A TSAKANKANIN SOYAYYA HAUSA NOVEL

A TSAKANKANIN SOYAYYA HAUSA NOVEL

         _IN BETWEEN THE LOVE_
        ❤ _Lies another love_❤




        _✍????M Shakur_



                    2⃣9⃣

Zama sukayi akan gado Abdul zai fara masifa da sauri Aliyu yace “please jekai wanka inaso karakani hospital ne” da sauri Abdul yadaura hanunshi kan goshin shi yace “bakada lafiya ne Leo? Mekema ciwo?” girgiza mai kai yayi yace “am fine” “tome zakaje kayi a hospital?” kaman baiso yay magana yace “I wanna go see someone” kallonshi Abdul yayi irin anya Aliyu ne yay maganan nan kuwa dan yasan baida abokanai shi yanama shiga mutane ne dahar yasan wani dazaije dubawa a asibiti, ahankali kaman mai koyan magana yace “s…o..meo..ne? Someone Leo, waye someone kuma?” dan shiru Aliyu yayi yana kallonshi yarasa taya zai fadamai, dariya Abdul yafashe dashi yakoma kan center table yazauna yana daura kafa daya kan daya yana facing dinshi yace “shegen gora, koka fadamin gaskiya kokuma ko nan da chan like chan fa kofar dakina dinan da sunan rakaka wani wuri bazani ba, so tell me d truth” dan yatsine fuska Aliyu yayi yace “please now, kaga nagaji ni nai driving har nan hannuna duk sun sage karakani mana,” da sauri Abdul yace “naji to tell me, who is someone, mace ne ko namiji?” hararan shi Aliyu yayi kafin yadauke kai murya chan kasan makoshi yace “mace” huuuuuu! Wani irin ihu Abdul yyi da ko Aliyu saida ya firgita yakoma cikin gado da sauri yace “are you okay me haka” hawowa gadon Abdul yayi da sauri ya dafa cinyar Aliyun yace “who is she? Yaushe kuka hadu Leo?” shiru Aliyu yayi kaman wanda ke tunani saikuma yadan numfasa yace “I just like her, she’s just a unique being, her uniqueness yasa zuciyata zabota” kallonshi Abdul yakeyi yanda yake magana a yangance yana fitar da kalaman daidai dan murmushi yayi yace “itace batada lafiya saisa duk ka rame haka?” lumshe ido yayi kafin ahankali yabude idanunshi harsun dan chanza launi sunyi ja murya chan kasa cikeda damuwa yace “please tashi ka shirya” yanda duk yay wani iri yasa Abdul yaji tausayin shi dan yaga son yarinyar a idanunshi hakan yasa yasauka kan gadon ahankali yawuce ya shiga bathroom baiwani jimaba ya watso ruwa yafito ayanda yabarshi yazo ya tarar dashi yawuce wajen wardrobe dinshi shiryawa shima yayi cikin manyan kaya kaman na Aliyun yay kyau ya feffesa turare yajuyo yace “let’s go” tashi yayi ahankali hannu Abdul yamika mai yace “car key karkazo ka kashe ni ahanya hakanan banyi aure na more ba” dan murmushi yayi saikuma ya yatsine fuska yazaro key yabashi karba yayi suka wuce suka fita, kallo Momma tabisu dashi kafin ma su karasa saukowa daga stairs tace “sai ina haka yan samari?” Abdul zaiyi magana Aliyu yarigashi yace “yanzun nan zamu dawo Momma” tabe baki Momma tayi tace “kwaji dashi kayan tusa, intai tsami maji, adawo lpy” wucewa sukayi suka fita suka shiga Abdul ke driving har asibiti, saukowa sukayi sukai ciki suka shiga reception, nurse din jiyace tana ganin Aliyu tagane shi da sauri tafito daga bayan kanta tasha gabansu tace “Sir barka da zuwa, kunsha bambam ne da patient din koba ita kazo nema ba?” gyada mata kai yayi ahankali, da sauri tace “ai bamasu dade da tafiya ba, an sallame su, wlh ansalame su suntafi gida, saida ma nataya namanta daukan jaka namusu rakiya har mota” shiru Aliyu yayi duk yaji ba dadi, ganin yama kasa magana yasa Abdul yace “thank you bari mubisu” ya kalli Aliyu yace “let’s go” binshi abaya Aliyu yayi suka fita ganin duk yanda Aliyun yayi yasa yace “kasan gidan sune?” gyadamai kai yayi. “inane?” ahankali yace “Suleja, Sulejan mu?” gyadamai kai yayi daidai sun karaso mota suka shiga Abdul yay reverse suka fita daga gidan.

