A TSAKANKANIN SOYAYYA HAUSA NOVEL

A TSAKANKANIN SOYAYYA HAUSA NOVEL

Da sauri ta shiga falonsu hijabin jikinta ta zare tawurga kan kofa tai wajen Ammin ta, zama tayi kusada ita tana kallon fuskarta tace “Ammi na menene? Maiya sami idanunki sukai ja? Kuka kikayi? Mesu Baffa suka gayamiki daya bata miki rai har kikai kuka?” tai maganan cikeda damuwa sosai, yatsa Ammi tasa ta dungure mata kai tareda kakalo murmushi tace “wayace miki kuka nayi eh uwar tsegumi? Toba kukanai ba kwaro ya shiganmin ido dazu saisa idanuna sukai ja, tashi ki dauko sabuwar wayar taki kisaka chaji kinga sun kawo wuta” murmushi tayi dudda tasan da abinda Ammi ke boyemata amma saita share taje ta dauko kwalin tazauna kusada ita tana bude wayan daga kwalin wayan tazauna gefen Ammi tana bude kwalin, fuskarta Ammi ta kalla idanunta suka sauka akan gefen bakinta daya kumbura, hannu ta takai ta taba wurin cikeda mamaki tace “maiya sameki anan Aneesa?” dan zaro ido tayi takai hanunta ta taba wurin sai a lokacin taji zafi shiru tayi takasa magana hakan yasa Ammi tace “maiya sameki anan? Fada kikayi a kasuwa? Eh ina magana kinyi shiru” dan matsawa tayi gefe kadan tana turo baki dan tasan bakaramin aikin Ammi ba ta maka mata duka tace “Ammi wata yarinya fa na taimaka” “kika taimaka wani irin taimako eh spider girl?” Ammi tai magamam cikeda tuhuma, shiru tayi tana zazzaro dara daran manyan idanuwanta dan lashe pink lips dinta dataji are so dry tayi tace “Ammi wani nefa keta janta akasa ya barka mata riga shine na shigan mata daga karshe ma yayanta yazo yako rama mata sanan nadawo” gyadakai Ammi tayi tanamata wani irin shegen kallo tace “aahh ba shakka Spider girl” kasa daurewa Aneesan tayi dudda fada Ammi take mata saida tai dariya sabida yanda Ammi tafadi spider girl din, tallabe mata keya Ammi tayi tace “nikike ma dariya inai miki magana” tabe fuska tayi kaman zatai kuka tana kallon Ammin, Ammi tace “wato saisa kika dade kenan ashe ko daman, Aneesa” Ammi ta kirata cikin kakkausar murya tace “banhanaki shiga shara ba shanu ba eh? Aneesa ina gujemiki matsala bakiji, baki fahimta, bakiji, wai yaya zanyi dakene iyye? Maisa bakijin magana na?” kaman zatai kuka tace “yakuri Ammi bazan karaba to” “yimin shiru anan haka kullun kike cewa, Aneesa karkije kajawo mana bala’i wataran, Allah duk randa kika kara Baffan ki zan kira nafadi mai abinda kikeyi dama sunce ban baki tarbiya mai kyau kinga saisuga balaifina bane” kallon Ammi take tunda tafara masifan hakan yasa tace “Ammi haka sukace wai baki bani tarbiya da kyau?” hararanta tayi tace “wuce kije kisaka waya achaji malama kizo kidaura abincin rana” gyadamata kai tayi ta tashi daga kan kujeran tawuce ta saka wayar chaji sanan tafita tsakar gida dan daura abinci awuta.


Ahankali yake bude ido shibaimasan lokacin da baccin gajiyan nan yay awon gaba dashiba, agogon dakin ya kalla yaga karfe biyar na yamman harda yan mintuna, tashi yayi ahankali yashiga bathroom alwala yadauro yafito ya shimfida dadduma akasa yay salla, yana idarwa yatashi gaban wardrobe dinshi yaje ya chanza kayan jikinshi zuwa kayan shan iska, wani brown 3quater da white short sleeve t-shirt yasaka daya kamashi tsamtsam, feffesa turare yayi yazura palm dinshi yafito, fita yayi daga part dinshi yay tsakar gida bayan yadau ball dinshi yana bubbugawa a compound dinsu shi kadai dudda he’s missing Dad but baiso yaje side dinshi yaga matayenshi a palorshi, buga ball dinshi yake shi kadai cikeda kwanciyan hankali sosai yaji hanun nashi yadena ciwon kana ganinshi kasan he’s so happy, horn din mota yaji anayi ba kakkautawa yasa ya daga kai ya kalli Gate dinsu dan yaga waye yacika mai kunne haka da ihun mota, yana wasa da ball a hanunshi soja yabude gate din motar ya shigo ayanda motar tai parking zaka gane ba lafiya, bubbude kofofin motar akayi aka fito Maman su Rauda ne data watsamai wani kallon tsana dawata mata mai bala’in kama da ita saidai tadan fita tsufa itama tafito daga motar takamo Khamis dake cikin motar tafito dashi ga wanan farin fuskan nashi yasha zanen bakin lalle radau idanun shi abude amma sunyi jajir yana sanye da dogon wandon shaddar shi ta dazu da farin singlet ajikinshi, fashewa yayi da dariya sosai ganin yanda fuskar Khamis din yayi looking so damn funny, yanda yake dariya looks so cute and adorable kasan cewanshi mutun that hardly laugh, dafa cikinshi yayi sabida ciwon dayaji yanamai sabida dariyan da yakeyi ahankali yace “dat girl is so naughty look at wat she did to him” yay maganan yana rungume kwallon a ciki yana kallonsu still yana murmushi dauke kai sukayi sukai falon Dady kana ganinsu kasan bala’i kecin cikinsu.

