa tare da lasan lebensa Yana me lumshe Ido, daukan ta yayi cak ya daura kan cinyarsa yana me juya zoben hannunta kamar yadda take yi, ahankali yace"

 Tamuddirincin zaki fahimceni idan na gaya miki??

Kanta ta sake dagawa acikin ranta take mamakin me yake son fada haka ne da yaketa zagaye zagaye"

      Lebensa na kasa ya sake lasa sannan yace, I love you so much my lovely wife, & I can't live without you"

 Wani irin zabura tayi cikin zillo ta kalleshi yayin da yai saurin tareta Saboda yadda ta zabura kamar zata Fadi, yadda ta kura masa Ido yasa shi yasa hannun sa daya ya cire gilashin sukayi Ido 4 da ita"

  Wani farin ruwa ne kwance karrr cikin idonsa, wani irin kallo take masa irin wadda bata taba masa shiba ganin inda shima ya kafeta da Ido yasa ta sauke kanta akasa tare da fadin"

      Aini basai kamin haka ba, daman bance zan gaya ba a gida ai"

 Lumshe Ido yayi sannan yace, menene bazaki gaya ba??

Bazan gaya masu naga kana taba Hafsat ba"

Kawar da kansa yayi tare da sauke ajiyan zuciya sannan yace”

       Ni ba wannan mgnr nake miki ba, idan kina da mgn dani akan wannan zaki iya min daga baya, ruwan ki ne kifada kokarki  fada, Amman dai Ina son ki aje wannan a cikin zuciyar ki, mgn ce ta gaskiya babu zancen wasa ko wani abu cikinta, ko nataba cewa Ina son ki ne??

  Lumshe ido Munirah tayi yayin takejin zuciyarta na mata zafi lokaci guda duk taji ranta ya bacci tare da shiga rudu wadda ta rasa abun yi, tsintan kanta tayi da fadin"

    Nidai a'a wlh, nasan baka sona, dan kaga Aliya bata raye, kasa ya rufe idon ta, shine ko kunya zakace ni kake so, idan babu Aliya ai akwai Bilkisu da Hafsat, Lubbunah ma ta raye ai bata mutu, ko basu kake so ba?

  Jimmmm yayi cikin lumshe Ido daker ya iya hadeye yawon bakin shi Yana jawota kirjinshi tare da fadin"

  Kanwata, tunanin ki ne wannan, ban taba ba, Kuma bazan taba son wata bayan ki ba, you're the only one I love in my heart"

  Turesa ta fara yayin da ya shiga riketa cikin kuka take ture kirjin nasa yayin da ya shiga fadin"

 Tsaya kiji mana, ina zaki kuma muna mgn"

 Amukarnin nika barni???? wlh ni banson ka  Sai da kagama wulakantani sannan kace min kana sona"

 Jawota yayi ya matseta akirjin shi Yana jin yadda take kuka sosai cikin siriyar Muryarsa yace"

   Wanni irin wulakancin nai miki?, sai dai in baki fahimceni ba"

Wlh wlh baka sona, ko ka manta tsanar da ka mun, sai munfito zamu unguwa duk kabar sauran su wuce nikace na koma gida, Kaine kafara sa kowa ya tsaneni acikin gidan da yawan fadin bani da kunya, ai sabo da tsanata da kayi kakeyiwa su Aliya abu ne ni kuma saidai ka harare ni, kaita saya masu abu gabana kake basu saboda tsata da kake yi"

   Ajiyan zuciya yayi tare da kawar da kansa can gefe yana dai rike da ita ta kasa kwatan kanta, zuwa can ya juyo yayi kissing dinta sannan yace"

      Ba inayi bane dan natsane ki ai, asalima wlh bantaba jin tsanarki ba"

        Ni banso ka wlh, duk abun da kayi ada yanzun duk kace ba haka bane, idan hakane meyasa wallpaper ka Aliya, password din ka Aliya????

       Sosai yakejin mamakin kalamin ta, ganin inda taketa tureshi tana haki sosai tare da hawaye yasa shi sakinta yayin datai saurin mikewa ta wuce daki"

 Mikewa yayi ya maida gilashin sa tare da zuba hannun sa duk biyun cikin aljihu yafara zagaye falon nasu wadda ya dauki tsayon lokaci yana abu daya"

Tsinta kansa yayi cikin wani irin damuwa duk da sharewa da yake yi Amman yanajin wani iri acikin jikin sa baki daya"

     Kiran Sallah mangariva yasashi wucewa masallaci duk jikinsa Babu wani karfi"

  Itako Munirah tunda ta shiga daki kuka take yi koda aka Kira sallah kasa mikewa tayi har Saida aka Kira Isha'i daker ta iya mikewa idonta duk a kunbure"

              *****

Misalin karfe 9 nadare Munirah ce zaune saman gado bayan tayi Shirin bacci, dakin Mamah taso zuwa saidai tana tuna yadda sukayi da Hafsat dazon taji ko ganinta ma bata son yi dan haka ta mike kafa kawai Saman gadon, cikin yanayin tunani”

Tsintan kanta tayi da son Kiran Umma dan ita kadai take kaiwa korafinta, Kuma yau tana cikinn damuwa sosai”

Bugu biyu Umma ta dauka tana Fadin"

 Rigimammiya, sai yau kikaga daman kirana?