Tunda suka isa gida Ammi ta shiga kitchen tafara hada musu abinci itakuma Aneesa dasu Baffa suna falon su suna mata fira danji da ita suke bana wasaba Baffa ma da kanshi yafita yasiyo mata gyada dafaffa gwangwani biyu aiko sai ci take aranta sai murna take ashe haka akeji da mutum idan yay rashin lafiya ko wash tace sai an tambaye ta meke damunta.
Shigowa Ammi tayi da manyan kulolin tuwo ta kalli su Baffa tace “akawo miya Alhaji kuci yanzu” girgiza mata kai yayi yana tashi saga gefen Aneesa yana kakkabe riga yace “bari mudan shiga gari nida Na Sani, bayan isha maci kokai zakaci yanzu?” girgixa mai kai Na Sani yayi yace kinji ko, yajuyo ya kalli Aneesa yace “mezan siyo miki inzan dawo?” washe baki tayi tace “Baffa kashu nakeso” hararanta Ammi tayi tace “aikin kenan kwadayayya” rufe fuska tayi da hannu tana murmushi Baffa yadaga ma Ammi hannu yace “kinga, kinga ki barmin diya tahuta yaushe duka duka tafarfado dan haka dole taci tasha abinda takeso, zan taho miki dashi, anjima ai wayanki kinada kati ko” gyadama Baffa kai tayi tace “to kimin flashing danna tuna” da sauri tace “to saikun dawo Baffa” wucewa sukayi suka fita ta kalli Ammi tareda kyalkyalcewa da dariya kwafa Ammi tayi tace “zan cinmiki ne” tawuce tafita daga murya tayi tace “Ammi nazo nataya ki?” daga kitchen Ammi tace “sha zamanki, nama gama kaye kayen kitchen zanyi” Ammi tadau tsintsiya tana gyara kitchen din dan ansoma kiran magrib, turo kofar gidansu da akayi yasa ta ijiye tsintsiya ta leko tsakar gidan wani dan yaro ne yakara so tsakar gidan, fitowa Ammi tayi daga kitchen din tana kallon yaron tace “kai lafiya baka iya sallama bane” murmushi yaron yayi yana jan hanci yana share majinan kan hancin shi yadaga murya yace “Assalamu Alayyykummm wai ance Aneesa tazo awaje” da sauri Ammi tace “injiwa ye?” “nima bantaniba” yay maganan yana goggoge majina da hannu tsumman dake jikin window kitchen dinsu Ammi taja tadan barki kadan tazo gaban yaron tace “zo ashare majinan” sharemai majinan hancin tayi dana hannun shi sanan ta wanke mai hannun da ruwan dake cikin bucket din gaban rijiya tace “wai ance waye?” da gudu yaron yajuya yafita, yaye labulen bakin kofar su Ammi tayi tadaure fuska tace “waye yazo neman ki?” zuru zuru tayi tace “nima bansaniba Ammi” baki Ammi tabude zatai maganan saiga yaron ya shigo da gudu yace “wai yace Yusuf security ne” dan zaro ido Aneesa tayi tace “laaa Yusuf, Ammi mai budema mutane kofan shagon mune, security, hala Madam ta aikoshi” dan jimm Ammi tayi kaman mai tunani kafin tace “dauko hijabi kije kecemai rashin lafiya kikayi saisa basu ganki ba” gyadamata kai tayi takoma falon tadauko baby pink hijabinta har kasa dayay mata kyau fuskanta yay dan fayau aciki ta zura kafanta a slippers batare data tsaya saka safa ba tawuce tafita ahankali tabude kofa tafita, a kofar gidansu taga Yusuf Security zaune kan dan machine dinshi dama uniform dinshi bai chanza ba zuwa kayan gida, ganin Aneesa tafito yasa yasauko daga kan machine yana murmushi yana kallonta daidai lokacin Abdul yayi parking next to kofar gidansu Aneesan daga shi har Aliyu sun zubama on Aneesan data fito daga gidansu tana tafiya ahankali ido, karasowa gabanta Yusuf yayi cikeda damuwa yace “lafiya baki zuwa aiki Aneesa? Maiya same ki fuskan ki duk yay wani iri haka kin kumkumbura idanunki sun fada ciki” ahankali tace “rashin lafiya nayi yau aka sallamoni daga asibiti, ya akayi kasan gidanmu” cikeda damuwa kaman zai hadiyeta danso yace “innalillahi Aneesa rashin lafiya, no wonder tunda nadena ganinki nadena jin dadin rayuwana wlh ko aikin bayamin dadi sam sam, na damu iya damuwa shine nace bari kaga ko bango duniya kike inhar a Sulejan nanne saina nemo gidanku naji ko lafiya” dan murmushin yake tamai koba komi yay kokari tunda har yay tattaki yazo yaji ko lafiya, dan murmushi tasake yi tace “nagode” yanda tai murmushin tana dan juyakai yasa yaji zuciyar shi ya narke ahankali yace “wayyo Allah na, murmushin ki na haukata min zuciya da kwanya” gimtse fuska tayi tana kallonshi ganin haka yasa yasaki dariya yana daga hannu yace “maida wukan to, haba Aneesa sarkin masifa, ke baki bari ta tafasa balle to kone ba’a dan zolayan ki”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57Next page

Leave a Reply

Back to top button