A TSAKANKANIN SOYAYYA HAUSA NOVEL

A TSAKANKANIN SOYAYYA HAUSA NOVEL

Ikon Allah ne yamayar dashi gida Gate aka budemai ya shiga Dady na tsaye a tsakar gida sanye da suit yana daura necktie dake hanunshi yanama gardeners dinsu magana, ganin motan Aliyu ya shigo yasa yabi motar da kallo, parking motar Aliyu yayi yafito daga motar a mugun zuciye ko tsayawa rufe motar baiyiba yay hanyar part dinshi batare daya kalli inda Dady ma yakeba yawuce part dinshi, bedroom dinshi yayi ya shiga yarufo kofar da key dan yasan sai Dady yabiyoshi yafada kan gado ya chusa kanshi a pillow, he’s boiling internally kaman zai mutu haka yakeji. Knocking kofar da akayi yasa yace “go away Dad, I wanna be alone” cikeda damuwa Dady yace “Gadangana open the door kaji yaron kirki, meya sameka? Bakada lafiya ne?” chusa kanshi yayi acikin filo da kyar muryan shi ya iya yafito yace “am fine Dad, I wanna be alone” da sauri Dady ya girgiza kai cikin tsananin damuwa yace “a’a son karmuyi haka dakai, remember am your best friend, open the door let’s talk kaji, tell me what’s d matter Aliyu na, I don’t want you to be alone, please open the door” dukan gadon yashiga yi da hannu yana tura fuskarshi a filo da sauri Dady yace “kai Aliyu kabude min kofa dan Allah karkasa hawan jini na yatashi, Gadanga open this door” daga murya yayi yace “go away Dadd, I said g…go aw….ay” yanda Dady yaji muryan Aliyu na breaking sosai yasa hankalinshi yatashi ainun, cikin tsatsauran murya yace “open this door Aliyu inba hakaba zanyi mummunan saba maka, katashi kabude kofan nan nace” jin shiru baice komiba yasa yace “wlh kaja na kira aka budemin kofan nan saina mugun sabama, open the door Aliyu, one! Two! Thre….” bude kofan da akayi yasa Dady yay shiru yana kallon kofan, idanun Aliyu yaga sunyi jajir sunyi ruwa-ruwa, da sauri Aliyun yajuya hakan yasa Dady yabishi ciki yace “Aliyu, Aliyu are you crying?” kifa kanshi a filo Aliyu yayi da sauri for the first time in his life baiso Dady yasan yay kuka dan yariga yacema Dady he’s not a baby kuma baiso Dady yafara maidashi kaman baby, kifa kanshi yayi akan pilo yana share fuskarshi da filo, da sauri Dady yazauna abakin gadon yadago shi cikin tsantsan tashin hankali yace “innalillahi wa innailaihi raji’un Aliyu, Gadanga na, boy menene? Menene eh why are you crying?” Dady yay maganan yana cupping fuskarshi cikeda tsananin son tsakanin uba da d’a da affection yace “menene boy?” girgiza kai Aliyu yayi yana trying his best ya danne zuciyar shi yace “bakomi Dad” da sauri Dady yace “is a lie Aliyu, tell me the truth meke damunka? Wani abun aka maka? Maiya faru daka fita bakacemin Suleja zakaba gidan su Abdul bakaje gidan bane? Wani abu yasameka ahanya ne? Aliyu bakaji, bakaji, kabari bodyguard su dinga rakaka duk inda zaka kaki Nigeria is not safe boy when will you understand that? Now tell me what happened to you? Wani abun kakeso ne? So kake kakoma California? Are you tired of here?” girgiza ma Dady kai ahankali yayi yama kasa magana, shafa kwantaccen sajenshi Dady yayi yace “to menene eh Aliyu? Am your father bakada kamanni aduk duniyan nan tell me menene, Aliyu” Dady takira shi cikin kwantacciyar