   Cikin girmamawa tace Ina wuni?

 Lfy lau ya kuke?

Lafiya lau"

Masha Allah, Ina Sadiq din yana kusa”

 A'a

Ina yaje?, Ko baki sani ba?

Ahankali tace eh"

Yadda take amsawa Umma yasata murmushi sosai takejin canji a tattare da Munirah

  Shiru sukayi hakanan Munirah taji takasa iya furta komai"

Yadda Annanin tajita shiru yasa tace, Munirah badai wata matsala ko?

Eh"

Toh yayi yau, yace min jibi zaku taso ko?

Eh

Toh Allah kawo ku lafiya, sallama sukayi yayin data sauke wayar idonta cike da hawaye, wannan karon mahaifiyar ta ce ta fado mata arai, rabon da suyi waya ta manta, kira tayi bayan ta dauka ta gaidata cikin girmamawa”

 Amsawa Annanin tayi sannan tace kuna nan dai lafiya ko"

Lafiya lau”

Ai muna gaisawa da Sadiq yana kiran mu shi tunda ke kinyi fushi damu"

 Annanin kece fa da Enisilim kukabar daukan wayata"

Korafin ki ne yai yawa, Kuma ke ban da baki da hankali ai saiki bada hakuri  har yanzun babanki ko sunan ki beson yaji an kira, yace baki da biyayya, tunda yaga kinbar kiransa yace har yanzun baki nutsu ba"

Hawaye ta share sannan tace kibashi hakuri Annanin kuma nifa ba abun da nake yi yanzun"

 A'a ke Zaki kirashi ki gaidashi kawai zaiji dadi"

Amsawa kawai tayi tare da fasa fadin abun da tai niyayya tana me share hawaye ta shiga Kiran layin Enisilim"

  Bayan ya dauka suka gaisa jin harta kashe Babu wani korafi yaji dadi sosai, saidai tana cire wayar akunnenta tasa kuka me tsuma xuciya"

   Saida tayi ma ishe sannan ta Kira Zahra bugu biyu ta dauka"

   Zahrah dan Allah ki danzo"

 Lafiya?

Kizo wata mgn zamu yi”

Munirah darene fah harnayi Shirin kwanciya"

Kizo yanzun Zaki koma”

Kai Munirah kawai sai Amukarnin ya ganni da daddaren nan??

Benan ma fah shi kizo dan Allah"

Kidai bari da safe zan shigo"

Shikenan daman keba Mutunci gareki ba Ina wannan ‘yar iskan fah”

  Wai Hafsat gata can tai bacci"

 Kwafa Munirah tayi tare da fadin"

Shegiya mayya dabe shigo dakin nan ba dasai na shake wuyan tsinanniya"

 Murmushi Zahrah tayi yayin da cikin zolaya tace, lallai sosai kike kishin Amukarnin Sadiq"

 Tirrrrr wlh Allah ya kauta, ni babu ruwana dashi idan yaga dama ma ba bakinta ba ya cinyeta baki daya babu ruwana, ni yanzun ma wai kinsan menene?

      Jitayi kawai ancire wayar a hannun ta yayin data daga kanta ta kalle hannun Sadiq ne tsaye cikin shirin bacci, kallo tabishi dashi yayin daya yake kallon wayar, ganin Zahrah rubuce kan wayar yasashi kashewa tare da fadin"

 Me zaki gaya mata?

 Cikin sunkuyar dakai tace bakomai? 

   Zama yayi gefen gadon yana fadin"

 Tamuddirincin bana son surutu fah, dazon Ina mgn dake kin rikecemin gaba daya, kinata kuka saikace wadda aka gaya mata sakon mutuwa........

   Ai da wannan mgnr gara fadan mutuwar ma????"

 Haba?

Dauke kanta tayi can gefe tana fadin, eh

    Hannunsa yasa ya tarota jikinsa tare da hade hannunta duk biyun ya matse sannan ya mika mata wayarsa"

Matse take dan haka tai saurin amsa ni mexan da ita"

    Cikin kunnemta ya rada mata wayar Sagir ce wannan bude kika wani abu"

 Jimmmm tayi sannan tace toh ka sakeni in duba"

Har ranta take daukin bude wayar, yayin data shiga saka password din da Sagir yake sakawa akomai nasa kamar haka, MUNEE

Budewa tayi yayin da wani rangadeden pic dinta ya bayyana akan wayar wadda bata taba sanin tana dashi ba, ta dai san kayan amman batasan sanda akwai hoton ba, ita kanta pic din ya tafi da ita da alama rawa take lokacin da aka dauka yayin da fuskanta take dauke da murmushi meban sha'awa"

 Yadda yaga ta kurawa pic din Ido Babu karewa yasa shi saka hannun sa ya amsa wayar Yana fadin bari ki gani"

Karban wayar yayi ya daddana sannan ya Mika mata wani ta sake gani kusan ma yafi wancen kau, ahankali tasa hannunta ta matsar da wancen haka taita ganin pic dinta bila adadin wani ma tun tana karama wani ma da kayan wasa agaban ta babu iyaka, sosai tabada hankalinta wajen kallon wayar dalilin gaba daya pic din babu daya da zatace tasan sanda aka dauka ya wance an dauka ne batare data sani ba Kuma sunyi kau sosai gani take ma aciki pic din da take dashi nata babu daya dayakai kaun wa dannan"

   Sosai tayi nisa gurin kallon inda duk ciki na kankanatar tata yafi burgeta, pic din Aliya 3 kawai tagani sai Kuma nasa dana Sagir amman sauran duk nata ne"

Hannun yasa ya zare wayar a karo na biyu sannan ya saketa ya mike tsaye Yana fadin”

 Wayana ne bana Sagir ba, nasan baki taba sanin akwai waddan pic din ba,  koshi Sagir din da kike cewa Yana son ki yana son ki, nasan Babu ko rabin wannan awayar sa, idan ma akwai rabin su to kila ke kika tura masa ko Kuma tare kuka yi, muko bama jira abamu.....

