A TSAKANKANIN SOYAYYA HAUSA NOVEL

A TSAKANKANIN SOYAYYA HAUSA NOVEL

Ahankali yabude door din part dinshi babu kowa a falon sai manyan jakunkunan kwali da aka rubuta Men by Robanni wears ajiki hakan yasa yagane kayan bikin dazasu sakan gobene Abdul ya karbo musu din, hanyar bedroom dinshi yayi, bude kofa yayi ya shiga babu kowa adakin sai car keys da waya dake kan gado karan ruwan dayaji yasa yagane yana bathroom, dan ajiyan zuciya ya sauke ya zare jallabiyan jikinshi yay hanging a hanger yasaka a wardrobe sanan yazo yafada kan gado.

Bude kofan bathroom da akayi yasa yadago kanshi wani guy ne kusan kansu daya da Aliyun saidai Aliyu yadan fishi dan kaurin jiki dakuma haske dan Aliyu farin sosai Abdul ma farine but baikai Aliyu haske ba, fitowa Abdul yayi daure da towel a waist harara yana rike da karami a hannu dayake goge gashin kanshi dashi yazubama Aliyun dayay lamo akan gado yana kallonshi yace “dan iska kafin laifi kawani kwanta forming innocent right, kama ta shine malam” yay gaban mirror yana tsane jikin da towel kafin yaje gaban wardrobe din Aliyu yabude yadauko daya daga cikin pyjamas dinshi milk color yasaka sanan ya shiga bayi yaje yay hanging towel din back sanan yafito yay kan gadon ganin zai fado kanshi yasa Aliyu yatashi da sauri yanadan dariyan shakiyanci yace “leave me alone jor, karka karyani, shine kazo koka kirani” wayarshi dake kan gadon yadauka yace “I know kana mosque saisa I didn’t call, wait before anything am hungry” hararan shi Aliyu yayi yatashi daga kan gadon yace “chop chop, Dady zai aiko mana da abinci, let’s go, muje falo” tashi Abdul yayi yabi bayanshi suka fita falon daidai lokacin akai knocking kofa, Abdul ne ya amsa shikuma Aliyu yafada kan kujera. “yes come in” bude kofa akayi bodyguard su biyu na Aliyu suka shigo dakin daya dauke da manyan warmers guda biyu sai dayan kuma dauke da tray da slice fruits a bowls kekai, dining Aliyu ya nuna musu suka kai abincin wajen sanan suka juya suka fita, hanyar dining din Abdul yayi yazauna yana bubbude warmers din yana kallon abincin dake ciki kafin yadau plate da spoon ya debi ofada rice da smoke fish stew ya ijiye a gabanshi, wani bowl yasake dauka yadau spoon yacika bowl din da fried pepper chicken sanan yadaga kai ya kalli Aliyu dahar ya kwanta akan kujera yana daddana remote yana lumlumshe ido yace “let’s eat Leo” yatsine fuska yayi yace “me aka dafa? Me acikin warmers din?” hararan shi Abdul yayi yafara cin abincin shi batare daya kulashi ba dan yaga iskanci Aliyu keji shikuma right now he’s starving bari yabama cikinshi hakkinshi tukunna yanda Abdul kecin abincin was tempting his taste bud ahankali yatashi daga kan kujeran ya mike tsaye, dariya Abdul yafashe dashi ganin yatashi, karasowa dining din yayi yaja daya daga cikin kujerun dining din na kusada Abdul din dakemai dariya ya zauna fizge spoon din hanun Abdul din yayi yaja plate din rice din ya shiga ci, dariya Abdul ya shiga yi yace “nadaiji shege waya gayama anama abinci yanga” yay maganan yana daukan wani spoon suka shiga ci tare, he hardly eat much but because yanaci tareda wani sosai yaci abincin har Abdul na karamusu sukaci, baiwani ci pepper chicken din sosai ba yazuba juice ya kwankwada shikuma Abdul yaci tass, saida suka gama yace “this fruit kasasu a fridge Leo ni banda inda zasu shiga acikina while I clear the dining” gyadamai kai yayi yatashi ya dai bowls din yakai fridge shikuma Abdul ya kwashi plate yakai kitchen.

