A TSAKANKANIN SOYAYYA HAUSA NOVEL

A TSAKANKANIN SOYAYYA HAUSA NOVEL

duk wacce takaranta batare data biyaba Allah ya isa
[4/5, 8:09 AM] Hijabi_muslimah????: A TSAKANKANIN SOYAYYA

         _IN BETWEEN THE LOVE_
        ❤ _Lies another love_❤




        _✍????M Shakur_



                    4️⃣2️⃣

Not edited

Knocking glass din yayi Aliyu ya saukar da glass din kasa cikeda girmamawa matashin yadan dukar dakai yace “barka da zuwa Ya Aliyu, ya hanyar saukar yaushe agarin” dan murmushi Aliyu yayi yace “nadan kwana biyu, ya Umma?” “tananan lpy” dan ajiyan zuciya Aliyu yasauke yace “I brought Hajiyata, jamb registration mukeso muyi” da sauri guy din yace “masha Allah mu shiga daga ciki amata Ya Aliyu shine harsai katambaya wlh kafi haka muje ciki” yay maganan yana budema Aliyu kofan fitowa ahankali Aliyun yayi yazagaya yabude ma Aneesa murya chan kasa yace “let’s go” gyadamai kai tayi tasanya kafa ahankali tafito gaba mutumin yayi Aliyu da ita suka bishi abaya suna tafiya dai dai looking sweet, sai kallonsu student dasuka cika wajen suke wani special daki mutumin yakaisu yabasu waje suka zazzauna sanan yakawo form din yabama Aliyu da byro cikemata komi Aliyu yafara tana fadimai saida yakai wajen date of birth da gangan yadago kai ya kalli fuskanta yace “your date of birth” dauke kai tayi ta shiga wasa da yatsunta ahankali tace “20yrs, march 1st aka haifan” wani irin murmushi yayi mai sauti dahar ita saida taji kunya taji shikenan yanzu zai dinga mata kallon wata yar yarinya, ko 1 hour cikakke basu bata awurin ba suka gama komi aka bata slip dinta ya karba sanan suka fito yabude mata mota ta shiga tana daure fuska sabida yanda taga anata kallon Aliyun shiga motan shima yayi yana yatsine fuska jikinshi namai ciwo bana wasaba, zama yayi sanan yatada motar sukabar wajen, agaban wani babba super market yay parking, kashe motan yayi yazagayo ta inda take yabude mata fitowa tayi ahankali tana kallon wajen hannunshi yamika mata hararanshi tayi akunyace hakan yasa yay gaba tana biyeda shi suka shige ciki, siyayya yadingayi harta dinga mamaki wayake ma siyayya haka, ya kwashi gowns na yan gayu da idan vatai mistake din lissafi ba zasu kai 16 ya kwashi kayan bacci da kayan kwalama sanan yabiya kudin komi aka kwashe musu suka dawo mota yatada motar gyangyadi tafara ya girgixa kai kawai yacigaba da driving a binshi har gida horn yayi aka bude musu ya shiga Maman su Rauda ce agaban flat dinta da Rauda agefenta dake mata rubuce rubuce, bin motan sukayi da kallo, parking yayi yafito yazagayo yabude side din Aneesa yana murmushi, ahankali tafito da kafafun ta, turomai baki tayi tace “to ka matsa so kake nabuge ka” dan shiru yayi yana kallon fuskanta, murya chan kasa yace “kinsan wani abu?” da sauri ta girgixa mai kai tace “menene” murya chan kasa kaman maison yin gulma yace “ina sonki sosai Aneesa, yau zan fadama Dady, nakosa na aureki” murmushi tayi tarufe fuskanta da hannayenta tace “nidai ka matsa na wuce” ahankali yace “bakice kina sona ba yau?” batare data bude fuskanta ba tace “kai da kake ta ihu ne kanka dan dauki dan karfe ne zance inaso hu’um, nisai kadawo mai karfi kaman zaki sanan zance ina sonka” ahankali ta zare hannunta daga fuskanta tadan kalli fuskanshi yanda yake kallonta da shagwababbun idanun nan tace “inaso kazama my lion, Boldest and bravest saida aji tsoranka badai ka kajiba, baka ganni ba, kataba ganin power na kuwa?” da sauri ya girgiza mata kai yana danne dariyan dayake ji, kyawawan idanunta tadazan zaro tace “kai namiji ne dana nunama, amma inada babban power, kaga ko a bakery mu in a day sainai baking su meat pie da cakes na buhu data saisa nakeda karfi, ranan nan nakusan yima Fatima duka” da zaro ido yayi surprisingly gyadamai kai tayi tace “yes tsokana take takan Yusuf security saurayinta namin magana toni mai ruwana dashi ninace yazo yamin magana aiba nibane ko?” ta kalleshi tana jiran amsa, gyadamata kai yayi tacigaba da zuba tace “shine tazo aiko nadau babban bowl nabita da gudu tafita daga bakery” ta kyalkyace da dariya harda tafi, this is the first time take sakin mai surutu haka ta masifan burgeshi ahankali yakira sunanta. “Aneesah” tsayar da dariyan tayi tadago kai ta kalleshi, wani irin luu yamata da ido ahankali yace “I love you so much, I will tell Dady about our love yau” ta gefenshi tayi tai hanyar flat dinsu da gudu tana murmushi ko lura dasu Mama daketa kallonsu batayi ta shiga flat dinsu, Booth Aliyu yabude ya kwalama mai sharan tsakar gidansu kira kayan daya saima Aneesa yanunamai flat dinsu yacemai yakai shikuma yawuce flat dinshi dan bacci yakeji sosai.

