A TSAKANKANIN SOYAYYA HAUSA NOVEL
Cigaba da wasada yaran Dady yayi daidai yana jira yaji any of matayen nashi wata tagaishe shi amma basu gaidashi ba, sai kumbure kumbure suke, cikin fushi Maman su Rauda tace “wai wa muke jirane haka ake batamana lokaci” cikin fushi da kunan rai Amarya tace “ganemin fa, kya tayani tambaya sai, an shanyamu saikace kayan wanke ko yar gidan sarki muke jira ai sai haka” baki Dady yabude zaiyi magana Momma tabude kofa suka shigo itada Ammi dake sanye da hijabi har kasa sai Aneesa, itama sanye da hijabin ta har kasa tana gefen Ammin ta har wajen kujera Momma takawo Ammi da Dady yabi da kallo tace “ga kujera ki zauna” zama Ammi tayi ahankali tadan dago kanta ta kalli Dady dake kallonta cikeda natsuwa da tsantsan girmamawa tace “ina yini Alhaji, barka da dare” har wani irin lumshe ido Dady yayi da Ammi ta gaidashi muryanta na ratsa kowani bangare najikinshi, kafin ma yabata amsa ta juya ta kalli sauran matan dan kallo daya ta musu tagane matayen Dady ne tace “ina yinin mu” zama Aneesa tayi gefen kafar Ammi tace “ina yini Abba” murmushi sosai Abba yayi yace “lafiya lau daughter na, ya gajiya” cikeda kunya tana kare fuskarta da hijabi dan dakin da mutane da yawa tace “Alhamdulillah” sanan ta kalli matayen da Ammin ta ta gaida basu amsa ba tace “ina yini” dan gajeren tsaki maman Rauda taja, har ranshi Dady yaji tsakin baice komiba yasan dama bazasu amsaba ya kalli Momma data tsaya kallon komi yace “sun wuce?” “eh sun wuce yaya, nima natafi saida safe” “nagode” hannu Rauda tadagama Momma tana murmushi tace “Momma saida safe ki gaidamin da Ihsan” murmushi Momma tayi tace “zataji Rauda” tabude kofa tafice.
Ajiyan zuciya Dady ya sauke kafin ya gyara zama yabude taro da addu’a sanan ya kalli yaranshi dake zaune kan carpet din yace “yarana” atare suka amsa dukan su “na’am Dady” murmushi yayi sosai yace “na kiraku nanne sabida na nuna muku new Mummy dinku, sunanta Mummy Aliyu kokuma kuce Mummy Aneesa” duk murmushi yaran sukayi suna kallon fuskar Ammi dake kasa banda Hajar datai kini kini da rai, ganin yanda suke murmushi Dady yace “ga Aneesa nan, y’atace itama sanan yar uwarku ce, Inaso kuhada kai kuso juna banda fada kunaji” da sauri duk suka gyadama Dady kai, murmushi Dady yayi shi yasan Allah has blessed him da yara nagari but iyayen su ke batamishi su, ahankali yace “kutashi kuje ku gaida new Mum dinku” da sauri suka tashi har ana rige rigen zuwa murmushi Ammi tayi ta rungume su tana shafa kansu sai gashe da ita suke. “Mummy Aliyu ina yini, Mummy Aliyu good evening” haka suketa gaidata, Rauda ma tazo tana murmushi tace “sannu da zuwa Mummy” murmushi Ammi tayi ta shafa fuskarta tace “nagode y’ata” Hajar ma tasowa tayi ba yabo ba fallasa tace “ina yini Mummy Aliyu” lafiya lau Ammi ta amsata ganin yanda ta gaidata da kyar sanan duk suka koma suka zazzauna, murmushi Dady yayi ya kalli Ammi yace “dukan su yarana ne, su goma sha tara ne Rukayya” ya kalli yaran yace “to duk kutashi kutafi ku kwanta zanyi magana da iyayen ku” tashi sukayi ahankali harda Aneesa da Rauda tamiko mata hannu dan tun dazu data shigo take kallonta tagane ta ita Aneesa bamata ganeta ba har yanzu dan ranan dataganta tai buzu buzu, murmushi Aneesa tayi Dady na dan dariya yaji yakara son Rauda suka fita daga dakin Mama nabin bayan Rauda da harara suka rufo kofan.
