A TSAKANKANIN SOYAYYA HAUSA NOVEL
Gamawa tayi tsaf sanan tajuyo zata bata wayan gani tayi sai leka wayan take tasa yatsa abaki tana taunawa tana murmushi tsabagen jin dadi, dariya ne ya kwashe amaryan da karfi hakan yasa akunyace Aneesa ta zare yatsan daga bakinta tana murmushi, mika mata wayan Amarya tayi tace “gashi nan yanzu saisu fara WhatsApp ko ga films nan ma duk ke kadai” cikin murna Aneesa tace “zanyi kallo yau, nagode sosai Anty, kinada kirki” gaban wani dankareren gida mai tapkeken Gate driver yay parking batare daya shiga cikiba, bude motan sukayi suka fiffito Aneesa ma tafito tana kallon wagegen gidan, fitowa kanwar tata tayi itama ta maida kofar tarufe amaryan tadubi Aneesa tace “mu shiga ciki” tabude Gate Aneesa biye da ita sai kanwar abayan su hadadden gidane babban gaske ashe saisa taga sunyi parkin a waje dan gidan cike yake da mutane da kuma canopy da aka mammakala ga kujeru mutane duk sun zauna akai, wani special canopy da aka shimfida babban rug ga pillows masu kyau jajaye sukaje amaryan tace “me kike bukata akawo miki, abinci, water drinks kokuma tea?” murmushi Aneesa tamata tace “a’a banjin yunwa abani ruwan zafi zan sa lalle ciki bayan nagama hadawa” gyada mata kai tayi ta kalli sister ta tace “ki zauna da Aneesa Nihal, lemme go and change zansa akawo miki ruwan” gyadamata kai tayi tawuce tajuya tai hanyar wani babban flat bata wani jima da shigaba saiga wata kaman yar aiki takwo flask din ruwan zafi da empty bowl karba Aneesa tayi ta hada lallen ta tsaya ya ruwan zafin a bowl ta wurga lallen ciki sanan ta shiga hada sajen yar aikin tadau flask din yakoma dashi ciki Aneesa sai kalle kalle take gidan ba karamin kyau yamata ba, wayansu matane taga sunzo an jera kwaryaye sun zauna sun fara bubbugawa suna waka saitaga Amaryan da wasu manyan mata sun fito da ita duk suna rawa suna tahowa inda take zaune itadai sai kallon culture take tana murmushi kawota wurin akayi aka zauna da ita wata babban mace tace “mai lalli fara mata” daukan lallin tayi da zuzzuba a ledan dazata amfani dashi ta ijiye sanan tadau sajen ta matsa kusada ita, ahankali ta cire hijabin jikinta ta linke gudun karya ba tashi da lalle taja handglove tasaka sanan tadau kafar tafara zana mata ja atafin kafa, guda aka farayi ana rawa, wani irin shegen lalle take zanama amaryan dan she already promise to give it her best ne amaryan nada kirki babu wanda saima lallen datake mata kallo daya yawuce saiya tsaya yacigaba da kallo lallen yay kyau ne to the extreme.
[4/5, 8:05 AM] Hijabi_muslimah????: A TSAKANKANIN SOYAYYA
_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤
_✍????M Shakur_
1️⃣3️⃣ & 1️⃣4️⃣
Free page
Bata wani jima akan amaryan ba dayake tanada sauri tagama mata lallen tsaf ita kanta amaryan takasa dena kallon lallen da Aneesa tamata, Subhanallah tsarki ya tabbata ga ubangijin dayabama yarinyar nan gifted hands, murmushi Aneesan tayi tace “nagama Anty sai wane zanmawa?” da sauri kanwarta taja skirt dinta sama tace “ni ne Aneesa mai lalle” murmushi amaryan tayi tace “Aneesa kin mugun iya lalle, lallan ki bayama kama dana yan Nigeria, kina zana lalle kaman wata yar India, thank you Aneesa” murmushi tayi tana juya kanta tana zanama kanwar, kafeta da ido amaryan tayi sosai taji kawai Aneesa na burgeta she’s so innocent da bazama kaji baka sonta bane, da ace tanada Yaya namiji wanda baiyi aureba da wlh saitace ga mata tamai, kwantattcen gashin keyanta dana gaban goshinta ta kalla sabida dan kwalinta yadan zamiye gashin ya kwanta sosai gadan ruwa ruwa ajiki na zufa, bakin fatarta na glowing sosai, just look at her pink lips ko ita fara bazata nunama Aneesan pink lips da yan kananu gasu so soft, tender and so moist, sai kallon Aneesan take yanda take zanama Nihal lallen tana mata fira, akwai yanda idanunta keyi idan zatai magana saikaga sunyi wani irin luuu ga bakin dogayen gashin idanunta dake karama fuskanta kyau.
