A TSAKANKANIN SOYAYYA HAUSA NOVEL

A TSAKANKANIN SOYAYYA HAUSA NOVEL

Dad ya juyo ya kalli Aliyu da duk yay wani iri ji Dady yayi kaman ya kurma ihu, hanunshi yakara kamawa yana kallo cikin dan fushi yace “why will you fight him eh? You would have called me danai contacting police headquarter na Sulejan koda i can come on time da nasa a tura police akamashi adaure shi, why will you fight him eh Aliyu?” Dady yay maganan abin namai masifan ciwo dan yasan waye d’an shi, ganin yanda Dady yayi yasa ya fizge hanunshi yana yatsine fuska yace “am fine Daddd, okay, am fine, bari naje nai wanka” yay hanyar shashin shi Dady yabi bayanshi da kallo cikeda tausayin Aliyun for the first time yau yaga jarumta a idanun Aliyu yasan hanun nan namai zafi amma yaki nunamai hakan saidai yace he’s okay he’s fine, dan murmushi yayi yace “Allah rayamin kai Aliyu na” yay kwafa yy hanyar shashin shi shiko Khamis mai rabashi dashi yau sai Allah dan wlh yay kuskuren taba Aliyu daya sani dashi yazo yataba fess zai iya yafemai amma Aliyu ko wlh saiya ramama marayan yaron shi yasakeyin kwafa ya shiga ciki.

Bedroom dinshi dake hadadden kamshi ya shiga ko ina a gyare dan cleaner shi yazo ya gyara, maida kofan da sauri yayi yarufe harda murza key dan yasan Dady zai iya biyo bayanshi hanunshi dakemai masifan ciwo ya shiga yarfewa kaman zaiyi kuka in fact duka hannayen ma kemai ciwo baitaba wani punching punching da mutum ba in his life, shi yanama shiga mutane ne balle har wani abu physical fight dazaisa yay exchanging punch da wasu yahada shi, cijan lips dinshi yayi ya shiga cire kayan jikinshi yabarsu anan kasa ya tsallekesu yay bathroom wanka yayi da ruwa mai zafi sosai yafito sanye da bathrobe akan gadonshi ya zauna kafin yawani irin fada kan gadon yana sakin ajiyan zuciya, lumshe ido yayi yana kara lumewa cikin lallausan katifar shi while relaxing all his nerves and body. “wai in tambayeka mana do you know who is a man? A man baya tsayawa physical fight da kowa dan physical fight downgrade one’s level, banda haka a man is someone who has control over his heart ayayin dayake cikin fushi which is abinda yayi yanzu” wani irin murmushi daya bayyana all his 32 teeth out Aliyu yayi. “kazaci kana ihu kana cika kana batsewa by the time dayake so yaci ubanka you can match his level ne eh? murmushi yasakeyi idanunshi a lumshe yaja filo daya ya rungume tight kaman zai fasa filon murya chan kasa yace “who is this Fearless Lady? Who are you Boldest?” “Aliyu, Aliyu, Gadanga” kaman daga sama yaji ana tapping nashi ana kiran sunanshi bude ido yayi da sauri abu yaji ya shigan mai ido hakan yasa yamaida idon yarufe da sauri, Dady dake tsaye a kanshi yasa hannu yana kakkabe feather filon yace “sai murje filo haka filo harya fashe bakada lafiya ne, cikin ka naciwo ne, tundazu nazo ina kiranka baka amsaba saida nadauko spare key nabude na shigo, bude idananun to na kakkabe maka” ahankali yabude idanun yanabin gadon da kallo yanda yafasa filon da abubuwan shi duk suka zuba akan gado, hanunshi Dady ya kama yace “stand up, stand up” tashi yayi daga kan gadon Dady yabude muscle and tissue pain killer balm din daya shigo dashi ya lakato yakamo hanun Aliyun zai shafa kaman Aliyu zaiyi kuka yace “Dadddd” “kai kamin shiru anan” ashagwabe yace “Dad but this balm is smoky hot, too peprish natuna shi idan naji ciwo da ina yaro shikake samin, ni gaskiya karka samin am fine” rike hanunshi dayake shirin fizgewa Dady yay kyau yace “idan nasa ka goge stubborn boy, give me the other hand jor nagani” ya saki hanun daya shafamawa zai karbi right hand din yashafa, turamai baki Aliyu yayi yamika mai karba Dady yayi yace “and on Monday zakai resuming office and take up your responsibility am I clear” “uhmm” yafada ahankali, sakin hanun Dad yayi yace “jeke saka kaya to yaron Dadyn shi” Dady yay maganan yana murmushi hanyar wardrobe dinshi yayi shikuma Dad Yajuya yafita daga dakin.

