A TSAKANKANIN SOYAYYA HAUSA NOVEL

A TSAKANKANIN SOYAYYA HAUSA NOVEL

Suleja, Nigeria.

Dan babban falone dake shimfide da ledan daki brown mai gida gida, ga saitin kujeru na daidai rufin asiri masha Allah dakin sai kamshin turaren wuta yake ko ina tsaf tsaf babu ko digon datti, wata matace a tsakar dakin dake kan dadduma tana salla, kana ganinta kasan tadan kwan biyu a duniya tanada jiki sosai, sallame sallan tayi cikeda natsuwa sanan ta daga kai ta kalli agogon bangon dakin tana istigifari, karfe 9:08AM, karfe tara harda minti takwas na safe, tashi tayi daga kan dadduman tadau charbinta tarike tafara tafiya ta doshi kofan fita daga dakin, yaye labule tayi ta leko tsakar gidan da maganganu kasa kasa ketashi wata matace zaune kan tabarma a tsakar gidan babu hijabi a jikinta, kafafun ta da aka zana mata bakin lalle irin na amare dayay mugun kyau ta daura kafafun kan wata yar pillow datai bakin kirin wacce kana ganinta kasan na lalle ne, ta mikar da kafafun anja skirt dinta sama har zuwa wajen gwuiwanta sabida lallen, sai kuma hannu ta na haggu da shima ta mikar dan yasha iska shima ba’a gama da zana mata shiba dan baima soma shirin bushewaba, sai kuma dayan hanunta da ke hannun mai zanen lallen tana zana mata. “Aneesah” da sauri yarinya data dukufa tana zanama matan lalle ta dago kanta da sauri ta waigo, bakar yarinya ce full definition of melanin skin, wani irin glowing dark skin take dashi dake shining bana wasaba, giranta a cike da gashin gira har giran na neman hadewa dan in between space din two giran ma gashine sai dan tawadiyan Allah a tsakiyansu dayay ma fuskarta kyau bana wasaba, tanada dogon hanci sosai kaman karas, kwayan idanunta farare fat kaman madara sabida hasken su, gashin idanunta bakake dogaye wara wara dasu, sai dan lips dinta dakenan pink sosai dayakara haska fuskarta, gefen fuskarta dogayen sajene lub lub a kwance, kanta sanye da bakin hula, kunenta babu dan kunne sai gashin keyanta dakenan a kwance lub lub wasu sunyi coils, kana ganin yarinyar kasan she’s so hairy, tana sanye da wata bakar rigan atampa. “Aneesah” Mahaifiyar tata takara kiranta akaro na biyu tana fitowa daga dakin gabaki daya rike da charbin hanunta ta tsaya agaban dakin, da sauri ta ware manyan fararen idanunta ta kalli Maman nata tace “na’am Ammi” “bakigama lallen ba kinsan karfe nawa kuwa tara harda yan kai” zaro ido tayi dan batasan lokaci yaja hakaba adan rude tace “innalillahi Ammi nayi latti, Madam yau zatamin fada, yanzun nan zan gama mata” tai maganan tana gyara xaman lallen a hanunta tacigaba da zanama matar lalle agurguje, ganin yanda take sauri yasa Ammi tace “ki kwantar da hankalinki kimata atsanake kar ayi shirme” gyadama mahaifiyar nata kai tayi tacigaba dayi anatse, komawa daki Ammi tayi dan xigaba da zikirinta.
Ko 5min bata karaba tagama yimata lallen tai murmushi tana kallon hannun tace “ki zauna anan yanzun nan zai bushe, zan jamiki ruwan dazaki wanke dashi inya bushe, ni yanzu wanka zanyi natafi wurin aiki” murmushi matar tayi tana kara kallon lallen nata dayay mata kyau bana wasaba mussamman ma tasan idan Baban Aisha yadawo daga lagos yau saiya yaba lallen shima dan yanason lalle shi arayuwanshi, tashi tayi a gurguje tai wajen rijiya ta kwalama Mamanta kira. “Ammi nagama zanja ruwa nai wanke wanken sainai wanka natafi” Ammi dake kan dadduma tana jan charbi tace “kibar wanke wanken zanyi, ja