A TSAKANKANIN SOYAYYA HAUSA NOVEL

A TSAKANKANIN SOYAYYA HAUSA NOVEL

Wuraren five na yamma yatashi daga baccin da tsananin ciwon kai, ahankali yabude ido ya yaye bargon da Dady yarufe shi dashi hanunshi dayaji yamai tsami ya kalla yaga an shafamai mai, dan murmushi yayi dan yasan aikin Dady ne ahankali yatashi ya zauna yana kallon wayarshi dake kusada side lamp ijiye, kafe wayar yayi da ido yanaji kaman yadauka yakira Aneesa, kawad da kanshi yayi da sauri daga kallon wayan yamike tsaye ahankali yana yatsine fuska yana tafiya ahankali, bathroom ya shiga yadauro alwala yafito, dadduma ya shimfida yay salla yadade kan dadduma yay shiru yana kallon wayar ahankali yamike tsaye ya linke dadduman yawuce yafita, abinci ya ganni kan dining ko kadan baijin cin komi, kitchen dinshi yawuce yabude fridge sliced fruits dinshi dasukai sanyi sosai ya kalla su yakeso yaci but baida karfin ci baida apatite, cup yadauka yadauko yogurt ya zuba farm fresh strawberry flavour yacika cup yamaida sauran fridge yafito yazauna kan dogon kujera yana kallon tashan kwallon dake aiki yakai cup din baki yana kurban yogurt din sanyin yogurt din na sanyaya mai wuya hakan yasa yasake relaxing tareda lumshe ido, fuskar Aneesa yagani tanamai murmushi.
[4/5, 8:09 AM] Hijabi_muslimah????: A TSAKANKANIN SOYAYYA

         _IN BETWEEN THE LOVE_
        ❤ _Lies another love_❤




        _✍????M Shakur_



                   2️⃣0️⃣ & 2️⃣1️⃣

How to subscribe
zaki turo 300 ta account number na 3107021073 first bank aisha Muhammad, saiki turo evidence of payment ta watsapp number na 07012181461 sainai adding naki a group din danake posting. Zaki iya turo katin MTN na 300 for those dabasu da bank

Today is the DAY!!! I must give you my sincere, warm and outstanding shout out to my VIP group, you people are not just Very Important people you guys are my BLOOD

The amount of love, patient and understanding danake samu daga wurinku is beyond tunanina, ina karatun exam ina exam I don’t get much time to type you guys supported me, oh my God, I mean o-h m-y G-o-d, am blown away da iskan kaunar ku, I Love my VIPs

Oh Hello, wanna join my VIPs and be having frequent updates? VIPs na are matured folks yo, manyan mata, issassu masu ji da kansu ???? marasa son jira, masu rike alkawari, chat me up a pc if you want to join too

