A TSAKANKANIN SOYAYYA HAUSA NOVEL

A TSAKANKANIN SOYAYYA HAUSA NOVEL

Kaman amafarki taji muryan Ammi na kiranta. “Aneesa, Aneesa wai bazaki tashi daga baccin nan ba” firgigit ta farka ganin yanda gari yay haske sosai har rana tafito ysa tazabura tamike tsaye, buga kofan dataji anayi yasa yakalli kofan tai wajen kofan da sauri tabude Ammi ce ta shigo tana sanye dawani black hadadden bakin riga taci gayu tabi Aneesa dake murza idanu da kallo tace “dan iskanci sai yanzu kike tashi iyye?” kaman zatai kuka ta janye hannunta daga ido tace “Ammi nagaji jiyane saisa bantashi da wuriba” “common wuce kije ki dauro alwala kizo kiyi salla kifito kisamen a kitchen” gyadama Ammi kai tayi tajuya tai bayi Ammi kuma tawuce kasa.

Salla tayi tazura doguwan riga na atampa tafito a kitchen tasami Ammi tana girki, ahankali ta shigo tace “Ammi ina kwana” hararanta Ammi tayi tace “wuce kidau tsintsiya ki sharo ko ina har baranda, ki tattara takalmomin nan dasuka hargitse gefe daya” gyadama Ammi kai tayi tadau tsintsiya tafita tafara gyara falon tsaf har dining sanan ta shiga shara har zuwa bakin kofa takai sharan sanan ta kwashe ta kunna turaren burner dinsu dtazuba turare dakin yadauki kamshi sanan tadau tsintsiyan tabude kofa ahankali dan gyara varandan su kaman yanda Ammi ta gaya mata, idanunta ne suka sauka akan wata babban mota irin ta company mai suna Fitness Equip ana sassauke wasu manyan machines dabata san na meye ba agaban flat din Aliyu, hango mazan datayi yasa takoma daki hijabi tadauko tasaka sanan tadawo wajen idanunta ne suka sauka akan na Aliyu data ganshi tsaye kusada wani mutumi yana sanye dawani Beach 3quter dawani logo brown shirt ajikinshi magana yake amma yana hango ta yay shiru ya tsaya yana kallonta har saida mutumin da kemai magana ya juyo dan yaga meyagani me yake kallo dayasa yay shiru baya magana, dauke kai da sauri Aneesan tayi taduka tafara shara, kwala mata Aneesa taji anyi da sauri ta dago daga sharan datake, Abba ne tagani yana sanye da farar jallabiya da hula as usual shiga shi ta asuba ya tattaro yaran gidan gabaki daya harda Hajar dahar lokacin fuskanta yake a suntume, da hannu yamata alamu yace “zonan Aneesa” ajiye tsintsiyan tayi ahankali tafito ta karaso wajen tana kallon fuskan Dady ahankali tace “ina kwana Dady” murmushi Dady yamata yace “kin tashi lpy, kumuje ku gaida yayanku” Dady yay gaba duk suka dunguma suka bishi abaya hannunta Rauda takama tace “Aneesa how are you” batasamu ta amsa ba sabida kaiwa inda Aliyun yake tsaye da mutumin dasukayi Abba yajuya ya kalli Hajar ya mugun daure fuska yace “zoki gaida Yayanki” dayake duk iskancin ta tana tsoron Dady yasa tataho ahankali kanta akasa Aliyu ya zubamata ido yana kallonta, ahankali tace “ina kwana Ya Aliyu” ba yabo ba fallasa yace “fine, how was your night?” ahankali tace “Alhamdulillah, uhmm Ya Aliyu am sorry about yesterday” murmushi Dady yayi jin taji warning din dayamata, gyadamata kai Aliyu yayi yace “never mind” ahankali tace “thank you” dan murmushi ne ya subuce ma Aneesa sosai abin yamata dadi, da hannu Dady yace “oya Aneesa you and Rauda kuzo ku gaida yayanku” Rauda dai da gudu tafada jikin Ya Aliyu yau wace rana tazo taganshi freely, makalkaleshi tayi tace “Ya Aliyu gud morning” “ke cewa nayi ki karyashi” Dady yafada yana hararanta, ahankali Aliyu ya kalli Aneesan hada ido sukayi sanan ya kalli Rauda yace “ya ciwon cikin?” kaman zatai kuka tace “yadena” gyadamata kai yayi ya kalli Aneesan ahankali ta saukar da kanta kasa tace “ina kwana Ya Aliyu” batare daya kalleta ba dan yasan idanun Dady na kanshi yace “how was your night?” batare data kalleshi ba tace “Alhamdulillah” dan juyowa yayi ya kalleta yanda hijabinta yadan zame baya ana ganin gaban gashinta ga gashin goshinta ya kwanta sosai, kasa daurewa yayi ahankali ya tsugunna yadau Amal dake ta kallonshi yana mata wasa sanan yadan kalli Aneesan hada ido sukayi da hannu yamata alamu yace “ja hijab dinki gaba” da sauri Dady ya kalleta yace “yayanki yace kija hijab dinki gaba suman ki awaje Aneesa” jan hijabin tayi gaba shikuma Aliyu ya tsugunna yana wasa da yan kanenshi yaran sai washe mai baki suke Dady na murmushi ganin yanda yake murna Hajar kam kaman ta chakamai wuka takeji, kallonsu Dady yayi yace “to kuwuce aje a shirya school” ahankali Aliyu ya shashafa kan yaran yace “bye girls” yaja kunen Rauda yace “bye” washemai baki tayi tace “bye Ya Aliyu na” tajuya tabi bayan Aneesa sukai gaba, kallonshi Dady yayi yace “Gadanga na, sport zaka farane wanan kayan gym din daka sayo fa” daure fuska yayi yace “I don’t wanna talk to you Dad” murmushi Dady yayi cikin kwaikwayan yanda yamai magana yace “haba Gadanga na har yanzu ba’a dena fushin da Dady ba, Dady fa yace a yakuri iyye, adan kalleni mana ko sau daya nai kewan yarona fa” murmushi ke cinshi amma ya danne yay kini kini darai shi adole fushi yake da Dady, murmushi Dady yayi cikeda son dan nashi yace “Baba Aliyu mangyada baya bacci, ranan haihuwan shi ba wahala ko daya, yafado turus kaman namijin tarwada, tashi ingank….” fashewa da dariya Aliyun yayi tun kafin Dady yakarsa wakan his Dady is just the best, ahankali yay hugging Dady murya chan kasa yace “I love you old man” murmushi Dady yayi yadan tallabe keyanshi yace “I love you too yarona, my one and only Son, rigimammen yaro kawai” murmushi Aliyun yayi yadago sai a lokacin ma yatuna aikin da akemai kallon Dady yayi yace “stop calling me rigimamme in front of people Dad” dariya
Dady yayi yajuya yana kallonsu yace “aikin me sukema haka?” dan yatsine fuska yayi yace “I want to create a gym ne, wanna start working out” haba Dady yakama cikeda mugun mamaki yace “working out, Aliyuuuu! Kaina zakai work out” murmushi yayi yace “yes, meet my instructor ma” yanunama Dady mutumin da suke magana dashi dazu, gaisawa Dady yay da mutumin Dady yakasa dena mamaki wai Aliyu ne zai fara exercise harda su gym instructor gareshi lallai, ikon Allah zaiga yanda hakan zaiyu yaron dabai jure wahala.

