A TSAKANKANIN SOYAYYA HAUSA NOVEL

A TSAKANKANIN SOYAYYA HAUSA NOVEL

         _IN BETWEEN THE LOVE_
        ❤ _Lies another love_❤




        _✍????M Shakur_



                    7️⃣ & 8️⃣

how to pay your subscription fee

zaki turo 300 ta account number na 3107021073 aisha Muhammad first bank saiki turo evidence of payment ta WhatsApp number na 07012181461, sainai adding dinki a group din danake posting

you can also send MTN card ta WhatsApp number na 07012181461 in baki da banki, sainai adding naki a group din danake posting

Free Page

Dan kallon ko ina yayi a anguwan ganin ba mutane yasa yaji dadi lemme just kill two birds with one stone, taku daya yayi ya fizgo hijabin Aneesa hakan yasa Rauda tai mugun faduwa sabida kayansu data kulle atare, bugawa kirjin Aneesa yashiga yi hakan yasa ta shiga kiran sunayen Allah a ranta, cikin karfin hali ta take kafarshi cikeda tsiwa tace “kasakeni” girgiza mata kai yayi yana kallon kwayan idanunta yace “saikinyi daga daga dani as you said Hajiya, thank God babu kowa a layin amfanin unguwan masu kudi kenan, oya fara” ya mika mata jikinshi jiran tadake shi, ganin hankalinshi baya kanta yasa Rauda data zube akasa ta mika hannu ahankali taja wayar Aneesa touch light phone dayadan zamo daga jakanta dake kwance akasan wajen, hannu tamika taja wayan tsabagen yanda tarude batasan lokacin data shiga saka number Ya Aliyu na Nigeria ba tana addu’a Allah yasa yasaka layin tai dialing, kaman ance yadaga kai yaga Rauda rikeda waya, ganin waya a hanunta yasa Khamis yawani irin ture Aneesa da karfi hartana buge gate yay kan Raudan cikeda bacin rai, fizgo bayan riganshi Aneesa tayi tace “kin kira, yi sauri an dauka?” komawa baya Rauda tayi tana sake dailing number Ya Aliyu daya gama ringing bai dauka ba tana kuka sosai tana kallon Khamis dake kokarin fizge riganshi daga rikon da Aneesa tamai….

Uban gudu yake shararawa kan titi ya kunna waka dake tashi kadan kadan, shi kadai a motar da kamshin ciki yahadu da kamshin jikinshi sai abin ya gauraye yabada wani d’adadden kamshi mai melting zuciya, sai murmushi yake rabonshi daya fita alone, sanan rabonshi daya rike starring mota yay tukoi harya manta wlh, yauma bakaramin rigima sukai da Dad ba kafin ya yarda yafito shi kadaiba dan saidama yace yafasa zuwa gidan Momma, ganin bakuwar number yasake kiranshi yasa yay dan tsaki tareda yatsine fuska yadau wayar yakara kunne batare dayace komiba. “Y…Ya Aliyu I…is me, me, me ne, Rauda, ka…g..kaga Ya Kham…Khamis is trying to ra…p..pe me” yanda Rauda tai maganan tana kuka sosai muryanta na breaking baima gane kan zancenta ba sai kalmar karshen rape dayaji yasa yaji kirjinshi yabuga sosai, gangarawa gefen titi yayi yaci brake cikin tsawa yakira sunanta. “Rauda, calm down, tell me who is Khamis and where are you? Keda waye ne, where are you?” arude ta kalli layin tace “Suleja bansan inane anguwan ba” da sauri Aneesa data rike bayan rigan Khamis da duka karfin ta ta bude murya tace “layin yan gayu a Suleja” baki Rauda tabude zatai magana danta fadamai sunan layin yasa kafa cikeda fushi ya bugi hanunta da kunenta data kara wayan hakan yasa wayar tai tsalle tawani irin tarwatse a gefe, yanda takalmin shi yadaki gefen kunenta saida idanun ta suka juya tai baya kaman wacce ke shirin sumewa kunenta yay wani irin dummmm bamataji jinta yadauke duka. “dan uwarki sabida tuntuni banso na dakeki angayamiki kin gagareni ne” arude Aneesa data rike bayan riganshi ta sakeshi ta rarrafo da sauri tana kallonta tace “innalillahi wa innailaihi raji’un, kai mugu ne wlh Allah ya saka mata, kunenta” tamika hannu zata taro Raudan datai baya zata zube akasa, wani irin fizgo Aneesan yay da hannu daya zatai magana yasa hannu ya dauketa da lafiyayyen mari mai kyau yace “you had your chance kitafi amma kika tsaya” bude Gate din gidan yayi ya wani irin tura Aneesan ciki da duka karfinshi tafadi akasa da sauri ta mike zata fito ya finciko Rauda datai kasa ya shigo da ita hakan yasa Aneesa tace “kabarmu mutafi Malam ga gidan nan babu kowa ciki, dama nafada tun dazu karya kake, kallo daya za’amaka agane kai irin yan iskan mazan nanne masu lalata yaran al’umma,

