A TSAKANKANIN SOYAYYA HAUSA NOVEL

A TSAKANKANIN SOYAYYA HAUSA NOVEL

Karasawa wajen motan tayi har direba yabude yaran duk sun shiga Hajar ne kadai agaban motan, wani matsiyacin kallo tama Aneesan tace “gasu agola nan anzo” daidai Aneesa takaraso wajen Rauda dake cikin motan dan ciwon cikin yasaketa sosai yanzu tace “kai Anty Hajar wlh babu kyau fa” ta kalli Aneesa datai kaman batajisu ba tasakin mata murmushi tace “shigo ki zauna Aneesa” murmushi itama tamata dan sai yanzu ne tagane Rauda itace yarinyan data taimaka ranan data fara ganin Aliyu sarkin kallo sai kallonta yake kaman baitaba ganintaba, shiga cikin motan tayi ta zauna kusada Rauda, Hajar ta shigo itama sanan direba yarufe kofan yakoma gaba ya shiga yaja.

Ahankali Rauda tasa hannunta takarbi hannun Aneesa data danyi wani zanen lalle ta around kumbunan ta tace “wow Aneesa wanan wani irin zanen lalle ne? Bbu kodaya a hannunki saita wurin yatsun ki it really looks nice, waya miki ya bala’in burgeni, waya miki?” murmushi Aneesa tayi tana kallon yatsun nata zanen datayi ne da bikin Ammi saitama Ammi kuma lalli mai kyau, ahankali tace “ninayi” “iyye kin iya lalle ne daman?” gyadamata kai tayi tace “na iya, kinaso namiki?” da sauri Rauda ta gyada mata kai tace “inaso mana, sosai ma” ahankali Aneesa tace “shikenan duk randa kika shirya zan miki wanda ma yafi wanan kyau” washe baki Rauda tayi tace “nagode, Awani aji aka saki dazu a hadda?” ahankali tace “aji hudu, islamiya ma aji hudu” bangaje mata kafada Rauda tayi cikeda jin dadi hira irin na kawayen nan tace “iyye ajinmu daya ashe, nima dazu dasafe cikina keta ciwo saisa banjeba wlh” ahankali Aneesa tace “sorry Allah ya sawake” cikeda damuwa Rauda tace “kema kinayin ciwon ciki idan zakiyi?” gyadamata kai Aneesa tayi batare datai magana ba she’s not just comfortable sabida Hajar dake wurin, dan tana ganin yanda Hajar ke hararanta itada Raudan kaman ta bubbuge su, cikeda damuwa itama Rauda tace “sannu kinji Aneesa, ance inkai aure yana denawa” “dalla malama kimana shiru ko kina maganan iskanci agaban yara” Hajar tafada cikeda masifa, cikin tsiwa Rauda tace “to wai me ruwanki dani Anty Hajar, yaran sunsam menake cewa ne, kinamin wani ihu saikace nayi dake” ta harari gefen side din Hajar din, murmushi Aneesa tayi hakan yakara harzuka Hajar tace “dan ubanki nikekema rashin kunya?” cikeda rashin kunya Rauda tace “karki kara zaginmin uba nidai, Dady na nagida yana hutawa abinshi kina duramai zagi, kuma ai badake nakeba daga ina firana da kawata saikiyi ta zagina, dakenayi? Neman tsokana kawai” kwashe wa da dariya yaran motan sukayi, wani mugun kallo Hajar tamusu hakan yasa at ukai shiru, Hajar tai kwafa tace “zamu koma gida kaman Mama taji komi” dauke kai Rauda tayi tacigaba da hira ta da Aneesa batakara cemata komiba harsuka kai makaranta suka tafi ajinsu a binsu.


