A TSAKANKANIN SOYAYYA HAUSA NOVEL
Har gaban kofar dakin Aneesa takawo Ammi dake wani irin jin kunya sosai sanan tawuce takoma cikin gida da gudu, bin bayanta da kallo Ammi tayi tana sauke ajiyan zuciya kafin ahankali tasa hannu tabude kofar dakin ta shiga ciki ahankali da sallama, mikewa tsaye Dady yayi yana yana gyara babban riganshi dayasha lafiyayyen aiki yana kallon Ammi, kasa jure kallon daya ke mata Ammi tayi hakan yasa ta saukar da nata kan kasa, ahankali tashigo tana taku daidai anatse har gabanshi kafin ta tsugunna ahankali zata gaidashi da sauri yawani irin riketa batare daya bari ta tsugunna ba yadago ta tashi tsaye tayi tana kallon fuskarshi kaman yanda shima yake kallonta wani irin kyakyawan runguma yabata tareda sata a kirjinshi da kyau yahada da malummalum da hannuwanshi yawani irin zagayeta yana sauke ajiyan zuciya ahankali tareda lumshe ido yana shakan dadaddan kamshin turaren dake tashi daga jikinta, lamo Ammi tayi tana sauraron yanda beat din zuciyar shi ke sauka a natse it feels gud to be back, bakaramin natsuwa taji ya shegeta ba da wanan runguman dayamata ba, sunkai kusan 5 minutes a rungume da juna kafin ahankali Dady ya dagota tareda tallabe fuskarta yana kallon simple makeup din da Aneesa tamata yace “karki kara cewa zaki tsugunna ki gaidani kinji Matata” gyadamai kai Ammi tayi tareda dan lumshe ido tabude su ahankali, ahankali ya sumbaci goshinta tareda rike mata hannu yay kan kujeran dayake ya zauna sanan ya zaunar da ita gefenshi yajawo kanta ya kwantar akan kirjinshi yanadan shafa mata baya, Murya chan kasa ta yanda daga ita sai shi zasu dinga jin abinda suke cewa yace “Alhamdulillah, ina tsananin farin ciki da wanan ranan Rukayya, I feel blessed dana same ki a matsayin mata sanan ina rokon Allah daya bani ikon kula da ke da yaranmu biyu yanda yakamata” gyadamai kai Ammi tayi kanta na kirjinshi tace “Ameen” murmushi Dady yayi yakama hannu ta da Aneesa tamata lalle yana shafawa lallen ya masifar mai kyau murya chan kasa yace “Rukayya anya zan iya hakura har kiyi satin dayan danace zan baki kiyi dan kikarasa shirye shirye kuwa?” yay dan jimm sai chan yace “ana daura auren nan dana ganki yanzun nan a matsayin mallakina, matata wacce nakeda iko da ita sainaji bazan iya daurewa ba kuma banso ko kadan na takura miki wlh” daya yanda yake maganan dudda kanta na kirjinshi bata ganin fuskarshi tasan yana cikin damuwa ne and one thing datama kanta alkawari shine kaman yanda har mahaifin Aneesa yakoma ga Allah yabonta da kyawawa dabi’unta yake haka zata kasance ga Dady, she will never give room dazaisa Dady yay complain akanta ba, zatabi mijinta zatai kyautatamai, zata karenshi sanan ta kare dukiyar shi, ta kula da komi nashi domin al jannar ta na karkashin tafin kafanshi ne, ahankali tadago da kanta daga jikinshi ta kalleshi tace “kayakuri kadagamin kafa kabani yau kadai sabida nasamu na hada komi nawa, inyaso gobe saikazo ka daukemu mutare, nima nakosa na kasance tareda mijina abin sona, sanan abin alfaharina, uba ga yarana biyu Aliyu da Aneesa, an dagamin kafan nahada komi yau Abu Aliyu?” Ammi tai maganan tana shafa gemushin har zuwa kumatun shi ahankali with love and compassion, Dady jiyayi kaman kanshi zai tarwatse arayuwan shi yanason mace data iya lafazi masu dadi da taushi sanan da sanyaya ran mai gida, matan shi babu abinda suka iya arayuwan su banda habaici da yada magana, wani zubin sukamai habaici saiyaje office yafara rubutu zai ma gane bakin zaren habaicin, just at yanda Ammi tanunamai he’s in total control of her, what a submissive wife sanan akarshen maganan tace mahaifin yarana biyu tasake karyawa da Abu Aliyu, tsabagen yanda maganan tamai dadi baisan sanda yajawo ta yadaura ta kan jikinshi ba, ahankali ya sumbaci bakinta ko kadan Ammi bata hanashi