Parking motar Aliyu yayi d’an almajirin dake zaune yace “nan ne layin yan gayun yallabai” kudi Aliyu yaciro dabaisan adadin yawansu ba yamikama dan almajirin yaron, yaron ya karba tareda washemai baki yana rike robar almajirin cinshi da kyau yace “nagode, Allah yabiya” yay maganan yanataba kofan motan yace “taki buduwa” matsowa yayi kaman matsoraci yabude mai kofar da gudu almajirin yafita yana tsalle yana kara kallon tulin kudin da tunda yake baitaba ganin kowani a gidansu yarike irinsu ba, tada motar yayi yana tafiya yana sake trying number data kirashi dashi baya shiga sanan yana kiran asalin number ta shima baya shiga, sosai yashiga cikin tsananin damuwa ahankali yake tuki a dogon layin da baya ma ganin jama’a ciki, harya shanye layin shi baiga kowaba hakan yasa yasake yo kwana yajuyo tundaga nesa yake hango gyalen Raudan daya gyara mata dazu dasafe da kanshi akasa kan wani dutse iska na karkadashi, tun kafin ya iso wajen da gyalen yake yay parking baima tsaya rufe motar da kyauba yataho dasauri tsugunnawa yayi yadau gyalen ahankali yana kara kallon gyalen this is definitely gyalen Rauda, sake bugawa kirjinshi yayi wats happening to my sister ya tambayi kanshi, rike gyalen gam yayi Yajuya yana kalle kallen gidajen kan hanyar yaciro waya yana kokarin kiran Dad…..

