A TSAKANKANIN SOYAYYA HAUSA NOVEL

A TSAKANKANIN SOYAYYA HAUSA NOVEL

Not edited.

IN kika karanta baki biyaba Allah ya isa, in kinason karanta littafin nan kiyi subscribing just 300

Yunkurin amai da Ammi taji yasa tabude ido daga dan baccin daya saceta da sauri tana kiran sunan Allah. “Bismillahi” tajuya tana kallon Aneesa dake kwance yanda tabarta tana yunkurin amai sosai amma babu abinda ke fitowa, kan gadon Ammi tahau ta dagota da sauri zafin jikinta dataji saida yasa Ammi taji tsoro jikinta yafi wuta zafi. “innalillahi, Aneesa, Aneesa menene meke miki ciwo eh? Fadamin” Ammi tai maganan tana shafa fuskarta tana rungumota jikinta, kasa magana tayi sai nishi datake sama sama kaman wacce ke shirin mutuwa bamata gane me Ammi kecewa, yunkurin amai tasake yi hakan yasa Ammi tace “babu komi acikin ki, sannu nahada miki kayan shayi kisha bazan baki tuwoba kinji, nahada miki tea? Kokuma nafita waje nasamo yaro yasiyo miki tsire da fanta?” Ammi ta tambayeta cike da damuwa tana dago kanta, jini taga yana fitowa daga hancinta idanunta na kafewa alamun tasamu. “innalillahi!” Ammi tabuga uban salati mai kama da ihu cikeda tashin hankali, saikuma ta shiga jijjigata tana kiran sunanta. “Aneesa, Fateema” ganin bata motsi yasa Ammi ta shiga kalle kalle cup din ruwan data kawo mata dazu ta dauka ta debi ruwan ta yayyafa mata a fuska tace “tashi tashi kinji bari naje na kira Abdul mai keke yakaimu asibiti” nishi tayi tabude ido ahankali hakan yasa Ammi tai cupping face dinta takirata dukta rude tace “Aneesa na, karki kara rufe ido kinji bari na kira mai keke nakaiki asibiti kinji, ina zuwa” tadau wayan Aneesan data gani agefen gado tana kunna tourch tawuce tafita hartana bugewa da kofa ta kunna haske, sillipas tasaka tawuce zaure tafita tabude kofa tafita daga gidan ganin babu mahaluki kodaya a anguwan su yasa ta kalli wayan Aneesan da sauri sha biyun dare tagani harda minti uku, hannu tadaura kan bakinta ta taushe kukan dake shirin zuwan mata ta kalli cikin gidan nasu yanzu yazatayi? Yarta mara lafiya zata bari ita kadai cikin ciwo da wanan tsakar gidan kokuma she should go ahead ta dandara gidansu Abdul mai keke ne? Hawayen daya zubo mata ta share da sauri tarufo kofar gidan nasu tareda tofa ma kofar gidan bismillah ta shiga haskawa tana tafiya da sauri danba wuta har gidansu Abdul tsayawa tayi tana bubbuga kofar gidan tana kiran su. “maman Abdul, salamu Alaykum, Maman Abdul, Abdul, Abdul” ta shiga kwalama mutanen gidan kira tana ihu, takai kusan minti bayar sanan taji kara kaman an bude kofa daga cikin gidan akace “waye da tsakar daren nan?” muryan ta narawa sosai tace “maman Abdul nice, maman Aneesa ce, dan Allah kutaimaka min Aneesa batada lafiya, Abdul zakidan tasomin yazo yakaimu asibitin General” bude kofa maman Abdul tayi tana haska fuskan Ammi da tocula tace “subhanallahi, aiko Abdul bayanan, kumama ai yadena parking keke agida agarejin su yake parking kinsan wacce yakema aiki da keken tace ya dinga parkin agareji, ya jikin nata” hijabi Ammi tadaura kan fuskarta tana kokarin hana hawayen dake shirin zubowa waje, dafa ta Maman Aisha tayi cikeda tausayinta tace “kiyakuri maman Aneesa ciwon da ba dadi sam wlh, gashi khalili na kyanda dana rakaki bakin titi munsamo abin hawa, babansu kuma kinsan baidawo daga tafiyaba, kiyakuri kinji ki dandara bakin titi kisamo abin hawa Allah yabata lpy, kiyakuri” Maman Abdul tai maganan tana zare hannun Ammi daga fuskarta, gyada mata kai Ammi tayi tajuya da sauri tai hanyar titi tana goge kwalla tana addu’a Allah ya tsare mata Aneesan ta. Abakin titin ta tsaya babu wasu motoci sai tsirarru dasuke gittawa aguje, hawaye Ammi ta shiga share wa uncontrollably sai kallon agogo take yanzu karfe sha biyu da rabi, minti a shirin da bakwai kenan databar Aneesa ita kadai agida, ganin wani mota na zuwa da gudu tasan shima zai iya cewa bazai tsayaba yasa yafada titi tana kuka sosai dataji yazomata kawai dan hankalin ta a mugun tashe yake tana dagama motan hannu alamun motar ta tsaya.