Gamawa da kafan Nihal tayi tsaf sanan tajuyo ta kalli Amaryan hada ido sukayi, murmushi tayi ta kalli kafar da hannayen tace “Anty naki yabushe kin iya wankewa kona wanke miki?” da sauri Nihal datai kaman zatai kuka tace “Anty please ki wanke da kanki takarasa min nawa kafin su Umma suzo su farayin nasu” hararan Nihal din tayi tai kwafa kafin tamike tsaye tace “don’t worry Aneesa karasa yimata sai kizo kici abinci kiyi salla kafin kicigaba, lado ma yaje dauko friends dina daga Airport saikiyi musu suma insun iso” gyadamata kai tayi ahankali ta karbi hanun Nihal ta cigaba da mata, batawani bata lokaci ba tagama yima Nihal tsaf ta ijiye lallen akasa tana sauke ajiyan zuciya murmushi Nihal tayi tana kallon lallen ta tace “thank you Aneesa kin iya lallen wlh, bantaba yin lalle mai kyau irin wanan ba, nagode kinji zan nunama baby idan yazo anjima” murmushi Aneesa tayi batare da tace mata komiba daidai lokacin yar aikin su ta taho wajen ta kalli Aneesa tace “muje Amarya tace nakawoki kiyi salla kici abinci” gyadamata kai tayi ta zare handglove din hanunta tadau hijabin ta dayar karaman jakanta tabi bayan yar aikin nasu sai kallonta akeyi kaman ansanta upstairs sukayi itadai sai kallon ko ina take bata taba ganin gidamai kyau hakaba wani daki yar aikin tabude ta shiga hakan yasa tabi bayanta amaryan na zaune kan gado daure da zani tanacin salad da fridge chicken akai, murmushi tayi ganin Aneesa tanuna mata bathroom tace “shiga ki dauro alwala” gyadamata kai tayi ta ijiye jakanta ta shiga da kyar dai tagane kan bayin tai abubuwan dazatayi tadauro alwala tafito babu kowa a dakin sai dadduma dataga an shimfida mata hawa kai tayi tai salla abinta ta sallame tana zaune kan dadduma ta kurama hoton pre wedding picture dinsu ido sun mata kyau, bude kofa da akayi yasa ta dago kanta yar aikin suce ta shigo dawani babban tray dake dauke da abinci almost kala hudu jellof rice ne sai moimoi mai kyau, da kuskus da miyan kubewa lafiyayyen abincin yan maiduguri sai waina d miyan taushe, baki tabude dan bata San inda zata saka uban abincin nanba jellof rice tadauka tafara ci tana kurban cold drink dinta abincin dadi hakan yasa taci iya cinta sanan ta ture tasha ruwa, bude kofa akayi aka shigo amaryan ne itada kawayenta murmushi tace “wai har kin koshi Aneesa?” gyadamata kai tayi ta kalli kawayenta tace “sun iso suzo muje namusu” kallonsu Amarya tayi tace “better kuyi yanzu kafin su Umma and her friends sufara” dunguma duk sukayi suka bita.
