A TSAKANKANIN SOYAYYA HAUSA NOVEL

A TSAKANKANIN SOYAYYA HAUSA NOVEL

Addu’o’i Ammi takaranto aranta danji tayi tamafi Aneesan shiga damuwa, yanzu idan wani abu yasame ta ubanme zata fadama yan uwan babanta da dama jira suke batayi bama sunce tayi balle kuma tayin, ajiyan zuciya ta sauke ahankali ta kirata. “Aneesa” ahankali tace “uhm” “stop crying, kinsan sunan anguwan dakike?” girgixa mata kai tayi tace “a’a bansani ba” “kina inane yanzu haka?” cikin crying voice tace “ina lungun motocin da akai parking a anguwan kaman na yan biki ne” “okay, fito to duk wani wanda kika gani kibashi wayan nai magana dashi naji a anguwan dakike, a ina kika sami katin waya haka naga bai kareba har yanzu?” cikin kuka tace “amaryan ta turamin dazu” “okay tashi duk wanda kikagani kibashi wayan to” tashi tayi ahankali tana goge hawayen daya gama batamata fuska tafito daga lungun motar ta tsaya abakin hanyan tana kalle kalle babu kowa sai security dake bakin Gate har lokacin saikuma tulin uban motocin yan biki kowa na ciki kida na tashi da alamun event din ya kankama ne, ganin ba kowa yasa taji wani kukan yazo mata tsugunnawa tayi a wurin wayar na kunenta tarufe fuskarta da hijabi tana kuka sosai, a rude Ammi tace “menene bakiga kowa bane? Stop crying mana kina dagamin hankali wlh” gyadamata kai tayi cikin kuka tace “Ammi babu kowa” tasake fashewa da kuka hankalinta yatashi ainun bamatasan mezatayi ba, batasaba yin dare hakaba a ko ina, dama ace Suleja ne tasan ko ina dakoda kafane saita dandaro, koma bahaka ba anyhow anyhow she wi definitely find her way back home, but nan babu inda tasani, batasan cikin Abuja ba batasan ko inaba, Brain dinta yagama chuchewa. “Hi Fearless lady” wani sassanyar murya, very cool, calm yet husky murya yadaki dodon kunnuwanta, Ammi dahar lokacim take kan waya tace “naji muryan wani bashi, bashi wayan namai magana da sauri” dago kai tayi ahankali tasa hijabinta tana goge fuskarta dayan hanunta kuma tamikama mutumin da bama ta kallaba wayarta da mistakenly hanunta ya danna speaker. “Bawan Allah dan girman Allah help my daughter, batasan ko ina a Abuja ba, wanda yakamata yadawo da ita kuma yatafi, please ka taimaken badan niba dan Allah kasata ahanya, koka kaita bakin titi koka sata a hanyar dazai sadata da main road tanemi motar dazai kawota Suleja, please help a mother, am so worried, dan girman Allah help my daughter, kasamin ita a hanya dan Allah tadawo gida kar y’ata tabata kaji bawan Allah” yanda taji Ammi narokan mutum itama kanajin muryanta kasan tana cikin tsananin damuwa yasa taji wani sabon kukan yazo mata kaman wacce akama mutuwa tacigaba da kuka kaman tata takare aduniya da karfi, jin kukanta yasa Ammi tace “hello Aneesa me kuma kike kuka eh, karki damu dazaran kin fita titi zaki sami motan Suleja, inma baki samuba nima zan taho na dauke ki dakaina, bari na nemo yaron Hadiza mai keke napep na makotan mu, dena kuka babu abinda zai sameki okay kinajina, stop crying Aneesa, stop” Ammi tafada cikeda lallashi cikin kuma tsananin damuwa, gyada kai tayi tana shashshare fuskar da Hijabi tana kokarin hana kanta kukan, katse wayan yay ahankali yana kallon yanda take share fuska da Hijabi, ahankali yakai hanunshi yadaura kan hanunta dake saman kan fuskarta wani irin sanyi taji tundaga kan feet dinta har zuwa kwakwalwanta, ahankali yakama hanunta gam wani irin hannu mai taushi taji dakeda sanyi sosai, ahankali tadago kanta in a very slow and steady motion, hada ido sukayi da Aliyun dake sanye cikin wani fitinannen white magic gizna dake wani mahaukacin kyalli anmai aikin hannu a kayan, yana wani irin cool kamshi dakesa kaji zuciyarka