A TSAKANKANIN SOYAYYA HAUSA NOVEL
Keke napep ta tare tace “Suleja ICT center zaka kaini malam” “hamsin, hau muje” hawa tayi dan batason tsayawa ciniki da masu abin hawa har gaban ICT center taje taga students dayawa duk yan registration din jamb, kudin tabiyashi ta wuce ta shiga ciki wayarta dake cikin jaka sai ringing yake.
Ciki ta shiga ko ina dalibai da kyar tasamu taje gaban kanta daya daga cikin ma’aikatan ta gaida tace “malam dan Allah nazo registration ne yaya zanyi?” zufan daya cika goshin shi ya goge dan wajen is so crowdy dudda akwai manya manyan fankoki amma kaman bakomi wani takarda ya nunamata yace “keji ki rubuta sunan ki, za’ayi ta kiranku according to numbers ne” gyadamai kai tayi tace “nagode” tawuce da sauri wajen paper dataga wasu dalibai na rubuta sunansu tsayawa tayi abayansu suka gama sawa sanan taciro byro daga jakanta ta matsa tareda daukan paper number 178 anan zata sa suna, kambu mutane har nawa agabanta itada awa biyu madam tabata sunanta tarubuta kaman wacce ke tsoron paper duk tunani ya kasheta. “Fateema Rufa’i Mai Kwato!” da sauri ta daga kanta jin ankira full name dinta ware ido tayi ganin wani malamin su daya koyar da ita tun daga SS1 a makaranta har zuwa SS3, shine malamin further mathematics dinsu, Malam Auwal Mazimaziz haka yan makaranta suka radamai ko maganan shi ake idan kace Malam Auwal baza’a taba ganewa ba saidai kace Mazimaziz kokuma kace dy/dx daga wani bene taga yake saukowa rikeda wasu takardu da yawa a hanunshi yana kallonta dogon namiji ne handsome black dashi yana sanye dawata faran yadi kanshi da hula yana kallonta murmushi tayi sosai tana kallonshi harya karaso mutumin data tambaya dazu yaje wurinshi yabashi takardun sanan yakaraso ta inda take akunyace tace “good morning Malam” murmushi yayi shima yace “good morning Fateema” murmushi tayi tace “Malam dama kananan” dan hararanta yayi yace “look at you tunda kukai waec da Neco muka sallameku kin kara waiwayan school kizo kidubamu ne? Inda kinzo aida kin gani ai mara zumunci kawai” a kunyace tarufe fuskar ta da Hijabi ita tai mamaki ma dayake mata fara’a haka Mazimaziz ai shine the most wicked Teacher a makarantan su, ko sajent saiya sallama mishi a iya duka, gashi ko test dinshi kafadi saiyay duka sunci dukanshi a makaranta kaman ba gobe. “jamb kikazo siya?” tambayar dayayi ya katse mata dan tunanin dataje da sauri ta gyada kai tace “eh nazo ai registration amma mutane nice number one hundred and seventy something” dan murmushi yayi yana zama akan kujeran gaban kantan yace “banda abinki ai da sassafe ake zuwa dan dalibai nada mugun yawa anan” dan zaro ido tayi kaman zatai kuka tace “bansani ba ne wlh” dan shiru yayi yana kallon fuskarta yanda tai kaman zatai kuka tana kallon wajen yanda aka cika ko ina. “Fateema” da sauri ta juyo ta kallai mikewa tsaye yayi yace “lemme see you off, kizo gobe da sassafe as early as seven zansa wani yay miki, ko yanzu ma aiki yamai yawane danasa yay miki but kizo gobe as early as seven fa kina jina” gyadamai kai tayi tana binshi abaya suna kukustawa dan fita daga wurin tace “okay sir” fitowa sukayi tana biyeda shi wani irin mummunan faduwa gabanta yayi Aliyu tagani tsaye yana sanye da jeans black dawani sky blue shirt yadan bude boturin kirjinshi idanunshi sanye da bakin glass ya rungume hannunshi a kirji dayake rikeda wayarshi Samsung galaxy fold, yana facing cafe din, yan matan premises din Cafe sai kallonshi suke dan yay bala’in yin kyau kaman bature, da sauri ta dauke kai daga kallonshi kirjinta na dukan uku uku ya akayi yasan tana nan? Ya akayi yabiyota? da sauri zuciyata yace a’a bake yabiyoba hala yakawo wanan kanwar tashine itama tai registration din jamb bake yabiyoba, dan ajiyan zuciya ta sauke. “Fateema kinajina kuwa?” Malam Auwal yamata tambayan da sauri ta dago kai ta