Gamawa sukayi sukai falo Abdul yadau jakunkunan kayan su yace “kaga kayanmu gobe zamu fita dawuri fa, mune abokan ango” tabe baki yayi yadan shafa kai yace “am sleepy sosai bangane mekake cewa, let’s go to bed” waya Abdul yadauka yana gyara kwanciya kan kujera yace “kai kaje ni waya zanyi da” ya kashemai ido, tsaki Aliyu yayi yay hanyar bedroom yace “dan iska aikin kenan soyayya” daga murya Abdul yayi yace “bari kafara naka bazaka bari muhuta ba, kardai kazo kana mana kuka idan tace bata sonka” daga murya yayi daga bedroom yace “never” shima daga murya Abdul yayi daga falo yace “is a bet” tsaki Aliyu yaja yana cire rigan jikinshi yace “rubbish, why will I ever cry over soyayya? Allah kyauta” yatabe baki ya shiga bathroom yana tafiya da kyar so yake yay wanka yazo yay bacci.
Asuba tagari!!!!

Suleja
Shigowa dakin tayi tana gyara tsintsiyan laushin dake hanunta tana satan kallon Ammi, harara Ammi ta watsa mata tace “wai lafiya kike kallona haka?” dakin Ammi ta shiga da sauri ta ijiye tsintsiyan tafara gyara gadon saida tagama tsaf sanan ta sharo dakin tafito da sharan ta shiga dakinta ta sharoshi shima sanan tafara sharan falon Ammi sai hararanta take dan tai mata laifi tunda tai sabon wayan nan da Baffa yakawo mata take uban danne danne awayan data rasa nameme, tarasa uban me take dannawa awayan dababu komi aciki, dasafen nan ma daga ta dumama abincin kari saida taji kauri koda tafito taje kitchen abincin ya kone ga Aneesa agefe agaban murhun kan kujera tana daddanna waya bamata saniba tsabagen nisan datayi shine ta zuba mata dunddu ta karbe wayan har yanzu bata bataba saisa taketa satan kallonta tanaso ta roketa tabata amma bataga fuskar hakanba, karasa share falon tayi ta fitar da sharan tsakar gida sanan tawuce kitchen ta debo rushi ta dawo falon ta zuba turaren wuta ta shigar dasu dakunan kafin tafito da turaren wutan ta ijiye a tsakar falon tawuce tafita tsakar gidan, tsintsiyan kwakwa tadauka tana gyarawa ta shiga share tsakar gidan tana tafiya zaure dasu bude kofar gidansu da akayi yasa ta dago daga sharan da sauri wata farar yarinya ce doguwa tadan yafa dan ficicin gyale ta shigo tsayawa Aneesa tayi turus tana kallonta murmushi yarinyar tayi tace “yakuri hala na tsorataki dan Allah tambaya nake wlh tun safe muke garari a Suleja nan mun kasa gane gidan dan Allah nanne gidansu Aneesa mai lalle?” jin gidansu ake nema yasa ta gyadamata kai tana murmushi tace “nanne” wani irin ajiyan zuciya yarinyar ta sauke tana shafa kirjinta tace “Wai Alhamdulillah laaaa koma kece Aneesa mai lallen?” dan murmushi tamata tace “eh, nice” da sauri yarinyar tabude kofar gidan wani babban motane pake a kofar gidan nasu ihu tayi dagangan zauren tace “Anty nanne gidan, gama Aneesa mai lallen nan” bude kofar bayan motan akayi wata budurwa fara itama wacce tafi ta zauren tsawo da dan kiba tafito kana ganinsu kasan Ya da kanwa ne tana rike da wani hadadden designers bag na Charles and Keith da sallama ta shigo zaure. “Assalamu Alaykum” daga kai Aneesa tayi tace “wa alaykumus salam, ina kwana” tagaidata ganin babba ce, murmushi budurwan tayi tace “lafiya lau Aneesa, ashe kece mai lallen kinga wuyan damukasha kafin mugano gidanku kuwa” dan murmushi Aneesa tayi dake karama fuskanta wani irin siriintaccen kyau tace “lalle kukazo ne?” atare ya da kanwar sukace “eh lalle mukazo” “to kushigo, bari na shimfida muku tabarma ku zauna saina hada lallen mufara” da sauri yayar tace “a’a munzo daukan kine home service mukeso bamu kadai zamuyiba duk yan uwanmu na gida, tundaga Abuja aka mana kwatancen gidanku akace mana u are one of the best masuyin lalle in the whole Abuja, please home service mukeso yau za’a fara events din bikina wushe wushe za’ayi da daddare shine zakimana lalle” dan zaro ido tayi ganin yanda macen ke magana ayangance zaka gane irin yaran