A TSAKANKANIN SOYAYYA HAUSA NOVEL

A TSAKANKANIN SOYAYYA HAUSA NOVEL

How to subscribe
Zaki turo 300 ta account number na 3107021073 aisha Muhammad first bank saiki turo evidence of payment to WhatsApp Number na 07012181461, sainai adding dinki a group din a tsakanin soyyayya.
[4/5, 8:09 AM] Hijabi_muslimah????: A TSAKANKANIN SOYAYYA

         _IN BETWEEN THE LOVE_
        ❤ _Lies another love_❤




        _✍????M Shakur_



                    3️⃣6️⃣

Gabaki tayi tayi loosing control bama tasan metakeyiba kokarin tashi take takasa, kalaman shi nada wani irin asirtaccen power akanta data kasa fassawara, ganin yanda takeyi takasa tashi jikinta sai rawa yake yasa cikin wani low voice yana kallon fuskarta yace “in dagaki wife?” ko kallonshi batayiba saima wani karfi dataji yazo mata ta mike tsaye da kyar daidai lokacin Dady yabude kofan flat din Ammi yafito, wani irin murmushi tayi tajuyo ta kalli Aliyun dake kallonta tace “kagani ko zakajama kanka, ga Abba nanan yafito yau sunanka sorry banga abinda zai hana Abba na karya kulleka ba, bazaka tashi katafi ba” make mata kafada yayi a shagwabe yace “uhm’uh jiran shi nake yazo yabani auren ki inba hakaba zan mutu” dauke kai tayi da sauri ita yanda yakemata shgawaba ma wani bambaran yake mata but she must admit he looks damn handsome idan yanayin, harara ta watsa mai tace “chab Allah kyauta na aureka, huu’um bari Abba na yazo nagayashi dakai kaga abinda zai faru” tai kwafa tajuya tai wurin Dady dake tahowa wurin su da sauri yana kallon Aliyu da kafafunshi ke kasa kaman wanda akasa punishment, wurin Dady tayi kafinma tai magana Dady da hankalinshi gabaki daya kekan Aliyu yace “wat are you doing haka Son akasa? Eh Gadanga na menene?” da sauri yayi wurin Aliyu yana maganan, dagoshi yayi yanabin jikinshi da kallo tareda kakkabe mai guwiwan farin wandon shaddan shi dayadan yi datti kadan dan gidan fesfes ne yace “me kake yi akasa haka?” murmushi yayi batare dayace komiba yanuna Aneesa data tsaya turus tana kallon ikon Allah zatakaima Abba karan Aliyu taga kuma yanacemai Son, ahankali yace “Aneesa ne tafadi akasa Dadd!” yawani irin fadan Dad din da karfi dayasa Aneesa tadago kai ta kallai suka hada ido yamata wani shegen kallo mai tafiya da zuciyan mace, juyowa Dady yayi ya kalli Aneesa yana sakin Aliyu cikeda damuwa yace “subhanallahi garin yaya kika fadi Aneesa?” murmushi takakalo tana kakkabe kumatun ta da hannu tama rasa me zatace da bakinta yabushe tace “ahhh, ummm Abba, dama littatafan da aka banine sukamin yawa a hannu banje da jakaba shine nai tuntube nafadi” cikeda tausayinta Dady yace “sorry bakiji ciwo bako?” gyadamai kai tayi ahankali, yace “okay ga yayanki nan” yajuya ya kalli Aliyu yace “kai kuma tayata kwashe littafan ka kaimata daki kadawo wurin Nafisa ka barta ita kadai” yay maganan yana kallon Nafisa dayaga tana zaune kan kujera a bukka tana kallonsu, yace “akwai wanda zangani awaje am coming” yay hanyar gate, ahankali Aliyu ke kwashe books din yana kallon fuskanta yana murmushi yace “mai Abba” da sauri tarufe fuskanta da hijabi cikeda kunyan abinda tayi, fitowa daga bukkan Nafisa tai zuciyanta namata zafi ganin yanda Aliyu yama manta da ita, taya za’ayi tazo wurinshi amma baida lokacin ta, tana tafiya takalmin ta na kara kwas kwas kwas hakan yaja hankalin Aneesa yasa ta dago kai ta kalli direction din, wata kyakyawan yarinya daga gani zata girmeta tana sanye dawani hadadden lace ne tagani ke karasowa inda suke, daidai inda Aliyu yake a tsugunne yana kwasan books din Aneesa ne ta tsaya akanshi tadan kalli Aneesa dake binta da kallo, yatsine fuska tayi kaman taga kashi ta kalli Aliyun cikin muryanta nayan gayu tace “baby leave the parking of the books for her, tana tsaye kana kwashe mata littatafai kaman wani dan aikinta” dagokai ahankali Aliyu yayi ya kalleta batare dayace komiba yadau last book din kasan ya mike tsaye ahankali yajuya zaiyi wurin Aneesa kaman baimasan anamai maganaba, cikin jin haushi ganin iskancin dayake mata Nafisa tace “am talking to you fa Aliyu kakuma shareni, kan yarinyar nan kake shareni, who is she by the way? Ba Rauda bace ba kuma Hajar bace who is she, banma santa ba I know all the girls in this house, kabar mata book dinta muje muyi hiranmu” wani irin haushi da bakin ciki Aneesa taji yatokare mata wuya batasan lokacin data juya azuciye tai hanyar flat dinsu ba, juyowa Aliyu yayi ranshi abace yama Nafisan dake bayanshi dab dashi kaman zata shige jikinshi wani irin mugun kallo yace “you see that girl” yanuna mata Aneesa dake kokarin bude kofar flat dinsu yace “wanan zuciyan dakike gani” yanuna mata zuciya shi da hannu yana kallon fuskanta yace “my heart beats for her only, Only Her! She occupy every single space aciki babu ragowan waje dazan iya sakala ki Nafisa, I can’t love mata biyu, she’s the definition of the woman I want in my life, so goodbye and thanks for the ziyara bani nakiraki ba daman, Pops nawaje” yajuya yay hanyar flat din Ammi yana tafiyan nan cikeda isa.

