A TSAKANKANIN SOYAYYA HAUSA NOVEL
Ba karamin faduwa gabanta yayiba jin kalaman dasuka fito daga bakinshi, rawa lips dinta yafara tanadan zaro idanu zatai magana yamika hanunshi ya karbi wayanta dake kan hanunta ya bude ganin ba key, danne danne ya shiga yi kafin ahankali yamika mata wayan yace “take” hanunta tamiko ta karbi wayan da sauri tajuya tai cikin gida tarufo kofa, hakanan yaji ko kadan baiji dadi data tafiba kaman yabita, komawa cikin mota yayi yabude ya shiga, kifa kanshi yayi akan starring mota ya fuzar da iska he seriously don’t know what’s wrong with him, tun daga fitowan Aneesa daga gidan bikin tareda Nihal idanunshi suka sauka akanta lokacin yana tareda Abdul a cikin mota, Abdul yacemai sutafi yace yaje shizai shigo anjima, haka ya dinga kallonta ta mota har lokacin databi motan su Lado da gudu da lokacin data shige lungun mota da lokacin data fara kuka tana waya, shidai baisan mesa ba he just love natsuwar yarinyar, yanda take tafiya a natse, da yanda take magana a natse, da yanda muryanta ke fita so gently and innocently bala’in burgeshi yake, boldness din yarinyar use to melt his heart, bai taba ganin yarinya dat match his taste like her ba, hakanan yaji he just wanna be her friend, a girl like her is worth associating himself with, wayarshi dayay kara yasa ya kalli wayan ganin Dad ne yasa ya ijiye wayan yasan fada Dady zai fara baifito da bodyguard dinshiba, tada motar yayi yaja yana lumlunshe ido he’s so tired dan driving dinan dayayi, and he’s so sleepy Allah dai yakaishi gida lpy kawai.
Dakinsu ta shiga da sauri Ammi tace “meya daddar dake haka?” rasa abinda zatace ma Ammi tayi hakan yasa ta shiga kame kame kafin tace “uhmm Maman Muhammad ne ta shiga wanka saida najirata tafito fa Ammi” tai maganan tana hawa kan kujera dayake tanada tsawo tana hawa takai ta makala kwan lantarkin aiko wuta yakawo sanan ta sauko, dakinta tayi tacire kaya tadauro zani tafito, tsakar gida tawuce tadau bucket tajuye ruwan zafin da Ammi tadaura ta shiga bayi tayo wanka tareda dauro alwala fitowa tayi tawuce ta shige dakinta wani dogon rigan atampa tasaka sanan tadau hijabi tafito Ammi dake binta da kallo tace “bakiyi salla ba?” gyadamata kai tayi tana hawa kan dadduma tace “banyiba” magrib da isha tayi bayan ta idar tai shafa’i da wuturi, sanan ta cire hijabin tana sauke ajiyan zuciya ta kwanta akasa tana mikama Ammi kafafunta a shagwabe tace “wash Ammi kafana ciwo” murmushi Ammi tayi ta karbi kafafun ta daura kan cinyanta tace “raguwa kawai” matse kafafun nata ta shiga yi hakan yasa ta lumshe idanu wani mugun bacci na neman dibanta, kafeta da idanu Ammi tayi tana kara godema Allah daya bata yarinya mai natsuwa ga hankali, Aneesa is just a gift to her life duk rashin jinta inhar tace tak to ta natsu, she just pray Allah yabata miji nagari dazai kula da ita yabata all that she deserves, karasa matse kafafun tayi sanan tadan bubbugata ganin tai bacci. “Aneesa, Aneesa, tashi kije ki kwanta” bude idanu tayi dake cikeda bacci ta kalli Ammi, Ammi tace “tashi kije ki kwanta sannu yau mata sun aikatu” murmushi tayi ta mike tsaye tana tafiya ahankali tawuce, wayarta tadauka dake kan kujera ta wuce dakinta kwanciya tayi kan gado bayan tai bismillah sanan tai addu’an bacci wani bacci mai dadi yau awon gaba da ita.
