A TSAKANKANIN SOYAYYA HAUSA NOVEL

A TSAKANKANIN SOYAYYA HAUSA NOVEL

Kulle kofa yayi yana rikeda hannunta sukai upstairs, makeken master bedroom dinshi yabude ya shiga yana rike da Ammin wani hadadden kamshi ya daki hancin ta, maida kofar yayi yarufe tareda sa hannu yazare mata hijabin dake jikinta, tana sanye dawani Jan dogon riga har kasa bin jikinta yay da kallo kafin ahankali yanuna mata bayi yace “shiga ki dauro alwala kizo”
Asuba ta gari Ammi da Dady????????????????.
[4/5, 8:09 AM] Hijabi_muslimah????: A TSAKANKANIN SOYAYYA

         _IN BETWEEN THE LOVE_
        ❤ _Lies another love_❤




        _✍????M Shakur_



                    3️⃣4️⃣

how to subscribe
zaki turo 300 kota card kota bank, 3107021073 aisha Muhammad first bank, saiki turo evidence of payment ta watsap number na 07012181461, marasa account can also send MTN card to my watsapp number 07012181461

duk wacce ta karanta min book batare data biyaba, da wacce ta fitarmin da book bada saninaba ban yafemuku ba

Sai wuraren karfe hudu na asuba Dady ya farka daga dadaddan baccin dayay awon gaba dashi, ahankali yamika hanunshi ya kunna bedside lamp dakin yadanyi haske, tsayawa yayi yana kallon fuskar Ammi dayake rungume da ita, ba karamin farantamai rai tayi jiyaba, kasa hakura yayi ya shiga shafa kumatun ta, bude idanu Ammi tayi, murmushi ta sakin ma Dady takai hannunta ta shafa gemunshi tana murmushi, shafa ta ya shiga yi kafin cikin salon so irin tasu ta manya ya shiga sarrafata yanda yakeso Ammi nabashi hadin kai, wanan karan har ihu saida Dady yayi dan Ammi gave him the ride of his life, da kyar suka bar juna ganin ana kiran asuba atare suka shiga bayi tun Ammi najin kunyan shi dan sai kallonta yake harta saki jiki tamai wanka tass dan umurtan ta yay datamai shima yamata wankan tass sanan ko wannensu yay wankan tsarki da kanshi kafin su fito, agurguje Daddy ya share jikinshi yabar Ammi na tsane kanta da towel yadauko jallabiyan shi ya shirya tsaf sanan yadau hula yasaka white itama, yazo gaban madubi ya feffesa turare ya kalli Ammi dahar lokacin ke goge gashin kanta da karamin towel yace “natafi masallaci gimbiya, bari natado Aliyu dan yacika son bacci kina ganin yaron nan mutafi tare” murmushi Ammi tayi tace “haka yara suke ai, yi sauri karku rasa jam’i” gyadamata kai Dady yayi yay hanyar fita daga dakin Ammi tabishi da kallo tana murmushi, saida ta tsane gashin tass sanan tadau doguwan riganta ta zura tahau kan dadduma tai salla abinta kafin ta cigaba da lazimi.

