A TSAKANKANIN SOYAYYA HAUSA NOVEL
Tagumi Ammi tabuga tana tunani sosai sai hango fuskan Dady take, dan motsin da Aneesa tayi yasa tadago kanta ta kalleta ganin idanunta abude yasa ta tashi da sauri tareda daura hanunta kan goshin Aneesan tana murmushi tace “Aneesa na kin tashi zakiyi fitsari nakaiki bayi?” girgixa ma Ammi kai tayi tana murmushi, murya chan kasa tana lum lumshe ido tace “Ammi ki yarda ki aureshi ni inason shi wlh, inason Abba Ammi, please ki yarda kinji” Aneesa tai maganan tana murmushi sosai baki Ammi tabude cikeda mamaki tana kallonta tace “ke, so dama idanunki biyu kinajin duk abinda muke cewa ko” gyadama Ammi kai tayi tana murmushi sosai tarike hanun Ammi tace “Ammi please kinji ki yarda, dan Allah” hararanta Ammi tayi tace “Common kimin shiru anan, zakiyi fitsarin ko bazakiyi ba” turo baki tayi tace “ni banaji, kuma inyazo gobe sainace mai Ammi na ta yarda su Baffa su daura auren” haba Ammi tarike tana kallon Aneesan cikeda mamaki tace “kaman rashin lafiyan nan yasamiki rashin jine ko Aneesa wanan magana haka” dan murmushi Aneesa tayi tace “inda ni namiji ne dani zan badake Ammi” daka mata duka kadan Ammi tayi acinya hakan yasa tafashe da dariya sosai Aneesan tana safe kanta dake mata ciwo Ammi tace “ahh lallai lafiya tasamu, zanci gadanku ne” rungume cikin Ammi tayi tace “please Ammi na ki yarda kinji for me Ammi na, ni inason shi” shiru Ammi tayi tana sauraron ta kafin tadan sauke ajiyan zuciya tace “to shikenan, zanyi tunani in sha Allah” matseta Aneesa tayi tace “yauwa Ammi na, my Ammi najin magana ta, my Ammi is a good girl” dariya sosai Ammi tayi tana shafa kanta tace “Allah shirya” haka suka dinga hira kasa kasa harta sake komawa bacci.
[4/5, 8:09 AM] Hijabi_muslimah????: A TSAKANKANIN SOYAYYA
_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤
_✍????M Shakur_
2️⃣8️⃣
Tunda asuba ta tashi ganin tanada dan karfi yasa Ammi ta kaita bayi tamata brush tareda dauraye mata jiki da towel da ruwan zafi ta taimaka mata ta chanza kaya hakan yasa taji dadin jikinta sosai suka fito, a zaune tai salla sanan takoma kan gado Ammi tahada mata hot tea mai kauri tabata tasha dan yamata dadi sosai nan da nan tafara zufa dan sauki yasoma samuwa kafin daga bisanni tai bacci.
Wuraren biyun rana su Baffa suka iso kowannen su dauke da murmushi akan fuskar shi suka zazzauna nan suka shiga bama Ammi labarin binciken dasuka yo, Dady nada kirki ainun ga taimakon musulmai, sanan baida zalunci, matayen shi duka suna tare bai taba sakin mata kodaya ba, gidan shi ba’ajin kansu awaje atakaice dai basuji any bad halin Dady ba daidai da kwara daya, hakan yasa Baffa ya gyara zama yace “todai kinji komi, me kikace dan kiranmu yake jira, eh maman Fateema me kikace?” dan ajiyan zuciya Ammi tasauke kafin ahankali tajuyar da kanta ta kalli Aneesa dake bacci tai shiru kafin tafara zancen zuci. “hukuncin dazan yanke yanzu sabida kene Fateema na, I know, ni karan kaina nasan yanda zuciyar ki ta kwadaitu, tana neman wanda kowani safiyar Allah zaki kalla ki kirashi da Baba ko Abba ina kwana, kema ki sami wanda zaki kalla ki kira da mahaifi, bakomi zaisa na yarda da auren nan ba saidan inga farin ciki akan fuskarki, farin ciki wanda ni mahaifiyarki ce tasanyaki ciki, nothing beat seeing your child happy