muryan lallashi, daga kai yayi ya kalli Dady ahankali, Murya chan kasa Dady yace “tell me menene, meke damunka?” hawaye ne ya gangaro daga idanunshi sharrr da sauri Dady yakai yatsa yataba hawayen yace “subhanallah tears, Aliyu you are crying” lumshe ido yayi da sauri tareda cije lips dinshi in so much pain wasu hawayen na fitowa baimasan kuka yakeba, rungumshi Dady yayi yace “come here Son” Dady ya rungumshi tsamtsam yana bubbuga bayanshi yace “don’t cry, stop crying Aliyu komi maganin shi Allah, calm down, just calm down, relax your heart dan is beating way too much, calm down Gadanga na, Gadangan baban shi” rungume Dady yayi tight yana sauke ajiyan zuciya, shafa kanshi Dady yakeyi ahankali trying to calm him down dan yadade rabon dayaga Aliyu yay wanan fushi tun yana yaro, ahankali yace “katuna wakan danake maka dakana karami? Bari namaka kaji” Dady yay murmushi ahankali looking sad, ahankali yace ” Baba Ali-li mangyada baya bacci, ranan haihuwarshi ba wahala kodaya, yafado turus kaman namijin tarwada, tashi inganka tun makiya na bacci” murmushi yayi ahankali, duk in Dady yamai wakan nan saiya sashi murmushi, Dady is such a funny and sweet father, murmushi yasakeyi tareda kankame Dady tsamtsam murya chan kasa yace “I love you Daddddd” peck Dady yamai a forehead dinshi yace “I love you too Gadanga na, Ali Gadanga gusar yaki” kwanciya yayi ahankali yadaura kanshi kan cinyar Dady yay shiru, ganin yanda yayi yasa Dady bai karamai wani tambayan ba bari yabarshi, Aliyu is now a Man is not everything he have to tell him, maybe he feels he can solve it on his own, bari yabishi ahankali, amma dai koma menene ke damunshi haka Allah ya yaye mai, jin yana saukar da numfashi ahankali yasa ya kallai yaga yay bacci, daga kai Dady yayi yaja tattausan bargon kan gadon yakawo zai lullubeshi dashi idanunshi suka sauka kan hanun Aliyun dayay jajir some part ma na fitar da jini kadan kadan kaman wanda ya kurkurje, salati Dady yayi. “innalillahi, Aliyu!” saikuma yay shiru yana tunani Maiya sami danshi dambe yayine? Inaaa!! Bazata yuwa duk fadan da zasuyi shida Aliyun saidai suyi amma yagama fita daga gida batare da bodyguards dinshi ba, filo yajawo yadaga kanshi yadaura kan filon, yatashi yabude clean bathroom dinshi ya shiga yadebo warm water awani small bowl da karamin towel yazo ya tsugunna anan bakin gadon yakamo hanun yasa towel din yana gogewa, yatsine fuska Aliyu yayi cikin bacci alamun yanajin zafi ba karamin tausayi yabama Dady ba hakan yasa ya shiga huramai iska akan hannun ahankali yasake relaxing cikin baccin yacigaba da baccin tareda sauke ajiyan zuciya, tashi Dady yayi yakoma bathroom din ya ijiye komi yafito yadau wani pain relief balm daya ijiye a dakin nashi yazo yakamo hanun ya shafamai sanan yaja bargo yarufamai yarage karfin AC yajuya yafita daga dakin yana tunanin Maiya sameshi kafin yawuce yaje falon shi yadauko briefcase dinshi yafito bodyguards dinshi suka budemai mota ya shiga yamayi latti wlh yau zai shiga Chambers dama dayanda zaiyi dabaije ba Aliyu is his number in this life, haka yadinga tunani har yakai House of Representative, Federal Republic of Nigeria.

