A TSAKANKANIN SOYAYYA HAUSA NOVEL
_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤
_✍????M Shakur_
2️⃣5️⃣
Gently yay sucking bottom lips dinta, omg he has never ever kissed anyone before, yanda lips dinta keda taushin nan ga dumin bala’i yasa yaji all organs din jikinshi sun soma amsawa da sauri yasaki lips din nata and move back towards the wall kaman wanda aka tura ya jingina da bangon tareda lumshe ido yana sauke ajiyan zuciya anatse trying to get his self back to normal, bude kofan dayaji anyi yasa yabude ido ya taso daga jikin bangon yana kallon kofan, Dr yagani shi kadai rikeda takarda da byro, karasowa ciki Dr yayi yana kallon Aneesan da idanunta kenan a kulle hawaye nafita ta gefen idanunta ancire mata oxygen din dan babu shi akan hancinta, da sauri yakara sa jikin gadon yana kallon yanda ta cire shi ta ijiye gefe yace “cire oxygen din kikayi patient dina sabida kin tashi kin soma samin lafiya? And why are you crying, your mummy is coming back yanzun nan abinci taje tadafa miki” yajuya ya kalli Aliyu dayazo ya tsaya a gefenshi batare dayace mai kalaba yarungume hannu a kirji yana kallonta, tsayar da abinda yakeyi Dr yayi yace “Sir may I know you please? Yaushe kazo?” dan juyowa Aliyu yayi ya zubamai mayun idanunshi yace “Bandade da zuwa ba” yamikama Dr hannu, hannu Dr yamiko mai suka gaisa Aliyu yace “am Aliyu, her husband to be” ware ido Dr yayi saikuma yay dariya yace “I see, no wonder takema kukan shagwaba anki bude ido a kallemu” dan murmushi Aliyu yayi yajuya ya kalleta har lokacin idanunta a lumshe jiyake kaman ya sunkuceta daga kan gadon nan yay gidanshi da ita let them just stay there forever and ever, dan juyo dakai yayi ya kalli Dr dake yan rubuce rubuce yace “what’s wrong with Love of my life Dr?” dago kai Dr yayi ya kallai yace “I must say, kayi dacen mace, your wife is a very very strong, she’s a fighter, masu maleria datake dashi giving up suke but ita tace ina she must live to tell the story of her love life” dan murmushi Aliyu yayi yasake kallonta batare daya janye idanunshi daga kanta ba yace “yeah, my baby is very strong, bold and above all fearless, she don’t wanna leave me dan tasan bazan iya rayuwa bataba” tafi Dr yashiga yi dayake yanada son surutu hakan yasa Aliyu tajuyo ya kallai, tsayar da dariyan yayi yace “maleria take fama dashi 4+, an shigo da ita jiya tana seriously convulsing ga wani uban high temperature datake running finding it difficult to breath, but fear not muna bata best treatment, yanzu ma Mum dinta muke jira takawo abinci dole saitaci abinci sanan zamu bata magani musamata wani karin ruwa dan wanan yakare tun dazu dasafe nazo nacire mata” gyadamai kai Aliyu yayi batare dayace komiba, Dr yace “bari nabarku tare karna katse muku hira” , yasa hannunshi a aljihun lab coat din jikinshi ya ciro new toothpaste da new toothbrush da asibitin kebama all patients dinsu yace “ga abinda nakawo mata, ta wanke baki kotaji dadin jikinta” hannu Aliyu yamika ya karba yana kallo Toothpaste din dako kadan baimai ba, Dr yace “bari naje before 10 her Mum will be back, ka lallabata please makesure she tadena kukan” yay maganan yana fita daga dakin yarufo musu kofa, kujera yaja ahankali ya zauna yana ijiye su brush din akan drawer kusada gadon yana kallon yanda taki bude ido har yanzu saidai tadena kukan dan hawayen sun dena zuba, murya chan kasa yakira sunanta. “Aneesah” ganin taki kallonshi ko motsi ma batayiba yasa yace “please open your eyes” kin bude idanun tayi tana saukar da numfashi ahankali, tarasa mesa duk in Aliyu na kusada ita rasa natsuwan ta take sai zuciyarta yadinga wani unusual beating, dan shiru yayi batare dayasan mezaiyi ba, tashi tsaye yayi daga kan kujeran yace “am coming” yay hanyar kofa yabude kofar dakin yafita yana tafiyan nan dai dai dake dauke ma mata hankali, ahankali tabude ido tabi kofar daya rufo mata da kallo kaman shi take gani, batada karfi ko kadan saima cikinta dataji yana mata wani mugun ciwo hade da maran ta kaman she’s about to have her monthly flow, dan