A TSAKANKANIN SOYAYYA HAUSA NOVEL

A TSAKANKANIN SOYAYYA HAUSA NOVEL

         _IN BETWEEN THE LOVE_
        ❤ _Lies another love_❤




        _✍????M Shakur_



                    3️⃣5️⃣

Dady yace “Ummu Aliyu akwai enough food yar abokina na hanya, wacce zata zo muga yazata kasance ai nafada miki ko” fashewa da dariya Abdul yayi ganin yanda Aliyu yay kini kini da fuska, kallon fuskar Aliyun Ammi tayi tadanyi murmushi tace “shikenan Alhaji, kutaso kuzo kuci” tashi dukansu sukayi sukai dining banda Aliyu da ranshi yake abace, Momma tace “Beta are you not eating?” daure fuska yayi yace “am not” Momma zata kara magana ahankali Ammi tace “kuna damun min d’a fa” dan dariya daga Momma har Dady sukayi Momma tace “Aliyu kayan haushi, munkusa ganinku arana indai wanan rubabben yaron ne” girgiza kai Ammi tayi tadau tray ta daura plate of fried rice da chicken akai sai coconut juice a jug da glass cup tafito daga dining duk Dady dayay kaman yanacin abinci yana kallonta, dan karamin stool taja takawo gaban Aliyun da kunya yakamashi ganin itada kanta tazo, stool din taja ta daura tray akai sanan ta zauna gefenshi abincin ta dauka ta mikamai tace “don’t mind them ga abincin ka kaci bazasu ganmu arana bako” ahankali as usual yanda yakema Dady, a shagwabe yace “banda apatite nacin abincin Mum” dan shiru Ammi tayi tana nazarin fuskanshi kafin tace “okay let’s do this” tai maganan ta yanda daga ita sai Aliyun zasu ji, hakanan takeson yaron sanan yana bata tausayi ganin yanda yakeyi, komi babanshi, komi babanshi, ahankali tace “anama iyaye biyayya ne dan asami albarka right” gyadamata kai yayi tai murmushi tace “gud, give it a chance, idan tazo kaganta bakasan wazaka gani ba kuyi gaisuwa na mutunci koba komi kanwar kace itama ai ko, so karkaji komi inhar ina gidan nan you get to marry wacce kakeso, am your Mummy I will always stand by you against all odd, are we gud now” tunda Ammi take maganan yake kallonta ta bala’in burgeshi kawai ya girma ne da baiga mezai hanashi rungume ta ba maganganun ta sunmai dadi sosai, wani irin cute gamshashen smile yasakin mata tareda gyada mata kai yace “Alright Mum” murmushi itama Ammi tamai tace “ga abincin ka, bari naje naji da baban ka” da sauri yamika hannu ya karbi abincin yafara ci murmushi kowa na dining din sukayi dan hankalin su na kansu kuma tsaf sukaji abinda Ammi tafadin mai dudda bada karfi take maganganun ba, Dady karkada kafa kawai yake yana tunanin mezema Ammi, shi inhar mutum zaiso Aliyun nan nashi to wlh zaima iya bama mutumin kanshi ta hanyar zama bawa agreshi, Aliyu is his life so duk wanda zaizo Aliyu yagamamai komi aduniya, kujeran kusada shi da Ammi taja ta zauna yasa ya yadaga kai ya kalleta itama kallonshi tayi cikeda so da kauna, abincinshi yadeba da spoon yakai bakinta akunyace ta bude baki ta karba batason tai turning nashi down but she’s shy ga yara awurin kuma saisa kawai ta karba, sosa keya Abdul yayi ganin soyayyan tsofaffi kafin yaja plate dinshi ya sauka daga kan dining table din yakoma kan kujera wurin Aliyu, daga Momma har Ihsan sukai murmushi duk aka cigaba dacin abincin.