Almost to seven Dady da Aliyu daya saka milk jallabiya suka shigo gidan, Daddy ya tambayi Aliyu abinda ke damun shi yafi sau goma dan duk yay mai wani iri, juyawa Aliyu yayi zaiyi hanyar side dinshi Dady yarike mai hannu da sauri ya juyo yana kallon Dady da manyan idanunshi dasukai haske sosai sabida tashin dayayi daga bacci kaman yazuba madara, cikeda damuwa Dady yace “wai bazaka gayamin meke damunka ba Gadanga? Aliyu” Dady ya kirashi da dan tsatsauran murya hakan yasa ya kalli Dad din asanyaye kaman wani mara lafiya, cikin tsatsauran murya Dady yace “nace kafadamin meke damunka wlh Aliyu kasa hawan jinina yatashi just know is you, Son what happen to you dabaka iya gayamin matsalolin ka yanzu? Batun yau nalura abu nadamunka ba tun ranan daka shigo gidan nan hanunka duk bruises, what is wrong? What is disturbing my baby Boy dina Aliyu?” Dady yay maganan cike da sigan lallashin yaro yana shafa kumatun Aliyun, wani irin ajiyan zuciya Aliyu ya sauke arayuwan shi yanason lallashi kodan Dady ya raineshi a hakane oho, jikinshi nason ana lallashi shi, ahankali hawaye suka shiga taruwa a idanunshi batare dayay magana ba yana tuna kalaman Aneesa datana watsa musu kasa a mota she hates him kuma karya kara dawowa anguwan su, ganin yanda hawaye suka shiga xiccikowa a idanunshi yasa Dady yace “subhanallah Gadanga na” hanunshi yaja sukai part dinshi akan kujeran falonshi Dady yazaunar dashi yadawo ta gabanshi yaja center table yazauna akai cikeda damuwa yace “menene? What’s bothering you? Maman su Rauda ko any one of them ne suka batama rai komene” girgizama Dady kai yayi yana kokarin hana hawaye zubowa, hannu Dady yasa ya share hawayen yace “to menene kafadamin” ajiyan zuciya ya sauke yana kokarin controlling zuciyan shi, kafin yadago kai ya kalli Dady ahankali yace “I want to go back to California, nagaji da Nigeria, am tired of everything here Dad” wani irin daure fuska Daddy yayi kaman bashi bane ke lallabashi yanzun nanba, strictly babu alamun wasa yace “kaga Aliyu idan kasaka kafa ka kara barin Nigeria nan tokai da matarka ne, ina gayamaka, inbako hakaba to gaskiya kagama tafiya outside, I told you I want you to settle down, marry I want to see my grandchildren, ga yar abokina dana fadama sunyi makaranta da Hajar yau zamata zo gidan nan kace kai a’a da kanka zaka nemo da wace mace kake magana da zakace kai da kanka zaka nemo eh” shiru Aliyu yayi yanajin yanda Dady kemai fada kaman yafasa ihu, agogon dakin Dady ya kalla ganin bakwai tadan gota yasa yamike yace “zamu gama maganan nan anjima, yanzu inaso nakai yaran gidan nan hadda dakaina sabida nai enrolling yar yar new Mum dinka idan nadawo sai muje ka gaida new Mum dinka, go and shower son don’t conclude yau idan tazo zaka ganta okay” yay maganan yana bude kofa yafita ajiyan zuciya Aliyu ya sauke kafin yaciro wayarshi daga aljihu yana kallo ahankali ya kunna wayan yay dialing number Aneesa.

