A TSAKANKANIN SOYAYYA HAUSA NOVEL

A TSAKANKANIN SOYAYYA HAUSA NOVEL

duk wacce takaranta bata biyaba itada Allah, duk maison book dinan ta tuntubeni ta 07012181461 watsapp
masu fitarwa dama ku watstsatsu ne, saika kuka watsawa, ban yafemukuba kuma, rubabbu kawai
[4/5, 8:09 AM] Hijabi_muslimah????: A TSAKANKANIN SOYAYYA

         _IN BETWEEN THE LOVE_
        ❤ _Lies another love_❤




        _✍????M Shakur_



                    3️⃣1️⃣

Gida suka karasa bayan sun tsaya sunyi sallan isha’i, thank God Momma bata falo dakinsu ya wuce direct dan ko kadan bazai iya tsayawa mata magana ba, ko takalmi bai cireba yafada kan gado yaja bargo yarufe tundaga kanshi har zuwa kafafunshi, inda ace zai biyema zuciyan shi kuka kawai zaitayi batare dayasan mezaiyi ya sanyayamai raiba, he’s so soo maddd, so angry, ya tsani yaga Aneesa dawani tanamai magana jiyake kaman zai fadi yamutu, baima san tayaya zaiyi describing yanda zuciyan shi kemai zafiba idan ya ganta dawani, jiyake kaman ana daddatse mai zuciya da babban wuka, wani irin wahalallen bacci ne yay awon gaba dashi yana cikin tunani. Abdul ne yabude kofar dakin ya shigo zaimai magana yaga har yay bacci ya dunkule agado looking so innocent ko kayan jikinshi ma bai cireba yana sauke ajiyan zuciya daddaya, ahankali yazauna abakin gadon yana kallonshi yana tunani yaushe har soyayyan barkono yakama shi haka? Rashin amsan tambayan shi yasa shima duk yunwan da yakeji yaji takoma ciki ya kwanta gefen Aliyun shima batare daya cire kayaba nan wani shegen bacci yay awon gaba dashi.

Momma dake kitchen dasuka shigo ne tafito Ihsan dake biyeda ita tafito itama, Ihsan ta kalla tace “jeki kiramin su suzo suci abinci” sama Ihsan tayi bata wani jimaba ta sauko tana dariya tace “Momma duk sunyi bacci ko takalma basu cireba” girgiza kai Momma tayi tace “Aliyu da Abdul ai saidai Allah ya shirya domin kam duk kanwar ja ce” ta gyara zama tana kokarin daukan remote dake kan dayan kujeran tace “jekici abincin ki Ihsan”.

Sai wuraren shadaya sanan Aneesa tabaro wurin Baffa dasuka wuce dakin zaure dasuke kwana itakuma tadawo daki, kulle kofa tayi dan tasan Ammi ta riga ta kwanta, dakin Ammi ta wuce straight Ammi na zaune kan gado tana linke kayan data cire, kallo daya tama Aneesan ta dauke kai, murmushi Aneesa tayi takarasa kan gadon ta zauna kusada Ammin, kayan ta karba takarasa linkewa ta tashi tai wajen sip din Ammi, sip din tabude tana kokarin maida kayan ciki tace “Ammi kinason Abban? Naga su Baffa sunce jibi ne bikin” tana maganan tana jera kayan a sip, jin Ammi ba tace komiba yasa ta juyo ta kalleta, hada ido sukayi da Ammi dake kallonta, washe baki tayi takaraso ta zauna kusada Ammi tareda daura hanunta kan cinyar Ammi tace “eh Ammi, bakice komiba” dan murmushi Ammi tayi tace “kina sonshi to Aneesa, ba dole na yarda ba” washe baki tasake yi tace “nagode Ammi na, Ammi kinga ko nizan miki lallen biki, in miki kwalliya dakomi ko Ammi” tabe baki Ammi tayi tace “nine zanyi wani lalle saikace bikin yar yarinya” kaman Aneesa zatai kuka tace “wlh nisaina miki, Ammi na mai shegen kyau kinji” tabe baki Ammi tayi tace “naji to, Allah kaimu da rai da lafiya” Ameen Aneesa tace haka tacika Ammi da surutu har Ammi tagaji tace mata tamata shiru kota maketa, gabaki daya tama manta da batun wani Aliyu daya bata mata rai dazu, bamata so ta tuna ko kadan, mamanta is getting married so she’s super excited.

masu iya magana sunce rana bata karya, saidai uwar diya taji……..