not edited

Wani irin kukane Nafisa taji zaizo mata da sauri tabi bayan shi hanunshi tarike gam hakan yasa Aliyu ya tsaya chak zagayowa tayi ta gabanshi bakinta na rawa tana kallon fuskarshi kaman zatai kuka tace “please karkamin haka Aliyu cus I love you so much from the first time I set my eyes on you” dan yatsine fuska yayi yace “hardlock, nima from the first time I set my eyes on you naji bakimin ba, excuse me my hand” yanuna mata hanunshi data rike ahankali tasaki hannun yajuya yabude kofan flat dinsu Ammi ya shiga tabi bayanshi da kallo kafin ta kwasa da gudu tai flat dinsu maman Rauda fadawa dakin tayi daga Mama sai Hajar afalo tanacin white rice a plate fadawa jikin Mama tayi tasaki kuka sosai arude mama tace “subhanallahi, ke lafiya Nafisa zaki shigo gida da kuka kaman wacce akama rasuwa, minene?” cikin kuka tace “Mama Aliyu yace bayasona wai” daure fuska Mama tayi tace “wani Aliyun dai tukunna” cikin kuka tace “na gidan nan” tsaki daga Mama har Rauda sukayi atare Mama ta turata tace “uban me ya hadaki da Aliyu dama kinsan shine” girgizama Mama kai tayi tace “Dady yazo gidanmu wurin baba ranan shine yace nazo naga Aliyu innaumai ahada auren mu, wlh ina ganinshi yau naji ina sonshi sosai kuma wai bayasona” tsaki Mama takaraja tace “Allah na sonki ne yasa yace miki haka, me zakiyi da miji a matsayin Aliyu? Yaron daya rako maza duniya kina ganinshi haka koke a matsayin ki na mace kin fushi karfi, inda nabar Hajar tsaf zata iyamai lilis billahillazi, ki gujema kanki Aliyu ina miki fada, bari kiga neje nadubo Rauda da ciki kota tashi ga kawarki nan zata fadamiki waye Aliyun in kunne yaji ganganjiki ya tsira idan ma bakiji ba mamanki zan kira wlh” tai maganan tana tafiya.