Sosai tunanin Aneesa ya addabi zuciyar shi, ahankali yabude ido ya kalli yogurt din dake hanunshi ahankali yace “she’s a Nubian princess” knocking kofar da akayi tareda shigowa yasa yadaga kai ya kalli kofa, Rauda ce ta shigo tanamai murmushi, rabonshi da ita tun ranan daya kwatota daga hannun Khamis, tsareta da ido yayi ganin ta ramemai duktai wani iri, shiru yayi baice mata komiba dan haushinta yakeji danta mai karya ranan, karasawa cikin dakin tayi ta zauna gefenshi ahankali tana wasa da yatsunta ahankali tace “good afternoon Ya Aliyu” gyadamata kai yayi batare dayace komiba ya cigaba da kurban yogurt yana kallon TV, shiru tayi tana wasa da yatsunta saikuma takara dago kai ta kallai ganin yaki kallonta yasa duk taji wani iri, ahankali tadaura hanunta kan nashi takama hannun shi tarike, dago kai yayi ya kalleta, lankwashe kai tayi murya chan kasa tace “am sorry Ya Aliyu bazan karama karyaba wlh, kunyan fadama da Khamis zamu fita nake saisa ban fadama gaskiya ba, am sorry kaji please” ganin yanda duktai wani iri tana shirin mai kuka yasa ya gyadamata kai dan ko kadan baijin surutu yau baijin dadin kanshi shima, bedroom dinshi yanuna mata yace “daukomin wayana” tashi tayi da gudunta tai bedroom dinshi, bata wani jimaba tafito rikeda wayanshi karban wayan yayi yaduba yaga ba miss calls ba message, baida any notification, dan lumshe ido yayi zuciyarshi namai badadi ya ijiye wayan ahankali kan kirjinshi, Rauda dake kallon fuskanshi ne tace “menene Ya Aliyu? Are you expecting something ne awayan?” batare daya bude ido ba murya chan kasa yace “nevermind” ji yayi ma yogurt din ya isheshi hakan yasa yamikama Rauda kofin, karba tayi tawuce kitchen tana shan ragowan daya rage, ta ijiye ta fito tadawo kusada shi ta zauna, yanda taga duk yay wani iri yasa takama hanunshi tace “Ya Aliyu wai menene? Bakada lafiya ne? Kai wani iri sosai wlh yau, are you okay Ya Aliyu kona kira Dr?” girgiza mata kai yayi yana mikewa tsaye yace “go and pray ana kiran salla” daya daga cikin sweet din dake cikin wani flower bowl dake kan center table dinshi ne tadauka tana folding legs dinta akan kujeran shi tace “ni am off salat” yatsine fuska yayi ya dungure mata kai batare dayace komiba, dariya tayi tana jefa sweet din abaki ya harareta yawuce ya shiga bayin falo ya dauro alwala yafito yabude kofa yawuce mosque yana tafiya ahankali.

Karfe biyar daidai ta tattara komi tawuce backyard ta wanke kafa da hannayenta tadawo ta zare riga da hijabin tadau dogon hijabin ta tasaka tadau jakanta ta rataya tafito, ko kallon inda su Fatima suke batayiba tawuce bude mata kofa da sauri Yusuf yayi tafito yana binta da kallo yana murmushi kaman wani wawa yace “sai gobe Fatima” ko kallonshi batayiba tawuce ta shiga keke napep har zuwa anguwan su, yau gabaki daya ranta ajagule yake tarasa meke mata dadi sauka tayi daga kan keken tana dafa kanta dataji yafara mata ciwo taciro kudi tabashi batare datai magana ba tajuya ta shiga gidansu da sallama, a kitchen ta hango Ammi na tuka tuwo bamata ji sallaman taba sai aiki take abinta, jingina tayi da bango tana kallon Ammin, tana mugun son Ammin ta bana wasaba, she just wish tasan baban ta, dudda bata sanshi ba tasan Ammi was just the best wife he could have ever had, tanada kirki, gashi ta iya girki, ta iya kula da lura da yara, Ammi is everthing to her, she just wish zata sami second Dad dat will take care of her Ammi, ajiye jakanta tayi ahankali abakin kofa ta cire hijabin ta ta wurga afalo, sadaf sadaf ta shiga yin tafiya, ko kadan bataji shigowan Aneesa kitchen dinba dan hankalin ta yay nisa kawai jitayi an rungumeta tabaya. “oyoyo Ammi na” ajiyan zuciya Ammi tasauke tana murmushi cikeda so tana shafa hannayen Aneesan datai wrapping around her chest, ahankali tace “harkin dawo Aneesa, banmaji shigowan kiba” dago kanta tayi tana leka fuskar Ammi tace “yanzu nadawo Ammi, tashi nakarasa tuka tuwon inya salala na kwashe” girgiza kai Ammi tayi tana dauko mara daga cikin ruwan dake gefenta tace “a’a kibarshi keda kika daga wurin aiki kin gaji, ga ruwanki nan dauka kije kiyi wanka ki sa kaya marasa nauyi, jeki cire kayan kizo kijuye ruwan” gyadama Ammi kai tayi tajuya ahankali tawuce tsayawa tayi tadau jakanta dake bakin kofa sanan ta shiga daki, dakinta tawuce ta shiga, zama tayi akan gado tai shiru ko kadan batajin dadin komi gatanan ne kawai, jakanta tabude taciro wayarta tsayawa tayi tana kallon wayan kafin ahankali ta danna side button din wayan ya kunnu, tsayawa kallon wayan tayi tarasa mesa hakanan saitaji wani iri dataga batada miss call kodaya, kwanciya tayi akan gado ta ajiye wayan tareda lumshe ido wani bacci mai shegen dadi ne yay awon gaba da ita.