“why, why Aneesa? I trusted you, mena miki da zaki kasheni eh? I trusted you Aneesa, you are my friend, we are friends remember? I love you Aneesa, why, why, why, why, dama kin tsaneni, dama so kike ki kasheni, why Aneesa?!” yadaka mata wani irin tsawa da duka karfinshi daya rage kumfa na fita daga bakinshi, idanunshi sunyi jajir yana kakarin mutuwa hawaye na bulbulowa ta gefen idanun. afirgice ta farka daga baccin daya kwsheta tana wani irin zufa komi na mafarkin datayi na dawo mata fresh, mutumin dazu tagani kumfa na fitowa daga bakinshi yana kakarin mutuwa yana mata all this maganganun itakuma tana gefenshi idanunta sunyi jajir sai kuka take ga ankwa a hanunta, batasan mesaba fashewa tayi da kuka sosai tana girgizakai, karan wayarta daya cika dakin yasa ta mugun firgita, da sauri tasa hannu ta goge hawayen daya bata mata fuska tamika hannu tadau wayarta dake gefen filon ta kalli screen din. “Aliyu” taga yana kira, faduwa gabanta yasake tazaro ido ta kalli time a jikin wayan 12:25Am.
[4/5, 8:09 AM] Hijabi_muslimah????: A TSAKANKANIN SOYAYYA
_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤
_✍????M Shakur_
1️⃣6️⃣
How to subscribe
zaki turo 300 ta account number na 3107021073 aisha Muhammad first bank, saiki turo evidence of payment ta watsapp number na 07012181461 sainai adding naki a group din danake posting. You can also send MTN card ta watsapp number na 07012181461 for those dabasu da account
littafin nan na kudi ne, duk wacce takaranta batare data biyaba ban yafeba, pay anan ko pay alahira, your choice ????????♀️ gumina ne, hakkina ne inada iko akai
Gudun kar Ammi taji karan ringing wayar daya cika dakin da kara tafito tace me takeyi da waya ware haka, wayake kiranta this night yasa tai picking wayar da mugun sauri hana kokarin hadiye kuka datakeyi takai wayar kunnenta batare datai magana ba, ajiyan zuciya Aliyu daya kasa bacci tun dazu dudda mugun baccin da yakeji yakasa sai tunanin ta yakeyi yasauke ajiyan zuciya ganin tadauka, murya chan kasa mai kunshe da sakonni da dama wanda shi kanshi baisani ba yace “Aneesah are you sleeping?” girgiza mai kai tayi kafin ahankali muryanta narawa sosai tace “a…a’a” tashi yayi zaune daga kan gadon jin yanda muryanta ke rawa kaman wacce ke kuka, murya chan kasa yace “Hey, are you crying?” girgiza mai kai tayi tace “a’a” jin yanda muryanta kefita yasa yaji wani irin damuwa ya dira aranshi, cikeda damuwa yace “are you sick?” “no” ajiyan zuciya yasauke jin lafiyanta kalau yace “is Ammi sick?” girgixa mai kai tayi tace “n…noo” cikeda damuwa sosai yace “why are you crying then a irin wanan lokacin eh Friend?” magana takeso tayi saikuma tafashe da kuka sosai sabida yanda ta tuna mugun mafarkin datayi, tashi hankali shi yayi da sauri yace “kidena min kuka yana dagamin hankali, talk to me” kaman bada ita yakeba ta cigaba da rera kuka ahankali, katse wayar yayi da sauri danjin kukanta yake har jijiyoyin zuciyan shi, ya lumshe ido tareda jinginar da kanshi jikin gado ya fuzar da iska, he’s so damn worried sabida kukan dayaji tanayi zuciyarshi batada natsuwa, shi baimasan lokacin da zuciyarshi tafarajin damuwan wata aranshi ba sai akan Aneesa, tsaki yaja ya kalli wayan dayaketa jujjuyawa a hanunshi, sake dailing number ta yayi kaman zai katse saikuma ta dauka, murya chan kasa dake cikeda damuwa sosai yace “wats wrong with you Aneesa? Why are you crying?” murya chan kasa tace “babu komi” girgiza kai yayi yace “a’a, akwai abinda ke damunki tell me we are friends remember” yanda yake mata maganan ataushashe kaman mai lallshin ta shikuma ba lallshin yakeba yasa taji zuciyata ta natsu sosai. “tell me friend what is wrong with you? Why were you crying? Kinyi laifi ne Ammi tamiki fada?” hawayen fuskarta ta share tass kafin ahankali ta girgiza mai kai kaman yana gabanta tace “mafarki nayi” dan murmushi yayi for the first time tunda suka fara wayan yace “wat!! Mafarki kikayi kikema kuka haka?” dan murmushi