Ahankali Aliyu yabude kofar falon Abdul ne kawai a falo yana kallon kwallo su Mami duk suna sama, shigowa yayi yamaida kofan yarufe yakaraso tsakiyan falon da sauri Abdul yatashi zaune yace “kai dama Barkono anan….” alamun Aliyu yamai dayay shiru hakan yasa yay shiru yana murmushi shima murmushi Aliyu yayi yana kallon ko ina nace “ina take?” sama Abdul ya nunamai da hannu yace “sun tafi sama tareda Ihsan” gyadamai kai yayi ya ijiye books din kan center table, alamun tafiya dayaji yasa ya dago kanshi Aneesa ce ke saukowa daga stairs tana sanye dawani baby pink hijab iya guiwa daga gani irin nazaman gidan nanne tasa wata yar shimi da straight skirt mai tsagu ta gefe daya, fuskanta da dan lema lema alamun daga wanka tafito kaya kawai tasa tana tafiya ahankali, tundaga kan yatsun kafafun ta dake dauke da fararen kumba yake kallo gasunan ajere gwanin ban sha’awa yake kallo har zuwa kan side slit din skirt din da idan tana tafiya yake fito da fatar yar kafarta dakeda kwanta cen gashi kaman irin yarannan dabasu san wahala ba wani irin serious murdamai cikin shi yayi dayasa yadauke idanunshi daga kan kafar nata yamaida kan fuskarta sabida wankan datayi har wani extra glow fuskarta yakara kan normal glow dinta karasa saukowa kasan tayi batare data kalli indama sukeba shi dama Abdul kallon match abinshi yake baima kufada itaba hanyar kitchen dinsu tayi ahankali tabude kitchen din ta shiga, kallon stairs Aliyu yayi ganin babu mai zuwa yasa yatashi daga kan kujeran yay kitchen bude kofan yayi ya shiga da sauri Aneesa dake kokarin daukan plate ta juyo suka hada ido maida kofan yayi yarufe ya shigo kitchen din dauke kai tayi daga kallonshi dan wani irin haushin shi takeji tadau kulan da Ammi tace ta zuba mata abincin ta gudun karyay sanyi tadau chokalin dinan abinci zata diba, ahankali ya tsaya agefenta yana kallon abincin datake shirin diba murya chan kasa yace “Aneesah nah!” wani abune taji yatokare mata zuciya sabida yanda yakirata kokarin diban abincin take tamasa a plate takasa hakan yasa ta ijiye kulan cikeda tsiwa ta kallai tace “karka kara cemin Aneesan ka, no karma kakara kiran sunana, na fadamaka baruwan ka dani, kuma ka koma inda kafito kabarmana dakinmu, su baby kakide, mutum kato dashi ana cemai baby, a’a ba baby baibo” ta harari bango tajuya tadau kulan abincin with annoyance kaman shi yamata laifi tana kokarin diba, dudda shi ba ma’abocin yin soyayya bane but from the look all he sees is jealousy a fuskan Aneesa so that means Aneesa na sonshi harma tana kishin shi, wani irin dadin yaji, hannunshi yamika ya fizge kulan abincin datake yin dambe dashi da sauri ta kallai tana kokarin danne feeling of kukan da takeji tamikamai hannunta cikeda masifa tace “kabani kulana” make mata kafada yayi yana karanta sakonni daban daban dake kwance akan fuskanta, cikin fushi tace “zan hadaka da Ammi na, kabani kulana nace” sake make mata kafada yayi ya ijiye kulan kan fridge dake bayanshi kafin ahankali yatako yazo dab da ita yana kallon fuskanta kasa jure kallon dayake mata tayi ta dauke kai ta matsa gefe zata wuce tafita da sauri yatare ta ta kusan fadawa kirkin shi hakan yasa takoma baya da sauri zuciyata na boiling takasa daga ido ta kallai sabida kwalla daya taru a idanunta, cikin wani murya chan kasa mai kama dana lallashi yakira sunanta. “Aneesa” hannu tasa da sauri kanta akasa ta share hawayen dasuka dan zuvo dan bataso yaga hawayenta taki dagokai. Ahankali yace “I love you so much Fateema, you are the only one in my heart, ke kadai zuciyata ke tsananin kauna daga ranan da idanuna suka ganki, I love everything about you, am sorry the way I treated you back then, please kibani dama na nunamiki irin son danake miki, zaki aureni Aneesa?” batare data kalleshi ba tace “Allah kyauta na aureka” lumshe ido yayi dan ya tsani kalman, Murya chan kasa yace “kina sona?” cikeda tsiwa tace “banson ka, mezanyi da masifaffe” ita kanta batasan mesa takemai tsiwa hakaba kuma bahalinta bane kawai tsiwan zuwan mata yake, dan murmushi yayi tareda cizan bottom lips dinshi yana kallonta yace “to mesa kike kishina?” da sauri tadago idanunta dahar sundan chanza kala ta kallai tace “me ruwana dakai