A TSAKANKANIN SOYAYYA HAUSA NOVEL

A TSAKANKANIN SOYAYYA HAUSA NOVEL

Tanunamai gefen cikin Khamis, farin hanunshi Aliyu ya kalla ya dunkule ahankali yana kallon Aneesan data cije lebe irin ya dunkule hanunnan da kyau dinan tana kallon hannun tana nunamai cikin Khamis din dake sosa ido, daddagewa Aliyu yayi yabugama Khamis uban nishi aciki atare daga Aliyun har Khamis din sukai ihu harsaida Aneesan takoma baya da gudu dan tsoro sabida ihun da Aliyu yayi yana yarfe hannu kaman zaiyi kuka ya kalleta yace “it’s hurt, ahhhh, aucchhhh, alottt” sosai yake yarfe hannu hakan yasa ta matso ahankali tana leken Khamis din daya zube akasa dan naushin ya shigeshi gashi yakasa bude ido balle yarama, tsayawa kusada Aliyun tayi dake yarfe hannun nashi dayay jajir tasaka yatsa abaki tana cija danso take suci uban Khamis sosai, kalle kallen compound din ta shiga yi kafin idanunta su sauka kan rigan Khamis din dayacire ya yar da sauri tai wurin rigan tsugunnawa tayi ta dauka ta shiga wurga rigan tana kaman lilo dashi rigan ya shiga kanannadewa danso take tamaida rigan dorina, binta da kallo Aliyu yake yana murza hanunshi harsaida tagama tazo gabanshi da sauri ta mikamai dorinar rigan tace “gashi yayan mu, rama mana da wanan tunda baka iya fadaba, yimai shegen duka da wanan” tamikamai rigan, karban rigan yayi yana kallon fuskarta, nunamai Khamis din tayi tace “zaneshi karka ragamai, ko akotu irinsu bulala tamanin ake musu kaima yimai 80” da sauri ya kalleta yace “80?” kallonshi tayi akaro nabiyu idanunsu yakara sarkewa faduwa gabanta yayi hakan yasa ta kyafkyafta ido sau biyu ta gyadamai kai batare data iya magana ba ta kawad dakanta, ahankali Aliyu yakarasa inda Khamis din yake azube yana sosa ido ya daddage ya shaudamai ihu yayi. “Aliyu wlh idan idanuna suka bude saina kasheka dagakai har shegiyan na…” zubamai nabiyu Aliyu yayi da karfi hakan yasa Rauda ta rungume Aneesa cikeda murna suka shiga tsalle kaman sunsan juna Aneesa harda tafi wani masifar dadi takeji fiye da tunanin mutum, cigaba da dukanshi Aliyu yayi da rigan sunamai tafi itada Rauda harya yarda rigan ya zauna agefe yana haki yagaji, da sauri ta kalli Rauda tace “ina zuwa bari kuga” da sauri tabude gate tafita jakanta tabude ta ciro wani kwababben bakin lalle da mai saida lallenta yahada mata as sample dan kafin tasiya saitasa ya dama mata tadanyi Zane kadan a hannunta ta wanke dan taga iya bakinshi dan kwanaki tasai lalle ko kadan baya baki dudda hydrogen din datake zubamai, shigowa tayi da sauri rike da ledan lallin ta kalli Aliyu tace “Yayan mu daga shi ka zaunar dashi kaga” kasa mata musu Aliyu yayi Yajuya yadago Khamis din da karfi ya zaunar dashi, tace “yauwa rikemin hanunshi tabaya” tsayawa abayanshi Aliyu yayi yarike hanunshi gam, da kyar Khamis dabaya iya bude ido ke magana yace “wlh duk kun shiga uku koba yauba yau ranan kuc….” bai karasa maganan ba Rauda tazare flat shoe kafarta tai bugamai abaki aiko sai jini, dariya sosai Aneesa tayi dayasa dimples dinta lotsawa tana kallon Raudan tace “dama kinada karfin nan tuntuni kiketamai kuka matsoraciya” takarashe maganan tana dariya sosai kafeta da ido Aliyu yayi ko kyafta ido bayayi kaman ance ta kalli gabanta suka kara hada ido shiru tayi ta saukar da idanunta kasa tadan matsa gaban Khamis din sosai kirjinta na bugawa tana gyara bakin ledan lallen, ahankali ta shiga zanamai bullen mage tundaga gefen bakinshi har zuwa wajen sajenshi uku uku sanan taja wani dogon layi tundaga kan hancinshi har zuwa goshinshi shidai Khamis sanyi sanyi da waiwayi waiwayi yakeji akan fuskarshi amma yarasa me akemai, fashewa da dariya sosai Rauda tayi ganin abinda Aneesa tamai harda bubbuga kafa akasa kaman ba itace tagama kukaba da barkakken riganta, mikewa tsaye Aneesan tayi itama tana kallon fuskanshi ta harari Rauda cikeda murmushi tace “am happy you are now smiling nidai nagudu gida, you guys should run for your lives, kugudu kafin idanunshi subude” ta kwasa da gudu tabude Gate tafita da sauri Rauda tabita tana kwala mata kira tace “baiwar Allah, baiwar Allah baki fadamin sunanki ba to” juyowa Aneesa dake kwashe kayanta nakasa awajen Gate din tayi ta kalli Raudan tai murmushi tareda rataya jakanta akafada tace “sunana Nana Fateema” “can we be friends? Inason ki sosai you are so bold wat a fearless lady, a ina kike? Inane gidan ku? Anan Suleja kike?” Rauda tai maganan tana karasowa gabanta murmushi tasakeyi zatai magana idanunta suka sarke dana Aliyu dake tsaye jikin Gate yazuba mata idanu hanunshi zube a aljihun riganshi yana kallonta sosai gabanta yafadi, dan kyafkyafta ido tayi tana kallonshi kafin ta juya da sauri tama Rauda waving hannu tace “bye Friend” daidai lokacin keke napep na zuwa tareshi tayi ta shiga ciki sukai gaba dukansu tsayawa sukayi a inda suke sukabi keke napep din da kallo har yafita daga layin.
[4/5, 8:05 AM] Hijabi_muslimah????: A TSAKANKANIN SOYAYYA