Haka tawuni tanama mutane lalle dabazata ma ita kirga adadin su ba salla kawai kedaga ta daga wurin kuma ko kadan bata gajiba sabida kayan dadin da aketa kawo mata tana tattaunawa, tana lallen sai kara gyara filin da za’ayi event din ake mata sai wanka suke suna saka wani anko na white and orange mai kyau, jin ana kiran magrib yasa tafara sauri tagama hanun matan datakemawa dan tafiya gida zatayi. Daidai lokacin Nihal ta iso taci gayu sosai an mata makeup tana sanye cikin ankon itama ganin Aneesa tsaye yasa tace “kin gama bazaki tsaya ki kalli event dinmu ba yanzu za’a fara fa su ango sunzo fa” girgixa mata kai tayi tace “ah a Ammi zatamin fada, tafiya zanyi” “muje to nakaiki wurin Anty makeup ake mata”
Tai maganan tanajan hanunta sukai wani flat daban inda Amarya take, babu kowa a part din sai amaryan da aka gama mata makeup ta sanya wani orange lapaya tai bala’in kyau tana waya, saikuma kawayenta dasuma sun saka anko irin na Nihal, ganin Aneesa yasa tace “baby am coming barina sallami mai lalle I will call you back” ta katse wayan ta taso daga kan gado tana murmushi tace “Aneesa kingama zaki tafi?” gyadamata kai tayi tace “eh” wani jakan souvenirs na bikin ta dauko tace “ganaki tsaraban bikin kikaima Mama” takama hanunta tasaka mata aciki sanan tadau jakanta ta bude taciro wayansu kudi yan dubu daidai ta kirga 30k ta zare ta mika mata tace “ga kudin lallinki mun gode” kasa karban kudin tayi hakan yasa takara kama hanunta tasa mata kudin adan rude kaman zatai kuka dan batasaba rike kudi dayawa hakaba tace “sunyi yawa kudin, lallen danayi baikai hakaba, please kirage Anty” duka yan matan dakin harda amaryan dariya suka shiga mata da kyar amaryan tai shiru tanunata da yatsa tace “kinga banison mu tsaya dogon zance magriba tayi nama Mama alkawari zan kula dake” ta fizge jakanta tareda kamo hanunta tacire kudin ta chusa ajakan ta zage jakan ta rataya mata a kafada ta kalli Nihal tace “jeda ita waje kicema Baba lado nace yamaida ta gida” ta kalli Aneesa da tama kasa magana tace “bi Nihal kuje amaida ke gida kinji nagode sosai ki gaidamin da Mama” gyadamata kai tayi ahankali tanaji kaman zatai kuka tace “nagode Anty, Allah sanya alheri sai anjiman ku” tadaga ma sauran kawayen hannu ahankali daga mata hannu sukayi suna atare sukace bye tabi bayan Nihal suka fita, kida sai tashi yake compound din yacika makil da jama’a gari yadan soma duhu amma ba sosai ba amma ko ina wutan lantarki ne bauuuu ya haska ka ko ina kana ganin bikin kasan bikin manya ne, hanyar Gate sukayi Nihal tafice tana biyeda ita karo Nihal taci dawata babban mata mai jiki taci gayu tasa wani lace dake walkiya, harara ta watsama Nihal din tayi tace “ina zaki baki ganin gabanki ne mara kai?” sunnar dakai kasa Nihal tayi wanan yar baban tasu Anty Hindu tacika masifar fitina, ahankali tace “Anty Hindu Anty ne ta aikeni zan kai mai lallen nan wurin Baba lado ne yakaita gida” wani mugun kallo tamata tace “ga lado chan taje tasame shi yakaita baya komi hirama yake da abokanenshi, ke come with me I want you to serve my guest banson ma’aikata suyi serving nasu, yanzun nan suka iso daga Dubai” ta kalli Aneesa datai zuru zuru tana kallon yanda katuwar matar ke masifa tace “wuce mai lalle ga lado chan tafi yakaiki” tamata pointing inda driver yake cikin tulin uban motocin dake anguwan ya zauna akan boot din mota shida wasu maza guda biyu suna hira, ta kalli Nihal tace “wuce mutafi” tai ciki waving hannu Nihal tamata tace “sorry Aneesa kije wajen ladon ai yasanki kuma yasan dama zai maidake gida, bye mungode” gyadamata kai tayi ahankali Nihal tai murmushi. “Nihal!” Anty Hindu ta leko tana hura hanci da sauri tabita tace “ganinan Anty” tawuce sukai ciki binsu Aneesa tai da kallo kafin ta sauke ajiyan zuciya gabanta sai faduwa yake duk ma