Sannu Sannu bata hana zuwa, let’s take everything daki daki dan nasamu na isar da desired sakona, love you????
[4/5, 8:05 AM] Hijabi_muslimah????: A TSAKANKANIN SOYAYYA

         _IN BETWEEN THE LOVE_
        ❤ _Lies another love_❤




        _✍????M Shakur_



                    1️⃣1️⃣ & 1️⃣2️⃣

How to subscribe

zaki tura 300 ta account number na 3107021073 aisha Muhammad first bank, saiki turo evidence of payment ta watdsapp number na 07012181461. For those da basu da account you can also send MTN card ta watsapp number na saina saki a group din danake posting

Free page
Shigowa dakin Dady yayi sanye da jallabiya fuskarshi lema leman ruwa alamun kaman alwala yayi hada ido sukayi da Dady yana zaune kan kujera, bedroom dinshi Dady yawuce baiwani jima acikiba yafito dawani white iron jallabiya mai kyau namaka yafito daga dakin nashi yace “tashi kasa mutafi masallaci” turo baki yayi yana karasa shan yoghurt dinshi yace “ni banyi alwala ba” ajiye jallabiyan Dady yayi kan saman kujera yazo inda yake ya karbe cup din hanunshi yace “you and yogurt, give me the cup” ya karbe cup din ya ijiye akan center table yace “to tashi kashiga nan visitors toilet kadauro alwala Son, kaga anma fara kiran salla” gyadamai kai yayi yamike tsaye ahankali yana tafiya kaman baison yi ya shiga bayin Dady yabi bayanshi da kallo kafin yadau cup din yogurt din daya ijiye yawuce kitchen yaje ya ijiye a cikin sink, fitowa yayi daidai shima yafito daga bayin daure da alwala Jallabiyan Dady yadauka yamikamai karba yayi yasaka suka fita daga dakin sukai masallaci Dady nabashi labarin yanda yayi dasu Mama da Khamis dazu har mari saida yama Khamis lafiyayyu guda uku da yaso ya kulleshi ma da kyar yahakura bayan sunbabbashi hakuri, murmushi kawai yayi yanajin Dady harsuka shiga masallaci. Saida sukai isha’i sanan suka dawo gida zaiyi part dinshi Dady yace “let’s go to side dina muyi dinner” girgixa kai yayi yanadan lumshe ido ahankali yace “am sleepy and am not hungry Dad, I love you gud night” tsayawa Dady yayi yana kallonshi kafin yadan numfasa yace “shikenan gud night kiddo I love you more” turo bakinshi yayi yace “Daddd kiddo kuma” hancinshi Dady yaja yace “kafito da mata namaka aure kaga idan nakara kiranka da Kiddo” dan dariya yayi yace “nay nay na” tallabe keyanshi Dady yayi yace “zakaci gidanku da nay nay na ne, motar waye a pake a gaban side dinka?” Dady yay maganan yana kallon gaban shashinshi dansai yanzu ya lura da motar, juyawa yayi ya kalli shashin dan murmushi yayi yace “is Abdul Dady, bye gud night bari naje” yafada da sauri yana tafiya, murmushi Dady yayi yace “su aboki anzo har ana sauri ko an manta dasu Dady” juyowa yayi da sauri jin maganan da Dady yayi da sauri yaje ya rungume Dady yay lamo a jikinshi ahankali yace “you know you are the best Dady in the whole world” shafa bayanshi Dady yayi yana washe baki yace “and you are the best son in the whole world Aliyu am a proud father to this yaro maijin magana just a lil stubborn and annoying atimes” dariya dukansu suka fashe dashi a tsakar gidan atare kafin sundanyi shiru yana jikinshi har lokacin, murya chan yace “Dad” anatse Dad dake rike dashi yace “na’am Gadanga na” ahankali yace “you are my Dady and My Mummy, kamaye gurbin Ummi, baka taba bari naji kewanta ba, you feel that hole in my heart, you are my everything Dad, and happy Fathers day” rungume shi tight Dady yayi his heart is so swollen kalman Mum daya fada yasa yatuna da marigayiya matarshi the best wife daharyau yakasa samun kamanta shiru sukadanyi for a while kafin yasaki Aliyu yana share hawayen dasuka cikamai ido da sauri dan karya gani sanan yay murmushi yace “wuce katafi Abdul na jiranka, zan aiko muku da abinci” gyadamai kai yayi ahankali yace “bye Dady” “bye son” juyawa yayi yay part dinshi Dady ya tsaya yana kallonshi saida yaga shiganshi yawuce yay part dinshi shima.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57Next page

Leave a Reply

Back to top button