Dady ne yafara gama cin abincin dayamai shegen dadi yajuyo ya kalli Aliyu dahar yanzu baiyi rabin plate ba shi dama bai iyacin abinci da sauri sauri ba, baikuma iyacin abinci mai zafi sosai ba, bai kuma iyacin mai yaji ba yawuce yabude kofa yafita waje daidai lokacin yaga anbude gate wata mota ne ta danno kai cikin gidan hakan yasa yarage saurin dayake yanabin motan da kallo awajen parking space motar tai parking sanan aka bude kofa wata fine farar kafa ce dake sanye da prada hill mai ruwan gold, dayan kafar aka fitoda kafin wata yarinya tafito gabaki daya daga cikin motar, kyakkyawan yarinya ce fara tana sanye dawani riga da sket na Black lace yanada flawa mai ruwan gold tana sanye da takalmi Hill sosai mai ruwan gold tayafa wani siririn mayafi mai ruwan gold gold sai yar jakanta na Monalisa itama gold tasa wani sunshade a idanunta, zare glases din tayi fuskarta dauke dawani fine makeup an mata carving eye brows masu kyau sosai, da sauri Dady yace “oh Nafisa ce!” yay wurin motan maida kofan motar tayi tarufe da sauri tajuyo ganin Dady tana murmushi itama ta nufoshi, adan kunyace kanta akasa tace “Dady ina yini” cikeda fara’a Dady yace “sannu da zuwa Nafisa ke kadai kikazo, dakanki kikai driving?” gyadama Dady kai tayi, Dady yace “oh is risky, nafadama babanki fa ya dinga hadaki da bodyguard amma bayaji” murmushi tayi a shagwabe tana make kafada tace “Dady ni banaso fa” tabe baki Dady yayi yace “ahhh lallai taku kam tazo daya da Aliyun, ai yaron nan baya bari su bishi yanzu banma sanin lokacin dayake sabewa yafice daga gidan sabida karnace su rakashi, yara bakujin magana ba kusan kome mukeyi sabida kare lafiyanku bane” dariya tayi zatai magana Dady yace “common bance ki cikani da surutu ba, muje ki gaida matata, maman Aliyu, sai Momma shi my sister duk sunzo suna ciki” suna tafe suna hira da Dady har part din Ammi ahankali Dady yabude kofan tareda yin sallama hakan yasa dukansu suka dagokai, shigowa Dady yayi yana kallon waje yace “shigo Nafisa ki gaida iyayen ki” matsawa gefe Dady yayi ahankali ta shigo dakin batare data cire hills dinta ba, kallo daya tamusu ta sunnar dakai kasa ganin mutane cike adakin, tundaga kafa Aliyu yake kallonta har zuwa kai daidai da abu daya baigani tattare da itaba daya burgeshi, dauke kai yayi yacigaba dacin abincin shi Abdul na mintsilin shi tabaya amma yay kaman bayaji, tahowa Ammi da Momma sukayi ganin ta tsaya gefen Dady bata gaishe su ba bakuma takaraso ba yasa
Ammi tace “barka da zuwa Nafisa” dagokai tayi ta kalli Ammi da Momma murmushi tayi tace “ina yinin ku” duk murmushi suka mata sukace lafiya lau, dining Momma tanuna mata tace “kinzo adaidai muje dining kici abinci” da sauri Dady yace “No, fita zasuyi da Aliyu” ya kalli Aliyu dayay kaman baimasan da zuwan waniba yace “Gadanga na tashi kuje bukka ku zauna Ihsan zata taho muku da abin tabawa abaki” dago kai Aliyu yayi ya kalli Dady zaiyi magana Ammi ta girgiza mai kai wani irin nauyin Ammi yaji yamaida kanshi kasa, ahankali Ammi tace “taso kutafi kabarta atsaye Son” dan murmushi Nafisa tayi tadan dagokai ta saci kallon Aliyun dat she’s seeing for the first time da Hajar tasha bata labarin shi cewa Dady su yafison shi agidan, oh wow dama haka yake da kyau, kawar da tunanin tayi ganin yataso tai kaman bata kallonshi nanko tsaf take kallon komi nashi bamashi kadaiba “my God he’s so f*cking handsome, look at how tall he is, ohhh God, very very tall, My Gaint!” tafada aranta tana wani irin murna tanadan gyara tsayuwa tana addu’a Allah yasa