Tun asuba Aneesa ta tashi dan wani irin jin dadi da alfahari da sabon gidan yan gayun su take dudda babu datti amma saida ta gyara ko ina tun daga kan dakin Ammin ta har kasa, sanan ta dauko burner da turaren wutan da Ammi su tasa amata ta kunna wani shegen turare dayasa ko ina na gidan na kamshi sanan ta wuce kitchen so take tama Ammin ta da Abban ta breakfast din safe, kitchen din ta shiga tana kallon ko ina abubuwa ma dayawa tasan yanda ake amfani dasu irinsu gas din dasu oven da akwaisu a bakery datake aiki, store ta shiga ganin su Irish da sauran su yasa tadebo su Irish dayawa ta fere ta yanka ta wanke sanan tai hitting oil a pan tafara frying, takoma wajen fridge din datagani a kitchen din tabude ganin su frozen kaji ne da kayan ciki yasa ta dauko wani babban liver da kidney ta shiga yankasu so take tai liver and kidney source, sosai aiki ya kankama.
Wayarta data daura kan saman fridge ne ya shiga kara da sauri ta waigo tana kokarin kashe tap din datake dauraye plate, murmushi tayi taja towel tana goge hannunta tace “hala Ammi nane” karasawa tayi tadau wayan da saurin ta ganin ba Ammi bane number ne yasa ta tsaya tai turus tana kallo tadan turo baki tace “waye wanan? Ashema ba Ammi na bane, ni idan yan lalle ne koma kunzo gidanmu mubar gidan” tai maganan tai picking call din tareda dakaiwa kunnenta, cikin siriruwan muryanta tace “Hello, hello waye?” lumshe ido Aliyu yayi har chan cikin zuciyan shi yaji muryan nata wani irin ajiyan zuciya ya sauke mai kara dahar saida Aneesan taji, faduwa gabanta yayi hakan yasa tai shiru batare data kara cewa komiba, murya chan kasa irin na wanda ke cikeda damuwan nan sosai Aliyu yace “am sorry Aneesa, am sorry for what happened the last time I came, I…i…was…jea…” katse wayan Aneesa tayi tareda kashe ma wayan gabaki daya ta ijiye kan saman fridge din kirjinta na racing har lokacin ba tadawo daidai ba tarasa mesa mutumin nan nada wani irin strong effect akanta ita bata taba ganin namijin da ko magana yake mata saitaji wani iriba, cikeda tsiwa tace “ni me ruwana dakai dazaka wani cemin sorry, koma kazo gidan namu basai inka kara ganinaba, masifaffe kawai, sai yima mutum ihu akai kaman wani uban mutum” tajuya ta cigaba da aikinta tana kwashe Irish din tana zubawa Awani hadadden kula sanan tana hada source kuma. “iyye me daughter na take dafamana haka?” jin muryan Dady yasa tajuyo da sauri yana ta bakin kofan kitchen din a tsaye murmushi tayi tadan dukar dakai tace “ina kwana Abba” shigowa kitchen din Dady yayi yace “ai har sama naje banganki ba nace waya daukemin ya, ashe kina nan, naga kin gyara ko ina tun karfe nawa kika tashi haka?” murmushi tayi tace “tun asuba na tashi Abba shine bayan nagama komi na daura muku breakfast” sosai Dady yaji yanason Aneesa sanan yakara son Ammi dan abinda yaranshi mata basu iyaba kenan yanzun nan ma yaje yatada yaran kowani daki dan su shirya hadda yau lahadi, ji yayi kaman yama kwaso duka yaran yabama Ammi tabasu tarbiya irin wanan databama Aneesa, he wish tuntuni yamasan Ammi ya aureta, karasowa gaban gas din yayi ya shafa kan Aneesan yana kallon abincin yanda yay kyau sosai cikeda murmushi Aneesa tace “na zubama Abba?” murmushi Dady yayi yace “a’a saina dawo daga kaiku makaranta zanci, ai kinkusa gamawa ko?” gyadamai kai tayi da sauri tace “eh nagama miyan, wanan Irish din dake wutane na karshe” gyadakai Dady yayi yace “gud, kina gamawa kije kiyi wanka ki shirya hadda zan kaiku, inkin fito zan kawo miki lunch box daga store saiki zuba naki ciki dan tawas yayi babu lokacin da zaki zauna kici inkinje makaranta sai kici” cikin murna sosai tace “to Abbana, nagode” murmushi shima Dady yayi duk inta cemai Abbana dadi yakeji sosai gatada yawan godiya kaman maman ta, wucewa yayi yafita yay part dinshi, tundaga falo yaga falon yay tsaf tsaf abinda matayen shi basayi Kenn saidai mai aikinshi yamai, murmushi yayi yanabin ko ina da kallo yay bedroom akan dadduma yaga Ammi sanye da hijabi tana karanta wani littafin zikiri nashi, ganin Dady yasa ta rufe ahankali ta ijiye ta mike tsaye tana kallonshi yanda ya jingina da kofa yay folding hannu a kirji yana kallonta,