Cikin tsabar jin haushin sa tace ai daman basai ka fadaba nasan abu kona Allah yasa ne ci kuke"

 Jinjina kai yayi  tare da tunanin inda zamcen ta ya dosa sannan yace"

    Kinga abun da yake hadani dake bakin ki, idan hakkin mune ko mutun yayi Allah ya isah ai yaiwa iska"

   Ai iska kala biyi ce wanne aciki?

  Cikin tsabar haushi yace duk yadda kikace ko kika zaba haka ne, ficewa falon yayi ya zauna cikin yanayin na tunani, mgnr Mamah ce ta dawa masa data ce saiya bita ahankali tare da lallashi, tsaki yaja sannan ya tashi ya koma dakin inda ya samu har wannnan lokacin tana kuka"

 Zama ya sake yi abakin gadon sannan yace"

Yanxun sabo da Allah kukan nan da kike tun rana na meye ne?, Jiya baki yin kuka haka fah?

  Ni Kaine ka tayar min da hankali Kaine kasani kuka"

  Hannunta ya roko yace toh Mena miki??

  Dakace wai Sona kake????????

Jimmmm yayi Yana kallonta sannan yace yanzun me kike son ayi?

 Karka Kara cewa kana sona, ni bana son ka wlh"

Jimmm yayi sannan yace”

Toh shikenan naji, yanzun dai kinyi sallah ??

Kaita daga alamar eh"

Toh ki kwanta kiyi bacci”

Kwanciyar tayi kamar yadda ya bukata bayan ta rufe jikinta da bargo tace karka tabani……

Bazan tabaki ba, ya fada tare da dafe kansa, yajuma ahaka sannan ya koma gefenta ya kwanta”

 Ya jima bacci yaki zuwa masa saidai kawai ya juya ya kalli Munirah ya girgiza kai yayin da zuciyarsa ke gaya masa kamar yanayin kalamin Munirah akwai kishi acikin sa, daya zuciyar ko cewa take rigimace kawai irin tata, abun da take cewa bata so Ina zancen kishi"

 Sosai yakejin tashim hankali wada ya rasa inda zaiyi gashi ga Munirah amman saidai kallo duk da irin tarin bukata da yake dashi

gashi haka kurum yaji ayou beson yai mata dole”

          ********

Yauma tunda da ta farka bacci kirjinta ke dakan Tara tara, tashi kawai tayi ta zauna bayan ta ida sallah, Sadiq ma bayan ya dawo Masallaci tsaye yayi a kanta kawar dakai tayi tace”

Ina kwana?

Cikin sakin fuska ya amsa sannan yace"

 Kindai fara Shirin zuwa gida gobe ko?

Ni ashirye nake"

Toh goben sammako zamu yi"

Toh ta amsa dashi kawai, to idan kin shirya kije part din Mamah ki zauna nima fita zanyi sai dare zan dawo"

Har cikin ranta taji dadi cikin kankanin lokaci ta shirya zata fita taji yana fadin”

   Kirki tsokani fada, kar inji ance anyi fada dake, kinajina ko?

Lumshe idonta tayi tafice abunta batare data amsa ba”

 Zahrah da Mamah kawai ta tadda adakin sosai Mama ta fahimci Munirah nadamuwa sosai gashi lokaci bayan lokaci tana dafe kirjinta dan haka ta matsa kusa da ita tace"

    Mamah tsoro nake ji, Kuma na kosa mukoma gida"

  Ance miki ki kwantar da hankalin ki wai ba gobe zakuje gida bane?

   Mamah ni ba wannan ba, sai Ina ganin kamar zan koma gida inga Babu wasu cikin gidan"

A'a zaki tarar da kowa insha Allahu"

  Haka Munirah ta wuni wani iri mgnr ma bata cikayi ba duk irin rarrashin ta da Mamah take taki sakin jikinta, gashi yau tun safe Sadiq beko leko ba gashi har yamma"

 Misalin 05:15pm suka fara jin hayaniya tare da iface iface, Zaharah ce tashigo cikin dariya tace"

Mamah?

Na'am Yaya aka yi?

Ga Amukarnin Sadiq can da Amukarnin Moh’d suna wasa da mota awajen gari”

 Murmushi Mamah tayi tare da fadin"

Masha Allah, kicemin Sadiq ya tuna dah, yakamata ace Ina gurin”

Mayafi Mamah ta yafa yayin da Munirah ta mike tace nikadai zaku bari?