kalleshi tace “sorry sa banji mekace ba” dan murmushi yayi yace “hayaniyan dalibai ne yay yawa but gobe idan kinzo ina jiran amsan kinji” da sauri tace “amsan mene malam?” dan shiru yayi yana mata wani kallon daza’a iya kirada naso yace “Fateema, tunda kikabar school I’ve been looking day and night for a way dazan hadu dake, from the first time dana taba shigowa ajinku a SS1 dan daukan ku further Maths Allah ya jarabceni da sonki Fateema, na yaba da natsuwanki ainun, kinada baiwa daba kowane zai iya sanin hakan ba, burin kowani kamilin namiji shine yasamu mace irinki a matsayin mata ya killaceta a gida a binshi babu mai ganin mai ita, tundaga SS1 nake rainon sonki har zuwa yau saisa kikaga nafi tsananta miki a aji kan kowa, in duka ne kece tafarko kuma alhamdulillah ina alfahari dan kin kasance daya daga cikin dalibai na dasuka fi kowa iya further maths a makarantan nan” tunda yafara ambato kalaman son nan ta saukar da kanta kasa dan wani kunya ma taji yabata aranta tace kagamin mugu yagama cin uban nawa a makaranta ne yanzu kuma yake sona. “Fateema” da sauri tadago kanta ta kallai tareda dan kakalo mai murmushi yace “bakice komiba” rasa mezata ce tayi sotake ta kalli inda Aliyu yake kuma har wani shakkun kallan wajen take zatai magana yadanyi dariya yace “don’t worry nagane nagane, bani wayanki kiga nasa number na” rasa yanda zatayi tayi hakan yasa tazamo jakanta daga kafada ahankali ta zage zip din jakar tana kokarin ciro wayar kokadan batason ta bashi number kuma tarasa yanda zatayi, wayar taciro tadago kai ta kallai yanda yasakin mata murmushi yasa tadanyi mai murmushin yake tamikamai wayan ahankali.
Tunda yake baitaba undergoing wat he’s going through a tsayen nanba ganin yanda Aneesa takema wani kato murmushi yasa yaji zuciyar shi tamai wani irin masifar daci, internally jikinshi ke rawa ganin tadauko waya ta mikamai yasa taji wani zuciyan dabaita bajin irinshi ba yataso azuciye ya shigo cikin premises din cafe ya dumfaro su.
duk wacce ta karanta batare data biyaba ban yafeba, in kinason book dinan ki tuntubeni ta WhatsApp number na kaman haka 07012181461
[4/5, 8:09 AM] Hijabi_muslimah????: A TSAKANKANIN SOYAYYA
_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤
_✍????M Shakur_
1️⃣8️⃣ & 1️⃣9️⃣
how to pay your access fee to IN BETWEEN THE LOVE
zaki turo 300 ta account number na 3107021073 first bank aisha Muhammad saiki turo evidence of payment ta WhatsApp number na 07012181461 sainai adding dinki a group din danake posting. Zaku iya turo katin 300 MTN for those dabasu da account
Yana tafiya kaman wani bijimin zaki tsabagen yanda zuciya yazomai wuya. Wani mutumi ne yafito daga cikin cafe da dan gudunshi rike da adaptor a hanunshi yazo wajen Mazimaziz yace “Malam Auwal you have to come with me akwai matsala babba, systems din row 2 are crashing wlh” da sauri yace “wat?!” mikama Aneesa wayan yayi yace “sorry Fateema, sai gobe zamuyi magana kinji, make sure you come early” yay maganan yanabin bayan mutumin da sauri suka shiga cikin cafe daidai lokacin Aliyu yawani iso gabanta yana wani irin kallonta tacikin black glasses din kan idanunshi, dudda bata iya ganin fuskarshi sosai amma saida gabanta yay wani mummunan faduwa, rawa lips dinta suka shiga yi tana kallon fuskarshi ganin yanda yake kallonta kaman zai wani watsa mata kyawawan mari yasa tafara komawa baya ahankali tana kallonshi kafin tajuya da sauri zata koma cikin cafe hanunta ya fizgo chak yarike gam, da sauri tajuyo tana zaro ido ta kallai, hanunshi sanyin bala’i ga taushin tsiya kaman baya aikin wahala, kokarin fizge hanunta tashiga yi tana kallon fuskarshi amma ko gezau baiyiba saima wani irin fizganta dayayi takusa faduwa yay wajen premises din da ita jama’a na kallon su, wani irin bugata yay da jikin mota saida tai kara yasa kafanshi ya daki gefen