A TSAKANKANIN SOYAYYA HAUSA NOVEL

duk wacce takaranta batare data biyaba Allah ya isa
[4/5, 8:09 AM] Hijabi_muslimah????: A TSAKANKANIN SOYAYYA
_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤
_✍????M Shakur_
3️⃣8️⃣
Bude door din flat dinshi Dady yayi ya shiga Aliyu yabiyo shi abaya hannunshi ma duk zafi yakemai yadai daure baiso yanunama Dady, maida kofar dakin Aliyu yayi yarufe ya shigo ciki, cikin fushi Dady ya juyo ya kallai yana karasowa cikeda fada yace “sabida babu kyau yima babba fada agaban kaninshi ne that’s d reason why bance komiba, why will you be beating Hajara like that kana so kajimata cewo ne eh? Wat if kamata illa? Aliyu kadinga controlling wanan zuciyan fa, wats up with wanan zuciyan dakake yi this days abu kadan ka harzuka eh?” daure fuska yayi tamau yakaraso yafada kan kujera ya kwanta batare dayace komiba dan yasan yay magana fada zasuyi da Dady sosai this night, cikin fushi Dady yace “ba dakai nake magana ba Aliyu? Badakai nake magana ba ka shareni haka?” kaman zaiyi kuka cikin kunan rai Aliyu yace “Daddd leave me aloneeee” baki Dady yasaki yana kallonshi, cikeda jin haushi yet bakuma jin haushin shi yakeba but yabatamai rai, cikeda fushi Dady yace “nikake cema nabarka alone Aliyu? Zan sassaba makafa, babu kyau dukan mata duk abinda su Maman yaran sukemin kataba ganin I raise my hand on them? they don’t hit woman Son ba’a dukan mace” cikin fushi sosai Aliyu yace “leave me alone Dad, Allah kadamen I will leave this house for you and your wives, kun isheni, am tired, am tired Daddd, kowa hates me, what have I done haaa? Hajar doesn’t respect me, my own siblings don’t respect me, what have you done about it Dad? Kataba kiransu kamusu fada? Kullum they keep pretending niba wansu bane, pretending we aren’t bloodties, we are not blood related, idan Rauda tazo wajena adake ta, amata this amata dat mekake cewa akai? You think am not hurt because I keep mute bana magana? Banda wata kanwa dat I can go out with and say this is my sister she’s my sister, kannin nawama basu sona, common small Amal (auta) idan taganni she will be running Mama tace kartamin magana intamin magana Mama will beat her, koda yaushe am alone, am alone, am alone, am soo lonely, so soo lonely Dad, you think abin baimin ciwone? you think banson kannina ne ko bandamu da yanda suke behaving am dead to them
basu sanni ba? Dad my 19 sisters, all of them like all of them, I love them with all my heart because they came from you, dsame blood ke running in my vein shike running in their veins, sabida nahukunta Hajar which bantaba yiba shine zakazo kana questioning nawa are you also trying to show me I don’t have any right over them ba kannina bane Dad? Are you telling me nafita daga harkan su kaima? Banda kanni ko Dad, banda iko a kansu ko Dad?” tashi yayi da sauri zaiyi ciki Dady yarikemai hannu zuciyar shi tai rauni sosai, maganganun Aliyu sun sosamai zuciya, sun tabashi bana wasaba kaman yabuga uban ihu yayta kuka yakeji, ahankali yace “Aliyu na, wait Gadanga na ina zaka?” fizge hannunshi Aliyu yayi da karfi yay bedroom dinshi kafin Dady ma ya iso yamaida kofan yarufe yasaka key yafada gado yaja pillow yana kara matse idanunshi yana kokarin hana kanshi kwallan dake shirin zubomai.