Toh kema muje mana kiga yadda ake wasan"

Ganin zasu barta ita kadai yasa ta mike itama ta bisu da mayafin ta a hannun ta…….

????????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????
????
SAWUN BAYA
????
Book 2 ????????
????????????
????????????????????
????????????????????????????

                    Na
          _Fadeela Lamido_

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

PEN: WRITER’S ASSOCIATION ©

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️


~only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers~


https://mobile.facebook.com/Pen-Writers-Association-100990022185172
            Page 59- 60

Typing…..

Tun kafin su karasa wajen suke hango tashin kura, Zahrah ko balakin kosawa tayi ta ganta gurin dan haka duk ta wuce su sai sauri take yi”

Suna daf da zasu Isa inda yakamata su tsaya Munira ta kwace Hannunta daga na mamah ta kalleta tare da fadin”

Muje mana”

Ninagaji mamah Kuma ma meye abun sha'awa a data kurar?

 Kidai je ki gani yadda ake wasa kema ki karar da zuwan ki ingall jawo hannunta tayi suka karasa,   sun Isa ba dadewa suka gama wasan, Sadiq da Muh'd sunyi kura sosai tare da abokan su, saidai gani kasan suna cikin nisha di"

        Dariya taga suna tayi tare da sowa shikuwa Sadiq murmushi kawai yake dan haka Munirah ta hade fuska sosai inda ta kula ya kafeta da Ido tundaga nisa"

Kamar an tsikareta ta fara tafiya cikin sauri kamar zata tashi sama yayin da takalminta yake lumewa cikin kasa ganin haka ta cire takalmin ta rike shi a ahannu tanata zafga sauri tare dajin yadda take taka karsu ta gado me laushi"

  Ganin inda taketa zafga sauri ya sauka amotar yabita Yana kiran sunan ta"

     Waigowa tayi tana ganin Sadiq nabin bayanta ta kwasa da gudu"

    Tsaye yai Yana Murmushi sannan ya dawo ciki sauri ya bude motar daya fita ciki ya zauna yayin ya tada yana fadin barin bita Mamah sai kunzo?

       Fuskarta dauke da Murmushi ta amsa sannan ya wuce cikin guduz, nan danan ya isa inda take, lokacin ta tsagaita da gudun"

      Tsayawa yayi cak sannan ya fito ya riketa ya nufi cikin motar da ita yayin data shiga fadin karka shafamin kasa"

  Murmushi yayi sannan ya kalli jikin shi duk kasa yace kema ai kafar ki babu takalmi "

     Zama tayi cikin motar badan ranta ya soba, sannan ya shiga suka kamo hanya"

           Kaitsaye part dinsa ya wuce, bayan yayi wanka itama ta shiga tayi lokacin data fito bata tardashi cikin dakin ba dan haka cikin sakewa ta shirya cikin shirin bacci tahau gado"

      Cikin baccinta taji ana lalubarta hannunta ta sa da saurinta ta rike nasa, jikinsa ya sake matsowa daf da ita sosai yasata ajikinsa cikin kunenta ya rada mata Ina bukatar ki"

   A'a tafada tare sa sake ture hannunsa yayin da cikin kokawa ya maida hannun nasa yana fadin"

   Rigimar ki tayi yawa fah, ada banyi tunanin zan dinga bin wata ba tana tureni, banyi tunanin akwai yariyar da zan dinga binta kamar yadda nake miki ba sannan barin gaya miki wani abu wadda nake tunanin har yanzun baki fahimta ba, bana wasa da wannan bangaren, idan ke bakisan mahimanci sa ba nina sani, haka kikamin jiya kikace karna tabaki dole natsiri wasan da rabon danayisa na manta, idan ke jikin ki be gaya miki ninawa yana gaya min, bazaiyuwu ga hakkina Ina kallo Kuma na dinga kwana da wahala ba"

    Ni dai nace banso Amukarnin dan Allah kabarni bacci nake ji"

Numshe ya sauke tare da Kara rikitota ya hayeta Yana fadin”

Bancci dole sai kinyi ba, kiyi baccin ki kawai, ahankali ya shiga sarrafata cikin kokawa tare ta ihu wadda idan wani na kusa da part din zai iya jin su, har yanzun bata daina kiraye kirayen da take ba, tare da kokawa sosai take yi, har yai nasaran tsinke bra dinta kamar yadda ya saba sosai ya rikice yayin da adaidai wannan lokacin haukan da take ya rage, duk da cewa dai ya rike hannunta amman tayi lakwas sarrafata kawai yake yi, jin yadda ya jima Yana abu daya yasata fara kuka domin harga Allah tagaji yayin da cikin kuka take cewa"

   Nagaji Amukarnin, zan mutu shuuuuuuuuu wayyo Allah nagaji, akwai gajiya narantse da Allah wayyo kafata bayana nagaji"

 Jin ta dameshi da surutu ya rufe bakinta dashi har Saida hankalin sa ya dawo jikin sannan  ya saki Yana maida numfashi"

  Itama numfashin take saukewa tare dason kaucewa daga gareshi Amman takasa, Saida ya dauki tsayon lakaci ahaka sannan ya sauka ya koma gefe tare da daura hannun sa kan marar ta Yana fadin"

     Surutu surutu, koda yaushe Baki gajiya da surutu, wayyo Annanin wayyo Enisilim, Sagir Aliya Amukarnin Mubarak wai harda Lubbunah, wannan da gida ne ai saiki tada wani daga bacci, ragowa kawai, miti nawa nayi har kike Kiran gajiya?