[14/03, 08:14] Aishat Muhammad: Karasowa tayi har gabanshi hanunshi daya rungume takamo takai bayanta kafin ahankali ta shige jikinshi ta rungume shi murya chan kasa tace “ina kwana yallabai na” lumshe ido Dady yayi yana shafa tattausan bayanta murya chan kasa yace “best greeting ever, morning Yallabiyar Yallaban ta” dan dariya dukansu sukayi atare dan yanda Dady yay maganan was damn funny, yana rungume da ita yay wajen wardrobe dinshi yabude wani fitinannen shadda mai ruwan sky blue yaciro nashi da nata dinkaku nata doguwan riga an mata stone work daga sama zuwa kasa murya chan kasa yace “ataimaka a shirya ma yallabai cikin kayan nan” murmushi Ammi tayi batare data ce mai komiba ta cire hijabin ta shiga shiryawa kaman yanda shima Dady ya shiga shiryawa cikin kayan yana kallonta, rigan kaman an aunata juyowa Ammi tayi ganin ita yake kallo yasa ta nuna kanta tace “aunani kayi batare da nasani ba ne Alhaji na” dan dariya Dady yayi yace “dole nasan ya abinda nakeso yake tahonan kiga” yaja hannun Ammi zaunar da ita yayi agaban kujeran madubi ta zauna sanan yakoma wajen wardrobe din wani dan akwatin sarka yadauko yadawo yaboye a bayanshi yace “rufe idanun” kulle ido Ammi tayi ahankali yabude akwatin wani sakan zinare ne mai bala’in kyau yaciro ya sanya mata ahankali Ammi zata bude ido yace “a’a ba yanzu ba” da kunne da awarwaro yasaka mata yana kallonta ta madubi yanda tai kyau ahankali yace “bude idanun” ahankali Ammi tabude idanunta tana kallon kanta amadubi yanda sakan zinaren yamata kyau wani irin dan ihu Ammi tayi ta rufe bakinta tana zaro ido ganin gold sarka ajikinta kafin ta tashi da sauri tafada jikin Dady da gudu tana tsalle kaman wata yarinya tace “is so beautiful, so gorgeous, oh I love it, thank you mijina, abin alfahari na” yanda ta kanannade Dady yasa yaji yana neman zaucewa cikin dishashewan murya yace “zaki hanani kai yara makaranta ko Rukayya kike min wanan abu haka wash Allah” dariya sosai Ammi tayi ta daga shi tareda tashi dashi zaune tace “tubanake” dariya Dady yayi yadau mayafi ya yafamata da kanshi kayan data cire ya linke yasaka a wardrobe dinshi yakama hannunta yace “muje” fitowa sukayi daga dakin sunyi kyau bana wasaba har store compound din ya kaita yana nuna mata komi kafin ya dauko new lunch box na yanmata da kuma goran bottle na yan gayun yaran nan karba Ammi tayi daga hannu shi ta tayashi rikewa sanan suka fito sukai shashinta, daidai lokacin Aneesa ta sauko tana sanye da dogon rigan atampa milk da gold sai wani milk color hijabinta mai hula har kasa ganin Ammi yasa tai wajen Ammi da gudunta Dady na dariya yazauna kan kujera, kallonta Ammi tayi tace “ina zaki kika shirya haka” murmushi tayi tace “Abbana ne yace na shirya zai kaimu hadda” ahankali Ammi ta kalli Dady intace bataji dadi ba tai karya yanda Dady ke nuna ma Aneesa so yasa ta cikin yaran nashi da gaske shine yafi komi yimata dadi a lamarin, batare da Dady ya kalleta ba yana kallon TV yace “bazaki je kibama yarinya na abinci ba sai kinsata latti tawas harta wuce da minti goma” murmushi kawai Ammi tayi cikeda son Dady ta kalli Aneesa tace “muje kitchen din, mekika dafa haka yaketa kamshi?” binsu da kallo Dady yayi harsuka shiga kitchen yanajin yanda suke hira Aneesa na dariya Ammi ma nadan dariya, hada mata abincin Ammi tayi sanan ta hada tea tajuye agoran Ammi sai kallon Aneesan take the joy she’s seeing a fuskar Aneesan kadai yasa taji she can withstand koma wace irin kaddara ce inhar daga gidan nan just so wanan happiness dinan bazai gushe daga fuskan Aneesa ba, goran tamika mata Aneesa ta karba duk tarike suka fito Dady ya mike tace “yauwa muje” hannu Aneesa tadagama Ammi tace “bye bye Ammi na” hannu Ammi ta daga mata tace “ayi karatu da kyau, Allah bada sa’a, Abu Aneesa adawo lafiya” wani irin kallo Dady yamata kafin yafaki idanun Aneesa ya kashe mata ido tareda wurga mata kiss, girgiza kai Ammi tayi tana murmushi aranta tace “na auri dan duniya dan boko” parking space sukayi inda Aneesa taga kusan duka yaran datagani jiya yan manya manyan suna wurin duk sanye da maroon hijab mai baje da alamu shine hijabin makarantan, babban sune wacce bata mata fuskan taba ta jiya dake ta Harare Harare a falon Dady tagani tsaye tana danna waya tana taunan cingum, “ban wayan nan Hajara” Dady yay maganan babu alamun wasa kaman zatai kuka tace “Dady fa kirana akayi ka yakuri” “will you give me that phone ba’a hanaku zuwa makaranta da waya ba” and kiyarda cingum din bakin nan naki kafin na kifa miki mari” yarda cingum din tayi tamikama Dady wayan kaman zatai kuka ta tsani islamiyya da wanan had dan mutum yagama University amma Daddy yace saita dinga zuwa haba bude musu babban motar family car Dady yayi mai kiran sienna amma tafi sienna ma girma yace “ina Rauda maisa bata fitoba” ahankali Hajar datai kini kini da rai tace “cikinta ke ciwo” baice komiba dan yasan Rauda nason zuwa makaranta shiga motan sukayi ko wanne dauke da lunch box dinshi yaran sai gaida Aneesa suke Dady yarufe motan ya shiga gaba yaja motar soja yabude Gate suka fita.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57Next page

Leave a Reply

Back to top button