and as a mother I have to make you happy, zan yarda da auren nan for you Aneesa na dan naga yanda kikeson Alhajin nan banda hakaba ma ta sanadinki muka hadu” ajiyan zuciya ta sauke ta juyo da kanta ahankali ta kalli su Baffa dasuke jiran me zatace gyadamusu kai tayi ahankali tace “na yarda Baffa” wani iri washe baki da sukayi zaka dauka an musu bushara da aljanna ne Baffa yace “masha Allah Masha Allah, naji dadi, ina kuma rokon Allah daya sanya albarka awanan lamarin, ya kade fitina, yanzu Na sani tashi muje musanar dashi me akeciki kaga nasan zaiyi farin ciki sosai” cikin jin Dady suka tashi suka fita, dan murmushi Ammi tayi harga Allah tunda Aneesa ta nuna tanason Alhajin sai itama taji tana sonshi sosai bana wasaba kuma zata so ta kasance tareda shi har abada, dan dugo dakai tayi ta sumbaci goshin Aneesan dake bacci tana murmushi tanata kallonta ahankali tace “Allah yabaki miji nagari wanda zai soki sanan ya kulanmin dake aduniyan nan” karan dataji na shigowan message a wayanta ne yasa ta mike tsaye ta dau Jakarta dake kan saman drawer, wata savuwar number ce tatura mata sako, zama tayi abakin gadon tabude.
Assalamu Alaykum, Rukayyah
Hakika yau kin sani cikin tsananin farin cikin dana dade ban shiga irinshi ba, naji amsan ki daga bakin Alhaji, Masha Allah, Alhamdulillahi Rabbil Alameen, alkawari daya zan miki shine bazaki taba samuna dacin amana ba, zan rikeki amana, Aneesa tadawo y’ata zan riketa amana sanan zan bata tarbiya amatsayina na mahaifi agareta, karkiji komi zan kasance miji nagari da zaki dinga alfahari dani akodayaushe. Ina kaunar ki sosai Rukkayah Sainazo
Alhaji Muhammad
Dan murmushi Ammi tayi ta ijiye wayan tareda sauke ajiyan zuciya tana tunani wai yanzu itane zatai aure? Abinda bata taba kawowa zai faruba, Allah kenan dazaran yace lokaci yayi to yayin nefa, Allah sa mudace! Ameen.
Da sallama Dady ya shiga part din Aliyu, jin shiru bai amsaba TV ne kawai ke aiki a falon yasa yay bedroom dinshi, ahankali yabude kofan babu kowa a bedroom din sai kamshin da dakin yakeyi, fitowa yayi yana kwalamai kira. “Aliyu, Son, Gadanga na” fita yayi daga part din yana mamaki to ina yaje yaga motarshi ai, har zai wuce idanunshi suka sauka kan wani fine paint brush dake kasa, tsugunnawa yayi ya dauka yana murmushi yace “yau yan zanen sun tashi kenan jibi ya yarda wanan baima saniba” garden din dake side din Aliyun yawuce dan yasan anan yake zane, garden ne mai kyan gaske an gyara wajen iya gyarawa gawasu kujeru da table da aka jera awajen kaman wurin picnic, hango Aliyu yayi zaune kan wani dan kujera, yana sanye da gajeren wando na Paco Rabanne sai wani dark blue logo t-shirt na Marni kafanshi cikin wani white bedroom slippers, hanunshi rikeda paint brush yana 3D zane dabai riga yagama ba akan babban drawing board, kunenshi makale da head phone, jingina Dady yayi da bishiyar mango dake wurin yay folding hannu a kirji yana kallonshi yana murmushi Aliyu is damn gifted. 1st degree dinshi architecture yayi, 2nd degree dinshi kuma yay law, bai dade dagama masters dinshi ba, dukda first class yake fita, yanzu haka construction company dinshi is ready amma yaki fara zuwa office ko kadan baiso yana takuramai saisa ya barshi yasa wani PA dinshi yana managing wurin kafin Aliyu yay ready finally.