datake tsaye ajikin motan, jiyake kaman zai mutu da bakin ciki kafin yasa hannu yay punching motan da karfi with all his heart saida wurin yadan lotsa aciki yace “damn it!” sake daukan motan yayi da karfi dahar saida ta tsorata idanunta sukai ja, cikin ihu yace “who was that Man Aneesa? Who is he?” ya daka mata mugun tsawan da saida yasa duka idanun mutanen dake cikin cafe din yadawo kansu, ganin yanda mutane ke kallonsu yasa ta daure sosai tahana kanta kukan dayake shirin zuwan mata, ganin yanda kirjinshi ke tafarfasa hartana hango bugawan heart dinshi tagaban riga yasa tace “c…calm d…dow…” sake buga motan yayi dayasa ta runtse ido da sauri tsabagen tsoro dan har kwakwalwanta takejin karan buga motan, yace “don’t tell me to f*king calm down, uban waye wanan katon dakike ta yima murmushi eh?” yasake dukan motan kaman da motan yake fada, shigewa jikin motan tayi jikinta ko ina rawa yake kaman zata tsaga motan ta shige gabaki daya ta kame kamar wata yar sanda, ahankali tadan bude ido ta kallai numfashinta nafita da sauri da sauri, ahankali bakinta na rawa sosai tace “kaga ana kallonmu please kadena dukan motan nan, am so scared, kadena ana kallon mu” punching motan yayi da hannu kaman wanda ya zare yadaki motan da kafa cikin tsananin zuciya dashi kanshi baisan daga ina zuciyan takeba yace “who d fck is dat Man?! I said who is he? Talk!” yadaka mata wani mahaukacin tsawan da saida tasake firgita ta runtse ido da sauri jikinta ko ina narawa takasa magana, buga motar ya shigayi ganin takimai magana yace “damn it, damn it, dammmmnnnn it” hanunshi dasukai jajir tsabagen yanda yake punching motar suka shiga rawa kaman wanda ke farfadiya yana kallonta. “I’ve been calling you, so you are here with this stupid man eh Aneesa” yay ihu kaman zai shige jikinta, buga mota yayi ganin tama maidashi mahaukaci taki cemai komi yace “who is he? Who is he Aneesa kifadamin karkija ma mutumin nan dan he talking to you could cost him alot, tell me who the fuck is he” yasake buga motan, at this point kuka sosai yazoma Aneesa makogoro, bude ido tayi ahankali ganin yanda dalibai duk suka fito wajen Gate din cafe ana kallonsu kaman sun dawo film yasa ta kalli Aliyun dake kallonta bakinta narawa sosai tana kokarin hana kanta kukan dake zuwan mata tace “please please Ya Aliyu stop this you are embarrassing me, ana kallon mu, dan Allah kadena you are embarrassing me” glass din dake kan idanunshi yazare saida taji tsoro dataga idanunshi sunyi masifaffen ja, cikin fushi yanuna cafe da yatsa yace “because saurayin ki na nan shine nake baki kunya eh? Are you telling me this Aneesa, how dare you talk to that man? How dare you?” yanda yake mata ihu yana tozarta ta yasa taji she can not take it anymore, danne faduwan da gabanta yakeyi tayi, ta dake iya dakewa ta kallai tace “to wai meruwanka eh? Meruwan ka dani? Koma dawa nai magana ina ruwanka? Ka sanni ne? Mena hada dakai? Sai bala’i kakemin kaman wata yarka, anyi magana dashi din do you wor…..” “Aneesah!” ya daga hannu zai kai mata wani irin wawan mari da sauri ta kawad dakai tareda rufe fuskarta da hijabi gabanta na faduwa gabaki dayan jikinta yadau bari, tsayar da hannun daya daga zai mareta dashi yayi yana kallon yanda tarufe fuskan jikinta narawa sosai kaman an jonata da transformer, ahankali yace “just thank God I love you dasaikin yi nadaman fadamin kalaman nan dakikayi” yamaida hanunshi kasa tareda wucewa azuciye ya shige mota yaja motar d masifar gudu yay reverse da sauri daliban dake gaban gate suka koma ciki danyi yayi kaman zai kadesu yaja motar yabar wajen da masifan gudu zuciyarshi har ciwo takemai tsabagen fushi, ruwan dayaji akan fuskarshi yasa yakai hannu yataba fuskar hawaye ne masu mugun dumi suka gangaro daga idanunshi, da sauri ya share fuskar da bayan hannu yakarama motar gudu.