Wuraren magrib suka shigo gidan, derevan su yay parking yafito tareda zagayowa yazo yabude musu, saukowa sukayi Rauda ta dubi Aneesa data sauko bayan ita tace “saida safe ki gaishemin da Mummy, gobe zanzo na gaisheta kinji, bari naje part din Ya Aliy….” fizgan hannunta Hajar tayi kaman tafizgo barauniya tace “dan ubanki bazaki ba, ba Mama tahanaki zuwa bangaren shiba” cikin tsananin jin haushi Rauda tace “wai me haka Anty Hajar, wlh kisakeni kona hadaki da Dady me ruwanki dani sai samin ido kike kina sauraron conversation dina” cikin fushi Hajar tadunkule hannu ta sakin mata mugun dundun abaya da har Aneesa saida tajishi har cikin ranta sabida karan dayayi dumm! wani irin ihu Rauda tasaki kaman zata fasa gidan tai kasa tana bankarewa daidai Aliyu ya shigo gidan daga masallaci, rike ciki Rauda tayi dan har cikinta taji dundun tasaki wani irin mugun kuka tana kama cikinta, kaman Aneesa zatai kuka ta kalli Hajar dake huci kaman wata kumurcewatu???? tace “me tamiki zaki mata wanan dukan bayan kinsan cikinta naciwo” da yatsa Hajar ta nunata tace “ke kalleni nan am 25 niba tsaran wasan ki bace, ba ruwanki idan nida kanwata na fada agol….” wani irin wawan mari da aka dauketa dashi yasa takasa karasa kalman dazata fadi tadago idanunta da sukai mata dishi dinshi tsabagen zafin marin tana sosa wurin ta kalli wanda ya mareta Aliyu ne yana sanye dawata white riga mai dark blue short hands sai dogon black jean dayasaka kamshin turaren shi yabi yacika wurin, hanunshi yadaura kan wandonshi yana kwanto belt dinshi dama bala’in haushin ta yakeji tun ture Aneesa datayi dazu tafadi, cikeda rashin kunya Hajar ta kallai tana ganin belt din dayake shirin kwancewa ita tafi karfin tagudu tace “wlh karma kasake kayi gigin ciro belt dinan kace zaka dakeni dashi agaban kannina kajamin raini agaban yaran da aka haifesu jiya, meruwana dakai nasan kane shiga shara ba shanu, wlh ka zaulamin belt dinan saina hadaka da Mama na tafito ta ramamin mugu kawai” wani irin zuciyane Aliyu yaji tarufe shi ya tsani rashin kunya, ahankali Aneesa ta saukar da kanta kasa jitake kaman tarufe Hajar da shegen duka yanda takema Aliyu rashin kunyan nan harda zagi.