Ahankali ya sanya hanunshi dasuka dan baci da paint ya janye headphone din kunenshi batare daya waigoba yace “Dad why are you looking at me?” ware ido Dady yayi cikeda mamaki kafin yatashi daga jikin bishiyan yakara so inda Aliyun yake ahankali ya dafa kanshi yace “Son yan zanen ne yau suka tashi, mekake zanawa haka?” Dady yay maganan yana janyo dayan stool din dake gefe ya ijiye ata gaban Aliyun ya zauna yana kallon yanda paint din yabata rigan daya saka. “Aliyu” kallon Dady da sauri yayi yana tsayar da zanen jin yanda yakira shi, ajiye paint brush din yayi acikin cup din ruwan dake kan table yace “Dad, wat is it?” gyara zama Dady yayi yace “I want to talk to you” hannu yasa ya kashe headphone din da waka ke tashi daga ciki Aliyu yayi yace “OK, am listening” dan shiru Dad yayi kaman mai tunani, ahankali yace “aure nakeso zan kara Gadanga na” yay dan shiru yana kallon fuskan Aliyun ganin baiga wani chanji ko wani yanayin tattare dashiba yasa yace “Son kasan bana boyema komi ko, kawai sabida na kasance namijin da banso ina yawan sakin mataye nane bazan ma karya ba da tuni na saki duka mata uku nan danake dasu, basuda mutunci, basu da kirki, ga shegen son abin duniya, they’ve spoilt all my children Aliyu da yau inda zan fadi namutu yaran wanan ba ruwan su da yaran wanan, cikin dukan ku ku 20 daga kai sai Rauda ne Allah ya tsamo min, am worried Son, how many hours nake samu na zauna agida dazan samu nai uniting yarana, y’ay’ana iyye? Na auro jakunan mata babu abinda suka iya sai koyama yarana bakaken hali da tsanan junan su, mata uku amma banda ta arziki ko daya” yadanyi shiru dan ko kadan baiso yana tunawa da matsalolin gidanshi da hawan jininshi zai iya tashi, ahankali yace “I told you shekaran jiya abinda yasa nai latti was because I helped one woman da yarta batada lafiya na kaisu asibiti ne ko” gyadamai kai Aliyu yayi alamun eh, cigaba da magana Dady yayi yace “Aliyu when I saw how caring and loving that woman is towards her daughter I immediately saw myself in her, na yaba da natsuwan matar, sanan na yaba da tarbiyan data bama yarta, she’s good, she’s educated duka fanin boko da islamiya ahaka banma riga na tambayeta duka abubuwan data saniba tukunna, Ustaziya, kamilan mace, da natsuwa da kamala, ga fikra, all this abubuwan duniyan nan basu dameta ba, sosai naji ina sonta, nama yan uwan ta magana sufada mata tace ta yarda, dazaran an sallami yarinyar daga asibiti nakeso a daura auren, I don’t wanna do anything dazai batama rai I need your support Gadanga na, should I go ahead and marry her?” dan shiru Aliyu yayi yana kallon mahaifin nashi deep down ya tsani yanda Dad ke aure but wani zubin baya blaming nashi danko shi kanshi baiga mata tagari acikin matayen ba, he just hope wanan will give his Dad the peace din dayake nema da kwanciyan hankali tunda dai yaga tsantsan son da Dady ke mata a idanunshi, dan murmushi dake karamai kyau yasakin ma Dady yace “marry her Dad, Allah sanya alheri” ajiyan zuciya Dady ya sauke tareda lumshe ido jiyayi duk wani nauyi da zuciyan shi yamai ya sauka baiso yay auren Aliyu bai yardaba saigashi ya yarda, cikeda tsananin farin ciki yace “thank you Gadanga na, zan kira Momman ka tahada min akwati, kaje gidan kuwa tunda kazo?” yatsine fuska yayi tareda girgiza kai, dan batarai Dady yayi yace “kabar zanen nan kawuce ka shirya, bodyguards dinka su kaika kanajina ko” ahankali yace “to” tashi Dady yayi yace “zan kira a gyara the flat that is next to mine, bari naje office” “bye Dady” “bye Gadanga” fita Dady yayi Aliyu yay shiru yarasa mekemai dadi aduniyan nan mugun so yake yaje asibitin but baiso yahadu da Ammi, Abdul yafado mai arai hakan yasa da sauri yatashi yay part dinshi wanka yashiga yafito ya shirya cikin wata hadaddiyar shadda yaja mota ko inda bodyguards din da Dady yace subishi baiyiba yafice abinshi.