ruwa kawai kitafi wajen aikin ki kinyi latti dayawa” guga tadauka tazura a rijiyan tace “tom Ammi” a gurguje taja ruwan tacika botikin takai gefe ta ijiye ta kalli matar datama lallen tace “ga ruwan ki nan” ruwan data ijiye mata agefe matar ta kalla tai murmushi tace “nagode Aneesa” murmushi tayi daya kara mata kyau tadau ruwan wankanta data jawo takai gaban kitchen dinsu ta ijiye kitchen dinsu ta shiga tadau tsumman cire abu awuta tadauko tukunyar dake kan rushi tafito ta juye ruwan zafin a cikin botikin ta ijiye tukunyar tadau ruwan tai bayi. Bata wani jimaba tafito da sauri tana sharce ruwan fuskarta fatarta sai shining take sabida wankan datayi, dakinsu ta shiga har lokacin Ammi nakan dadduma hakan yasa ta wuce ta shiga wani daki wanda yakenan dan karamin gado ne adakin sai wani tsohon sip, sip din ta bude ta ciro doguwan rigan atampa da wani farin gogaggen hijabi, shiryawa tayi tsaf tasaka kayan bayan ta shafa mai, wani irin cool kyau kayan sukamata doguwan rigan saiya kara fito da tsayinta sosai dan dagowa ce, hijabin ta warware ta saka batare data tsaya su shafe shafeba dantai latti, hijabin yay ma fusjarta kyau, hulan ya zauna akanta sosai tadau yar karaman crossing bag dinta ta rataya tafito ta kalli Ammi tace “Ammi natafi” “adawo lafiya, ki kula dakanki kinji” murmushi tayi tana daukan kofin kokon dake saman TV stand ta kurba ta ijiye hakan yasa Ammi dake binta da kallo tunda tafito tace “ki zauna kisha mana, kin tsaya kina kurban koko a tsaye” girgiza mata kai tayi tace “Ammi nai latti madam zatamin fada wlh, banama jin yunwan sosai, natafi Ammi kimana girki me dadi kinji” tai maganan tana fita daga dakin tana leken fuskan Ammin dantaji mezatace, binta Ammi tai da kallo batare datace komiba, tsakar gida tafita matar datama lallen tace “harkin fito, ga kudin lallen” ta mika mata yan dubu daidai guda biyu karasawa wajen tai akunyace ta mika hannu ta karba ganin dubu biyu ne yasa ta zari daya ta mika mata dayan tace “dubu dayane kudinki” kin karba matan tayi tace “wanan hadadden lallen kona amarya albarka shine zakice dubu daya, a’a nidai kirike to nabaki” murmushi tayi akunyace tace “nagode” “yauwa Aneesa mai lalle nima nagode adawo lpy” juyawa tayi takoma daki tai sallama ta shiga kudin tamikama Ammi tace “Ammi ga kudin lallen, natafi” ta juya harda dan gudunta harda dan gudunta tafita ta kalli matar tace “sai anjima” “adawo lpy Aneesa” fita tayi daga gidan, da sauri sauri take tafiya harta fita anguwan su ta tare keke napep abakin titi ta shiga d sauri tace ” Modest bakery & dessert home zaka kaini malam” tada keken yayi yace “naira dari zaki bada Hajiya” “muje” tacemai tana duba jakan ta dari taciro kudin tarike tana kalle kallen hanya, kusan tafiyan minti ashirin yakaisu wajen, Babban bakery ne sosai dakenan abakin express road, sauka tayi daga kan keken tamikamai kudin tajuya da sauri tai cikin wajen security bakin kofan ne yabude mata kofa yana kallon fuskarta kaman zai hadiyeta shidai arayuwan shi yana mugun son Aneesa yarinyar na burgeshi over amma haryau yakasa gaya mata, tun ranan da tafara zuwa wajen nan baya manta ranan itada mamanta sukazo tana sanye da wani pink hijabi har kasa tanata kalle kallen wurin, tun ranan yaji yarinyar ta shiga ranshi. Kawar da tunanin yayi daga ranshi yasakin mata murmushi mai kyau yace “ya akayi kikai latti haka Aneesa? Kije Madam na office