  Sunne kanta tayi cikin filon ganin yabita da Ido dan haka yacigaba da cewa dan Allah ki dinga hakuri da mgn da daddare, nagaji nagaji kafata bayana zafi shuuuuuuuuuuuuu, Amukarnin mu, aikin ki kenan fah, ko yaushe nazama Amukarnin naki bansani ba bayan ada kince ni badan gidan bane ....

Nika bari bana so”

 Me din baki so??

 Cewa shuuuuuuu"

Naki nabari bake kike yi ba?, abin da kike yine na maimaita idan baki son afada kibar yi”

     Kaima ai saikabar tabani"

A'a wlh bazan bari ba meya daman da shuuuuuuuuuuu din ki?

 Kawar da kanta tayi yayin daya riko jigidarta yace"

   Yaushe kika sa wannan abun?

  Jiya"

Okay Ina kika sameta nasan dai baki taho dashi ba??

    Zahrah ta sawo min jiya"

  Jimmmm yayi sannan ya sake cewa meyasa kuke sata, meye kuma amfanin ta??

    Kwalliya ce"

Lallai kuwa, ai saifa kwalliyar, kwalliya ko wahala ba, itama Zahrah tasa ne?

  Ina ruwan ka?

  Babu"

Hafsat bata sawane????

  Jimmm yayi sannan ya lumshe Ido tare da fadi"

  Ni ban sani ba"

 Itama shiru tayi tsayon lokaci sannan taji ya Kuma rike jigidar tata , yana fadin amman Ina da ruwa da wannan ko?

Itama hannunta tasa ta rike sabo da yadda taji ya rike kamar zai tsinka"

Sake mun abuna????????

  Bansonta kicire har in kinason, maza kicire kona tsinka ta"

  Sanin da tayi ba abun mamaki bane yatsinka ta awajen shi yasa tai saurin cewa zan cire toh"

Ahankali ya zame hannun sa, yayin da Munirah ta tashi ta nufi toilet, zuwa can ta fito bayan tayi wanka tana rike da jigidar”

Shima tashi yayi Yana kallon jigidar Yana fadin abu ko sha’awa babu”

   Bayan yayi wanka har ya rigata shiryawa ya koma gado, duk da cewa ba kwalliya tayi ba Amman ta dauki tsayon lokaci tana busar da gashin kanta wadda take ta takaicin ganin gashin ta duk ya lalace"

        Misalin 01:30am ta nufi gadon idonsa rufe saidai ba bacci yake ba, tana kwanciya gefen sa ya bude idon sa"

    Kallonta yayi sannan ya lumshe Ido tare da kamo gashinta yakai hancin sa Yana Kara runtse idon sa"

  Cikin yanayi na firgita da maitan sa tace ni kabari bacci zanyi"

       Hannun sa yasa ya ruko kogunta sannan ya matso da ita jikin sa sosai ya runtse ta, kiyi bacci Nima baccin zanyi"

      Toh ka sakeni mana"

Muyi ahaka”

Badan ranta yasoba ta kwanta kawai tsayon lokaci taji yacigaba da tabata, wannan lokacin ma bebarta ba harsaita ya samu nutsuwa yayin da yana kan kirjinta bacci ya dauke sa, haka itama Munirah da wahala ya hade mata da gajiya tuni tai bacci”

   Washegari ma bayan ya dawo Sallah asuba Saida ya Kara sannan wani bacci me dadi ya suresu gaba daya"

 Misalin 08:45am Sadiq ya tashi Yana kallon yadda Munirah take baccin wahala, aransa yace gara kisaba yariya Allah ya hadaki dame lafiya"

   Kansa ya dauka ya daura kan mararta dan haka tai saurin bude idonta cikin kuka tare da bude murya Baki daya"

  A'a ya isah mana, menene Kuma haka"

Tashi tayi zaune nina gaji"

Toh sannu kinji Allah yai miki Albarka, yanzun kitashi kiyi wanka karmu makara"

     Hannu tasa tadan ture kansa dan haka ya tashi wanka tayi yayin da ta fito daure da towel kallo Sadiq yabita dashi sannan shima ya  nufi toilet din, yayin da tunanin yai masa yawa"

  Cikin ransa yace, gadai aure nayi, Kuma na samu yariyar da nake so wadda zuciyata ta dade tana son mallaka yanzun na mallake ta, Ina samun abun da nake so Kuma Ina sauke damuwata duk lokacin da nàso, amman narasa abu daya, akullum Tamuddirincin fadi take tana maimaitawa bata kaunata sannan nikadai take yin kidana in Kuma yi rawana ko kad'a kafa bata yi balle insa ran zata kada kai wata Rana, duk wani kalma tawa ta rarrashi tagama karewa zuwa yanzun bansan yadda zanyi da ita ba????