dazanyi kishinka? Allah kyauta” murmushi yayi tareda dan juyamata gira yace “okay tunda bakisona bari inkoma wajen maisona nama barta ita kadai nabiyoki” wani irin kashine ya tokare mata makogoro batason ta furta kalaman dasuka cikamata baki amma saida suka fito. “kamafi ruwa guda, su baby kakide, ba baby ba bobo rubbish” ta finciki plate din datadan zuba rice aciki kafin ya fizge kulan tazo zata wuce kaman zata fashe, fashewa yay da dariya ya kama hijabinta da sauri tajuyo ta kallai idanunta sun cika da hawaye sosai tace “ka sakenmin hijabi kona cire maka hijabin na barmaka” dan ware manyan idanunshi yayi cikeda tsokana yace “zaki iya bari naganki da dan singlet din dake jikin ki?” da sauri ta kalli jikinta tayaya yagane singlet tasaka ajiye plate din abincin tai da sauri ta maida hannayenta tacikin hijabin tana turo hijabin gaba dan ya kwanta mata ajiki dayake hijabin robaroba ne karyaga jikinta ta ballamai harara zuciyanta na tafarfasa tace “kawuce kabarmana kitchen dinmu kona hadaka da Ammi na” ta kawad dakai tana kunkuni tace “wanan katoton ne wai baby” murmushi yayi sosai yace “inba ga tsoroba kifada da karfi naji” ko kallonshi batayiba, daukan kulan abincin ta yayi cikeda tsokana yace “bari na kaima babyna abincin nan” da sauri tadago kanta ta kalli kulan daya dauka yana rufe marfin da kyau hawaye ne suka cika idanunta gam tare kofan tayi tareda mikomai hannunta tabude baki zatai magana saiga hawaye sharr sun zubo da sauri tasa hannu tashare hawayen tace “wlh bazaka kaima wata abinci naba, Ammi ta dafa ta ajiyemin, babu wacce zata cim…..mi….” takasa magana sabida yanda bakinta ke rawa saiga wasu zafafan hawayen sharrr da sauri ta daura hannunta akan fuskanta tarufe fuskanta tana kuka mara kara bataso yagani hawaye nabin hannayenta, wani irin rawa zuciyan Aliyu yafara jiyake kaman yakamata ya rungume ta and assure her cewa ita kadai yakeso ita kadai ne azuciyanshi, ahankali ya ijiye kulan akan fridge ya tsugunna ahankali tareda kai guiwanshi kasa yana kallon fuskanta yanda har lokacin take kuka sabida yanda kafadarta ke rawa, hannayenshi yakai ahankali ya daura akan guiwowinta hakan yasa ta janye hannunta daga kan fuskarta daya gama wankewa da hawaye idanunta harsunyi ja sundan kankamce ta kallai, girgiza mata kai yayi ahankali, Murya chan kasa yace “am sorry for making you cry I was only trying to show you that kinaso na just dat you hate some part of me, and I promise to change for you, bazan kara miki fadaba, I will take care of you, I love you so much, let’s build foundation of love da babu wata ko wani dazai iya gizgixata, let’s build SOYAYYAN da ATSAKANIN TA babu wata SOYAYYA data isa ta shigo, Ina miki tsan-tsan so, son aure, I want you to bear my children, I love you Fateema, I love you you Anebaby, stop crying I belong to you ke kadai, wipe your tears kona goge miki?” makemai kafada tayi tareda sa hannu ta goge fuskan nata tass tana kallonshi ita kanta batasan ya akayi take sonshi ba, bama tasan lokacin data fara sonshi ba kawai taga tana sonshi dama haka so yake, murmushi yayi yanaji kaman yay kissing nata yace “bazaki ce na tashi ba Baby” dan murmushi tayi akunyace tareda rausaya kanta tace “ka tashi” tashi yayi ahankali tareda daukan plate dinta yadau kulan yazuba mata abinci sai kallonshi tabaya take, spoon yadauka yasa mata akan abincin ya mikamata yana kallon fuskanta ahankali tasa hannu ta karba batare daya sakin mata plate din gabaki dayaba yace “bakice min kinaso na ba” akunyace ta fizge plate din tajuyamai baya tareda sa hannu zata bude kofan ahankali tace “ni banson lazy man, I want My Aliyu to be the strongest man alive on earth, unbeatable, champion, kai karfi kaman wanda muke gani a TV suna wrestling da masu zuwa gym, ni banson lazy I want to see the strong you” tadan juyo tamai wani irin kallo dayasa numfashin shi yakusa tsayawa tace “until then amsan dakake so kaji bazakaji ba” tabude kitchen din da gudu tafita yabita da kallo yana murmushi kafin yadan shashafa gemushi yace “fair enough, I can do anything just to win your heart Anebaby”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57Next page

Leave a Reply

Back to top button