         _IN BETWEEN THE LOVE_
        ❤ _Lies another love_❤




        _✍????M Shakur_



                    1️⃣0️⃣

How to subscribe

zaki turo 300 ta account number na 3107021073 aisha Muhammad first bank, saiki turo evidence of payment ta WhatsApp number na 07012181461, you can also send MTN card ta watsap number na 07012181461, sainai adding naki a group din danake posting

Free page
Cigaba da buga kwallon yayi ko ajikinshi dudda dai yanajin yanda hayaniya ke tashi daga falon Dady amma ko agefen kumatunshi, sauran matayenshi Dady sai bude kofa suke suna fitowa suna tafiya falon Dady, tabe baki yayi yace “I hate this house with passion” cigaba da buga kwallon shi yayi yana wuwurgawa a backboard din dake wurin.

Azuciye Maman su Rauda tafito daga falon Dady tana tafiya kaman ana ingizata tana yowa inda Aliyu ke buga kwallon shi hankali kwance, kwallon yadaga zai wurga cikin backboard tawani irin sha gabanshi tanamai wani matsiyacin kallo kaman zata kasheshi, kwallon hanunshi ya kalla ganin yanda tasha gabanshi yasa yadan yatsine fuska yace “Opssss” “Aliyu” takira sunanshi dawani irin kakkausar murya hakan yasa ya kalleta tareda daga gira daya alamun me? Wani irin cizan labbanta tayi tace “till today Aliyu banma taba nuna nasan da existence dinkaba, ba ruwana dakai sanan naraba yarana dakai, kayi mugun kuskure daka shigo gonata wanan karan dan Wallahi bazan taba yafemaka ba tunda kai, kai Aliyu, kasa Alhaji yafasa hada auren nan tsakanin Rauda da Khamis wlh sainasa ka yabama aya zakinta, me ruwanka ina ruwanka da sabgarsu? This children are cousins, yau koda fyade Khamisu yama Rauda mai ruwanka d’and’an yayatane sai mene? Meruwan ka bashi zai aureta ba, you’ve messed with the devil itself this time around Aliyu and you are going to pay darely wlh” dan murmushi yayi yadan wurga kwallonshi sama tareda chabewa yamata wani irin kallo irin na yan iskan sangartattun yaran nan yace “oh really?” dan murmushi yayi yamata pointing bayanta wurin backboard din kwallon shi yace “excuse me Ma’am” kwafa tayi ganin yanda yake mata isgilanci, yatsunta biyu tanuna idanunta dashi tace “watch out for me Aliyu just watch out” tai gaba cikeda bala’i tadade rabonta datai fushi haka, yanda sukaci burin bikin nan dan so sukayi bayan bikinsu ta kalallame Alhaji tasamu yabama Khamis daya daga cikin kamfanoninshi amma yanzu Aliyu ya watsar musu da plan, fitowar yayar tata da Khamis da idanunshi sukai jajir fuskarnan yasha bullen mage yasa ta tsaya turus tana kallonsu tace “Yaya kiyakuri dan Allah” hannu yayar nata ta daga mata tana kallon yanda Aliyu ke buga kwallo abinshi a tsakar gidan ko kallonsu bayayi cikin fushi da kunar rai Khamis dake kallon Aliyun shima yace “wlh, wlh Mummy saina kas….” da sauri Yayar Mama tasa hanunta ta taushe bakin Khamis din tace “wuce mutafi” janshi sukayi dukansu maman su Rauda tabude musu mota suka shiga tana daga musu hannu tace “Yaya kiyakuri zan shawo kan Alhaji yanzu ranshi abace ne, itakuma aidai nasan ba’a shashin baban nata zata kwana badai ko, to zata fito zata samenine wlh na lahira saiya fita jin dadi” dan murmushi yayan tayi tace “karki damu Kareema zamuyi waya, muje driver” tama driver daya tukosu magana yaja motar, bin motarsu Mama taida kallo harya bace daga gidan, fitowa sauran matan Alhaji sukayi tsaki Amaryan Alhaji tayi datazo zata wuce tana habaici tace “ci akace yarana kedashi kaman gara, Alhamdulillah bandai haifi munafuka ba cikinsu mai siding da enemy, mtsssss” taja tsaki tawuce flat dinta tana turoma Mama dankwalin kanta gaba, bata gama dawowa daga iskancin da amaryan Dady tamata ba dayar matan Dady itama tazo zata wuce saida tazo daidai