Bodyguard din Dady ne dake tuki ya kalli dayan bodyguard din dake gefenshi yace “who is that woman? Get your gun” da sauri Dady dake bayan mota yana daddanna laptop idanunshi sanye da medicated glass jin suna magana get the gun yasa yadago kai, idanunshi ne suka sauka kan matar daya hango kan titi tana kuka sosai tana musu alamun su tsaya, ganin bodyguard din yakara gudu sosai yana shirin ya kwashe ta yasa yace “slow down Jeff, slow down” da sauri yace “what if is a trap sir” cikin fushi Dady yana kallon fuskan Ammi yace “slow down, Allah shine ke kare kowa, slow down let’s listen to wat she have to say, most time inna biyo ta Sulejan nan haka nake ganin mutane alot of them are the poors talakawa basuci abinci bane, let’s listen if is help we can offer then we help her” Dady yay maganan yana kallon Ammi still, rage gudun bodyguard din yayi har suka iso inda Ammi take da sauri Ammi ta zagayo tana kwan kwasa glass din motar.

Duk wacce ta karanta min littafi batare data biyaba ban yafeba wlh, saikin biyani a lahira
[4/5, 8:09 AM] Hijabi_muslimah????: A TSAKANKANIN SOYAYYA

         _IN BETWEEN THE LOVE_
        ❤ _Lies another love_❤




        _✍????M Shakur_



                    2️⃣3️⃣

how to subscribe

zaki turo 300 ta account number na 3107021073 aisha Muhammad first bank, saiki turo evidence of payment ta watsapp number na 07012181461 sainai adding dinki a group din danake posting, for those dabasu da account, zaku iya turo 300 ta katin MTN

To My GGM General Group Members, idan banso kuba wetin I gain? You guys are my backbone, all I know is that I made a strong fanbase akanku, you guys build me to Maman Shakur din danake yau da duk inka shiga ka kira sunana ansan dani, so how can I not express my gratitude??? Hats off to you guyss
The amount of love, kyaututtuka and many more danake samu am grateful wlh, Allah ya barmin ku, duk lokacin dana mike nace zan fara book kafin nace me kunfara biya like you guys are ever ready to pay inhar littafi daga nine abin alfahari ne agareni, I Love you and Allah ya barmin ku

*gareku masu karatun Allah ya isa ohhoho????????‍♀️ kumafa ina bala’in sonku amma ku daure kubiya kuyi joining group dina, banso ranan lahira na kwashe ladan ayyukan ku nagari na barku bakuda lada ko daya wayyo Allah na????, this writing shine baiwar da Allah yamin, support a sister, pay your access fee just 300 naira kidena karatun Allah ya isa dan zai biki , hakkina ne, duk wanda yay supporting business Allah zai bashi lada, kuma ina sonku amma dai duk wacce ta karanta bata biyaba dai toh toh toh wanan page din dai na yafe amma next page or any other next update ban yaheba.