    Irin wannan tunanin yaitayi har yagama ya fito inda ya sameta tayi kau matukar cikin shirgarta dake nuna zallah buzuwa ce babu hadi"

     Yana goge jikin sa yake fadin kinyi kau sosai"

Batare data kallesa ba tace nagode"

 Wani sanyi yaji cikin ransa jin kalmar godiya agunta, kayan su tacigaaba da tattarawa inda shikuma yake shiryawa Saida tagama hada komai sannan ta rurrufe akwatunan su tayi falon, shima shiryawa yayi tsaf sannan ya fito falon ya sameta zaune tana danna wayarta"

   Kallon sa tayi ta dauke kanta ahankali ya karasa gabanta ya dafa kafadunta yace"

  Nayi kau??

 Kai tsaye tace a'a

 Dauke kansa yayi ???? sannan ya juyo yace"

  Banyi kyau ba??

Eh"

Haba?

Wlh”

Meyasa toh?

Ni ban sani ba, amman wani ko wanni irin kaya yasa yanai masa kau kamar nima nasan kowanne nasa inayin kau ko ba’a fada ba”????

 Murmushi yayi sannan yace hakane kanwa ta nima shaida ne, yanzun ba wannan ba, matsowa yayi ya zauna sannan yace"

  Kinga dai yau zamu gida, Ina son kimin alkawari guda biyu ko uku, idan kika min wannan alkawarin zan miki koma me kike so gwargado karfina"

 Bakinta ta turo gaba fiyeda da sannan tace ni banson komai naka"

Kamar me misali??

 Kudi ko kaya karka kawo min banso"

 Toh naji, amman sabo dame??

Kawar dakai tayi ai idan kudi ne kafin kabani kabawa wasu, hakama kaya ko wani abu, Saida aka kagama rabawa duniya sannan ace za'a wani bani"

 Shiru yayi Yana nazari sannan ya Kara daidaita gilashin sa yace"

 Suwaye duniyar da naraba  mawa??

 Kowama"

Inajin ki kibani misali

   Aliya Lubbunah sannan Hafsat da Bilkusu"

Cikin tsananin mamaki yake karewa bakinta kallo tana mgnr kamar ana karawa muryarta magi, cikin daure fuska yace”

  Kicire Aliya aciki bata raye, ita addu'ar mu take bukata yanzun, koda nasan ni dai kikafi jin haushi, lallai lokacin bakaramin laifi nake yi ba, yanzun kinsan me za'ayi?, Ki kimanta abun da na kashe masu lokacin, nikuma zan Kara akai in biya k......

Banso, ai lokacin ba rokonka sukayi ba hakanan ka dauka ka bada”

 Wani irin kallo ya mata sannan yace"

 Toh shike nan, namiki alkawarin daga rana mekamar ta yau Babu wani Wanda zai Kuma cin kudina sai in akwai amince wayar ki, duk wani abu nawa nakine kawai  babu shamaki"

   Wani irin sanyi taji cikin ranta wadda gefensa kemata zafi tuni, betaa hucewa ba sai yau har ta dan saki ajiyan zuciya batare data sani ba, tsinta kanta tayi dajin dadin kalamin sa har karkashin zuciyar ta, saidai tanata kokarin kar fuskanta ya nuna amman aikin gama ya gama tun lokacin datayi karamar ajiyan zuciya yayi murmushi a siniyance sannan yace"

Ya kirjin ki yabar bugawa??

   A'a har yanzun Yana yi"

  Kina addu'a?

   Eh"

 Yayi, ingaya miki abun da nake so dake??

Kanta ta daga alamar eh"

   Banson ihun dare, tare da surutun da kike yi, can gidan bashi da fadi kamar nan za'a iya jin mu"

Jinta ta yayi shiru yasa shi fadin"

  Zaki bari?

   Kawar dakai tayi tare da girgiza kanta alamar a'a

 Bazaki bari ba??"

 Wannan karon kin amsawa tayi dan haka yace shikenan, yanzun gaya min kina sona??

 Cikin sauri ta girgiza kanta"

 Cikin rashin kuzari yace shikenan"

Mikewa yayi yasa hannun sa cikin aljihun sa sannan ya fice adakin”

     Yana fita ba jimawa aka shigo daukan kayan su, Dan haka Munirah ma tafice apart din"

   Can gurin Mamah ta sameshi da alama sirri sukeyi ganin inda sukayi saurin yin shiru tada shigo, ganin haka ta juya da sauri, gurin Zahra ta zauna dake zaune afalon"

       Yau sai gida

 Wlh gobe war haka cikin gida zan wuni, Amman kinsan me?

A'a

Wlh sainaji inajin kewan ku kamar karna tafi”

   Nima haka nake ji tamkar kuyi zaman ku anan"

Shiru Munirah rayi zuwa can tace kema da kindawo can basai ayi yar gida da Amukarnin Mubarak ba"

  Kekiji iskanci, rabani da wahala, saidai nazo da yawo badai zama ba ko, Ina ni Ina auren wanan kusan halin su daya da Amukarnin Sadiq"

A'a wlh ba halin su daya ba, Amukarnin Mubarak barshi da mugunta da cinzali  Amman baya tamke fuska Kuma idan kikajishi Yana wasa da dariya saikisha mamaki kusan irin su daya da Amukarnin Sagir saidai shi Sagir yafishi son wasa da kowa, ni wlh dama shi aka aura min sainafi jin dadi akan auren wannan abu"

Caff di, wai kikuwa Munirah kina da hankali kuwa?, da auren akanki kike irin wannan mgnr"

 Kinfi son inbarta acikina?, ai gara in fitar karta kasheni, ai gaskiyata nafada ba karya ba"

Kidaiji tsoron Allah ki daraja auren ki, yakamata ace yanzun kin hakura, Amukarnin Sadiq ma banda abun ki duk yafiso kyau wlh, Kuma yafisu gayu da son kyle Kyle matsalarsa daure fuska da nuna be daukan wargi Kuma wannan ai hallita ce"

 Me yadaman da gayun sa, ke bakima san menene ba?, wai shekaran jiya saiga dan mutumin ka ya lallabo wai dan rashin kunya Amukarnin ne ya zauna gabana yana furta min so, ke kiji iskanci????