yatsine fuska tayi idanunta na lumlumshewa juyar dakai tayi ta kalli hanunta taga anriga ancire mata drip din hakan yasa ta tattaro duka dan karfin datake dashi ta tashi zaune tana jingina da bangon gadon tana numfashi sama sama tana sauke ajiyan zuciya cikinta na masifar mata ciwo kaman ma harda yunwa, dakin har wani dan juyawa juyawa yake mata, lumshe ido tayi tana sauke ajiyan zuciya saida tai kusan minti biyu ahaka sanan tabude idanun ganin dakin yadena juya mata yasa ta saukar da kafanta daya ahankali tana yatsine fuska tsayawa tayi tana hutawa dan the pain she’s going through yay yawa, almost minti uku tabata sanan ta saukar da dayan kafan shima kasa ahankali tana yatsine fuska, ahankali ta sanya duka hannayenta takama karfen da ake makala drip tarike gam sanan ta mike tsaye kasusuwan jikinta nawani irin kas kas kas, jikinta yay tsami sosai kaman takai shekara daya a kwance ko kadan batada karfi kaman an mata alluran kashe karfin jiki, jin kaman tana neman tafadi kanta namata zuuu zuuu yasa tarike karfen gam trying to have control over her body, takai kusan minti hudu ahaka sanan tadanji daidai taji ciwon cikin ma yadan lafa, sakin karfen drip din tayi ahankali tamika hanunta tadau toothpaste da toothbrush din da Aliyu ya ijiye kan drawer tarike danko kadan bakinta bai mata dadi, gently ta daga kafanta tai taking first step sotake taje bayi tai brush then ease her self dan fitsari takeji sosai, tana numfashi da sauri da sauri tasake taking second step.
Kadan kadan take tafiyan tana hutawa hartakai kofan data kyautata zaton bayine sabida signboard din toilet dake jikin kofan, murdawa tayi ahankali ta shiga ciki ta mayar da kofan ta rufe ta shiga kallon bayin, bayin badai kyauba komi very clean and neat, juyawa da idanunta suka farayi yasa ta daura kanta jikin kofan ta lumshe ido saida taji daidai sanan tabude idanun tadago kanta tafara tafiya, ahankali takarasa gaban wash hand basin kunna tap din tayi ruwan ya shiga zubowa tabude brush din da kyar tarike ta tana kokarin matsa toothpaste akai hanunta ya shiga rawa, faduwa daga toothpaste din har brush din sukayi akasa daga hanunta jikinta ya shiga rawa maranta yafara daurewa, matsawa tayi gefe, wani irin murdamata da cikinta yayi yasa da sauri tai releasing bladder ta tai fitsari tai tsarki sanan ta tashi tana dafa bango tana kallon kofan fita datake so taje tafita dan jirin data fara gani yasoma fin karfinta, da kyar ta iya daga kafa tana tafiya tana layi kafin tawani irin zube akan dry clean tiles din bayin tasaki wani irin wahalallen kara…
Fitowa yayi daga cikin babban super market din rikeda wasu manya manyan ledoji guda biyu yay wurin motarshi ya shiga yana zuba kayan akan dayan kujeran yatada motar cikin mintoci dabasu gama kai biyu ba yakai asibitin dan babu wani nisa da super market din daya shiga, parking yayi ya sauko daga motan ya kwaso ledojin ya maida kofar yarufe yay cikin asibitin yana tafiya da sauri har gaban dakin nata, ahankali yabude kofa ya shiga ganin bata akan gado sai bargon data bari laying on the bed kusan rabin shi akasa yasa da sauri ya shigo yana kallon ko ina ajiye ledojin daya shigo dashi yayi akan plastic chair din yajuya da sauri zai fita dan ya tambayi nurses dinan ko sun kaita tai scanning or stuff like that dan baiganta adakiba, hannu yasa zai bude kofa yaji kaman sheshekan kuka, da sauri yasake juyowa idanunshi ne suka sauka akan kofan bayin dakin dabai gama rufuwa dukaba da sauri yay wajen bayin ya tsaya a jikin kofan tareda kara kunenshi, chan kasa yaji sheshekan kuka. “A….Am…mi” hannu yasa zai tura kofan ya shiga cikin bayin sabida yanda kirjinshi yabuga saikuma ya tsaya adan rude yace “Aneesah in shigo, are you okay?” jin shiru batamai magana ba yasa yawani irin tura kofan bayin ya shiga ganin ta akasa yasa da gudu yay cikin bayin yana kallon ko ina. “mesa zaki tashi dakanki baby, your body is so weak” yay maganan yana daukarta da sauri, mikewa tsaye yayi rikeda ita yana kallon fuskarta yanda take kuka tana kallonshi kofa yabude yafito da