Da sauri Dady yace “nose bleed kuma Aliyu, mekuma yakawo maka nose bleed ana zaune lpy?” yay maganan yana kai hannu zai taba hancin Aliyun da tip din yay jajir, da sauri Aliyu yarike hannun yana kawad da fuskan shi dan baiso ataba dan zafi zaiji yace “nikarka tabamin hanci am fine, ba zafi yakemin ba kuma tuntuni ya tsaya, are you just coming back now Dad? ina kaje kadade haka?” goran ruwan da Dady yagani kan table dinshi mara sanyi ya dauka tareda budewa zai sha yace “bamu gama meeting din dawuri bane, and on my way coming back kuma something happen saida na taimaka ma wata mata da yarta batada lpy na kaisu asibiti gwanin ban tausayi wlh” dan lumshe ido Aliyu yayi tareda shigewa cikin kujera more yace “am sleepy Dad” hanunshi Dady yaja yace “tobaza kaje ka kwanta ba afalo zaka kwana? Ehen Gadanga na that reminds me of something, taso kaji wata magana, tashi, tashi kaji” yadaga Aliyun da sauri yana dan murmushi, turo baki Aliyu yayi kaman zaiyi kuka yatashi zaune yakallai yace “uhmm tell me” matsowa kusa dashi Dady yayi sosai yadaura hanunshi akafada yace “daman kagane wanan aminin nan nawa Alhaji Hassan?” dan yatsine fuska Aliyu yayi yace “what about him?” murmushi Dady yayi yana kara matsowa kusada shi yace “to agidanshi mukaje meeting dazu dana fita, yarshi ce tazo tai serving dinmu, na yaba da hankalinta da natsuwan ta, kasan tareda sukayi school da kanwar ka Hajara a Dubai, sa’an Hajara ce, she’s just 24 Zainab, na yaba da natsuwan ta, tama cemin gobe zatazo wajen Hajara, inaso idan tazo kusasanta ka aureta Gadanga, so karkaje ko ina inaso ku sasanta ka aureta batada matsala very quite and obedient girl, kaga yanda kakeda shegen zuciyan nan you need yar yarinya maijin magana, mara hayaniya dazata bika sau da kafa, is just the best choice Son namaka trust you Dad” dariyan iskanci Aliyu ya shiga yi irin na sangartattun yaran nan, Dady yabude baki yana kallonshi instead of yamaji haushi saima washe baki yayi arayuwan shi yanaso yaga Aliyun shi na dariya, yanaso yaganshi he’s free and very happy, da kyar Aliyu ya tsayar da dariyan yace “are you for real Dad, like are you serious about this eh Babana?” da sauri Dady daya tsaya yana kallonshi kaman wani TV yana murmushi yace “yes now Boy, am serious, nafada maka she will make a best wife” dan tabe baki Aliyu yayi yadauki wayarshi yana kallo kafin ya dago kai ya kalli Dady yace “please, please Dad kaga am begging you don’t start with this neman min mata stuff, am I a kid daza ka wani nemomin mata, ni nama isa aure ne?” baki Dady yarike yana kallonshi yanda yakemai maganan yana turo baki sounding serious saikuma yay murmushi yana girgiza kai yace “kace kaikama isa aure ne, sanan kace are you a kid, wat does your statement and your question makes you now?” dan murmushin rashin gaskiya Aliyu yayi baice komiba ya dauke kai hakan yasa Dady yadanyi dariya yace “stop taking the advantage of the love I have for you Aliyu, kasan dai burin kowani uba ne yaga danshi yay aure ko, I want to see my grand kids Aliyu, banso namutu banga y’ay’anka ba Aliyu” da sauri Aliyu ya kallai jin kalman mutuwan daya fito daga bakinshi dan ko kadan baiso yaji Dady ya ambaci kalman mutuwa, gyadamai kai Dady yayi ganin tarkon daya dana mai yakamashi dan finally yasami full attention nashi, hakan yasa yasake kwantar da murya yace “yes Gadanga, banso namutu banga jikokina ba, kasan shekara na nawa yanzu aduniya? Talatin da takwas ga ishirin da tara ka lissafa, inada shekaru talatin da takwas aduniya mamanka ta haifamin kai kaga yanzu shekaruna sittin da bakwai, rayuwa taja Aliyu, Aliyu tai nisa kullum kara kusantowa da kabari mukeyi, nasan bazan taba kara shekaru dari akan wanan shekarun nawa ba, idan ma nakara to komi mini za’a dingayi” dan shiru yayi yana kallon yanda maganganun shi sukasa Aliyu yay sanyi sosai, dan fuzar da iska Dady yayi yace “is alright, naji nakuma yarda bazan nemama mata ba, konima nafison kazabo mata kafadamin choice dinka, na tattaro abokanai na da yan uwa muje munema maka ita but promise me zaka fito da mata nan da one month, you are 29, a graduate, har masters kanada shi, your company na running perfectly fine wat else kake jira? Promise me zaka fito da mata kwanan nan Son” dan lumshe ido yayi yana ganin fuskar Aneesa namai murmushi kafin ahankali yabude idon ya kalli Dady, hannun Dady yakama yarike ahankali yace “I promise Dad, and karka karamin maganan mutuwa, nothing will happen to you, jikoki harsaika gaji, duk wacce zan aura triplets triplets zata dinga haifowa and every year so get ready jekokin ka will break all your bones and fibers” dariya sosai Dady yayi yace “haka nake so ai, abun nema kenan hausawa sukace wai matar direba ta haifi mota kaga ai tuki har nijar” yasake fashewa da dariya kafin yay shiru ya shafa gashin kan Aliyun yace “nagode Aliyu na, yarona maijin maganan babanshi, Allah yamaka albarka kaji” murmushi yayi yace “Ameen Dad” hanunshi da har yanzu bedawo normal ba Dady ya karba yana kallo yace “tell me the truth what happen to you dazu Aliyu, eh what happen to you? Why were you so angry dazu?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57Next page

Leave a Reply

Back to top button