A TSAKANKANIN SOYAYYA HAUSA NOVEL

Wani irin Uban harara Hajar tama Aneesa dake gefenta tace “aisai afita ko Malama tunda ba motan ubanki bane” ko kallonta Aneesa batayiba dama tun dazu take mata surutai bata tanka taba dan bataso tabatama Ammi rai da wlh dudda tafita girma saita lallasata karfi ba ajiki bane fess zata fasamata baki, ahankali tasa hannu tadau lunch box dinta da bottle din ruwanta ta tattara uban littatafan da aka bata kusan guda goma sha shida a hannu dan bataje da jakaba ta sauko daga motan da kyar kaman zata fadi abubuwan hannunta duk sun mata yawa, wani irin faduwa gabanta yayi dabata San mesa ba, kodai ciwon kirji ke neman damunta ne tana yawan having faduwa gaba this days, dan gajeren tsaki taja batason zagin da Hajar tamata yabata mata rai tafara tafiya ahankali zuwa shashin su, tunda motar tai parking Aliyu yake bin masu fitowa daga motan dai dai da kallo ganin Aneesa ta sauko ahankali daga motar yasa yawani irin mike tsaye yana kallonta ganin still ita yake gani tana tafiya ahankali as usual yasa yarufe ido da sauri yasake budewa yadaurasu akanta, still Aneesa yagani as usual da wanan dogon hijabin nata da safa akafafunta yasa yaji zuciyar shi na bugawa is he dreaming or what? Is he okay kodai yasoma samin matsalan kwakwalwa kaman yanda Abdul yake cewa? Is this his Aneesa ko idanunshi gizo sukemai?…..
Duk wacce takaranta batare data biyaba Allah ya isa, duk wacce tafitar min da book Allah ya isa.
Kwasan lunch box Hajar keyi agaban motar tana kallon Aneesa yanda take tafiya ahankali, jitake kaman ta kasheta tsaki taja tace “tana mana tafiya cikin gidanmu agadarance kaman gidan ubanta ne, agola kawai” daukan bottle water dinta tayi da sauri tafara tafiya tace “zakici ubanki ne yanda kikazo gidan nan saikin gudu da kafafun ki kinbarshi munafuka” dawani irin sauri tahau tafiya harta cimma Aneesa, wani irin bangaje Aneesan tayi tasa hannu tawani irin turata, wani irin juyi juyi sau biyu Aneesa tayi tsabagen yanda tajuyata kafin tayi wani irin mugun faduwa tai wani irin ihun azaba lunch box da littatafan hannunta suka wawwatse a compound din hijabinta yadaga yarufe mata fuska tabuge gefen bakinta sosai da mandibular bone dinta, dawani irin sauri Aliyu yafito daga bukkan ganin abinda Hajar tayi, ganin Ya Aliyu yasa Hajar ta kwasa da gudu tai flat dinsu dan bamata luradashi ba tabude kofa ta shige tareda garkamewa da key, karasowa inda take Aliyu yayi tana kokarin tashi takasa, ahankali ya tsugunna batare daya tadata ba danso yake yakara tantancema idanunshi cewa Aneesa ce yagani ba daya daga cikin kanninshi ba dan zuciyar shi nacemai gizo idanunshi kemai, hannu yasa gently yadaura kan hijabin daya rufe mata fuska yanaja ahankali kaman wanda baiso yaja, ahankali hijabin kezamowa kasa tundaga kwantaccen gashin goshinta dake nan a kwance yakebi da kallo heart dinshi nawani irin racing har zuwa kan eyebrows dinta dake nan acike har inbetween dinsu gasu so dark kaman ta kwabasu da kwalli, gently yacigaba dajan hijabin kasa ahankali karan hancinta da idanunta dakenan alumshe suka bayyana dogayen zara zaran gashin idanunta suka bayyana, wani irin gasping yayi iskan daya fitar suka sauka akan fuskarta kadan kadan ta shiga bude idanunta dakatar dajan hijabin kasa yayi yana kallon yanda kwayan idanunta kerawa tana shirin budesu kadan kadan take bude idanun, dishi dishi take gani dan tabugu sosai barin ma bakinta dataji yana mata zafi sosai saikuma goshinta kaman an bugamata guduma, dukda dishi dishin datake gani bai hanata ganin wani farin halitta da fuskan shi ke dab da nataba yana sanye da fararen kaya, bakin sajemshi da pink lips dinshi ta take kallo