 Dariya Sosai Zahrah tayi sannan tace lallai Munirah kin cire tuta, tunda har Amukarnin Sadiq ya zubar da son girmansa yake miki wannan kalamin, wlh da gaske yake yi son naki yake yi, lallai kinyi sa'a banyi tsammanin haka da wuri daga gareshi ba sabo da halin ko in kula danaga Yana nunawa, lallai aure daraja garai, toh ke me kikace masa??

 Cewa nayi banson sa"

Kiri kiri, wlh kibari Munirah karki kuresa ya Kara aure, naga sai lallabaki yake yi yanata wani ji dake, ji inda ya waske Hafsat da mari kanki, idan ba sa’a akaciba sun kullah gaba kenan dan Hafsat ta shaka”

   Tsaki Munirah taja, wlh banson Amukarnin Kuma bazan taba son shi yaje can su karata da yar iskar"

Mudai abar cika mana baki kar anan gaba kadan muji ana soyewa”

 Allah tirrr wlh, shi kanshi yasan baya gabana, Kuma ki tambaye shi kiji ya san ba son shi nake ba"

A'a Munirah fa ranar nan fa kiketa zagin Hafsat kan kin ganta da mijin ki"

 Toh ai saikita yi, nidai nasan ba son shi nake ba Kuma zaki gani, ni yanzun ma kinsan meke damuna"

 A'a

Namasifar kosawa inganni agida saboda yadda nakejin gabana nafaduwa”

   Toh Allah ya kauta Munirah wannan faduwan gaba ko na menene kike tayin sa kwana da kwanaki????

     Wlh kuwa nafi ganin kamar wani abu ne zai faru"

Kila Kuma daukin ganin yan gida ne Kuma fa"

Toh Allah yasa haka ne, Amman nifa ko tunda Amukarnin Sagir ya rasu banki duk samarin duniyar su mace ba kowa ma ya rasa 

   Subuhanallahi, Munirah saikace me bakar zuciya, kowa zai mace amman saiya cinye lokacin shi.... 


  Fitowan Sadiq yasa sukayi shiru shida Mamah, Munirah ma mikewa tayi ta koma jikin Mamah cikin shagaba suke sallama inda suka rankaya falon tsoho, can ma albarka yaita sa masu sannan suka fito bakin motar da hannunsa yasa Munirah acikin motar yanai mata addu'a haka shima Sadiq yanajin yadda tsoho keta masu fatan Alheri "

        Hawaye ne ya zobowa Munirah lokacin dataga Motar su tafara tafiya yayin datasu Moh'd da wasu abokan Sadiq guda biyu ke bin bayan su, waigen Mamah da tsoho Munirah ta fara harma da Zahra dake dago masu hannun"

 Ganin sunyi nisa Munira batarbar waige ba yasa Sadiq ya kama kanta cikin murmushi ya juyo da ita yayin da yaga hawaye nabin idonta murmushi sa ya fadada sannan yace"

  Yi hakuri kwanwata, har kinsaba dasu har haka?, Ki hakura zamu dawo wata rana kinji kan kirjin shi ya kwantar da ita Yana rarrashin ta tare da kissing dinta Yana goga mata gemun shi"

      Koda suka Isa filin jirgi sallama sukayi dasu Moh'd  yayin da Munirah tacigaba da share hawaye, mannata yayi da jikinsa Yana shafa bayanta tare da fadin kodai in barki anan ne?

 Kanta ta girgiza dan haka yace toh meyesa kike kuka??

  Ni banajin dadi ne Kuma kirjina na bugawa"

Cikin gajiya da kalaminta yace"

Bar kula faduwan gaban nan kiyi harkar ki Babu komai kinji, ba abun da zai faru"

Amsawa tayi tare da danjin dadin kalamin sa har jirgin ya tashi tana makale dashi har bacci tayi jikin sa batare data sani ba, can cikin baccin ta taji yana waya, yayin da yake fadin abashi minti 30 gashinan zuwa cikin harcen turanci"

  Tana bude idonta taga anfara sauka yayin da Sadiq ya mike tare da ita har suka sauka, tundaga nisa ta hangi Mubarak da Anass suna tahowa, sakinta Sadiq yayi. Suka rungumi juna da Mubarak sannan yace"

 Anajirana a office zan bada sako, ka wace da Tamuddirincin yanzun zanzo"

 Hannun Munirah ya kama yasata amotar Mubarak sannan ya sunbaceta tare da sakar mata murmushi ya rufe motar yana fadin banda surutu"

 Binsa da kallo tayi har ya shiga motar anass ya zauna sanan ya dago mata hannu"

Bakinta ta murguda masa tare da galla masa  harara.......

