A TSAKANKANIN SOYAYYA HAUSA NOVEL

A TSAKANKANIN SOYAYYA HAUSA NOVEL

Ana kiraye kirayen salla ta shiga gidansu da sallama babu kowa a tsakar gidan, hijabin ta tacire ta daura kan igiya tadau butan datagani gaban rijiya tai hanyar bayi sanin Ammi na salla yasa bata kirata ba ta shiga bayin, bata jimaba tafito ta tsugunna tai alwala tadau hijabin da jakanta tai sallama ta shiga dakinsu, agefen Ammi dake salla taje ta tsaya ta tada sallanta.
Sallame sallan tayi tadaura kanta kan kafadar Ammi data idar da sallan tuntuni ashagwabe tace “wayyo Allah na Ammi nagaji wlh, yunwa nakeji” dagota Ammi tayi tace “sannu kinji, nasamiki ruwan zafi akan rushi, wanka zakifarayi kokuma abinci zaki faraci?” hijabin jikinta ta zare ta wurga kan kujera tana yatsine fuska tace “abinci Ammi, ni abinci zan faraci, mekika dafa? Tuwo Ammi?” tai tambayan kaman zatai kuka, hararanta Ammi tayi tace “common je dakinki kidauko kulan abincin ki kizonan kici, shi tuwon meyamiki dabaza kiciba?” tashi tayi kaman zatai kuka tai hanyar dakinta tace “ni banson Tuwo wlh” dakin ta shiga tadau kulan dakenan kusada gadonta tafito tana daure fuska dauke kai Ammi tayi tacigaba da addu’oin ta kaman bata ganta ba, zama tayi ahankali gefen Ammi tabude kulan kaman bataso tabude, karo taci da hadadden jellof rice harda su carrot da green beans aciki, gadan Babban bindin kifi nan guda daya asaman kan abincin, batasan lokacin data saki wani gamshashen murmushi ba ta dagakai ta kalli Ammin, hada ido sukayi ta watsa mata harara hakan yasa tasa hannu ta rufe fuskarta tana dariya akunyace ta mike tsaye taje tadauko cokali da ruwa a kofi tadawo tazauna tafaraci bakaramin dadi abincin yayiba Ammi ta iya girki sosai, tass ta tada abincin Ammi ta kalli yanda ta tada abincin tace “inzaki kara akwai a tukunya kije kidebo” girgiza kai tayi tanacin kifinta tace “nakoshi Ammi na, nagode, Ammi shinkafan yay dadi wlh, kifin washh soo crunchy Ammi” tana maganan tana lumlumshe ido tsabagen dadi, dan murmushi Ammi tayi cikin tsananin son yar tata tace “tashi kije kiyi wanka dare nayi” “to” tashi tayi ta tattara kayan dataci abinci dasu tawuce tafita takai kitchen sanan tadau bucket tahada ruwan takoma daki ta cire kaya tadaura zani tafito tadau ruwan da ta shiga bayi tana gamawa tafito ta wuce dakin dogon rigan baccinta tasaka tasa hijabi tazo tai isha agefen Ammi tana idarwa tai shafa’i da wuturi ta mike tsaye tace “Ammi bacci nagaji sosai” “jeki kwanta sannu kinji, saida safe” gyadama Ammi kai tayi tai hanyar dakinta, Ammi databita da kallo tace “kiyi addu’an bacci kafin ki kwanta” “to” tace ta shiga daki da Bismilla tafada gado ta lumshe ido addu’an bacci takaran to sai bacci.


Avalon Hollywood & Bardot, California .