duk wacce takaranta book dinan batare data biyaba ban yafeba wlh, pay your access fee is just 300, wtsapp 07012181461

Takai kusan 2min atsaye chak awurin takasa matsawa sai rawa da jikinta keyi, kafin ahankali ta janye hijabinta tana kallon wajen, mai keken dayazo wucewa ta tare da sauri dan kunya takeji bana wasaba yanda kowa ke kallonta a wurin, shigewa tayi tace “express road zani” tada keken yayi yaja sukai gaba har express road yasauketa tafito dari biyu ta dauko tamikamai tajuya da gudu Yusuf zai tsaya yimata magana tabude kofa ta shiga abinta, Fatima sai kallonta take kaman yau tafara ganinta, backyard tawuce straight ta bude staff toilet ta shiga da gudu tarufe kofan tabude tap ruwa na zuba tafashe da kuka sosai tana taushe bakinta she’s so angry, Aliyu ya mugun bata mata rai, ita wata irin mutum ne da ta tsani dizgi a bainar jama’a tun tana yar yarinya, ko dukanta Ammi zatayi inhar tamata agaban mutane saitai kusan kwana biyu bata fitaba taita kuka agida dan tanada kunya, kuma inhar Ammi tadaketa agaban jama’a kozata kasheta bazatai kuka ba saita daure sai jama’a sun tafi saitafara kuka, batason amata fada agaban mutane she’s just naturally like that abin gets to her ne emotionally, shine Aliyun nan da bamata sanshi ba yakama yana mata tsawa kaman wata yarshi harzai mareta, sosai tafashe da kuka, cikin kuka sosai tabude jakanta taciro wayarta hanunta har rawa yake ta shiga contact dinshi ta danna ma number shi delete ta ijiye wayan takara kifa kanta awurin tana kuka sosai, jin ana shirin bude kofa yasa da sauri ta deba ruwan ta shiga wanke fuskarta, Fatima ce tashigo bayin tana hararanta tazo gefenta gaban wash hand basin din tana dan rera waka. “angwada nawa yace bayayi, da akaje gidan namiji saiya kadomu yace bazai bayarba shine muka gudo bayi muna kuka ahayye nanaye” Aneesa najin ta amma ba tace mata komiba, gama wanke wanke hannun tsokana Fatiman tayi tazo zata wuce tana waken ta ta bangaje Aneesa zata wuce, cikin tsananin fushi Aneesa ta fizgota batai wata wataba ta daga hannu ta daura mata clean mari, ihu Fatima tayi zata rama Aneesa tasa kafa ta kwashe ta sai kasa, tabita kasa ta kara daura mata wani marin tace “nasha gayamiki kifita daga harkana kinki, mene miki kika bangaje ni, ba fada kikeso ba zan koya miki hankali yau” takara zuba mata wani mari ta hade hannayen Fatiman ta murde su da karfi, ihu Fatima tayi, gwabe bakinta Aneesa tayi ta tashi daga kan cikinta tace “ki kara tonana” taja hijabinta da wayanta da jakan tafita daga bayin cikeda fushi, Fatima kasa tashi daga kasan tayi ta daga murya tace “wlh sainaga bayanki aduniyan nan Aneesa, sainaci mamanki dan ubanki, wayyo Allah na reshen bayana” dafa bango tayi tamike tsaye da kyar da sauri ta kakkabe jikinta dan batason Yusuf yagane Aneesa ta kayar da ita akasa ta wanwanke hanunta daya baci da kasa tawuce tafita daga bayin ta shiga store kitchen tabiyo Aneesa ta tsaya abakin kofa tarike kugu tace “ni kika mara Aneesa? Wlh sainaga bayanki aduniyan nan zaki ga” cikin masifa sosai dan ranta abace itama Aneesa yake tawani buga bowl din dake hanunta akan table ta kalli Fatima tace “ga fili gamai doki ubanki kafasa, kin zaci ke kadai kika iya hauka ko, sainaci ubanki” tafinciki bowl din tai kofan da gudu inda Fatiman take tsaye da gudu Fatima tafice ganin Aneesa ta haukace mata tana haki Ashe Aneesa ta iya fada haka, tsayawa Aneesa tayi abakin kofa tarufe kofan da karfi tana masifa. “dakin tsaya kiga inban kakkarya kasusuwan jikin ki da kwanon nan ba, da wlh saina kwaba cake dinan da namomin jikin ki” taja tsaki ta tsugunna jikin kofan Aliyu nafado mata arai sosai sama da dama, takai kusan 1min a tsugunne kafin tamike tashare hawayen daya zubo mata ta mike tawuce ta debo flour, kana ganin yanda take aikin kasan ranta abace yake.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57Next page

Leave a Reply

Back to top button