ta natsu, da sauri ta lumshe ido dan her eyes couldn’t stand haske da haiban dake tattare dashi takai almost one minute ahaka ita bata karbe hanunta ba ita batai motsi ba ita bata bude idoba shima kuma haka, hanunta dataji yaja ahankali yafara tafiya da sauri tabude idanunta, samun kanta tayi da daga kafa tana binshi gaban wani Brabus jeep dat is directly opposite to lungun motar datake tsugunne tun dazu yakai ta yabude gaban motan zai sata ciki tsayawa tayi chak tafashe da kuka sosai ta fizge hanunta tace “ina zaka kaini niban sanka ba?” shiru yayi yana kallon fuskarta kaman yasami tv batare dayace komiba itakuma sai kukan takeyi takasa kuma matsawa konan dachan sanan kuma taki shiga sunkai almost 5 minutes ahaka wayarta dake hanunshi har lokacin ne tahau kara da sauri ta kalli wayan, janye idanunshi yayi daga kanta ya kalli screen din wayar ganin sunan kan screen din Ammi yasa ya kalleta ahankali yace “get in” yanda yamata maganan ba wasa sanan kuma ba tausayi yasa tasami kanta ta daga kafa tazo har gabanshi inda yake tsaye rike da marfin motan tana share hawaye tai bismillah ta shiga cikin motan, hijabin ta data saki yafito daga motan ya kalla ahankali yatako ya tsugunna da sauri ta juyo ta kallai hada ido sukayi yana wani irin kallonta, sosai gabanta ke faduwa kaman zai fito gashi takasa janye idanunta daga kanshi kaman eyes dinshi are compelling her to look at him by fire by force, ahankali yake tattaro hijabin batare daya dena kallonta ba tattarawa yayi ya dunkule yadaura asaman kan cinyarta, da sauri ta kalli kan cinyar nata jin hanunshi akai hijabinta tagani ya tattaro ya ijiye mata mikewa tsaye yayi yamaida kofan yarufe ahankali sanan yazaga yana tafiyan nan kaman baiso yayi yabude dayan side din ya shiga tareda rufo kofar yaja sit belt dinshi yana sawa batare daya kalleta ba yace “fasten your sit belt” juyawa tayi tanajan igiyan sit belt din da karfi amma yamaki fitowa sai fama take hakan yasa ya juyo ya kalleta ganin yanda take fama da sit belt din yasa yacire nashi yataso daga kan kujeran shi ya matso da kanshi ta gabanta wani irin sakin sit belt din tayi da gudu ta makale jikin kujeran, yanda takejin kamshin turaren akan fuskarta yasa numfashin ta yafara fita da sauri da sauri kaman zata kurma ihu, hanunshi yadaura kan sit belt din yaja ahankali yana wani irin kallon fuskarta shi kanshi baisan mesa yake kallonta hakaba and anytime ya kalleta the beating of his heart use to change. “m….me ha..k…haka?” Aneesa tai maganan muryanta na breaking sosai, makala sit belt din yayi yakoma inda yake tareda sauke ajiyan zuciya he’s not just himself da sauri ya kunna motar yay reverse yaja yafara gudu, ringing da wayar Aneesa yafara yasa ya kalli wayar ganin Ammi ne ya mikamata wayan yace “answer d call, tell her you are on your way”.

anan nakawo karshen free pages. Duk wacce takaran tamin littafin batare data biya dari uku ba nabarta da Allah ban yafe mataba duniya walahira

duk maison cigaba da karanta littafin ATSAKANIN SOYAYYA zata tura naira dari uku kacal ta account number na 3107021073 aisha Muhammad first bank, saiki turo evidence of payment ta watsapp number na 07012181461, saina saka ki a group din danake posting

wayanda tun kafin ma nakawo karshen free pages suka biya nagode Allah barmin ku, trust me zakusha dadi a book dinga, M Shakur mai sabon salo ce kuma kunsani Always!!!

ku tuntubeni kan wata magana ko business ta nan 07012181461
[4/5, 8:09 AM] Hijabi_muslimah????: [18/02, 18:01] Aishat Muhammad: A TSAKANKANIN SOYAYYA

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57Next page

Leave a Reply

Back to top button