????????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????
????
SAWUN BAYA
????
Book 2 ????????
????????????
????????????????????
????????????????????????????

                    Na
          _Fadeela Lamido_

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

PEN: WRITER’S ASSOCIATION ©

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️


~only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers~


https://mobile.facebook.com/Pen-Writers-Association-100990022185172
            Page 61- 62

Typing…..
Cikin Mamaki Mubarak ya kalli Munirah cikin tsawa yace”

Ke!! har yanzun bakibar rashin kunya ba ko?

Nan danan ta gyara fuskanta tare da satan kallon Motar da Sadiq ya shiga, gani tayi ya dago mata hannu yayin data sinnen kanta askarshe ma ta kauda ka gaba daya"

 Shiko Mubarak cikin tsabar takaici yaja motar acikin ransa Yana mamakin taurin kai irin na Munirah"

 Bayan sun Isa gida gaba daya gidan waje suka samesu inda kowa ke kokarin rungume Munirah, saidai abun da ta lura dashi duk jikin su yayi sanyi da akace Sadiq ya wuce Office dan haka gaba daya mazan bayan sun gaisa da Munirah suka wuce gurin kasuwancin su Amman banda Mubarak dayai ta jiran dawowan Sadiq"

  Yau Munirah tana gaban Annanin ta inda take ta bata lbrn ingal da Arlit  Mubarak dake zaune falon yanajinta sai zuba take Annanin da Lubbunah ko sai shan hira suke suna dariya"

Kallon Munirah mahaifiyar tata taita yi duk da batai kibaba amman tayi kau shar da ita gwanin ban sha'awa, cikin zolaya Lubbunah tace"

Kinata bamu lbrn Ingall Baki bamu na Amukarnin Sadiq ba????

 Dauke wuta Munirah tayi cikin runtse Ido tace, wani kaya ne Kuma haka?

  Amukarnin Sadiq dinne kaya?

Idonta rufe tace kinga ni Lubbunah kibari banso, Ina abun da ya daman dashi”

Allah ya Baki hakuri na dauka yanzun kina son shine ?

Allah ya kauta me zandashi….

Annanin ce ta katseta da fadin”

  Ke!!! Ya Isa haka, ke Kuma Lubbunah  rabu da ita, ni dazakuji ma danace muku kar Wanda ya sake mata mgnr Sadiq acikin gidan nan tunda ita bata da Mutunci ni dazasu gane subashi ita yakaita gidan shi mubar ganin mara hankali"

  Kuka Munirah ta fara tare da fakan idon Mahaifiyar ta tana hararan Lubbunah, muryan Mubarak taji yace ke dan ubanki kina nan da halin ki ko, tasowa yayi yana mazorai sosai yayo kanta cikin sauri Annanin tace karka taba ta, ta dai tashi ta wuce dakinta kawai"

Cikin fada Mubarak ya kori Munirah inda ta fice tana share hawaye shikuwa har harabar gidan ya biyota Yana ta faman zaginta, ana suka hadu da Umma wadda fitowanta kenan daga part dinta ta kalli Munirah tace yaya dai?

Kwalkwal tayi da Ido tana me komawa kusa da Umma, inda cikin baccin rai Mubarak ya shiga gayawa Umma Munirah taki canza hali"

  Jikinta da sanyi sosai ta kalli Munirah sannan tace"

 Shine ka biyota da zagi haka, ina ruwan ka?

  Amman Umma ai be daceba, rashin duka ne ke damun Munirah ba wani abu ba, da za'a bata kashi databar wannan shagwabar"

Hannunta kawai Umma ta rike suka koma cikin part dinta yayin da Mubarak ya daga waya Yana neman layin Sadiq"

    Kamar jira yake ya dauka, Yana fadin ganinan zuwa"

   Nagaji da jira barin fita kawai, idan ka dawo ka kirani a waya"

 Okay toh shikenan Ina Tamuddirincin?

Yanzun ta shiga gun Umma wlh naso ma inzane shegiya har yanzun bata da kunya”

     Ai daka gwada????

Allah ba wasa nake ba daga dawowanta harta fara baza hali, ita bata sonka bata son ka????

 Kashhhh ????????????, injita ko?, Cikin tsananin bacin rai yai tambayan inda ya kasa jurewa kafin Mubarak ya amsa shi ya kashe wayar"

    Idon shi jawur yayi lokaci daya inda ya fada tunani, takardun dake gaban sa ya fara tattarawa dan gaba daya ya fara yasa ne yake yi , afili yace meyasa ma nabarta taje gida ita daya????????

 Cikin sauri ya fito harabar bakin su yana tsaye hannun sa cikin aljihu, sabo da kosawan da yayi kasa jiran Anass yayi ya karaso, dan haka yana ganin wani abokin aikin sa zai fita ya nemi daya sauke shi agida"

              ******

Tunda Annanin ta shiga part dinta da Munirah kallota kawai take aranta take fadin ga mutum har mutun amman babu hankali, sosai abun ya isheta, sosai take tausayin Sadiq ayanzun domin idan ta kirashi koshi ya kirata baya taba numa mata akwai wata matsal, shiyasa kwana biyu taji ta Samu nutsuwa sosai Amman yau hankalinta ya tashi sosai”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button