A TSAKANKANIN SOYAYYA HAUSA NOVEL

Wuraren 3 na rana Dr ya shigo dakin rikeda leda dake cikeda magunguna yana kallon Aneesan data tashi zaune ta jingina da gado tana shan tea da Ammi tahada mata Baffa na zaune kusada ita rikeda plate da soyayyan kwai kekai tanaci, tarame sosai, raman saiya kara karamata kyau, lips dinta sukai pink suka tattare sosai bana wasaba, baki Dr yarike yace “iyye patient dina da bata son allura ne takecin dadi haka, mesa akabata? ” dan murmushi Aneesan tayi akunyace, Baffa yace “yo kaiko bazaka barmin diya taci dadi ba, kukenan saiso kuna chakama mutum karfe daku za’a chakamawa da ansha kallo kuka wiwi zaku dinga yi fa balle yar diyata yar karaman nan” dariya duk akayi adakin Dr yakara so yana duba Aneesan ya bama Ammi ledan magungunan yace “an sallame ku, ga magungunan ta na narubu tamuku yanda zata dinga sha, ki kula da ita da kyau sanan a kiyaye kar sauro yacijeta sanan ta dinga shan maganin ta akai akai, kina yawan bata abinci mai Gina jiki, nariga na sanar da Alhaji nasallameku yama turo mota dazai maidaku gida motan na waje ku shirya sai a fitar da kaya” ya kalli Aneesa dake wasa da tea yace “Allah kara sauki my patient banda rashin ji da tsoron magani kinji ko” gyadamai kai Aneesa tayi tana murmushi ahankali Dr yawuce yafita, kayan su da dama a killace suke tsaf Ammi ta shiga gyarawa, shanye tea Aneesa tayi Ammi ta karba ta gyara komi Baffa ya karbi hijabin Aneesan daga hannun Ammi yasamata sanan yadaga ta tashi tayi ahankali yace “sannu kinji, sa takalmi” takalmi tasaka yana rikeda hannun ta suka fito shikuma Na Sani ya tsaya yataya Ammi kwashe kayan suka fito, da Ammi da Aneesa ne suka shiga jeep din da Dady ya aiko musu da shi sukuma su Baffa suka shiga tasu motar suka tafi gida sukai Suleja.
duk wacce takaran ta batare data biyaba Allah ya isa
how to subscribe
zaki turo 300 ta account number na 3107021073 Aisha Muhammad first bank, saiki turo evidence of payment ta watsap number na 07012181461, sainai adding dinki a group din danake posting
Gaban wani babban gida Aliyu yay horn, budemai gate gateman din yayi yana ganin Aliyu yahau washe baki yana dagamai hannu, shiga gidan Aliyu yayi yay parking da sauri gateman din yazo daidai Aliyu yabude mota yafito, washe baki Gate man din yayi yace “sannu da zuwa Alhaji yaushe kadawo Nigeria” dan murmushi Aliyu yayi yace “nadan kwana biyu” cikeda barkwanci gateman din yace “shine bakazo bikina bako, ko Abdul fa yaje a kauyen mu akayi, sunan matata Talatu mesa bakazo ba” “dalla chan kawuce kabama mutane wuri bazoba ba din” sukaji muryan mace daga bayansu tana magana, juyo dakai daga Aliyu har gateman din sukayi wata kyakkyawan budurwa ce mai kama da Abdul sosai kana ganinta zaka gane kanwarshi ce tsaye gaban tap din tsakar gidan, wani irin mugun kallo Aliyu yamata dayasa da sauri tajuya zatai backyard cikin kakkausar murya Aliyu yace “come back here” juyowa tayi ahankali kaman wacce kwai yafashe mawa aciki ta tako tazo ta tsaya a gefenshi, gateman din yanuna da hanunshi yace “say sorry” dan turo baki tayi tace “toni Ya Aliyu menayi?” da sauri gateman din yace “tabarshi Alhaji, basaita bani hakuri ba, haka muke wasa da Hajiya ai ni natafi” cikin fushi Aliyu yace “karkaje ko ina” tsayawa yayi dudda baiso ba, Aliyu ya kalli yarinyar yace “kinsan Allah Ihsan idan bakice sorry ba saina kakkaryaki anan sanan zan wuce ciki” idanun Aliyun ta kalla ganin da gaske yake kuma tasan zai iya dukanta dan Ya Aliyu mugu ne kaman ya Abdul yasa ta kalli gateman din tace “sorry” hararanta yayi yace “bacemin daga gani” da gudu tajuya ta shiga falon su, kudi yaciro daga aljihu dabaisan yawansu ba yamikama gateman din da sauri ya karba yace “innalillahi wanan kudi haka Alhaji, me za’ayi dasu?” murmushi yayi yace “gudunmawata, agaishe da Amarya” wani irin ihu gateman yayi hakan yasa Aliyu yajuya yay ciki yanadan murmushi, mamaki yake haryau gateman dinan bai chanza haliba, daga murya gateman yayi yace “Allah baka mata kyakkyawa wacce zata dinga saka farin ciki kaman yanda kasani yau nagode Yallabai” ganin Aliyu yama shige ciki a binshi yasa yajuya yana murna.