Wani irin sanyi jikin Dady yayi jin maganganun Aliyu, ahankali yadaura hanunshi kan kofan yay knocking murya chan kasa yace “open the door My Boy” shiru yayi baima da karfi sabida yanda yay hurting Aliyu, ahankali yace “you’ve made me realise that you are not more yaron nan dan shekara goma danake dauka up and down muna yawo, you’ve made me realise that you are now a man, namiji dazai iya rike iyali, mai hankali da sanin yakamata” shiru yayi zuciyar shi nawani iron swelling with emotions ahankali yace “am sorry Gadangana, Dady is sorry for hurting his boy, Daddy have made a mistake, his boy misunderstood Dady, am sorry Aliyun Daddy shi, open the door okay we have alot to discuss” shiru yayi kalaman Aliyu nakara dawomai zuciya runste ido yayi saiyau ya yarda cewa yay sake ya tsaya yabude ido yana kallon matayenshi najuyamai kan yara, shine uban yayan shi shine zai hada kan yayan shi idan matayenshi basa son danshi wanan is understandable not yaranshi basa son Aliyu, yau idan yafada yamutu ubanwa ye zai tsaya musu amatsayin uba? Ubanwa zai aurar dasu naba dasu aure? What was he doing all this while yana kallo matayenshi nakoyar da yayan shi cewa Aliyu is nobody he is not their brother enough is enough! Knocking kofar Dady yayi yace “Aliyu na open the door” jin ana tada sallan isha yasa Dady yace “at least kabude kofa kazo mutafi masallaci kaji” jin shiru yasa zuciyan Dady yay rauni sosai yasan Aliyu da taurin kai yasanshi farin sani, yasan yanda ranan nashi yabaci yau kome zaifadamai bazai bude kofan nanba, juyawa yay ahankali yawuce yafita masallaci yatafi, isha’i yayi yay shafa’i da wuturi sanan yadawo gidan shashin Aliyun yakoma yay yay yay dashi yafito bai fitoba hakan yasa yafito yarufo ai kofan shashin nasu yawuce flat din su Ammi.
Ahankali yabude kofan flat din wani hadadden kamshin turare ne yamai sallama, Aneesa ce kadai a falon tana sanye da dogon riga tana rubuce rubuce da alamu assignment takeyi, sallama Dady yayi ahankali da sauri Aneesa tadago kai ganin Dady yasa tasaki murmushi tace “sannu da zuwa Abba” gyadamata kai Dady yayi yasami wuri kan kujera ya zauna tareda fuzar da iska yana shafa gaban goshin shi kaman wanda kefama da ciwon kai, ganin yanda Dady yayi yasa ahankali Aneesa tace “Dady bakada lafiya ne?” janye hannunshi yayi daga goshin ya kalli Aneesan murmushi yadan kakalo mata tareda girgiza mata kai yace “No am fine, ina maman ki?” ahankali tana nazarin Dady tace “tana sama a dakinta” gyadamata kai yayi tareda dan lumshe ido yace “okay jeki kiramini ita” gyadamai kai tayi tamike tsaye tai sama dakin Ammi ta shiga Ammi datai wanka tana cikin fesa turare Aneesa tai sallama ta shigo hakan yasa ta kalleta, shigowa Aneesa tayi dakin tace “Ammi Abba na nakiranki kaman baida lafiya” da sauri Ammi ta ijiye turaren datake fesawa ta kalli Aneesan tace “kaman baida lafiya” gyadamata kai Aneesa tayi da sauri Ammi tai hanyar kofa tanunama Aneesa yan kayan da taciro daga sip tace “kimaidamin kayayyakin nan cikin sip” gyadama Ammin kai tayi tace “to” Ammi tajuya tafita da sauri, tundaga kan stairs Dady ke hango hasken fuskan Ammi dake mugun sanyayamai tana kallonshi tana zuwa da dan saurinta, ajiyan zuciya ya sauke ganinta ahankali takaraso ta zauna kusada shi hanunshi daya sanya yadafe kan goshin shi ta karbe tare da shafa goshin wani irin sanyi yaji, ahankali tace “meyasami farin cikina abin alfaharina, wats d matter meke damun mini mijina?” Ammi tai maganan tana tattaba tundaga kan goshin shi har zuwa wuyan shi, hannunta Dady yarike ahankali tareda sauke ajiyan zuciya murya chan kasa yace “is your Son, Aliyu ne” chak Aneesa da fitowan ta kenan daga dakin Ammi bayan tagama gyarama Ammi sip din ta tsaya sabida yanda kalman Aliyu ne yadaki har zuciyan shi.
“meya sami dana Alhaji baida lafiya ne?” Ammi tafada cikeda damuwa sabida yanda taga Dady yayi, hannun Ammi Dady ya matse gam murya chan kasa yace “fushi yake dani, ya kulle kofa yaki budemin, am so angry at my self Ummu Aliyu banda Aliyu adalci ba he made me realise that today, banma Aliyu adalci ba” Dady yafada araunane cupping face