A TSAKANKANIN SOYAYYA HAUSA NOVEL

A TSAKANKANIN SOYAYYA HAUSA NOVEL

Ringing da wayar da Ammi dake cikin mota tana dawowa yyi yasa ta kalli wayan Baffa tagani hakan yasa tai picking wayan da sauri daga tachan bangaren yace “kinkai asibitin Maman Fateema?” da sauri Ammi tace “a’a nakusa amma” dan ajiyan zuciya ya sauke yace “to shikenan zanje na saida daya daga cikin shanun Fateema kin yarda ko?” Baffa ya tambayeta, da sauri Ammi tace “duk yanda kayi Alhaji daidai ne yarka ce ai Fateema” cikeda damuwa yace “shikenan nasan yansun nan muna kaiwa kasuwa za’a siye, dazaran an siya zamu taho Sulejan, kome ake ciki kidinga sanar dani, Allah kara sauki, Allah bata lafiya, karki damu zamu iso kimin dare idan na iso za’asan meza ayi” gyadakai Ammi tayi tace “Allah yakawo ku lpy Baffa” ta katse wayan.

Abakin asibitin ta sauka rike da katuwar jakan dake hanunta takarasa cikin asibitin da saurinta har dakin su, bude kofar tayi tana kallon manya manyan ledoji data gani kan kujera saikuma kwalin yogurt data gani da cup kan drawer ga Aneesan na bacci peacefully, karasawa ciki tayi bayan ta mayar da kofan tarufe ta ijiye abubuwan datazo dashi tana bude ledojin data gani manya manyan madara da milo ne sai kellogs cornflakes da manya manyan chocolates da biscuits harda minti mai tsinke da wasu abubuwan ma da batasan mesuba, maida ledojin tayi ta ijiye inda suke takai hannu tashafa fuskar Aneesan ahankali, bude ido Aneesan tayi ta daura kan fuskar Ammi da sauri tai yunkurin tashi taimaka mata Ammi tayi tana murmushi tace “oyoyo Aneesa, nadawo” ta rungume ta tana shafa bayanta kafin ta dagota ta jinginar da ita da bangon gado tace “meke miki ciwo yanzu?” murya chan kasa kaman na wacce ke mura ta nuna cikinta tace “cikina Ammi” dan murmushi Ammi tayi tace “sannu kinji hala yunwa ce, bari na kawo roba ki wanke baki na soyomiki kazanki kici , su Baffan kima na hanya zasuzo anjiman nan” Ammi tai maganan tana shiga bayi tadauko wani roba tabude jakan datazo dashi taciro brush da maclean da kanta ta wanke mata bakin tass sanan takoma bayi ta zubar da komi tareda wanko hannu tafito tana sake kallon kayan tazo gaban gadon ta zauna tana dauko kulan abincin da takawo tace “waye yakawo kayan nan Aneesa?” manyan ledojin Aneesa ta kalla kafin ta dauke kai tace “wani ne” shiru Ammi tayi bata kara cewa komiba dan atunanin ta mutumin jiyane yakawo, ta zuba shinkafa a plate tasa mata tsokan soyayyen kajin har guha uku tamika mata ta ijiye kulan akasa tareda daukan spoon takarbi plate din daga hanunta tasa chochalin tadebo abincin zatakai bakinta akai knocking kofar tareda shigowa. Dady ne ya shigo dakin yana sanye da manyan kaya shdda bugagga da hula sai kamshi yake Dr biye dashi murmushi yayi sosai cikin ba’a yana kallon Aneesan dake tanuna shinkafan ahankali yace “lallai y’ata tasami lafiya tunda gashi har baki yabude tanacin abinci” dan murmushi Ammi tayi tana gyara hijabin jikinta Allah yasa bata cireba tace “ina kwana Alhaji” kafin ma ya amsa ta kalli Aneesa dake cin abincin da Ammi tasamata abaki ahankali tace “bazakiyi gaisuwaba, Alhaji shiya taimaka mana jiya yakawoki asibiti” hadiye abincin Aneesa tayi ahankali tadago dara daran idanunta cikin dan karamin muryanta tace “ina kwana Abba” wani irin murmushi Dady yayi yanda Aneesan ta kirashi Abba saiyaji ta masifan burgeshi daga gani anbama yarinyar tarbiya mai kyau zuba yay har gaban gadon yace “lafiya lau y’ata ya jikin?” ahankali ta gyadamai kai. “lafiya lau Abba” murmushi Dady yasake yi yace “gud girl, babu abinda ke ciwo ko? Ko asakeyin allura ne?” da sauri ta girgiza kai tai kaman zatai kuka, dariya Dady yayi hakan yasa Ammi ma tadan murmusa koba komi maison naka abun kaji dadi ne, dariya Dady yayi ya kalli Dr daketa murmushi yace “tokanaji ko likita Ya’ta batason allura karka kuskura kamata” ya kalli Aneesa yace “idan Dr yamiki alluran zan dawo anjima kinfadamin kinji” da sauri ta gyadamai kai tana murmushi sai taji inama shi baban tane tanason Baba sosai tana bala’in son Baba, dan juyawa Dady yayi ya kalli Ammi da kanta ke kasa yace “cigaba da bama y’ata abinci ai baki koshi ba ko?” gyadamai kai tayi tana murmushi, Dady ya juyo ya kalli Ammi datamai kyau sosai dan tasaka wani maroon hijabi yace “kinji ko” dan dago kai Ammi tayi ta kallai hada ido sukayi da sauri tasauke nata tana kokarin debo rice din a spoon tace “angode Alhaji, Allah yasaka da alkairi, Allah yabiya bukatu yasa damu duka a gidan Aljanna” atare daga Dr har Dady sukace Ameen, Dady yasake kallon Aneesa daketa kallonshi tana murmushi yace “zan tafi anjima zan dawo nasake dubaki kinji, ki dinga jin maganan mahaifiyar ki kinji sanan kowani nagani aka baki kisha ki warke sabida kar mahaifiyar ki taitai shiga damuwa kinji” dago kai Ammi tayi ta kalleshi yanda yay maganan yatabata har zuciya, gyadamai kai Aneesa tayi ahankali tace “saika dawo, Allah yabada sa’a Abba” murmushi Dady yayi yanaji kaman yamaida yarinyar yarshi yace “Ameen nagode da Addu’an, muje Dr” Dr ya kalle Ammi yace “idan tagama ci ki danna alarm din gefen gadon nan zanzo” to Ammi ta amsa Dr yabi bayan Dady da sauri har wajen mota yarakashi Dady yamai kyauta mai tsoka sai godiya yake sanan ya shiga motan bodyguard yarufe yakoma gaba yatada motar suka bar asibitin, Dady sai tunani yake dan yaje shashin Aliyu bayanan ina yaje this early morning? Sai kirashi yake baya shiga.