Shirun da Ammi taji batazo tajuye ruwan ba yasa ta kwala mata kira. “Aneesah” kwafa Ammi tayi tana daukan wata yar roba da bushashen kubewa keciki dan ta kada miya tace “hala tana chan tana daddanna wanan wayan dake dauke mata hankali” kwafa tasake yi takwala mata kira akaro na biyu. “Aneesah” shiru bata amsa ba, cigaba da aikinta Ammi tayi har aka shiga kiraye kirayen magrib, sauke komi tayi ta tattare kitchen din ta zuba na Aneesa a kwano tabarshi nan kitchen tafito ta dau buta ta zaga sanan tafito ta tsugunna tai alwala, tashi tayi ta shiga kitchen din tadauko kwanon tuwon Aneesan tafito dashi tawuce daki ajiye kwanon tayi a kasa tadau dadduma tana shimfidawa tace “kika bari na idar da salla na shigo dakin nan bakifito bako Aneesa sai jikin ki ya gayamiki” hijabin ta tadauka tazura ta kabbara salla, ganin ta sallame Aneesa bata fitoba yasa ta tashi tadau wayarta tana kunna tocula dan babu wuta tawuce dakin Aneesan, labule ta yaye ta shiga dakin tana haska fuskarta tabude baki zatai magana ganin tana bacci yasa tai shiru tareda sauke ajiyan zuciya bakaramin tausayi tabata ba ganin yanda ta kwanta kasan tagaji azaune ta kwanta kafafun ta duka na kasa sai kanta kwance kan gado, karasawa gaban gadon tayi ta zauna gefenta hannun ta takai kan wuyanta zafin dataji yasa tai tapping ta da sauri. “Aneesah, Aneesah” bude ido tayi ahankali cikin nauyayyan bacci ta kalli Ammi, da sauri Ammi takamo kafadunta ta dagata tace “tashi daga baccin nan, bana hanaki baccin mangariba ba babu kyau fa yana saukar da zazzabi, tashi kije kiyi wankan” Ammi tai maganan tana mikar da ita tsaye, tashi tayi ahankali gabaki daya batada karfi, ganin haka yasa Ammi tazage mata zip din bayan rigan ta taja zanin wankan ta daga kofar sip dinta ta taba ahankali ta karba tana kallon Ammi, cikeda dan damuwa Ammi tace “cire kayan kizo kiyi wankan bari naje na hada miki ruwan” gyadama Ammi kai tayi Ammi ta ijiye mata toculan akan gado dan taga haske tawuce tafita daga dakin tai kitchen ta hada mata ruwan wankan takai mata bayi tafito ta shigo dakin dakin nata ta shiga azaune taganta kan gado daure da zanin a kirji, zama Ammi tayi kusada ita tana sake tattaba wuyanta da hannu tace “bakida lafiya ne?” murya chan kasa tace “kaina keciwo Ammi” “sannu, muje kiyi wankan kizo kici abinci saina baki paracetamol” gyadama Ammi kai tayi, Ammi ta mike tsaye tareda dagota ganin batada karfi suka fito har gaban bayi takaita tace “shiga kiyi, na ijiye miki tocula aciki” gyadama Ammi kai tayi tawuce ta shiga tana tafiya ahankali damuwa sosai Ammi ta shiga saikuma ta daure da sauri tawuce dakinta dan nemo kwalin paracetamol din datake dashi, dakin ta shiga ta tsugunna ta jawo drawer ta ciro wani kwalin paracetamol ta tabude taciro kati daya sanan tafito daga dakin ajiyewa tayi kusada abincin ta sanan tafito danta dubata, kujera taja ta zauna agaban kitchen tana jiranta tafito daga bayin, shirun dataji