yasake yi maidan sauti dayasa ta lumshe ido tabude su yace “you are one hella wired girl friend” yadanyi dariya kadan kaman ba Aliyu ba dat u hardly see him laugh, tsayar da dariyan yayi cikeda tsokana yace “tell me mafarkin mekika yi friend nima natayaki kukan to” juya idanunta tayi tareda dan turo baki a shagwabe tace “ai namiji baya kuka, kuma mafarkin tsoro ne sosai shiyasani kuka” cikin wani irin murya na shagwaba kaman yanda tayimai shima yace “frienddd come onnn is just a dream, just a dream” shiru tayi tasa hannu tadafe kirjinta heart dinta is beating way too fast sabida yanda takejin muryan shi, jin shima yay shiru kaman yana sauraron bugun zuciyan natane yasa tace “scary dream, very scary” gyara kwanciya yayi tareda jan bargo yana lallube kanshi dan sanyi yakeji gashi yakara karfin AC sosai, ahankali yace “scary how? Mafarkin is about wat?” da sauri tace “about you” hannu tadaura akan bakinta surprisingly dan bama tasan lokacin data fadi hakaba, gyara kwanciya yace “about me?” yay murmushi sosai yace “my friend had a scary dream about me, tell me about the dream, dodo nazama nazo nacinye ki kome am eager to know” girgiza kai tayi tana turo baki tace “ance babu kyau fadin bad dream” “but ai am your friend right Aneesah?” yatambayeta ahankali, faduwa gabanta yayi sabida yanda yay maganan, batasan lokacin data gyadamai kaiba tace “eh” murmushi yayi yace “alright, tell me, am all ears” shiru tayi na kusan 2min kafin tace “ni bansan meya faruba amma nai mafarkin na kasheka, but baka mutubafa amma nakasheka kumani bansan how ba, kumfa dai nata fitowa daga bakinka kana cemin mesa na tsaneka, maisa na tsaneka nakeson kasheka nikuma sai kuka nakeyi shine nafarka inata kuka” dariya yafashe dashi sosai harda dan dafe ciki, kaman zatai kuka tace “da gaske nake fa stop laughing” jin yanda tai magana kaman zatai kuka yasa yahadiye dariyan yace “okay, lemme ask you some questions” gyara zama yayi yace “kin tsaneni ne?” girgixa mai kai tayi tace “a’a, niban tsani kowaba” dan lumshe ido yayi yabude yace “kin kasheni but ban mutuba, kumfa nafita daga bakina my God wat if kumfan brush ne na toothpaste kinyi tunanin hakan?” yakara kyalkyacewa dawata yar karaman dariya, yanda yake dariyan bakaramin burgeta yakeba hakan yasa tadanyi murmushi, dan shiru yayi yace “worried not, is just a dream kinji Boldest” gyadamai kai tayi ahankali kafin da sauri tace “waye Boldest?” murmushi yayi yace “you mana my friend, Aneesah the fearless lady maima mutum zanen mage a fuska” dariya tayi mai sauti kafin tai shiru shima shiru yayi yana listening to the sound of her laughter kafin chan murya chan kasa yace “inzo gobe?” ware ido tayi tace “kazo kayi mene? Ni Ammi bata barina fita naje wurin kowa, banda hakaba gobe bananan” dan shiru yayi hakanan yaji baiji dadin maganan datayi ba, baiso taje ko ina yafison yaga koda yaushe tana gida akillace, ahankali yace “ina zaki friend?” “zanje shagon danake aiki sanan zandau permission naje nai registration din jamb” da sauri tarufe bakinta tace “laaaa banfa sanka ba inata maka surutu and is not good kaitama strenger surutu?” girgiza kai yayi yace “am not strenger, kin sanni, and I know you, you helped my sister once, and am your friend, your brother dabaki dashi from today, so allow me to do my duty okay” gyadamai kai tayi ta kwanta tareda lumshe ido, ahankali yace “inzo gobe? Inaso na sake ganin kine” ahankali tace “to bari mugani goben to idan Allah yakaimu, saida safe” takatse wayar da sauri, zaro wayar yayi daga kunenshi yana kallo jiyayi kaman ta katse zuciyarshi baiso ko kadan yadena jin muryanta, fuzar da iska yayi ya ijiye wayan ya kwanta yay shiru yana kallon saman dakinshi tunanin Aneesa yake banawasa ba, he really like the girl, yanason everything about her, he just wanna be her friend and take care of her and always support her kaman yar kanwar shi, tunanin Aneesa ya dinga yi har bacci yay awon gaba dashi.