ita kaman baidau wani abuba ko kadan baiji nauyinta ba, zaunar da ita yay kan gado yadau filon gadon yasa abayanta zai juya dan bude ledojin daya taho dashi yaji tarike mai gefen hannun rigan jikinshi, juyowa yayi da sauri ya kalleta, fashewa da kuka tayi sosai irin na marsa lafiyan nan ahankali ya zauna ata bakin gadon yanajin wani irin wutar sonta na ruruwa aranshi, ahankali yace “menene, na kira miki Dr wani abu kemiki ciwo?” hannu tasa akan idanunta tana share hawayen dake ambaliya akan fuskarta cikin muryan marasa lafiya tace “Ammi na” dan lumshe ido yayi kafin ahankali yabude ya zuba mata su yace “stop crying, Dr yace taje gida tamiki girki but yanzun nan zata dawo stop crying okay” gyadamai kai tayi ahankali tana share hawayen dake zubowa akan fuskanta batare data kallai ba, yadade yana kallonta kafin yatashi ledojin dayazo dasu yabude farm fresh yogurt daya kawo maidan sanyi yaciro, yaciro wani portable fine mug daya sayo yawuce bathroom din yadaura yo kofin sanan yabude kofa yafito yana kallonta harya karaso gaban gadon bude yogurt din yayi yazuba a cup din yacika ya zauna yamika mata yace “sha it will give you energy” kaman wata matsoraciya tadago kai ta kallai hada ido sukayi da sauri ta dauke idanunta gabanta na faduwa, Murya chan kasa yace “please Aneesa kisha” yanda yay maganan kaman zaiyi kuka yasa ta mika hannu yasa mata ahannun, rawa hanunta ya shiga yi kaman zata kabar dan ba karfi ahannun saitaji yama hannun nata nauyi hakan yasa yarike hannun nata hade da cup din yana kallon fuskarta kaman yanda itama tadago kanta tana kallonshi lips dinta na rawa, da sublime eyes dinshi dayasa brows dinta suka fara wrinkling dan lumshe ido yayi yana kara matse hand dinta kafin ahankali yabude idanun nashi his eyes mimicking nata wani irin abu nayawo ajinin jikinshi, matsowa yayi ahankali batare daya janye idanunshi daga nata ba yana wani irin kallonta harya matso dab da ita, ahankali yadaga cup din hade da hanunta yakai saitin bakinta kasa kurba tayi sai kallonshi take, lumshe mata idanu yayi yabude tareda gyadamata kai alamun ta amsa, bude baki tayi ta kurba ahankali wani irin sanyaya mata rai yogurt din yayi har zuwa zuciyanta hakan yasa ta lumshe ido tacigaba dasha, ganin yanda taketa kurban yogurt din yasa yaji hankalin shi ya kwanta sosai, saida takusa shanyewa sanan tadan ture kofin tana sauke ajiyan zuciya hakan yasa ya janye cup din tareda daurawa kan drawer yana kallon ta, dan bude ido tayi suka hada ido da sauri ya nuna mata upper lips dinshi da yatsa alamun tabar yogurt a wurin nata, dan lashe upper lips din tayi amma bata gama gogewa ba, dan murmushi yayi yakama hannun rigan pyjamas din jikinshi dan baya tareda handkerchief yadan matso kusada ita sosai hartana jin saukan numfashin shi akan fuskarta da gudu ta runtse ido, ahankali ya share mata yana kallon lips dinta he’s feeling kaman ya rungumeta ya lallasheta, ganin his mind is skipping yasa ya janye hanunshi da sauri, zamewa tayi ta kwanta ahankali tana sauke ajiyan zuciya, ahankali yace “I love you Aneesa” runste ido tayi da sauri feeling somehow kafin ahankali jikinta ya shiga relaxing har wani irin bacci ya fizge ta, ganin yanda take sauke Jiyan zuciya yasa yagane bacci yay gaba da ita, tashi yayi daga kan gadon ya sauke kayan kan kujeran yazauna kan kujeran ya daura hannayenshi kan gadon yana kallonta, this the first time yake ganin jikinta batare data saka hijabi ba, jikinta is just the ideal body macen dat he has been wanting, her body is exquisite, Black skin dinta is damn bewitching just look at her gorgeous black neck dakeda chains line, wuyanta bulbul kaman batasan wahala ba, saukar da idanunshi yayi akan kirjinta da sauri ya dauke kanshi yace “subhanallah” daga kanshi yayi ya kalli agogon dakin tara saura baifi minti goma ba, baison ko kadan Ammi tazo tasame shi a asibitin hakan yasa yatashi tsaye tareda jan bargon yarufa mata yajuya yafita daga dakin da sauri yarufo kofa yawuce ya shiga motar shi yana fuzar da iska sanan yatada motar yawuce yatafi.