yasota dan gayen yahadu to the extreme, yanda yake dan wawware kafa cikeda isa da izza yana tafiya ta kalla taji numfashinta na barazanan daukewa “my fevorite part, I think he has big machine gun, Ohh, wayyo Allah na kalli yanda yake tafiya fa, my Spartacus, My Gladiator, he’s so fking sexy and super hot, uuhuhu” duk ita kadai take zancen zucin nan tana kallonshi ta gefen ido harya karaso wajen, lumshe ido tayi while taking a deep breath, he smells damn gooood! Mai sifili hudu baimai biyu ba, “awesome perfume” tana jiran yamata magana yabi ta gefenta yay hanyar kofan fita, murmushi Dady yayi yace “bishi kuje Nafisa” gyadama Dady kai tayi tajuya ta kalli bayan Aliyun daidai yabude kofa yafita tabishi itama tasakai tafice tareda rufo musu kofa, hanyar bukkan Aliyu yayi, hadadden bukka ne dake compound din nasu akwai table sai kujeru masu kyau dasuka zagaye table din saikuma wani white flower verse da flowers jajaye ke tsakiya akan table din wurin so neat, irin wurin shakatawan nan na gidan yan gayu, zama yayi akan daya daga cikin kujerun, ahankali ta zauna kan kujeran dake facing dinshi wearing a smile tana kallonshi, ko 3sec basuyi da zama ba saiga Ihsan dauke da babban tray da kayan sha ke ciki sallama tayi sanan halin Ya Aliyu karya disgata, da hannu yamata alamu data shigo, shigowa tayi ahankali ta sauke tray kan table ta ciro drinks din ta ijiye musu sanan ta ijiye plate din dake dauke dasu samosa and spring rolls da Momma takawoma Ammi, ta ijiye dambun nama sanan ta dau tray ta kalli Ya Aliyu dake dan daddanna waya abinshi tace “intafi Ya Aliyu” gyadamata kai yayi tajuya tafice, kusan 15min suka bata sai kallonshi take shikuma Aliyu na taba waya abinshi dagokai yayi ahankali hada ido sukayi, da yatsa yanuna mata abubuwan dake gabansu yace “have something” murmushi tayi tace “sure” juice ta tsiyaya a glass cup din tana kallon Aliyu kaman yanda shima yake kallonta kallon dabazaka taba gane na miyeba cika glass cup din tayi da drink bama tasaniba tsabagen yanda take kallon Aliyun tacigaba da zubawa har juice din yafara zuba akasa yana gangarawa kasa wasu na zuba ajikinta, dan yatsine fuska yayi yay smirking yamata pointing glass cup din da yatsan shi} da sauri ta janye idanunta daga kanshi ta kalli gabanta da sauri ta daga juice din datake tsiyayawa a cup saura dan kadan aciki ta ijiye kan table din tamike da sauri kunya ya lullubeta looking at the mess datayi sabida kallon Aliyu yanzu yaganota, dan tsaki tayi tana kallon yanda lace dinta yajike da juice ta kasan riganta da skirt dinta tace “sht” tana yarfe hannu murmushi yayi daidai lokacin an bude gate din gidansu babban motan kai yara makaranta ne ya shigo juyar dakai yayi ya kalleta yanda take yarfe hannu dukya bata mata jiki ahankali yazaro white handkerchief daga aljihun shi yamika mata, bama ta lura dashiba sabida yanda take kallon skirt din, cikin husky voice dinshi yace “use this” da sauri ta kallai, ganin yana miko mata handkerchief dinshi yasa wani dadi yakasheta, ahankali tamika hanunta takama handkerchief din zata karba taji yarike baisakin mataba yana kallon fuskanta kaman yanda take kallon nashi, ahankali yace “ki rage kallon mutane okay” subhanallah wani irin kunya taji kaman zata nitse kasa, hayaniyan yara dayaji yasa ya sakin mata handkerchief din yajuya yana kallon yaran gidansu dasuke gudu kowa nayin hanyan shashin su itakuma Nafisa ta tsugunna tana goge kayanta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57Next page

Leave a Reply

Back to top button