suna shining kaman ya shafa mai, tun ganin dishi dishi harta karasa bude idanun tass tana kallonshi kaman yanda shima yake kallonta har idanunta suka washe sukai clear. “you!” tafada da sauri akuma dan tsorace ganin masifaffen nan maima mutane ihu kaman yayan shi ne, tashi tayi da sauri daga kwancen datake akasa tana yatsine fuska sabida ciwo da jikinta keyi tana kallonshi kaman yauta fara ganinshi shima haka yake kallonta danko kyafta ido bayayi, akaro na biyu tace “you!” hannu tasa ahankali ta goge idanunta dan gani tayi kaman gizo suke mata ya akayi wanan mutumin yabiyota gidan Abban ta lallai wanan mayene kodai gizo idanunta kemata, ahankali tabude idanun danta kara tantancewa, ganin har lokacin shine dai yatasata agaba yana kallonta surprisingly yasa ta juyar da kai tana bin ko ina na gidan da kallo dan takara tabbatarwa da cewa gidan Abban ta take, cgidan Abba na nake tafada azuciyan ta, da sauri tajuyo ta kalleshi tareda daure fuska tamau tace “me kakeyi a gidan Abba na?” shiru yayi yana kallonta sai yanzu datamai magana yasake yarda da cewa itane, Aneesan shice, she’s the one, but me takeyi a gidan nan together da kanninshi? “wayace kabiyoni gidan Abba na eh? Kokatashi kafita konakira maka Abba na yanzun nan asa sojojin chan su fitar dakai nagayam….” kasa karasa maganan tayi dan kallon dayake mata yay yawa gashi ya mugun cika mata ido, yay kyau bana wasaba, dauke kai tayi tajuya tana kallon flat din Ammin ta sotake tamike tsaye amma kafafun ta zafi suke mata ganinshi datayi ne yasa ta daure da wlh saitai kuka dan hadadden faduwa tayi, ganin har lokacin ko motsi baiyiba yasa ta juyo ta kallai cikeda tsiwa tace “nace katashi kabarmana gidan mu, I don’t need your sorry kuma koma waye yabarka ka shigo gidanmu saina hadashi da Abba na, ka tashi kafita I don’t wanna see you ever again, nan gidanmu ne kamin masifa anan sainasaka wayan chan sojojin Gate din chan su kulle ka, katashi kabar mana gidanmu kafin nakira maka Abba na” dan murmushi yayi zuciyar shi tamai wani irin sanyi dan from the way Aneesa is talking yagane cewa itace yarinyar new Mum, wacce Dady yacemai zaije yasa ta a makarantan su Rauda yau, no wonder dayaji muryan Ammi yaji kaman yataba jin muryan dayake ranan kanshi na kasa bai ganeta ba. “dariya ma kake ko, okay saina kirama Abba na ko katashi katafi kona kirashi” wani irin murmushin yayi ko Allah yasan he just love this pretty girl, Aneesah is perfect, Mesmeric, charming, alluring, beautiful and above all she’s courageous this her boldness kills him gaba daya, cikin muryan shi mai bala’in dadi yana kallon kwayan idanunta yace “please call him dama shinazo gani yabani auren ki” wani irin kallo tamai saikuma ta dauke kai tana turomai baki tace “huu’um Allah kyauta na aureka” kaman zaimata kuka a mugun shagwabe yace “but whyyyyy?” sakin cute mouth dinta tayi wide open cikeda mamaki tana kallonshi ganin yanda yawani yimata magana a shagwabe kaman zai mata kuka yana kallonta, da sauri ta dauke kai gabanta na mugun faduwa dan yanda yamata har cikin kasan ranta tajishi, bakinta nadan rawa dan jitayi batada natsuwa kuma tace “k….ka w…ka wuce katafi kafin nakira maka Abba na, zaisa a kulle kafa” murmushi yayi yana kallon yanda take magana dimples dinta na lotsawa yace “inhar akanki ne zan iya jure komi, zaki aure ni?” makemai kafada tayi batare data kalleshi ba dan bataso ta kallai wani iri takeji tace “a’a” , Murya chan kasa yace “please Anebabyyy!” yanda yakirata dawani sabon suna da ba’a taba kiranta dashiba yasa taji kirjinta yakara bugawa, kin kallonshi tayi saima kokarin tashi datayi tana gyara hijabinta hannunta dako ina na jikinta na rawa.