gabanta tace “Allah Bani kudi insai gida inje aikin hajji, ayiriririiii” taja guda, kafin ta kalleta tadan tabe baki tace “saifa hakuri fa, matsalan haifan munafuka kenan wlh natausaya miki Kareema, oh ni yatsu Allah dai yasa kar hawan jini yakamaki fasa auren nan dakika gama yadama duniya ai jarfa ne” wani irin harara Mama ta watsa mata danji take kaman ta zubamata duka tace “kyaga hawan jini baniba kinji Maimuna” baki matar tabude saikuma tasa hannu tarufe bakin tana kallonta kafin ahankali ta zare hanun daga bakinta tana wani irin munafikin murmushi tace “wai da zafi haka hajiya uwargida? Maida wukar, amma wlh kinban tausayi, sai kinayi kina tofama Rauda ayatul kursiyu inba hakaba ta shirya tozartaki ta kwance miki zani a kasuwa musha kallo” “Maimuna! Ya isheki, Ya isheki, wlh kikace zaki shigo harkana wuya zaki sha, ni dakalin majina ce wlh duk wanda yahauni saiya fado na rantse miki, kawai kifita daga harkata fakat” wani bazan kallo Maimuna tamata tace “baridai nabarki karki mutu a hannuna nasan kina cikin tsananin bakin ciki, mtssss” itama taja mata tsaki tawuce flat dinta kwafa Mama tayi tahaura dan stairs din gaban flat dinta shiga dakinsu, wani irin fadawa tayi kan kujera tana bubbuga gaban goshinta, fitowa Hajar tayi daga kitchen dinsu dauke da bowl din Indomie data gama dafawa da 2 boiled eggs, ajiye bowl din Indomie tayi kan kujera tazo inda maman su takeda sauri ganin yanda take bubbuga goshinta tace “Mama menene? Maiya sameki menene Mama?” cikin wani irin low voice na wacce ke cikin tsananin damuwa tace “give me water Hajar?” da sauri tajuya fridge taje tadauko mata bottle water tabude ta tsayaya a cup tamika mata, karba tayi ta shanye duka ta mika mata cup din tace “karamin” kara mata ruwan tayi tasake shanyewa ta ijiye cup din ta buga uban tagumi, tsugunnawa Hajar tai kaman zatai kuka ta dafata tana kallon fuskarta tace “Mama menene? Meya faru? Maiya sameki, keda Dady ne kosu Anty Amarya?” girgiza matakai Mama tayi ahankali kafin ta fuzar da iska tasa hannu ta sharce dan guntun hawaye dayake neman zubo mata daga ido tayi, da sauri Hajar ta rungume ta tace “Mama menene kike kuka? Meya faru bakida lafiya ne?” girgiza matakai Mama tayi ahankali tace “a’a lafiya ta kalau Hajara, Rauda ce Hajar” “Rauda Mama? Mekuma tayi ni banmaga shigowanta ba nadaiga fitan ta dazu lokacin ina kitchen ina dafama su Ihsan Indomie kafin sutafi islamiyya, meta miki Mama?” cijan lebe Mama tayi tana wani irin karkada kafa cikeda takaicin abinda Rauda tayi tace “koma me Khamis yama Rauda dasuka fita dazu basai takirani ni mahaifiyarta tafada minba? Amma saita kama tana kiran Aliyu tunda kanin uwartane wai Khamis wants to rape her, shikuma yagayama babanku harda karawa da baza’a bama Khamis auren nataba, yanzu ubanku yace aure fa ata fafur, Hajar bansan mesa yarinyar nan ta dauko jinin ubanku ba ko kadan bata biyoni ba wanan wata irin munafukar makiran yarinya na haifa hakane? Ke kinsan uban burin danaci kan bikin nan amma ta hargitsamin komi wlh duk kishiyoyina sai habaici sukemin abin yadawomin abin kunya, Yaya zanyi eh Hajar Yaya zanyi da Rauda wai iyye?” tai maganan tana sake share hawayen dake zubowa dan sun kasa tsayawa, rungume ta Hajar tayi sosai tana bubbuga bayanta, kaman zatai kuka tace “Mama kiyakuri dan Allah kinji, ai zata dawo daki batada wurin kwana daya wuce nan, so karki damu idan kika mata shegen duka saita tsorata musata taje tafadama Dady da kanta cewa zata aureshi tana son shi, don’t worry Mama” Hajar tai maganan tana rungumeta cikeda tausayin mahaifiyar nata.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57Next page

Leave a Reply

Back to top button