Da sallama Aliyu ya shiga falon dayasha kayan alatu, wata kyakyawar matace zaune kan dogon kujera tadanyi kama da Dady kaman kanwar shi kokuma cousin dinshi, hanunta rikeda bowl din slice friuts ga Ihsan a gefenta idanunta sunyi jajir tana kumbure kumbure, hararan Ihsan din yayi yana tahowa yace “tashi daga wurin nan” tashi tayi daga kusada matar tai stairs shikuma Aliyu yazauna kusada Momma tareda karban bowl din fruits din hannunta yace “Momma na” tallabe mai keya tayi da hannu hakan yasa yadanyi kara. “aucch Momma zafi fa” hararan shi tayi tace “kamin laifi tunda kadawo bakazo ka gaidani ba sanan daga zuwanka zaka dinga cin zalun autana” yatsine fuska yayi yana kai fruits baki yace “Momma Ihsan batada kunya zan kakkaryata in batai hankali ba wlh” haba Momma tarike tace “ahhh lallai ba shakka to mafashi, kaji ko mafashi nace, daga kai har Abdul din duk wanda yatabamin auta saina rama mata wlh, yayyun banza yayyun hofi masu cin zalun kanin su kawai” dariya yayi sosai yatashi daga kan kujeran yana hawa stairs rikeda bowl din fruits dinshi batare daya tanka ba, Momma data binshi da kallo tace “gaurayen banza aje ayi aure anki sai mugunta, katada wanan mugafalin dabaida aiki sai bacci” dariya yayi yawuce wani daki na karshe a corridor, bude kofar dakin yay ya shiga hango Abdul dayayi yayi daidai akan gado yana bacci ba riga ajikinshi yasa yay kwafa yafito daga dakin ya kwalama Ihsan kira. “Ihsan” da sauri tafito daga dakinta tace “na’am, gani Ya Aliyu” “ehen get me a cold water, very cold one, wanda yafara kankara daga fridge” gyadamai kai tayi tasauka kasa ko 1min ba’ayiba tadawo rikeda ruwan sanyin a gora dayadan soma kankara tabashi tana kallon fuskar shi, bowl din fruit din yamika mata yace “take it to the kitchen” yawuce ya shiga dakin tareda rufo kofa, ahankali yake tafiya har gaban gadon yabude goran ya ijiye marfin ya kwantarda goran ruwan ya tsayayo abayan Abdul dake sharara bacci, ihu Abdul yayi tareda zabura yatashi zaune sabida masifaffen sanyin dayaji, fashewa da dariya Aliyu yayi yana komawa baya ya ijiye ruwan kan center table yana dariya sosai harda rike ciki, saukowa daga kan gadon Abdul yayi yadau ruwan yace “yasin saina rama” da sauri Aliyu yabude kofa yafita biyoshi Abdul yayi, Aliyu ya sauka da gudu ya zauna kusada Momma yace “Momma kinga Abdul ko zai watsamin ruwan sanyi” daidai Abdul ya iso shima ganinshi kusada Momma yasa yakasa karasawa wajen ya tsaya anan gaban stairs Momma dake kallonshi tace “kazo mana ishashe, sai shegen son bacci kaman zakara, ai koda baizo yatasheka ba dani dazo kaga ainihin tashi, nafadamaka bazaka kara bacci mai kyau agidana ba, kai aure kaje gidanka inkaga dama kai baccin kwana uku babu maidamunka kaida matarka ne, amma muddin anan gidanne to ko kagama baccin lafiya da lumana” yanda ya daure fuska yana kallon tijaran da Momma kemai agaban Aliyu yasa Aliyu ya fashe da dariya, keyanshi Momma ta tallabe tace “kaima harda kai ai” gwalo Abdul yamishi yace “Allah kara” turo baki Aliyu yayi kaman zai mata kuka, dan murmushi Momma tace “ga abincin ku chan a dining inkunga dama kuci, gaurayen banza” tashi Aliyu yayi sukayi sama abinsu ko takan abincin basubi ba.
[4/5, 8:09 AM] Hijabi_muslimah????: A TSAKANKANIN SOYAYYA