A TSAKANKANIN SOYAYYA HAUSA NOVEL

A TSAKANKANIN SOYAYYA HAUSA NOVEL

Da kyar Ammi ta tadata da asuba tazo tai salla sanan tai karatun Al ‘Qur’ani, saida gari yawaye sanan ta wuce tadauko tsintsiya ta gyaro dakunoni ta sharo tafito da sharan waje sanan ta wuce kitchen tahura wuta tasa ruwan wanka awuta sanan tadau tsintsiyan ta sharo tsakar gidan, ta gyara ko ina sanan ta koma kitchen ruwan wankan tahada ta daura shinkafar da Ammi ta dafa jiya jiya dan dumamawa tawuce tafita daga kitchen din dauke da bucket din ruwan zafi taja ruwa daga rijiya tahada tawuce daki tacire kaya tafito tadau bucket din tai bayi bata wani jimaba tai wanka tafito sanan ta shiga kitchen ta sauke abincin ta daurama Ammi ruwan wanka tazuba nata abincin a plate sanan tafito tawuce kitchen afalo ta ijiye abincin kusada Ammi sanan tawuce dakinta ta shafa mai, shiryawa tayi cikin Riga da skirt nawata maroon atampa dayay mata kyau sosai ajiki sanan taciro gogagen hijabinta maroon tafito falo kafeta da idanu Ammi tayi tanabin kayan jikinta da kallo harta karaso wajen zama kusada Ammi tayi dake kan dadduma tace “Ammi na bazaki yi karin yanzu ba muyi tare” girgiza mata kai Ammi tayi tanajan charbi hakan yasa ta shiga cin abincin cikin yan mintoci kalilan tagama ta tashi takai plate din kitchen sanan tadawo daki tadau hijabin ta tasaka ba karamin kyau maroon din yamata ba ta dau jakanta ta sagala tana kallon agogo karfe bakwai da minti arba’in da biyar tace “Ammi natafi” gyadamata kai Ammi tayi dan bataso ta katse zikirin datakeyi juyawa tayi tai hanyar fita daga dakin harta sa kafa zata fita saikuma tadawo a shagwabe tafada jikin Ammin tace “nikimin addu’a Ammi” shafa addu’a Ammi tayi ta ijiye charbin tadan buge bayanta tace “inkin karyani aisaiki nemo wata Ammin ko” dariya tasaki tana tashi daga jikin Ammin tace “Ammi nifa banida nauyi fa” hararan ta Ammi tayi takama habarta takai yatsarta gefen idonta tace “jibi kwansa a ido, bakisan idan zakisa kwalli zaki ciccire kwansa bako” turo baki tayi Ammi takarasa cire mata harda na dayan idon sanan tasaki fuskarta tace “saikin dawo to, Allah ubangiji yabada sa’a, Allah ya tsaremin ke” wani irin cute smile dake mugun karama fuskarta kyau tasakin ma Ammi tace “Ameen Ammi na, nagode natafi” tashi tashi ta wuce tafita Ammi tabita da kallo zaure tayi tabude kofar gidansu tafita tana tafiya anatse as usual tana kallon hanya tana fatan Allah ya kado wani mai keke napep danyau jinkanta take bata da karfin daddarawa har express road da kafa.
Bata wani yi nisa da tafiya ba saiga keke napep tsareshi tayi ta shiga tace “express road Malam” kunna keken yayi yace “dari da hamsin ne Hajiya” “to muje” Jan keken yayi sukai gaba har gaban shagon su yasauketa tun kafin ta sauko Yusuf security dake bakin kofa ya tsareta da ido kaman zai hadiyeta dauke kai tayi ta sauko taciro kudi ta bashi sanan ta rataya jakanta back tafara tafiya tana dosan gaban shagon nasu, washe mata baki Yusuf yayi yana binta da kallo tundaga kan kafafun ta dake sanye da black socks har zuwa kan hulan hijabin ta daya kwanta akan fuskanta, numfashin shi har neman daukewa yake sabida tsananin bugawa da zuciyanshi keyi sabida ganin ta dayayi karasawa tayi jikin kofan kafin ma ta gaidashi yarigata. “barka da zuwa Aneesa gimbiyan mata, sarauniya mai farin jini” bayabo ba fallasa tace “ina kwana” tasa hannu zata bude kofan da kanta da sauri ya tare yace “tsaya nizan bude miki Gimbiya ai ba’a barin gimbiyoyi suyi aiki da kansu baki saniba?” Yay maganan yana lashe baki yana kallonta cikeda da dan masifa tace “kabude min zanje naga Madam ne Yusuf” da sauri yace “karki damu Madam batariga tazo ba akwai abinda nakeso nafada miki ne” jitayi kaman ta kwasa mishi mari mugun haushi Yusuf yake bata hakan yasa ta kawad da kanta gefe, ko damuwa baiyiba yacigaba yace “Aneesah dan Allah sonake kibani dama naturo gidanku wlh ina bala’in sonki, wlh matukar burgeni wlh narasa yazanyi da raina kiwa Allah kibani dama naturo” juyowa tayi tamai wani irin mugun kallo tace “Yusuf kaga ina baka girman ka ko to kakama kanka, babu wani na shagon nan dabaisan kana soyayya da Fatima ba, banson rigima kadena shigar dani harkan ku kuma kacire hanunka ka matsamin na shiga shago inba hakaba idan madam tazo tace maisa banfara aikiba zancen mata kaine kahanani shiga shago tun dazu” washe mata baki yayi yana wani irin mahaukacin murmushi masifan Aneesa na masifar burgeshi dan matsawa gefe yayi yace “Allah huci zuciyar gimbiyar raina ki……” bude kofar Fatima tayi daga ciki da fushi tana ma Aneesa wani matsiyacin kallo.
[4/5, 8:09 AM] Hijabi_muslimah????: A TSAKANKANIN SOYAYYA