Karan saukan belt da ihun Hajar dataji yasa ta dagokai, takoina Aliyu ke zubama Hajar duka kaman dama anbashi contract din dukanta ne, murmushi Rauda tayi tana share hawayen daya gama wanke mata fuska ganin Ya Aliyu na rama mata, ihu sosai Rauda take tana kiran maman su. “wayyo Allah na, Mama, Mama, Mama kinga Ya Aliyu ko, Mama zai kasheni” fara bude kofofi matayen Dady sukayi suna kallon yanda Aliyu ke kilan Hajar dake ihu da magriban nan, bude kofa Mama tayi jin ihu da hayaniya atsakar gida idanunta ne sukaci karo da Aliyu na dukan Hajar da belt gasu Rauda da sauran yaran gidan jikin mota suna kallo kaman suna kallon show, ga kishiyoyinta ko alamun kwatan Hajar bamasu yiba dan Hajar dama ta addabesu duka yarinyar badai rashin, da gudu ta shiga sauka daga matattakalar benen gaban flat dinta daidai Abba shima ya shigo gidan dan dama dawani ya tsaya magana awaje da tare zamasu shigo da Aliyun daga masallaci. “Gadanga” Dady yakira Aliyu adan zafafe dudda yasan Hajar tai wani abune saisa yake dukanta haka but he’s strongly against dukan y’ay’a mata baiso dan sunada rauni. “Aliyu” kiranshi da Dady yasake yi akaro na biyu yasa yawani irin hankade Hajar da hannu, Mama dake tahowa ta tareta da sauri tanabin jikin Hajar din da kallo tana dubawa yanda hannayenta da fuskanta yay rudu rudu, mayar da Hajar din gefe tayi ta ijiye ta jikinta har rawa yake ta zabura tatashi tayo kan Aliyu tace “billahillazi la’ilaha illahuwa bazan yarda ba, y’ata ce kama rudu rudu da jiki haka, wlh saina rama mata” tai kan Aliyun dake mata wani matsiyacin disgusting look jiranta kawai yake tazo tace zata tabashi, azafafe tayo kanshi Dady daya karaso wajen yace “wlh, wlh kika tabamin yarona banga abinda zai hanaki barin gidan nan da daddaren nanba, baki da hankali ko Kareema, kan Yaya yadaki kanwar shi shine zakice zaki rama agaban kaninshi? Bismillah tabashi, tabashi ki gani” yay maganan cikin tsananin fushi yana rungume hannu a kirji yana kallon Maman su Raudan data tsaya tana kallon Aliyun da mahaifin nashi ke tsaye kusada shi, cikin fushi yace “Aliyu yarone mai hakuri, ko kyaran kaninshi bayayi, bantaba ganin yadaga hannu yadaki wani a gidan nanba danyau yadaki Hajara aisai kinsan da dalili ko, Hajara yakamata kima fada baki taso kice zaki dakeshi ba, Gadanga nawa zaki dama agabana, gaban babanshi Kareema, bari kiji daki tabamin yaron nan gwara ni ki tabani sau dubu wlh zan iya yafemiki sau dubu amma duk wanda yatabamin yaron nan kowaye shi aduniyan nan, Kareema kowaye wlh sai inda karfina yakare kinji na rantse miki, wlh kikiyayeni, ki kiyaye ni Kareema, ko gigin wanan haukan karki karayi in your whole entire life” cikeda bala’i da bakin ciki Mama tana kallon yanda Dady kemata bambami tace “ninasan babu abinda Hajar tamai tsabagen tsana ce irin ta Aliyu meruwan Hajar dashi iyee, me Hajar zatamai” da sauri Rauda tace “Mama wlh Anty Hajar ne taketa ma Ya Aliyu rashin kunya agabanmu” da sauri Dady yace “to kindaiji ko da kunenki dan haka ku tattara kowacee ta tafi flat dinta” ya kalli Hajar dake kuka har lokacin jikinta narawa yace “gobe ki kara mara kunya fitsararra, tausayi kikabani danazo nakara miki wani sabon dukan wlh, Aliyu tsaran wasanki ne, ko kallon banza naji kin karamai sainai mummunan sabamiki da idanu kaman na mujiya tashi ki wuce daki kiyi wanka kici abinci” juyawa Mama tayi ta kalli Rauda ta nunata da yatsa tace “badaike shaidaniya bace wlh bani bake Rauda, zanyi maganin ki, badai kinkini uwarki da yar uwarki ba zaki sanine, wlh bani bak….” cikin tsananin fushi Dady yace “waike kin fara zarewa ne Kareema? Me kikecema karaman yarinya bakiba ita iyyee? Mekike nufi? Zan mummunan sabamiki fa inbakibi ahankali ba” juyawa Mama tayi takama Hajar da dagata daga kasa tace “tashi muje, Allah zai sakamiki, wlh saina rama miki wanan alkawari namiki, kuma magulmata yan bakin ciki sai akoma daki masu daukan rahoto, ba kisankai akayiba ai” tai maganan tana kallon matayen Dady, tsaki Amarya tayi tace “aikin banza harara aduhu, gwara da aka lallasatan” da hannu takira yaranta dake gaban mota tace “let’s go kids acire kayan makaranta” da sauri sukazo suka shiga daki, dayan matar Dady takira nata yayan ta harari Mama tace “rahoto kam yadauku saura bugawa ajarida ko yarana” tai maganan tanajan kumatun yaran cikeda wasa aiko suka fashe da dariya sukai daki tarufo kofar flat dinsu da karfi, kwafa Mama tayi tace “duk zanyi maganin kune kunyi dani, yar halak ce kumani, muje Hajar” taja Hajar sukai part dinta suka bude kofa suka shige.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57Next page

Leave a Reply

Back to top button