how to subscribe
zaki turo 300 ta account number na 3107021073 aisha Muhammad first bank, saiki turo evidence of payment ta watsap number na 07012181461 sainai adding dinki a group din a tsakanin soyyayya
duk wacce takaranta batare data biyaba Allah ya isa
Gyara zama Dady yayi zaiyi magana Amarya tace “ansa y’ay’an mu sun gaidata amma ba’a saka yarta tagaidamu ba tun yanzu anfara son kai” da hannu Dady yanuna ta cikin kakkausar murya yace “Zainab ki shiga taitayin ki last warning” yay maganan babu alamun wasa atattare dashi hakan yasa kowaccen su tahadiye abinda ke ranta, Dady yayi shiru yana kallonsu kafin cikin fushi yace “data shigo ta gaida ku kun amsata ne? Anyway kubi ahankali inba hakaba zanyi mummunan saba muku” dan shiru yayi trying to calm kanshi down kafin ahankali yakira Ammi. “Rukayya” ahankali Ammi tadago kanta tace “na’am Alhaji” nuna su Mama yayi yace “ga matana nan, Kareema itace uwargida, sai Amina mai binta, sai Zainab” ya nuna amaryan shi yace “itace ta uku, inaso ki basu girman su banson neman fada da hayaniya, kwana bibbiyu ne ake amsan girki, ba’a girki General girki agidana ko wacce tana girkinta daban dan banson tashin hankali da korafi, duk randa nake dakin ki saikiyi dani, ko wacce ina samata abinci a dakinta idan wani abu yakare ba’a riga an kawoba akwai General store anan tsakar gida zaki iya dubawa in akwai abinda kike bukata saiki dauka, inaso ki zama mace mara hayaniya mara fada da kowa, ki kare mutunci kanki dana mijinki kome aka miki kifada min kafin kidau hukunci kinji Rukayya” gyadamai kai Ammi tayi tace “in sha Allah zan kiyaye duk abinda kace Alhaji, Allah yatayani yakuma yimin jagora” murmushi yayi yana kallonta yace “Ameen” sanan ya kalli sauran matan shi yace “ga yar kanwar kunan sunanta Rukayya nabaku ita amana, ku hada kanku kuyi bautan aure, ku kwantar min da hankali ku hada kan yarana, banda fada da hayaniya, Allah yamuku albarka dukanku, idan damai magana zata iyayi” da sauri Amarya tana kumbure kumbure tace “yanzu kwana nawa zakayi a wurin ta kafin kadawo wurin mu?” dan murmushi Dady yayi ganin yanda kishi ke cinta yace “kwana uku in sha Allah” Maman su Rauda cikin daure fuska tace “wanan yarinyan kuma fa damuka gani?” cikin daure fuska Dady yace “y’ata ce itama, sunan ta Fateema ana kiranta da Aneesa, dawata maganan ne?” Amina matar Dady ta biyu ne tace “badai makarantan da y’ayan mu suke zaka sata badai ko” cikin kakkausar murya Dady yace “Aneesah y’ata ce bakida ikon da zaki fadamin how da kuma tayaya zanbi da yarana, duk inda nasata wanan ba matsalan ki bace tunda dai bada kudin ki nake biyan kudin makarantan ba” zata kara magana Dady yadaga musu hannu alamun suyi shiru kafin yanuna musu hanyar kofa yace “zaku iya tafiya” tashi sukayi fuuu suka fice suka bugo kofar, ahankali Dady yatashi daga kan kujeran yakoma kan kujeran da Ammi ke zaune hannu yasa yadago fuskarta murmushi ta sakan mai mai taushi ajiyan zuciya ya sauke yace “am sorry Rukayya, kiyakuri dakome matana zasuce I know kalaman su have hurt you kiyakuri kinji” murmushi Ammi tayi ta kama hanun Dady tana shafawa ahankali tace “karka sake ban hakuri ko daya ban damuba, hasalima godiya zanma, thank you for standing as a father to Aneesa agaban kowa Abu Aneesa” murmushi Dady yayi yace “ni mahaifinta ne so don’t ever thank me akan anything dazanma y’ata Ummu Aliyu” ahankali Ammi ta rungume shi tana murmushi, bayanta ya shafa murya chan kasa yace “Aneesa ta iya kwana ita kadai?” gyadamai kai Ammi tayi murya chan kasa tace “eh” murmushi Dady yayi yace “tashi to muje mumata saida safe” murmushi Ammi tayi tace “to Allah ja zamanin Maigidana” tashi Dady yayi yana murmushi yadaga ta yana rike da hannu ta suka fito daga part dinshi sukai part din Ammi Aneesa bata falo hakan yasa sukai sama atare itada Dady suka shiga dakin Aneesa harta kwanta tafara gyangyadi tarufe da bargo dan karfin AC yamata yawa yanda ta dukunkune yasa Dady yace “lafiya Aneesa ko zazzabin ne” da sauri tace “Abba sanyi nakeji” dariya Dady yayi ya rage AC to the lowest Ammi ta zauna kusada ita ta shafa kanta tace “saida safe zan tafi bangaren babanki a chan zan kwana” murmushi Aneesa tayi tace “saida safe Ammi na” ta kalli Dady daya tsaya yana kallon su sun bala’in burgeshi sosai tace “saida safe Abba na” murmushi Dady yayi yakara so wajen yaja hancin ta yace “saida safe yarinyan Abban ta” tashi Ammi tayi ta gyara mata bargon Dady ya kashe wutan dakin suka fito tareda rufe mata kofan, dakin ta Ammi ta shiga Dady ya rungume ta tabaya yace “mezaki yi anan?” dan murmushi tyi tace “kayan da zansa gobe zan dauka” hanunshi yasa tacikin hijabinta yana shafa cikinta dabaida girma ko kadan ahankali yace “karki damu akwai kayan dana ijiye awurina danake so kisamin gobe mutafi” sakinta yayi yakama hannunta suka fito daga dakin sukai sukai shashin shi.