         _IN BETWEEN THE LOVE_
        ❤ _Lies another love_❤




        _✍????M Shakur_



                    1️⃣7️⃣

how to subscribe

zaki turo 300 ta account number na 3107021073 aisha Muhammad first bank, saiki turo evidence of payment ta watsap number na 07012181461 sainai adding dinki a group din danake posting. Zaki iya turo katin MTN na dari uku ta watsap number na for those of you dabasu da account

littafinan na kudine duk wacce ta karanta batare data biyaba ban yafe mata ba, nabarta da Allah

Tawani rike kugu cikeda masifa tace “ban fadamiki kifita harkan Yusuf dinaba ba, Aneesa banson shishigi kije kinemi saurayin ki mana saikinmin snatching” hararanta Aneesa tayi kafin taja tsaki tabi ta gefenta tawuce ta shiga cikin shago abinta so take tai sauri tai baking snacks sabida dazaran madam tazo tabarta tayi, bakery ta shiga tadau rigan aikin ta ta daura kan rigan jikinta tadau mini hijab din tasaka sanan tafara aiki, shigowa bakery Fatima tayi ta tsaya a bayan Aneesa tace “nike miki magana zaki wuce kiyi gaba abinki?” ajiye whisk din dake hanunta Aneesa tayi ta kalli Fatiman tace “Fati wlh idan baki fita daga harkana ba zan miki mugun jina jina, saurayin ki Yusuf babu abinda zanyi dashi ko shine namijin karshen duniya kifita daga harkana nagaya miki” itama ihu Fatima tayi tana mata tafi aka tace “eh, eh, kema kifita daga harkana ihu mayyar saurayi, saurayi snatcher” Aneesa zatai magana taji wayanta na kara da sauri tai wajen jakan ta tabar Fatima na surutan ta, ciro wayar tayi daga jaka ganin Aliyu ne yasa bata dauka ba ta maida ta ijiye tareda jan dan karamin tsaki tawuce ta koma ta shiga buga egg dinta da whisk bata kara cema Fatima komiba harta gaji da bala’in tafita daga wurin, cakes tafara hadawa tasaka a oven sanan ta shiga yin dough nasu chicken pie. Wuraren sha daya ta gama bakin almost 100psc tai recording ta dauko tafito takawo ma Fatima agaban kanta takoma tafito da sauran sanan tawuce backyard ta wanko hanunta da kafarta sanan tafio tanaji wayanta na ringing tasan Aliyu ne yasa batama bi takan wayan ba tawuce tafita tai sama tawuce office din Madam, knocking tayi aka bata izinin shiga bude kofan tayi ahankali ta shiga Madam ta dago daga rubutun datake ta tsareta da ido tace “Anesh na you” gyadamata kai Aneesa tayi tace “good morning ma” ajiye biron Madam tayi tana dauko wani paper tana dubawa tace “morning, why are you here? Menene yakare a store dama naga sugar yay kasa da corn flour, menene babu?” dan sosa gefen fuskarta tayi dan dagajin yanda Madam ke magana tadauka wani abune babu tazo fada, mayar da kanta kasa tayi tana wasa da yatsunta ahankali tace “Ma, ummm dama, dama sonake naje nai registration din jamb nariga nagama baking shine nazo daukan permission dinki naje yanzun nan nadawo saina cigaba da komi” nan da nan dan annurin dake kan fuskar madam ya bace tace “dole saikinje yaune?” dan rage murya tayi tace “Baban mu yace naje yau” wani kallo Madam tamata tace “baban ku?” gyadamata kai tayi tace “eh kanin baban mu” dan tsaki Madam tayi tace “ince dan nasan babban ku yamutu, kinyi baking abinda zai isa” da sauri ta gyadakai tace “eh bazan wani dadeba tunda rana batayiba lokacin ne ake cika wurin yanzun nan zan dawo” tsaki madam takaraja dan ko kadan bata so ta tafi tace “okay nabaki 2hrs,yanzu is eleven by 1 ko highest 1: 30 kodawo kobaki gamaba dan I can’t stand loosing customers due to your negligence again yau” gyada mata kai tayi da sauri ta tsaya tana jiran tabata izinin fita, buga taburin madam tayi tace “bazaki wuceba bakisan time dinki kikeci ba” da sauri tajuya tafita daga office din tawuce kasa ta shiga rigan aikin da hijab din tacire tadau dogon hijabinta tasaka sanan tadau wayarta dake kan saman jaka tana dubawa 20miss calls datagani yasa tace “20” bude wayan tayi da sauri ta shiga gabaki daya 20 miss calls din duka na Aliyu ne, maida wayan tayi cikin jaka tace “to menene yaketa kirana haka” dan murmushi tayi taunawa da yace she’s his friend tawuce tafita daga dakin tace zan kiraka anjima inmun koma gida, Fatima nata kallonta kaman zata hadiyeta wajen kofa tayi da sauri Yusuf yabude mata yana kallon fuskarta yace “ina zaki Aneesa?” batare data kalleshi ba tace “inda ka aikeni” tayi wucewarta, binta da kallo yayi yarike baki dama Aneesa bata da kunya? Yatambayi kanshi kwafa yayi dan duk Fatima ce taja Aneesa dake bala’in girmamashi ta raina shi haka.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57Next page

Leave a Reply

Back to top button