Jan Raudan yayi da batada karfi ko digi ajiki har yanzu jin kennenta take dummm kaman banata ba Aneesa da jikinta yafara rawa sosai ganin yanda yawani irin daure fuska tasaki wani irin wawan ihu. “Ammiiiiiii! Wayyo Allah n…” buge bakinta yayi azuciye yace “yau zakici uwarki, gwara wanan” yanuna Rauda dake sauke ajiyan zuciya kawai yace “su sunsan inda zasu ganni a duniyan nan , keko baki sanni ba, daga yau baki kara haduwa dani, shiga shara ba shanu banga uban abinda zai hanani yimiki fata fataba dama daga ganinki zakiyi man shanu” ya jasu duka biyun kaman raguna yay hanyar kofar dakin zai shigar dasu, Aneesa sai tutturjewa take, wani irin bugo Gate din da akayi da karfin bala’i yasa dukansu ukun suka waigo, ido da ido Khamis yay da Aliyu dake sanye cikin wani Milk wagambarin shadda da aka mishi dinkin fitted yaji aikin hannu, yasa takalmi irin na yan gidan sarauta dinan kanshi babu hula sai bakin gashin kanshi dake masifar kyalli kaman ya shafa man gashi, idanunshi sanye cikin dark shade abinda yaboye jan da idanunshi sukayi kenan tsabagen yanda ranshi yakai ga baci, yana tsaye wajen Gate amma saida kamshin turarenshi yakai har inda suke gaban kofa ko ina yadau kamshin shi, ganin Aliyun yasa wani irin karfi yazoma Rauda tawani irin fizge hannunta daga rikon da Khamis yamata ta tashi tsaye tazo da gudu tafada jikin Aliyu tasaki kuka sosai takasa magana, ganin haka yasa Aneesa ma da gabanta ke faduwa bana wasaba ta fizge hijabin ta da Khamis yarike ta taho da saurinta gefensu Aliyun ta tsaya kirjinta na bugawa kaman zai tsage, dan wayancewa Khamis yayi yakakalo murmushi yatako ahankali yana dumfaro su da sauri Rauda tasaki Aliyu takoma bayanshi ta labe tana kuka hakan yasa Khamis ya tsaya chak a tsakar gidan yakasa karasowa gabansu, hannu Aliyu yasa yazare dark shade din dake idanunshi ya zubama Khamis jajayen idanunshi dayasa yaji internal organs dinshi na girgiza cikin wani Husky harsh voice yace “how dare you raise those your filty hands on my sister, how dare you touch her” hausawa sunce tabarman kunya da hauka ake nannade ta, cikeda borin kunya shi adole shi shine yace “who is your sister? Raudan ce sister ka?” ya tambayi Aliyu cikeda kallon isgilanci yace “as far as am concern and base on wat I know ko mahaifiyar ta tacha cewa kai ba wan yaranta bane, you guys are not blood related, bama tasan da zamanka ba, kuma mahaifiyarta tabani izini na dauketa nakaita yawon ido karmu dawo sai dare gatanan u can ask her and hear for yourself, banda hakama who do you think you are to talk to me in such manner nafika matsayi da iko akan Rauda, am her Mum’s elder sisters first son, and her husband to be, ko ubanka yasan da hakan so back off please, ke Rauda let’s go” yay maganan yana tahowa yazohar gaban Aliyun yasa hannu zai jawo Raudan cikin wani irin fushi Aliyu ya kwasheshi da mahaukacin mari. “Tau!” da sauri Aliyu yarike hanunshi sabida zafin da hanunshi yadauka ya murza hanun kaman zaiyi kuka yace “aauchhhh” yana yarfe hannun, yanda yayi saida yasa Khamis fashewa da mugun dariya dudda marin ta shigeshi dan har gefen fuskar da Aliyun ya mara yay ja abunku da fari, da yatsa ya nuna Aliyun dake yarfe hannu yana yatsine fuska yace “wanan ne, wanan ajebotan kuka kira yay protecting naku daga ni? wanan malalacin namijin daya rako maza duniya wanan maza matan dayamafi mace yauki kaman kubewa ne kuka tunanin can beat me up?” hannu yakai yafara bude boturan gaban shaddan riganshi yace “zan nunama u have messed with the wrong guy ni haifaffen dan kwari ne ba girman turai ba, girman tasha, kar har purewater na saida a park” fashewa da kuka Rauda tayi dan tasan Ya Aliyu bai iya fadaba ko kadan ta jijjigashi tace “Ya Aliyu mugudu please” itama Aneesan jikinta rawa yafara ganin Khamis cikakken dan tasha ne kam yana magana kaman dan wiwi, riganshi ya zare ya yar akasa ya matso gaban Aliyu ahaukace yasa duka hannayenshi ya daki kirjin Aliyu da saida yay baya kaman zai fadi yace “kai ubanka yaci ubanka kaji, dan babar ka nataba kanwar taka uban me zaka iya? Eh nace ubanme zaka iya?” Khamis yay maganan kaman dan daba yana hura hanci, Aliyu ya kafeshi da ido he really do not know how tayaya ma zai fara fighting dinshi ba, indako yasani daya kusan kashe yaron nan, cikin kuri yay pointing Aliyun da yatsa yana murmushi ya kalli Aneesa da Raudan dasukai zuru zurun barinma Rauda dake kuka wiwi za’a dakinmata yayanta yace “do you all see what am saying, bakazo