wani tsoro tsoro takeji tarasa me yasa ita dayakamata taita murna yau tai lallen da aka kirgo dubu dubu har dubu talatin aka bata amma bataji ba, ajiyan zuciya tasauke tadaga kafa ahankali tafara tafiya tana dumfaran inda su Baba ladon suke, anguwan motoci sai shigowa suke ana parking ana sauka ana shiga gidan bikin, gani tayi lado ya dirko daga saman motan ya danna key yabude motan zai shiga da sauri takara sauri, gani tayi ya shiga sauran ma sun shiga yatada motar yayo reverse da gudu ta daga kafa bataso tai ihu dan mutane sunyi yawa gashi duk yan gayu ba kaman itaba datasha hijabi har kasa ba, ganin yajuya motar yasa tasa gudu amma kafin takai yaja mota dasauri rabi motar amma harya tafi hakan yasa ta tsaya chak kirjinta nawani irin bugawa not knowing what to do, ringing dataji wayarta nayi yasa ta kalli Jakarta da sauri zata ciro jakan tabude tacire wayarta aka wani irin danna mata horn daya mugun tsorata ta dan atsakiyan titi take, da gudu ta koma baya duk internal organs dinta na rawa ta jingina da wata mota, zip din jakarta ta zage ta ciro wayar data shiga kuka akaro na biyu ganin number Ammi ne yasa taja tai picking da sauri takara a kunne, kafin ma tai magana Ammi tace “bakisan dare yayi bako Aneesa, mena cemiki? Banace miki duk inda kike ko a ina kike kidena kaiwa magriba ba? Once kinga hudu tayi start preparing to come back home ba abinda nasha fadamiki kenan ba?” Ammi takarashe maganan tana mata ihu dayasa jikinta yakama rawa, in this world Ammi is her best friend yet babu masifa da fadan wacce take tsoro aduniyan nan irin na Ammi, intai laifi Ammi na fada har kuka take dudda batada yawan kuka amma wani zubin kafin ma Ammi tafara fadan tafara kuka tsabagen tsoron fadan Ammi. “ninake miki magana kikamin shiru Aneesa?” da sauri ta girgixa kai bakinta har rawa yake tace “Ammi wlh bahaka bane, nama fito but kafin nazo driver yafita kuma ina waje, Ammi am sorry” jin yanda muryan ta ke rawa yasa Ammi tadan sassauta karta rudata tace “to kikoma kice musu driver yafita susa wani yadawo min dake gida dare nayi yi maza” da sauri ta gyadakai tace “tom” ta katse wayan tajuya da sauri tai hanyar gidan, wasu manya manyan security har guda hudu tagani agaban gate din wanda basu dazu data fito, duk mutanen dazasu shiga gidan saisun nuna musu wani abu dabata san kome ba sai taga sun matsa musu sun wuce ciki gashi kida sai tashi yake, karasawa tayi suka sha gabanta. “Madam show us your invite?” da sauri ta kalli wanda yamata maganan kaman wacce bata iya magana ba ararrabe tace “I…n…v..ite?” gyadamata kai yayi yace “yes your event pass, show us” da sauri tace “amaryan zan gani nice mai lallen su” “we don’t know dat one madam kindly leave here if you don’t have invite, only invitees can grace this occasion, sorry Ma” yay maganan while sauran na duba invite din wasu suna basu wuri suna shiga, kallon abinda ake nuna musu tayi taga katin bikin amma wani hadadden dan karami ne. “madam kindly leave, this event is strictly kan wayanda aka gayyata, leave so that we will not have to force you leave” yanda yamata maganan yasa yasa tajuya ahankali, hankalin ta dukya tashi komawa tayi jikin motan data tsaya dazu taciro wayarta hanunta na rawa sosai tai dailing number Ammi tana sake shigewa dan lungun space din in between car to car dake pake a wurin, ta tsugunna ahankali, picking call din Ammi tayi hakan yasa taji wani kuka yazo mata dabatasan daga ina yazoba, sakin kukan tayi sosai hakan yamugun dagama Ammi hankali. “innalillahi, ke Aneesa, are you okay? Maiya faru? menene kike kuka? Talk to me dena kukan kinji, Aneesa menene?” cikin kuka sosai bakinta na rawa tace “Am… Ammi anhanani shiga gidan, ansa security a kofar gidan saika nuna ID card din bikin za’a bari kashiga ni bandashi basu barni na shiga ba?”