ba yakai kusan minti daya yanayi anatse kaman zai cinyeta sanan yasaketa yakai bakinshi saitin kunenta yace “nagode Gimbiya ta, Allah yamiki albarka Rukayya, gobe karfe hudu bayan sallan la’asar zan aiko motoci akawomin abin sona Ummu Aliyu, Abu Aneesa na tsummayan Ummu Aliyu ina sonki Rukayya sosai, don’t ever change wayan nan kyawawan dabi’un kinji abin sona” gyadamai kai tayi tace “naji abin sona Abu Aneesa, I love you wujiga wujiga, zan iya tafiya ko yallabai baigama daniba tukunna” washe baki Dady yayi yana dariya irin ta manyan nan feeling bossy yace “a’a Yallabai baigama da Yallabiya ba, yadai kusa, kafafuna sunmin tsami ne sosai nafi awa biyu a tsaye wajen daurin auren nan” tashi Ammi tayi daga jikinshi tace “wai wai bari muga kafan” zama tayi a gefenshi tareda dan dukawa takamo kafan Dady dake sanye da cover shoe ta daura kan cinyarta, ahankali ta zare cover shoe din Dady sai kallonta yake kaman zai hadiyeta safan tacire ta ijiye kan hannun kujera tasa hannu ta ahankali ta shiga matsamai feet din Dady ya lumshe ido sosai yakejin dadin yanda tamai, almost 20min tadauka tana mammatsamai kafan harsaida dan gyangyadi yasoma saceshi tun yana kallonta sanan tasaka mai safa ta mayar ma da takalman shi ta ijiye kafan ahankali gudun kar ta tasheshi sanan ta matsa kisada shi tashafa sajen shi bude ido yayi tareda kama hanunta ya sumbaci hannun yana murmushi yace “nabaki izinin zaki iya tafiya kar anemeki” wani irin rausayar da kai Mami tayi tace “godiya nake mai gida” har bakin kofa yarakata yabude mata kofa tafita tana mai murmushi tai cikin gida, guda kawayenta suka shiga yi suna mata kirari Aneesa sai dadi takeji kaman zata mutu haka aka wuni sai bayan magrib baki suka fara tafiya Aneesa ta gyara gidan tass Ammi taje tai wanka da ruwan turare dana yan magungunan data hadama kanta dan Dady yabata kudi dasu tasaisai abinda take bukata na gyarani jiki.
Washe gari koda gari yawaye daidai da tsinke Aneesa bata bari Ammi ta daga ba ita ta gyara ko ina tahada ubansun abinci a big pot dan tasan anjima kadan zasuyi baki, sanan ta hura wani wutan ta daura ruwan wanka kafin tawuce ta shigo daki tai wurin Ammi, kallonta Ammi tayi tace “sako hijabi kije wajen Maman Aisha ki kiramin ita, sonake ragowan abincin nan da baban ki yakawo ayi biki dashi duk tazo ta kwasa ko” gyadamata kai Aneesa tayi tace “zataji dadi sosai kuwan Ammi dama baban su yanzu baya aiki” hijabi tasa taje takira maman su Aisha tare suka dawo ita tawuce kitchen tadaiji yanda maman su Aisha keta godema Ammi harda kukan ta, girkin takarasa taje tai wanka tadawo daki dama tariga ta ijiye kayan dazata sa tai gayu sosai yauma lacey takara sawa pitch wayaga ansami lace daban daban kyau tayi.
Wuraren bayan la’asar din kaman yanda Dady yafada motoci suka cika anguwan kaman za’azo daukan budurwa, Momma ce tazo da kawayenta guda uku suka shigo dakin kebewa tayi da Ammi dataji tana so sosai dan kallo daya kacal tama Ammi tasan zatafi sauran matan Dady hankali ta shirya Ammi tasa mata alkyabba akan hadadden lapaya dake jikinta sanan aka hadu da kawayen Ammi yan anguwa aka kai Ammi mota, Momma ta turo bodyguard ciki Aneesa na nuna musu kayansu dazasu kai mota akwatin nan su dayan abubuwan dasuka tattara duk suka tafi dashi tadauko dogon hijabin ta har kasa pitch tasa da takalmin ta mai kyau look so decent and magical tafito ta kulle gidan tajefa key cikin jaka tazo da sauri motan da akasa Ammin ta aciki Momma dataji tanason Aneesa tace “zoki zauna wajen maman ki” da sauri tazo dan dama tafiso ta zauna wajen Ammi ba dayan motan ba, motan daga Ammi sai momma sai kuma ita, kawayen momma na motan farko su kadai, sai motan karshe kuma kawayen Ammi ne aka dau hanyar City Abuja. Aneesa sai kalle kalle take oh yanzu zasu koma new gidansu ne.