Suleja
Motar datagani Honda pake kofar gidansu yasa taji gabanta yafadi ahankali tafito daga keke napep din taciro kudinshi naira dari tamikamai karban kudinshi yayi yaja keken yay gaba, ahankali take daga kafafun ta tana kara kakkabe hijabin dayay butu butu da kasa ta shiga gidan da sallaman ta, ahankali tana kallon tsakar gidansu da aka shimfida babban tabarma wasu maza magidanta guda biyu zaune kan tabarman duk sun kafeta da ido saikuma Ammi datagani zaune kan yar kujeran tsakar gidan abakin kofar dakinsu idanunta sundanyi ja sosai kaman wacce taci kuka tagodema Allah, ganin yanda Aneesan ta tsaya chak ita bata gaidasuba ita bata karaso cikin gidaba yasa Ammi tace “bazaki shigo ki gaida Baffofin kiba kin tsayawa mutane aka kina kallon mu kaman kinga dodanni” dan murmushi tayi akunyace dan yanda taga idanun Ammi yasa ta manta da kowama dake tsakar gida kanta akasa ta shigo har cikin tsakar gidan gaban tabarman su ta tsugunna tana wasa da bakin hijabin ta ahankali tace “ina kwana Baffa, ina kwana Kawu” mutanen duk kamaninsu daya saidai kana ganinsu zaka gane wa da kani ne daya yafi daya manyanta babban cikin ne wanda suke kira da Baffa wanda tunda ya shigo yake kallonta ahankali yadaura hanunshi saman kanta yana kallon fuskanta yace “Fatima, zauna dakyau” yay maganan yana kallon yanda ta tsugunna sabida karta gaji, gyara zama tayi ta zauna kan tabarman inda yake nunamata da kyau tana gyaggyara hijabi ganin ta natsu yasa yace “tuntuni mukazo mahaifiyar ki tacemana kinje kasuwa mun tsaya mugakine kafin mukoma kadunan, ya kike Fatima?” kanta akasa tace “Alhamdulillah Baffa ina lafiya” kunyanshi takeji sosai bana wasaba, murmushi yayi ya gyadamata kai yace “Allah yamiki albarka kinji ko,” gyadamai kai tayi tace “Ameen Baffa, nagode” gyadamata kai yayi shima yace “ki kula da kanki kinji, ki tsare mutuncin ki, ga mahaifiyar ki nan kidinga mata biyayya kinji, in sha Allah zan kokarta nadinga zuwa akai akai ina dubaki ko dayake mun riga mun gama wanan maganar da mahaifiyar ki” dayan magidancin ya kalla yace “mikomin wanan jakan Sani” yar babban jakan dake kusa dashi magidancin yadauka yamikamai karban jakan yayi yabude ciki kwalin waya na Tecno pop2 yaciro yamika mata yace “ga wayanan nakawo miki kome kike bukata ki kirani kinfadamin kinji koda bandashi duk randa Allah ya horemin zanyi miki, sanan ga wanan” yasaka hannu a aljihun riganshi yaciro kudi yan dubu daidai har na dubu bakwai ya mikamata, ahankali tasa hannu ta karba yace “naji amfara registration din jamb kije kibiya muga ya Allah zaiyi kafin nan dawani tsayayye yafito mu aurar dake, kije kibiya cikin satinan dan naji ance idan kabiya dawuri ana turaka center a garinku ko Sani?” gyadamai kanin nashi yayi yace “eh hakane Yaya” kallonta yayi yace “masha Allah kije kiyi kinji, gakuma wanan” ya kara mata dubu uku yace “ki ajiye kidinga kashewa ahankali ahankali kinji Fateema, Allah yamika albarka, Allah yamiki albarka, dawata matsalan?” girgizamai kai tayi ahankali tace “babu Baffa, nagode Allah saka da alkahairi, Allah amfana” murmushi yayi sosai yace “bakomi kidena min godiya Fatima ni mahaifinkine so kidenamin godiya kinji, zamu tafi yanzu kome kikeso ki kirani kifadamin ga wayanki nan” ya kalli Sani yace “tashi mutafi Sani” mikewa duk sukayi Sani yasa hannu a aljihu, dubu biyu yaciro yamikama Aneesan yace “ga wanan ki kara kan wanda Yaya yabaki, ki kula da kanki kinji” akunyace ta karba tace “Allah amfana Kawu” wajen Ammi data zauna tana kallon su tayi tace “Ammi kinga abinda su Baffa suka kawomin” murmushi Ammi tace “akashe lafiya, jeki ajiye a daki kizo kirakasu” daki ta shiga Ammi ta dubesu kaman yanda suke kallonta suma tace “angode Alhaji, kuma kuyakuri idan abinda nace yamuku zafi yabata muku rai, Allah ya kiyaye hanya sanan agaida mutanen gida, mungode” tana maganan tabude kofa ta shiga daki, girgiza kai Baffan yayi yadubi Sani yace “muje Sani” sukai zaure, a falo Aneesa tahadu da Ammi tace “Ammi muje rakiyan ganinan na ijiye kayan a dakina” girgiza matakai Ammi tayi tace “yi maza kidawo ni ina nan” tsayawa tayi turus tana kallon Ammi ganin duk tayi wani iri, murmushin yake Ammi tamata tace “yi sauri mana kin tsaya kina kallona suna jiranki awaje” fita daga dakin tayi tai waje duk suna tsaye jikin mota murmushi tamusu takaraso tace “Allah ya kiyaye hanya, Allah yakaiku lafiya Baffa agaida kowa” gyadamata kai sukayi atare sukace Ameen, Baffa yace “wuce kikoma cikin gida, Allah miki albarka” Ameen tace tawuce ciki kaman yanda ya umurceta yayinda suka shige mota Sani ke tuki sukabar anguwan.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57Next page

Leave a Reply

Back to top button