batajin karan zuban ruwa almost 1 minutes yasa taji tadamu, tashi tayi taje gaban bayin knocking kofar bayin tayi tace “Aneesa wankan kike kome naji shiru” “A…..Amm….” muryan Aneesa dataji chan kasa na breaking sosai tana kiranta yasa Ammi ta tura kofan a rude ta shiga, Aneesa datagani kwance a kasan bayi kaman ma tafadi ne jikinta na rawan sanyi sosai duk kumfan sabulu jikinta tana kokarin tashi takasa yasa tama manta bayi take tsabagen rudewa tasaki salati. “innalillahi wa innailaihi raji’un, Aneesa” tai maganan tana tsugunnawa agurguje ta dagota a tsorace bama ta damu da abinda ke jikinta ba tasata ajikinta ganin yanda jikinta ke rawa, tace “Aneesa, ke Aneesa menene eh?” kasa magana Aneesa tayi sai jikinta dake dake masifaffen rawan sanyi idanunta na kukkulewa, ganin haka yasa Ammi tarike ta gam da hannu daya ta sa dayan hanunta a bucket din tadebo ruwan wankan ta watsa mata ajiki ta ijiye tasaba sabulu a soso jikinta na rawa ta shiga wanke mata jikin gabaki daya dan tafadi abayi sai rawa jikinta yake da ace zata saketa da zubewa zata sakeyi akasa, agurguje Ammi ta wanketa ta daura ye jikin nata tana rike da ita tasa dayan hanunta taja zanin ta dake kan kofan bayi ta daura mata ta kwance kallabin kanta tayafa mata tundaga kai har kirji ganin sanyi takeji tarikota gam tabude kofa suka fito, daki ta shiga da ita tawuce dakinta da ita akan gado tazaunar da ita da sauri tai sip ta jawo daya daga cikin dogayen rigunan ta zuwa tayi ta dagata a inda take rawan sanyi tace “sannu kinji, sa rigan” saka mata rigan tayi tacire zanin tayar sanan ta kwantae da ita taja bargon kan gadon tarufa mata, tawuce dakinta da gudu tadauko wani bargo takara mata amma dudda haka rawan sanyin take, fita Ammi tayi da sauri tadauko paracetamol da ruwa ta shigo ta zauna gefenta dagota tayi tace “sannu, sha magani” paracetamol guda biyu ta ballo tasa mata abaki tabata ruwa da sauri ta sha jikinta narawa tasake kwanciya tana nishi. “Aaa…m” da sauri Ammi ta tsugunna tana shafa kanta tace “sannu Aneesa, zazzabin yamma ya sauka akan ki, baccin magriba babu kyau” tashi Ammi tayi tarufo window dakinta ganin sanyin yaki sanan ta zauna tana shafa kanta tana kallonta hawaye nata ruwa a idanunta. Sai wajajen tara sanan taga rawan sanyin yaragu tafara sauke ajiyan zuciya ahankali bacci yasake dauketa jikinta zafi sosai, tagumi Ammi tabuga tana kallonta takai kusan 2min ahaka sanan tawuce tadauro alwala dadduma da hijabin nata tadauko tadawo dakin Aneesan ta shimfida tayi sanan tai shafa’i da wuturi bayan ta idar tabuga uban tagumi tana kallon Aneesan dake sauke ajiyan zuciya ahankali, bataso ta tasheta dan batasan kozata tashi da rawan sanyin ba amma kuma tanaso ta tadata taci abinci, abinci ma na rage rashin lafiya, tafi awa daya zaune tana kallonta kafin dan gyangyadi yay gaba da ita.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57Next page

Leave a Reply

Back to top button