manyan nanne yan gayu, wasa da yatsan ta tashiga yi tace “banayin home service kuyakuri duk maison lalle a gida nakemai” daga yar har kanwar yisukayi kaman zasuyi mata kuka ahankali yayar tace “dan Allah Aneesa karkimin haka kekadai ne hope dina yau dinan am so stress out, bansan kan Abuja sosai ba hutu school kawai kedawo dani daga abroad saikuma wanan bikin nawa da za’ayi, ta ina zan nemo wata me lalle dazata bini gida tamana, dan Allah Aneesa mai lalli help me kinji sister” sosai tabama Aneesa tausayi kana ganinta kasan tagaji kam ahankali tace “to shikenan amma kuzo kufadama Ammi na, inta yarda saina biku” da sauri amaryan tace “to muje” ajiye tsintsiyan Aneesa tayi tana gyara hulan kanta dafa yau taso tai tsifa taje kitso dan gashin kanta ya tsufa amma kuma gamasu lalle sunzo, bude labulen falonsu tayi ta shiga falon da sallama suna biye da ita har gaban Ammi taje tace “Ammi gabaki nan sunce nabisu wai namusu lalle home service nace ni bana zuwa home service sunce dan Allah shine nace bari na kawo su wurinki” zama take shirin yi kusada Ammi tace “wuce kije ki karasa sharan ki” gyadamata kai tayi tafice daga dakin Ammi ta dubesu atare dukansu sukace “ina kwana Mama” cike da fara’a Ammi tace “lpy lau sannunku da zuwa” cikeda girmama amaryan tace “dan Allah Mama so muke Aneesa tabimu tamana nida dangina lalle dan Allah Mama, wlh bansan kowaba garin nan, da kyar nagane gidan nan shima kwatance aka mana yau za’a fara event din bikina wanda zan aura yau zai iso daga Chad shine za’a mai tabar damuke cema wushe wushe, dan Allah Mama kitaimaka mana” dan murmushi Ammi tayi tace “Allah ya sanya alheri yabada zaman lafiya” dan murmushi matan tayi tace “Ameen, nagode Mama” murmushi Ammi tayi tace “a gaskiya bana barin Aneesa zuwa home service lalle duk wacce keson lalli har gida ake zuwa tamusu anan agabana, sonake kome takeyi idanuna akanta tarbiyan ya mace saika saka ido sosai sanan ka kula ita kadai gareni, banso nacemiki a’a dan kallo daya namiki nagane you are so stress out, nayaba da hankalin ki ainun, zata biku amma da sharadi zaku dawomin da ita dan Aneesa batasan cikin Abuja ba, rayuwan ta komi anan Sulejan mune kin yarda?” da sauri Amaryan dawani murmushin annuri ya lullube mata fuska jin Ammi ta yarda tace “Mama namiki alkwari zansaka driver gidanmu yadawo da ita da acema lokacin am free dana dawo da ita da kaina kodan karamcin da kikamini amma zansa Baba lado driver yadawo da ita har gida namiki alkwari dama shiya kawomu yanama waje, I promise” murmushi Ammi tayi tace “shikenan karfe nawa za’a gama lallen?” dan tunani amaryan tayi kafin tace “gaskiya bansani ba Mama nida yan uwanmu ne sai kawayena guda biyu da basuma riga sun isoba dan ba’a garin nan sukeba amma dazaran tagama bazan bari ta bata lokaci ba zansa adawo da ita” murmushi Ammi tasake yi tace “shikenan nabaki amanan ta, please kisa mata ido karki bari tabar sight dinki, Aneesa wani zubin batada kai akwai neman fitina, please ku samata ido kunji” atare sukace “to Mama” duk suna murmushi ganin yanda matar keji da yarta, kwalama Aneesan kira Ammi tayi. “Aneesah” shigowa dakin tayi da saurinta duk suka bita da kallo Ammi tace “jeki shirya ki cire kayan nan, fara tattaro kayan lallen dakika siyo a kasuwa jiya kisaka ajaka saikije ki chanza kaya kizo kutafi” washe ma Ammi baki tayi tajuya da sauri tanajin dadi hakanan taji tanaso tabisu itama kodan taga family wayan nan kyawawan yan gayun yan matan kaman ma buzaye ne su, lallen ta tattaro dasu ledoji da sajen ta hada ajakanta da handglove tafito tabama Ammi, jakan Ammi takarba tana kara dubawa to make sure ta kwashi komi dan wani zubin Aneesa ta iya annoying mantuwa dazakaji kaman ka maketa itakuma ta wuce daki dan shiryawa, wani black fited gown tasaka mai kyau dan har jerin stones gareshi ta wuyan sanan tadauko