Parking motar bodyguard dinshi yayi a parking lot din babban club din, baima san sun isoba sabida wayarshi dayake daddannawa yana sanye dawata buttoned shoulder strip wool sweater na Paco Rabanne, orange and black color ne sweater dayamai kyau banawasaba, yana sanye dawani Black Marni trouser kafafunshi sanye da wani black boot na Lanvin, yasaka sweater ne sabida muran dayake yi sai wani hadadden kamshi yakeyi kaman ka lashe kamshin tsabagen dadinshi, budemai kofan da akayi yasa ya dagokai ya kalli bodyguard din dake jiran ya sauko, saukowa yayi ahankali ya zuba hanunshi a aljihu yay gaba yana taku daidai, rufe motar bodyguard din yayi sukabi bayanshi da sauri, juyowa yayi fuskarshi adaure jin karan takalman su, wani irin haushin su yakeji yanda suke binshi dinan kaman wani karamin yaro, ahankali cikin soft voice dinshi dan baiso yamusu ihu ya janyo attention yace “you guys should wait for me in the car, give me some break” yawuce yay ciki cikin fushi sosai, sukuma babu yanda suka iya suka koma mota suka zauna.
Budemai door security wurin sukayi ya shiga cikin club din da waka ke tashi mutane na rawa a dance floor, wasu na buga bar games da sauran su, yatsine fuska yayi yadan cije lips dinshi yahau kan stairs din yay sama ya doshi wani waje da aka rubuta VIP Only, security dake wajen suna ganin shi suka matsamai ya shige yana shiga wasu maza hudu ne zaune wani black sai sauran farare turawa ga shisha pot agaban su da manya manyan bottle din wine da glass cups, suna ganin shi sukai ihu. “you are late Leo” haka suke kiranshi da Leo tun farkon shigan shi school idan za’a kira sunan shi Aliyu saidai suce Aleo shine friends dinan nashi kawai suka cire A din farko suka radamai Leo, zama yayi kusada black guy din Wanda shikadai ne yay kama da dan Nigeria cikinsu sauran duk da turawa ne. “ahhh wash, my legs” black din dake kusada shine yace “where are your guards Dady’s boy?” daga yanayin yanda yay maganan zaka gane tsokanar shi yake nema hakan yasa sauran suka fashe da dariya sosai, hararan su yayi yace “I came alone” “whowhowhow! Kai nawa, lemme just call this a white lie right guys?” ya tambayi sauran mazan atare sukace “yeah, is a white lie” sukahau dariya ganin iskanci sukemai yasa ya kalli bar attendant din wurin yace “non alcoholic wine pls” da sauri mutumin yajuya dan zuwa daukomai, juyowa yayi ya kallesu ganin duksun tsareshi da ido suna shan shishan su yace “wats up guys?” wani daga cikinsu ne cikin harshen turenci dan duk da turenci suke magana yace “magana muke akan irin matan damukeso mu aura in the future, I personally Leo want to marry sangartacciyar yarinya, yarinyar yar gayu mai kyau wacce tasan gata, yar gidan masu kudi, kai wacce irin mace kakeso ka aura Leo?” daidai lokacin bar attendant din yakawo mai wine din dayay requesting karban wine din yayi daya zubamai a glass cup, Bash dan Nigeria dake kusada shi ya kalli wanda yama Aliyu tambayar yace “me kake tambayar Leo irin matar dazai aura, kaima kasan Leo ready made yar gata zai aura, am sure yarinyar president zai aura?”.

Tabe baki yayi jin maganan da Bash yayi yakai wine dinshi baki yana kara shigewa cikin kujera da kyau, ganin baida niyyan magana sun saba dama da iskancin shi yasa daya daga cikin turawan mai suna Frodd yace “ni inaso na auri matan data girmeni sosai at least tabani 10 good yrs” atare dukansu sukai kallai harda Aliyu dake sipping red wine dinshi, daga musu gira yayi yace “yes, idan ka auri wacce ta girmeka tafi riritaka, tafi kula dakai, tana kuladakai kaman dan kwai cus it took her a very long time kafin tasameka so u will be well taken care of, you are just like an asset awurin ta” dariya dukansu sukayi banda Aliyu da yadanyi murmushi kana ganinsu kasan suna enjoying hiran dasukeyi abunsu ganin yana murmushi yasa sukace “come onnnnnn Leo tell us yours” dan bude ido yayi ya kallesu saikuma yay murmushi ya daga glass cup din hanunshi yana kallon wine din yay shiru kaman yana tunani dan fuzar da iska yay kadan ya gyara zaman dayay akan kujeran mai kama da kwanciya ya daura glasscup din akan kirjinshi yace “I don’t think I will ever get married but if I will matar danake so na aura” yay shiru yasa hanunshi yacire glasscup din daga kan kirjinshi yadaga sama tareda bude idanunshi ya kalli glasscup din dayake dan girgizawa ahankali yace “inaso na auri mace dat is not from a wealthy home, rich girls are too stupid and proud I hate them” ya yatsine fuska kadan cikin sassanyar muryanshi yace “I want a hardworking smart girl mara son jiki a kazar kazar girl” yasake yin shiru yana girgiza cup din yace “a good cook, obidient and gently being, a girl that She sees me for me, I want Inner Beauty in a lady not facial, if her heart is beautiful am okay” yay dan shiru kafin ahankali yace “I want a girl that am naturally attracted to, attraction is the basis of love and marriage, and if the spark isn’t there, it’s something that’s really hard to fake” yay shiru yace “a girl that is not too expose mai kunya, yarinya mai hankali da taimako” yadanyi shiru kafin ya yatsine fuska ahankali yace “I just want a girl that will beat my imagination, I want a girl that will beat all this qualities I listed and be more and more and more” dan murmushi yayi ya ijiye glasscup din yace “anyway nasan they’re no such girls on this earth, so I ain’t gonna stress myself with marriage, nowadays girls are too lousy guys” yasake yatsine fuska agajiye duk dariya sukahau yi Bash yadan buga kafadarshi yace “u are just talking ne, irinku har kuka kukema soyayya, aure maybe ma duk saika rigamu aure muna nan dakai” kabar da hanun Bash din yayi yay hamma yana duba rolex din hanunshi ganin kusan 1:30 nadare yace “night guys am sleepy, I will be travelling tomorrow” atare duk sukace “where to?” tashi yayi ahankali yace “home” Yajuya ahankali yana daga musu hannu yay waje, bacci yakeji bana wasaba da kyar yakai parking lot aka budemai mota ya shiga ya kwantar da kanshi jikin kujera ya lumshe ido sai bacci.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57Next page

Leave a Reply

Back to top button