duk wanda yakaranta bai biyaba, Allah ya isa, chat me up in kinason book Dinnan 07012181461
[4/5, 8:09 AM] Hijabi_muslimah????: A TSAKANKANIN SOYAYYA

         _IN BETWEEN THE LOVE_
        ❤ _Lies another love_❤




        _✍????M Shakur_



                    4️⃣1️⃣

Kallon Aliyun Dady yayi yana kokarin yagano wani abu dan shidai yasan inba wahayi akama Aliyu kowani abuba babu abinda zaisa yaron nan yatashi rana tsaka shi exercise zai fara, gyadamai kai yayi kawai dan he’s not convinced yace “to shikenan kayi sauri kagama sai kazo kai breakfast abangaren Mummy ka, kobaka ma gamaba kazo kayi breakfast dan nafiso mudinga breakfast atare” gyadamai kai Aliyun yayi yana lashe lips da sauri Aneesa data tsaya tana kallonsu sabida yanda suka bala’in burgeta ta duka tafara sharan, Dady nason Aliyu so ko dabata taba ganin irinshi ba, shima Aliyun nason Dadyn shi, kuma wani irin soyayya sukeyi irin na yan gayu, irin soyayyan uba da d’a na kasashen waje dasuke gani a TV, ganin Dady yataho yasa ta tsayar da sharan, murmushi yamata ya shafa kanta yace “sannu da aiki yar albarka, my brave girl mara kuwuya” dan dariya tayi Dady ya iya wasa da yara, kofa Dady yabude ya shiga ciki itakuma ta cigaba da sharan tanadan satan kallon Aliyu, inda dane da tuni ta gama sharan dan barandan dabaida wani girma, dayake da abinda take kallo shiyasa bata gama ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57Next page

Leave a Reply

Back to top button