duk shegiyar data fitar min da littafi waje Allah ya isa, duk kuma wacce ta karanta batare data biyaba Allah ya isa, ban kuma yafeba
[4/5, 8:09 AM] Hijabi_muslimah????: A TSAKANKANIN SOYAYYA

         _IN BETWEEN THE LOVE_
        ❤ _Lies another love_❤




        _✍????M Shakur_



                    2⃣7⃣

Saida suka fara tsayawa sukai isha’i sanan suka shiga asibitin, sallama sukayi tareda bude kofan dakin har lokacin Ammi na zaune kan kujera tana kallon Aneesan, zama sukayi abakin gadon sunama Ammi sannu, ahankali Ammi tace “nakawo abinci Alhaji?” girgiza mata kai Baffa yayi yace “bari tukunna yanzu akwai maganan damuke so muyi” dan gyara zama Ammi tayi tace “to Baffa” dan shiru Baffa yayi saikuma yace “Maman Aneesa tsawon wanan shekarun damukai tare tun ina miki kallon matar kanina yanzu kallon kanwata na jini nake miki wacce nakeda iko da ita koba hakaba?” gyadamai kai Ammi tayi tace “hakane Alhaji” gyadakai Baffa yayi cikin nuna gamsuwa da amsan data bayar yace “tsawon wanan shekarun dakika nuna kezaki rike Aneesa bazaki bamu itaba dudda naji haushi amma ban takura mikiba, kikazo kikace ke zaman rainon yarki zakiyi bazakiyi wani aure ba shima ban takura miki ba na barki, ayau nakawo miki wata babbar magana da bazan boye mikiba sonake yau kibani girmana a matsayina na mahaifin yarki sanan waliyinta, kimin biyayya sanan kisani kome nakeso nayi abu mai kyau ne agareki sanan abinda zai ban kwanciyan hankali ne kinajina” gyadamai kai Ammi tayi ahankali gabanta nadan faduwa, dan shiru Baffa yayi yana kallon fuskarta ganin yanda ta natsu duk tabashi hankalin ta tana sauraronshi yasa yace “sonake kiyi aure maman Fateema” da sauri Ammi tadago kai ta kallai cikin wani irin yanayi na damuwa tace “aure Alhaji?” “e, aure maman Fateema nakeso kiyi, aure rufin asirin mace ne, yarinya dake duka dukan ki nawane da zaki ce zaki zaune ahaka ke bazakiyi aureba zaki dinga kula da yarki ne angayamiki hakan zaiyu ne? Banda ma haka amusulunce hakan baida kyau, kin taba tunanin yanayin da zaki shiga duk randa zaki aurar da Fateema kiyi watanni shekaru baki ganta ba kintaba tunanin yanayin da zaki shiga yanda zakiyi coping?” shiru Ammi tayi tana kallonshi takasa magana, dan murmushi Baffa yayi yace “to kingani, gwara kiyi aure duk randa zatai nata auren kina gidan mijinki karkashin mijinki akwai wanda zai dinga debe miki kewa kinajina” gyadamai kai Ammi tayi ahankali, murmushi yasake yi ganin batamai gardama ba, ahankali yakira sunanta “Maman Fateema” ahankali tace “na’am Alhaji” anatse Baffa yace “Alhaji Muhammad Ibrahim wanan mutumin daya taimaka miki yakawo Aneesa asibiti dazu yasame mu da wata magana da tamin dadi ainun, ya nunamin shi daga ranan daya fara ganinki yaji yana matukar sonki ainun” wani irin murmushi Aneesa da tun dazu dasuka fara magana yatashi tayi cikeda jin dadi, da sauri Ammi ta kalli Baffa, gyada mata kai Baffa yayi yace “inaso kiyi tunani sosai bazan takura miki ba, gobe nakeso kibani amsa kuma ko kadan banso adau lokacin dazaran an sallami Aneesa za’a daura auren dan zanzo mu daura auren kafin mubar garin nan, Inaso ki natsu kiduba lamarin da kyau, kuma namiki alkwari gobe ni nan da Na Sani zamu fantsama garin nan muje muyi binciken halinshi inmun dawo zamu fadamiki maimuka gano sanan saimuji amsan ki saimu kirashi, inamiki kwadayin aure sosai, so kiyi tunani kinji karki takura ma kanki, Allah ya sadamu da alkhairan shi” gyadamai kai Ammi tayi ahankali tace “Ameen” murmushi yayi yace “to bamu abincin muci mutafi” plate tadauka ta zuba musu tavasu sunaci ana hira sama sama saida suka gama sanan suka mata sallama suka tafi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57Next page

Leave a Reply

Back to top button