wani ironed baby pink hijabinta mai hula ta zura ta zauna abakin gado tasaka safa akafa kafin ta tashi taje gaban madubin tadau kawalli ta zizara sanan tadau man baki ta shafa dayay kaman ta saka janbaki, ba karamin kyau tayiba wani irin asirtattcen kyau da only the seer kan see karamin jakanta ta rataya tafito falon hakan yasa yan mata suka mike, karasawa tayi gaban Ammi kaman zatai kuka tana kallon fuskarta, kwafa Ammi tayi tadau wayar daga gefenta tamika mata, wani irin murmushi tayi ta fada jikin Ammi tsabagen dadi tace “thank you Ammi na, bazan kara kona abinci ba kinji” gyadamata kai Ammi tayi tana tabe baki tace “common tashi kutafi kidenamin wani dadin baki, saikin dawo, ga jakan lallen” ta mika mata jakan lallen, karba tayi tace “bye bye Ammi na, kimana abinci mai dadi” yanda tai maganan yasa yan matan suka fashe da dariya, Ammi tace “aikin kenan acici kawai” murmushi tayi tareda rufe fuskarta da hijabi tawuce tafita daga dakin yan matan sukace “sai anjima Mama mun gode” “saikun dawo Allah sanya alheri” Ammi ta fada tana daga musu hannu fita sukayi daga dakin Aneesa na gaba har zuwa waje sukai wurin motar, baya amaryan tabude mata tace “shiga” shiga tayi ahankali amaryan ma ta shige, kanwar kuma ta shiga gaba suka rurrufe kofofin motar Baba lado yatada motar yaja tareda bata wuta, duk shiru sukayi sun ciciro manyan wayoyin su suna latse latse hakan yasa Aneesa tai wani murmushi irin nima inada soft touch dinan, bude jakarta tayi taciro tata tafara dannawa saikuma ta dago kai tana kallon abinda amaryan keyi awayanta ganin WhatsApp takeyi yasa takasa hakura dan matsowa kusada ita tayi tamika mata wayanta tace “Anty wai yaya ake WhatsApp dinan kinga wayata jiya Baffa na yakawomin inaso nai WhatsApp amma bansan wazai samin ba” murmushi amaryan tayi ta karbi yar tecno tana kallo tace “aiko wayan nada kyau” wani irin murmushi Aneesa tayi tace “nagode Anty, nima inason wayan wlh bansan haka touching screen keda dadi ba saida Baffa na yakawomin ita, jiyan nan nakusan raba dare ina tabe tabe, da yau nai niyyan naje shagon liti mai saida film din anguwan mu naira hamsin yake karba ya sassaka maka films awaya nace zanje asamin nima naita kallo abina” murmushi amaryan tayi ta kalli fuskan Aneesan hakanan taji yarinyar ta burgeta she’s so pure at heart dan wanan wayan ne tecno takema murna haka, Allahu Akbar rayuwa kenan abinda ka raina shi wani kesamu yakasa bacci sabida tsantsan farin ciki, saisa akace kadena duban nasama dakai wanda yafika ni’ima sabida zaka kasance mara godiya ga Allah, by the time ka kalli nakasa dakai wanda kafishi saika godema Allah more and more which of the favors of Allah will she deny?? Alhamdulillah, Allah has been super good, Alhamdulillah, tasake godema Allah, dan ajiyan zuciya ta sauke tareda gyara zama tace “nagama bakida data bazaki iya downloading WhatsApp ba” hannu Aneesa tasa abaki tafito da manya manyan idanunta tace “laaaa sub ko? Kash ancene sub dari biyar dubu daya akeyi, inna koma gida nacema Ammi tabani kudi nasiyo” murmushi amaryan tayi tace “don’t worry zan miki yanzu” kafin ma Aneesa tai magana tace “kiramin number ki” number Aneesa ta shiga kira mata ta tura mata katin dubu biyar sanan tamata subscription din 3gb, itadai Aneesa bamatsan meta keyi da wayan ba tadaiga tanata taba wayan, bude mata Gmail tayi screenshot din password din data bude mata dashi mai sauki sanan tamata setting up play store tai downloading WhatsApp tabude mata tsaf ta nuna mata sai dadi Aneesa keji sanan ta tura mata few movies din India datake dashi awaya wanda shine yawanci films dinta, dadi Aneesa kaman zata suma ta kudurta aranta yauko lallen dazata zanama wanga Amarya ko lallen matar sakin duniya ne sai haka.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57Next page

Leave a Reply

Back to top button