Yau dubannin jama’a wayanda suka halarci sallan jumma’a a babban central mosque in Suleja, wanda ya kunshi mutane da dama daga ciki harda abokanen Dady na wajen aiki da kasuwance, Aliyu, Abdul, dakuma Baban Abdul (mijin Momma), shi kanshi Dady dayaci wata fitinannan shadda wacce taci sunanta shadda, dakuma su Baffa da fuskokin su ke dauke da annuri, limami ya daura aure tsakanin Alhaji Muhammad Ibrahim da kuma Rukayya Hamisu, inda su Baffa da mutane da dama suka shaida sai murna ake ana hayaniya, sosai Aliyu ke murmushi he’s trying his best yaboye damuwan shi dan baiso Dady yagane, today is a happy day for Dady baiso yaga any sign of something a tattare dashi ya shiga damuwa, yanada matsala daya addabi zuciyan shi ainun rabonshi da Aneesa tun ranan nan, yakira layin ta taki dagawa daga bayama kashe wayan tayi gabaki daya, gajiya ma Yayi da amsa gaisuwan mutane ganin kanshi yafara masifan ciwo ya kalli Abdul dake kusada shi shima yana sanye cikin shadda fara kaman tashi yace “am going home” da sauri Abdul yace “me haka? Kasan Dady zai nemeka ko” yatsine fuska yayi yace “stay kai, am having headache, inya tambayeni kacemai naje gida” yana yin maganan yay tafiya yana kallon Dady dake washe baki kaman anmai kyautan makka yana gaisawa da mutane, yawuce ya shiga mota yaja zuwa chan Abuja dan yasan koyaje gidan momma dake nan Suleja dakwai hayaniya kuma baison hayaniya ko kadan, yana danna mota cikin gidan Maman su Rauda na fitowa daga motar ta datai parking, wani natsiyacin kallo tama motarshi ko damuwa baiyi a yabude yafito yay side dinshi batare dayama inda take second look ba ballema yasan wats she’s up to, kwafa Maman su Rauda tayi tace “inhar ban koyama Aliyu hankali ba aduniyan nan basunana Kareema ba wanan alkawari ne namaka, wlh kuwa” tai kwafa tawuce dakinta.

Bude part dinshi yayi ya shiga yaji ko ina na kamshin turaren wuta lumshe ido yayi yabude dan yana mugun son kamshi kuma yasan aikin Rauda ne hakan yamaida kofar yarufe yya hanyar bedroom dinshi, kaya yarage ya shiga wanka koyaji dadin jikinshi, baiwani jimaba yafito yana yatsine fuska sanye da bathrobe yafada kan gado tareda daukan wayanshi yana kallon number Aneesa yanaso yakira but yasan koya kira bazata dauka ba, ahankali bacci yay awon gaba dashi.

Bangaren su Ammi, Suleja
Yau jumma’a tun kafin a daura auren wuraren karfe takwas nasafe Momma da kawayenta suka kawo akwati guda goma inda saiti bakwai na Ammi ne dake cike da hadaddun kaya da an dinka wasu wasu kuma ba’a dinka ba saiti uku kuma na Aneesa ne da aka cikamata da kaya na yamma ta harda dogunayen riga Aneesa harda kuka, few kawayen Ammi na anguwan ne suka tarbesu itakuma Ammi taki fitowa har suka tafi anata guda daga baya aka daura hadadden abinci dan tun jiya Dady ya turo da motan kawo abinci Aneesa tama Ammi hadadden lalle bana wasaba ta shirya Ammi cikin wani lace mai kyau sky blue da fari ta rungume Ammi yafi sau dari sabida yanda Ammi tai kyau sanan takawo wani farin babban mayafi ta yafama Ammi, Ammi sai amsan gaisuwa take tana murmushi ka ganta itada Aneesa zaka zaci y’a da kanwa ne, Aneesa itama wani farin lace tasaka mai ratsin pink shima dadin ne yaaaimata takai aka dinka mata tai kyau telan dudda bai aunata ba amma chip chip yamata yafito da shape dinta sosai bana wasaba sai murna take ko ita ke aure albarka.

Wajajen karfe uku anguwan ya cika da maza da mawaka ana wake Dady, Baffa ne ya shigo ya leko ya kira Aneesa dake tsakar gida tana nan tai chan tama kasa zama waje daya da gudu tai wajen Baffa a zaure, baki Baffa yarike yace “wai wai wai, masha Allahu, ashe haka yar tawa keda kyau aida kyar naganeki wanan kyau haka” wani irin cute smile tayi cike da zumudi tace “Baffa an daura? Yanzu Abba yadawo mijin Ammi na?” tafada cikeda wani irin murna gyadamata kai Baffa yayi yace “kinsan mezakimin yanzu anjima zamuyi hira, yanzu jeki kawomin maman ki nan dakin mu ta zauna kifito, sabon baban ki keson yimata magana” da sauri Aneesa tace to Baffa tajuya da sauri takoma cikin gida Baffa yakoma waje ko minti daya ba’a yiba shida Dady suka shigo zauren tareda Baffa dakin su Baffa yabude ma Dady yace “shiga ka zauna na aika Aneesa takirata, cikin gidan mata sun cika abinka da gidan sha’ani” shiga ciki Dady yayi ya zauna yana murmushi yanadan girgiza kafa yawani irin kosa yaga Ammi ta shigo.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57Next page

Leave a Reply

Back to top button