shigarma kanwarka dat I was trying to rape bane? Then beat me up now Aliyu, are you scared Mama boy? Beat me mana, kawa Allah ka dakan, baku ganiba matsoraci bane, kai” ya dungure ma Aliyun goshi da yatsa Aliyu yasakeyin baya, Khamis ya nunamai yatsar shi ta tsakiya yace “fk you Aliyu, I said fk you mezaka iya? Daken mana kaji tsoro ne eh? Eh malalaci?” yanda yakema Aliyun daya tsaya kikam yana kallonshi tijara yamugun sosa ran Aneesa saitaji kaman tai kuka dan daga ganin yanda Aliyu ya mareshi da farko ya shiga yarfe hannu zaka gane baida karfi kona sisi, kallon yanda Rauda ke kuka sosai abayanshi take alamun batada hope zai musu dukan tsiya sanan yama yayan nata dukan tsiya shima hakan yasa taji wani karfi yazo mata da bata taba jin irin that kind boldness ba in her life, cikin wani irin izza ta shiga gaban Aliyu tana taku dai dai tana clapping hands dinta cikin isa da takama tana clapping din tana kallon fuskan Khamis din dake kallonta kaman yanzu yafara ganinta, tsayar da tafin tayi tace “kasan mesa nake tafa maka?” tai wani murmushi ganin baice komiba kawai kallonta yake kaman wani wawa tace “wani zubin idan kare na haushi idan kai tafi saikaga yadan natsu” cikin fada yace “nikike cema kare?” cikin dakewa ta nunamai yatsa tace “quit, am still talking” samun kanshi yayi dayin gum ganin yar yarinya namai magana kaman uwarshi, tace “what differentiate human being da animals is ability to think and reason which bakada duka biyun you are just a dog malam which yayan mu bazai taba iya biyema yadawo kaman kaiba ko?” tadan juyo for the first time ta kalleshi idanunshi da nata suka sarke faduwa sosai gabanta yayi tadan kyafkyafta ido sau biyu pink lips dinta sukadanyi rawa ahankali tace “ko?” gyadamata kai Aliyu yayi batare dayasan yamayi ba, juyar da kanta tayi tace “kai mailafine bagaremu ba kadai har agun Allah, sanan kanada bakin zage zage kana turashi kanaso yabiye maka kuyi fada, wai intambayeka man do you know who is a Man?” wani matsiyacin kallo tamai ganin yanda yasaki baki yana kallonta tace “A Man baya tsayawa yay physical fight da kowa dan physical fight dangrades one’s level, banda haka a Man is someone who has control over his heart ayayin dayake cikin tsananin fushi which is abinda yayi yanzu, kazaci kana ihu kana cika kana batsewa kana tunanin by d time dayake so yaci ubanka you can match his level ne eh?” tamai tambayan tana hura hanci daya kaman wata boss tana kallonshi, dan murmushi Aliyu yasaki for the first time ya rungume hannayenshi a kirji, ganin har lokacin Khamis din baice komiba ya tsaya yana mamakin tane yasa tace “and yanzun nan zan nunamaka idan yatashi yace zai ci uban naka u can never match his level of power, kwabaka zaiyi kaman yanda ake kwaba dibila tsaya kagani” tai maganan tana tsugunna wa a wurin duk suka bita da kallo kasan dake bakin Gate din ta kwasa da hannunta dayawa batare da duksun luraba dan hijabinta yarufe mata hannu sundaiga ta tsugunna mikewa tsaye tayi Khamis din nabinta da kallo hannunta tadaga un expectedly ta watsamai kasan a fuska aiko suka shiga idanunshi biyu, ihu yayi. “wayyo Allah na, wash Allah idanuna, sainaci durun uwarki yarinyar nan” yayo kanta yana sosa idanunshi dayakasa budesu tsabagen kasan data sakamai a ciki matsawa gefe tayi da gudu ta kalli Ya Aliyu dake binta da kallo tace “Yayan mu yimai shegen duka ramama kanwarka abinda yamata bazai iya ramawa ba idanunshi cike suke da kasa” ware manyan idanunshi Aliyu yayi yana kallon this wired girl, gyadamai kai tayi da sauri tace “ka zaneshi, daddaki azzalumin” jin daga ta inda take magana yasa Khamis yay wurin yana murza ido yace “dan uwarki ubanwa yace miki koni makahone zai iya tabani ne wanan ragon” dawowa tayi kusada Aliyun ta kallai tace “yimai lilis u can do it, zo zan nuna maka inda zaka dinga duka ajikinshi zokaga” tai gaban Khamis din dake bubbude kafa yana sosa idanu kaman mahaukaci tsabagen azaban kasan dake cikin idon, ta nunama Aliyu cikin shi daya fara dan tara teba dama babu riga ajikinshi tace “zoka naushi nan” turashi Rauda tayi tace “muci ubanshi Ya Aliyu ka rama mana” ahankali Aliyu yadaga kafa yana kallon Aneesa dake nunamai cikin Khamis kaman wawa yakaraso kusada inda take yana kallonta still, zare ido tayi tsabagen jin dadi zasuci ubanshi tarage murya kaman mai shirin gulma tace “yauwa naushi nan”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57Next page

Leave a Reply

Back to top button