Kayan da Ammi taga an shigo dashi yasa ta kalli Aneesa tace “wanan kayan fa” dan zaro ido tayi kaman wata mara gaskiya tace “nima bansani ba Ammi nadaiga yanata siyansu dazu” ajiyan zuciya Ammi ta sauke tana tunani saikuma ta kawad da tunanin hala Alhaji yace yadingayin haka, koma bahakaba yaron nada hankali danya saima Aneesa abu bawani abu bane dukansu Dady yarike a matsayin y’ay’a a yanzu.

Karfe hudu driver ya kwashe su zuwa islamiyya koda daddare data dawo batama iya tsayawa taci abinci ba sai bacci, da Ammi ma ta shigo tadata suzo suci abinci kasa tashi tayi tai nisa a baccin haka Ammi tafito tafadi ma Dady da Aliyu, abincin da Aliyu bai iyaci da kyau ba kenan sabida bata a wurin yaso yaga fuskarta kafin yay bacci amma baiganta ba, ture abincin yayi yamike tsaye da sauri Ammi tace “ina zaka bakaci komiba ai” murmushi ya kakalo ma Ammi yace “na koshi ne Mum, ban wani jin yunwa, saida safe ku” “say your prayer before sleeping okay” gyadama Dady kai yayi yawuce yafita.

Yau gudun kar Ammi tamata fada da sassafe ta tashi tai salla tai karatun Al ‘Qurani saida gari yay haske sosai sanan ta shiga gyaran gidan har zuwa kasa, a kitchen taga Ammi na hada breakfast ahankali tace “ina kwana Ammi na” “kin tashi lpy yi sauri kikarasa gyara falon da baranda sai kizo muhada breakfast inaso kiyi wanki kyau kayan wankin mu sundan taru” gyadama Ammi kai tayi tacigaba da gyara falon harta fitar da sharan waje Aliyu tagani kan 34 degree hyper extension yana excerise yanda taga yana nishi saida hawaye yatarun mata a idanu, he’s doing all this sabida ita, lumshe idanu tayi ahankali tace “ina sonka sosai Ya Aliyu na, I love you wlh” tsince yan datti gaban dakin tayi dan bataso ma yaganta tabude kofa tadawo daki, kitchen ta shiga alalen gwangwani taga Ammi nahadawa shidai Dady bai cika wani son abincin yan gayun nan as breakfast ba yafiso yaci lafiyayyen abinci a gida wanda koyaje office bazai damu dawani abinci ba, shi dama aka’ida sai biyu yakecin abinci safe da dare bayacin na rana awurin aiki, yau shida kanshi yacema Ammi tamai alale na gwangwani yana bala’in jin dadin girkin Ammi shidai he’s so lucky Ammi is just good takowani fanni in bed hulala Ammi is a killer, a girki kuma wuhuhu she’s a murderer, dan she murder anything she cook karyane kace kaci bai hadu ba, wuraren 10 suka gama Aneesa ta jera komi a dinning lafiyayyen alalen manja ne na gwangwani da akayi da kifi sai kunun gyada mai kauri, sai ruwan sanyi irin abincin nan ba’a hadashi da juice, sama Aneesa takoma dantai wanka Ammi kuma tadau waya takira Dady, ba’a wani jimaba Dady ya shigo sanye da suit necktie dinshi a hannu rungume Ammi yayi a kunnenta yarada mata “I will miss you yau da daddare, Ina kaunar ki yallabiyata, kin gamamini alalen?” gyadamai kai Ammi tayi takama hannunshi takaishi kan table zama tayi ta zauna a gefenshi ahankali yace “ina yaranmu suke?” daidai lokacin Aliyu ya shigo ya watso ruwa yasa jeans da riga murmushi Dady yayi yace “oh jama’a Gadanga na yadage, yaro duk yabi yanabama kanshi wahala iyye” murmushi yayi yaja kujera yazauna yana kallon Ammi yace “good morning Mum” “morning Aliyu, sannu kaji, Son anya baza’a rage excerise dinan ba kuwan yamaka yawa?” girgixa mata kai yayi yace “Mum ni inaso nayi please karki hanani” cikeda so Ammi tace “don’t worry, kacigaba but saisa saisa okay” “sure Mum” murmushi Dady yayi yana sama Ammi albarka a ranshi, ahankali Aneesa ke saukowa maroon hijabi tasa har kasa, kafeta da ido Dady yayi for the first time hakanan saiyaji yama Aliyu sha’awan yarinyan, Aneesa nada natsuwa gata ustaziya, har cikin gida yawo take da hijabi, karasowa tayi akunyace ganin kowa na kallonta tace “ina kwana Abba na” cikeda fara’a Dady yace “kin tashi lafiya yarinyar Abban ta” Aliyu tadan kalla kafin ta dauke kai tace “ina kwana Ya Aliyu” myrya chan kasa yace “how was your night little sis” murmushi daga Ammi har Dady sukayi jin sunan daya kira Aneesa dashi kafin Ammi tamike tai serving kowa sanan aka shiga cin abincin Aliyu da Dady santi kawai sukeyi, Dady ne yagama yafara musu sallama yatafi office sai Aliyu shima sallama yama Ammi yatafi flat dinshi soyake yasake wanka da ruwan zafi dan jikinshi ciwo yakemai na bala’i.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57Next page

Leave a Reply

Back to top button