dinta tace dazaran kinzo nace kisameta asama nasan fada zatamiki ki lauyance mata kice bakida lafiyane saisa kikai latti na tsani naga tanamiki fada” yay maganan yana kallon fuskarta cikeda damuwa, gyadamai kai tayi asanyaye tama kasa magana tsabagen yanda gaban ta ke faduwa, shiga ciki tayi tana kallon koina, few people ne zaune akan chairs da table dake zagaye a wurin some nacin cakes da drinks wasu kuma ice cream, karasawa gaban kanta tayi tabude ta shiga daidai lokacin wata ma’aikaciyar wajen mai suna Fatima tadauko two cup of ice creams data tsiyayo daga machine ganin Aneesa tsaye yasa tace “yauma kinyi latti ko, tun safe sai sintirin zuwa neman pancake dasu cakes ake barinma valvet amma bakizo da wuri kinyi ba, anyway kije Madam na kiranki yau ta sakko kasa tana duba kokinzo yafi sau hamsin” tai maganan tana daura ice cream cups din akan tray ta dauki tray din tafito dantaje takaima wayanda saukai order ice cream abinsu, sosai gabanta kefaduwa amma ta daure ta doshi stairs harta kai gaban office din madam din da aka rubuta CEO’s Office hanunta har rawa yake taciro daga hijabi ta kwankwasa kofan kaman wacce ke shirin guduwa, daga tacikin office din akace “yes, who is there?” bakinta har rawa rawa yake tace “i….is me, A.. Aneesa Ma” shiru akayi kafin chan ace “come inside” ahabkali ta murda handle din kofan ta shiga hadadden office ne da akai fentinshi fari sai uban haddadun office furnitures, wata matace da akalla zatai 45 zaune akan kujeran mai office, taci suit baki kanta dauke da attachment alamun ba musulma bace, sai wata mata da alamun bakuwarta ce zaune akan kujera duk suka zuba mata idanu kaman zasu hadiyeta da duka, kasa jure kallon dasuke mata tayi ta saukar da kanta tasa hannu ta goge zufan daya feso mata a goshi tace “good morning Ma” tadanyi shiru tana sauke ajiyan zuciya kafin ahankali cikin irin muryan mara gaskiyan nan tace “am sorry Ma, bazan kara zuwa latti ba daga yau, am sorry please” tai maganan ahankali kaman zatai kuka, biro Madam din tadauka ta shiga rubuce rubuce abinta ita bata bata izinin fita ba kuma batace mata kalaba, saida tai kusan minti biyar sanan ta dago ta kalleta tana tauna kan bironta saikuma ta janye byron daga bakinta tace “Aneesh” haka take kiran sunanta dan bata iyaba, adan tsorace tadago kanta ta kalleta tace “na’am” cikin fushi Madam tace “bazan jure wanan lazyness dinan nakiba do you know what it means a business customer yayta zuwa neman abu zai saya ana cemai babu?” tadanyi shiru tana kallon Aneesa data sunnar da kanta kasa tace “8 ne time dinki na zuwa aiki, come and make cake, meat pie, chicken pie, valvet and pancakes wanan shine aikin ki kawai a wurin nan amma baxaki zo da wuriba when you know most people have pancakes as breakfast, wat sort of unprofessional act is this? Coming late to work am not gonna take it, kunyan maman ki nakeji da tuni nakoreki, ga professional pastry chiefs nan all over Nigeria but because I want to help you, inajin tausayin mamanki I stick to you you this quack chief, and daga yanzu duk idan kika kara latti am going to deduct money from your salary stupid girl, get out my office kiwuce bakery and do your work, fita!” ta daka mata tsawa kaman tana koran kare, da sauri Aneesa ta juya tafita fararen idanunta har sunyi ja.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57Next page

Leave a Reply

Back to top button